-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sanarwa mai muhimmanci – Daukar ma’aikata a hukumomin tsaro

Sanarwa mai muhimmanci – Daukar ma’aikata a hukumomin tsaro

SANARWA MAI MUHIMMANCI – DAUKAR MA’AIKATA A HUKUMOMIN TSARO

Za a fara daukar ma’aikata a wasu hukumomin tsaro kamar haka: Hukumar Gyaran Hali (Correctional Service), Hukumar Shige da Fice (Immigration Service), Hukumar Kare Fararen Hula (NSCDC), da Hukumar Kashe Gobara (Federal Fire Service).

Ana sa ran buɗe dandalin yin rijista nan ba da jimawa ba, don haka ya kamata kowa ya fara shiri domin shirye-shiryen jarabawa.

Gwamnatin Tarayya ta amince da fara daukar sabbin ma’aikata ta hanyar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) domin cike guraben aiki a cikin waɗannan hukumomi guda huɗu da ke ƙarƙashinta.

Ga yawan mutanen da za a dauka a kowace hukuma:

  • Hukumar Gyaran Hali (Correctional Service) – mutum 5,150
  • Hukumar Shige da Fice (Nigeria Immigration Service) – mutum 10,000
  • Hukumar Kashe Gobara (Federal Fire Service) – mutum 5,000
  • Hukumar Kare Fararen Hula (Civil Defence) – mutum 10,000
  • CDCFIB – mutum 209

Za a buɗe dandalin yin rijista na musamman (portal) domin duk wani ɗan Najeriya mai cancanta ya nema. Rijistar za ta kasance na tsawon makonni uku kacal (3 Weeks).


Allah yasa mu dace baki daya 

0 Response to "Sanarwa mai muhimmanci – Daukar ma’aikata a hukumomin tsaro"

Post a Comment