1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya
1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya
Dafatan kintashi lafiya, jiya ina cikin damuwa, amma ganin ki ya kawar mun da duk damuwar dake zuciya ta. Ya rayuwa ta zata kasance ba tare da ke ba? Gaskiya nayi sa’ar samun ki a rayuwa ta.
Da zaki iya ganin irin halittar da ubangiji yayi maki, da kin gane cewa ke ta daban ce a cikin yammata hadaddu. Kyawun ki ba irin tasu ba ce.
Na fada maki wani abu da baki sani ba? Kina da maganin dake magance wata cuta da nake fama da ita. Murmushin ki ita ce maganin kuma wannan cutar ita ce damuwa. Duk inna shiga damuwa, murmushin ki kawai nasa na manta da damuwa dana ke ciki.
Gabanin sanin ki, bansan mene ake nufi da “mace mai kyau ba” amma fa ranar da na fara ganin ki a duniya na tabbatar da abunda ake nufi da kalmar kyau ga mace.
Wasu lokutan, nakan yi tinanin rayuwa ta babu ke aciki, babu komai a cikin ta face damuwa da bakin ciki. Ina matukar son ki.
Yana iya kasancewa ni ba irin saurayin da kike so bane, amma ina tabbatar maki da cewa zan iya bada rayuwa ta dan farin cikin ki matukar hakan zai sa kisan matsayin ki a zuciya ta.
Muna fada a tsakanin mu, muna samun saba ni, amma hakan bai taba rage son da nake maki a zuciya ta ba. In aka tambaye ni wannan wani irin soyayya ce, nace nayi mata lakabi da zanen kaddara.
A lokacin da mutane suke ganin raunin ki, ni babu abinda nake gani face mace mai cike da nasara.
Nasan wasu lokutan zaki rinka yin tinani soboda yawan kiran ki danake da sassafe da kuma cikin dare, bakomai yasa nake hakan ba sai dan inaso muryar ki tazamo na farko da zanji duk safiya inna tashi daga bacci kuma tazamo na karshe kafin na kwanta.
Muryar ki kawai na dauke da sinadarin sanya farin ciki da nishadi a zuciyar kowani dan adam. Shiyasa nake kara godewa ubangiji da ya hadani dake a wannan duniyar da muke ciki.
Wasu suka ce kina da girman kai, wasu kuma jan aji, amma na dauke hakan karya dan kuwa ni nasan baki da girman kai, tsare girman ki ne kawai dan haka ki cigaba.
Na fada maki wani abu guda daya? Ki zama mai yawan murmushi a koda yaushe, domin murmushin ki na da matukar kayatarwa.
Farin ciki, annashuwa da kuma nishadin da nake fuskan ta a kullin, ba dan komai bane sai dan nayi nasarar samun ki a zuciya ta. Kaunar ki ta maimaye zuciya ta.
Daga ran da na fara ganin ki nasan cewa ke tawace ni ka dai. Sai dai kuma bakizo lokacin da nake tsammani ba.
Wasu lokutan ji nake kamar ina mafarki dan duk wani damuwa da nake ciki, kina dauke da maganin ta.
Samun budurwa irin kina da matukar wuya, duk halin da saurayi zai nema a wurin ya’ mace duk nagan su a tare dake. Nayi sa’a matuka.
Sarauniyar rayuwa ta, dafatan kina lafiya? Tin da muka hadu nake ta farin ciki, farin cikin ya kasa boyewa a fuska ta, ji nake kamar anyi mun kyautar aljannah tun a duniya.
Wasu mutanen sunce soyayya tana da dadi ne a farkon haduwa, amma kullin gani nake kamar duk ranar duniya soyayyar ki a gare ni karuwa take.
Bana waka ko kadan, amma zanje na koya dan na rinka rera maki wakokin soyayya masu dadi da sa farin ciki.
A duk sanda na wayi gari ban gan ki ba ko banji muryar ki ba, wannan ranar cikin bakin ciki nake kasancewa. Ina so ki ringa kasacewa a kusa dani a koda yaushe dan zuciya ta ta samu sauki.
Duk in aka tambaye ni me nakeso a rayuwa, amsar da nake basu itace kasancewa tare dake har tsawon rayuwa ta. Nagode sosai masoyiya ta dan kin kara wa rayuwa ta ma’ana.
