
Muhimmin Bayani Kan Cike Shirin Tallafin Kuɗi na TVET na Gwamnatin Tarayya (Horon Fasaha da Sana'o'i na Ilimin Tarayya)
Muhimmin Bayani Kan Cike Shirin Tallafin Kuɗi na TVET na Gwamnatin Tarayya (Horon Fasaha da Sana'o'i na Ilimin Tarayya)
Lokacin da ka ke zaɓar tsarin horo a cikin shirin TVET na Gwamnatin Tarayya (Federal Education Vocation Training), a lokacin aikace-aikacen, ya kamata ka sani cewa idan mai neman shiga shirin ya zaɓi Tsarin Takardar Shaida Na Gaggawa (Short-Term Certificate Programme) na watanni 6, ba ya buƙatar loda ko wace irin hujja ta ilimi a cikin bayanan sa.
Yayin da kuma, idan masu sha'awar neman Tsarin Horon Sana'a da Ƙirƙire-Ƙirƙire (Vocational Education & Innovation Programme) na Shekara 1, wajibi ne a gare su su loda kwafin takardun shaidar su mafi girma ko takardun duk wani horon da suka halarta a baya wanda ya yi kama da shirin da suke neman shiga.
Don haka, idan ka zaɓi tsarin watanni 6, ba ka buƙatar gabatar da takardar shaida ko wace iri, amma idan ka zaɓi na shekara 1, dole ne ka gabatar da su. Ta haka ne zai ba ka damar cin gajiyar shirin. Allah ya sa a dace.
Mai tambaya ya yi a sashin sharhi (comment). Insha'Allah zan ba da amsa daidai gwargwadon sani na.
Allah ba mu sa'a da rabo mai amfani.
Yauwa nace ya za.ayi musan anfara shirin
ReplyDelete