-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

MUHIMMIYAR SANARWA: Kar Ku Sake A Ba Ku Labari! Tallafin 'Renewed Hope Ward Development Project' Ya Kankama

MUHIMMIYAR SANARWA: Kar Ku Sake A Ba Ku Labari! Tallafin 'Renewed Hope Ward Development Project' Ya Kankama

MUHIMMIYAR SANARWA: Kar Ku Sake A Ba Ku Labari! Tallafin 'Renewed Hope Ward Development Project' Ya Kankama

Jama’a barkanmu da wannan lokaci. Akwai wani tallafin kudi da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi domin al'ummar Nijeriya mai suna RENEWED HOPE WARD DEVELOPMENT PROJECT.

Ga abubuwan da ya kamata ku sani:

  1. Babu Link: Wannan tallafin ba a cika shi a yanar gizo.

  2. Yadda Ake Cikewa: An raba jami'ai a dukkan kananan hukumomi 774 na Nijeriya. Su ne ke raba fom (form), ku cike su kuma ku mayar musu domin su shigar da bayanan a kwamfuta.

  3. Kyauta Ne: Kar ku biya kowa kudi; ana yin wannan rajista ne kyauta.

  4. Wuraren Da Ake Yi: Ana gudanar da aikin ne yanzu haka mazaba-mazaba (ward-by-ward).

Ko da yake muna ganin ya kamata a ce an ba mutane damar cike wa kansu ta yanar gizo don sauki da gaskiya, amma tunda tsarin ya zo haka, muna shawartarku da ku tashi tsaye.

Ku hanzarta zuwa Sakatariyar Karamar Hukumarku (LGA) don neman karin bayani da karbar fom dinku. Kada ku bari wannan damar ta wuce ku!

Allah ya taimaka. 

0 Response to "MUHIMMIYAR SANARWA: Kar Ku Sake A Ba Ku Labari! Tallafin 'Renewed Hope Ward Development Project' Ya Kankama"

Post a Comment