Nazamo mai muradin kasancewar ki a rayuwa ta, dan tarayya dake yasa abubuwan alkhairi kawai nake fuskan ta aduk lamarina. Inaso wannan alkhairin da nake gani su cigaba da kasancewa a tare dani.
Aduk sanda nake cikin wani hali da nake bukatar agaji, Allah ya turo sarauniya cike da soyayya ta agaza mun, gaskiya sarauniya irinki nada wahalan samu.
Masoyiya ta, nazama saurayi wanda yasamu babban rabo a duniya dan samun budurwa kamar ki a rayuwa ta. Duk wata rana na rayuwa ta na zuwa da abubuwa na ban mamaki kuma kece silar faruwar hakan.
Duk in akace na misalta irin soyayyar danake maki, kalamai, kwatance, da kuma bayanai basu iya tabbatar da asalin yadda nakeson ki kuma nasan kinsan da hakan.
Baby na, duk wani wahala da damuwa da nake ciki, mantawa nake da ita duk sanda na hadu da ke ko kuma naji muryar ki.
Masoyiya ta, gara na zauna a cikin zuciyar ki da na kasance a cikin tinanin ki dan zaki iya manta abun da kike tinani cikin sauki, amma kuma duk abunda ke cikin zuciya ya samu wurin zama.
Inason ki kuma banson na rabu da ke dan kuwa rayuwa babu ke a cikin ta cike take da bakin ciki da damuwa. Kizama tawa nikadai kinji?
Masoyiya ta, inaso ne kawai na tina maki cewa arayuwa ta kece a farko kuma kece a karshe. Kinzamo mai sani cikin nishadi da farin ciki.
Duk lokacin da idanuna suka kalli fuskar ki, sai naji kamar nazama sarki, in kuma naji muryar ki, sai naji kamar rayuwa ta bani kyautar da banta samun irin ta ba, sawun tafiyar ki kuma abun koyo ne ga wasu yammata.
Yammata adan gari, abokan rayuwa, masu zuwa da abubuwan alkhairi, masu dauke da sinadarin dake magance damuwa da farin ciki, na shaida kuma na gas gata hakan dan na samu farin ciki mai yawa.
Kamar yadda dubbanin taurari ke haskaka samaniya, haka murmushin ki ke haskaka rayuwa ta.
Babbar kwarin gwiwa da na samu a rayuwa ita ce karfafa wa dana samu daga wurin ki. Babu ta inda zan iya biyan ki daya fi na so ki fiye da yadda kika taba jin so a zuciyar ki. Ina godiya sosai.
Kullin tinanin ki cike yake a cikin zuciya ta kuma inason hakan, dan damuwa bai iya zuwa inda nake ba ta dalilin samun ki a rayuwa ta.
Masoyiya ta, babbar abun farin ciki a rayuwa ta itace natashi da safe tare da tinanin ke tawa ce ni kadai. Hakan ma kawai ya ishe ni farin ciki a rayuwa ta. Ina sonki bil haqqi.
Da zaki san irin farin cikin da nake shiga soboda soyayyyar ki, da kin kara godewa ubangiji soboda wannan babbar kyauta da yayi miki.
Wasu su kirani mara hankali, wasu suce bansan me nakeyi ba, amma kuma hakan bai dameni ba, dan kyautata maki itace babbar muradi na.
Duk sanda muke tare, jina ke kamar ranar muka fara haduwa, soyayyar da nake maki kara mamaye zuciya ta take fiye da yadda nake tinani.
Ganin da yafi kowani gani a rayuwa ta itace kallon cikin idanun ki naga irin kaunar da kike mun. ke din ta musamman ce a cikin mata.
Samun ki a rayuwa ta tasamo ma rayuwa ta mafita wuce yadda nake tinani, duk abunda na gwada yi a baya da bai samu karbuwa ba, ta dalilin shawarar ki nasami hakan cikin sauki ba tare da nasha wuya ba.
Inda ace zan iya bude maki zuciya ta kiga irin soyayyar dake cike a cikin ta, da kingane cewa duk abunda nafada maki gaskiya ce.
Zuwar ki rayuwa ta tasa na fahimce me ake nufi da so na gaskiya, kaddara, da kuma nasara, domin ke dukkan su ce gare ni ya yar budurwa ta.
So dayawa na kan yi tinanin sunan da zan kira ki da ita, amma kuma sai na kasa samun amsa, dan kuwa duk sunan da zan iya tinani akai ba dace da a kira ki da it aba.
0 Response to "1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Zuciya"
Post a Comment