-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

An Bude Daukar Ma’aikata a Gidauniyar New Incentives – Dama Ga Masu SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, MSc da Ph.D

An Bude Daukar Ma’aikata a Gidauniyar New Incentives – Dama Ga Masu SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, MSc da Ph.D

Ana sanar da daukacin masu Kwalin Sakandare (SSCE), Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc da Ph.D cewa an bude shafin daukar ma’aikata a Gidauniyar New Incentives

New Incentives gidauniya ce da ke tallafawa iyalai masu karamin karfi domin ceton rayuwar jarirai ta hanyar karfafa musu gwiwar yin rigakafi. Shirin yana aiki ne musamman a yankin Arewacin Najeriya, a jihohin Zamfara, Jigawa, Katsina, Sokoto, Bauchi, Gombe, Kano, Kaduna da Kebbi.

Ta karkashin shirin All Babies Are Equal, gidauniyar na bayar da kananan tallafin kudi ga iyaye ko masu kula da jarirai bayan sun kai ‘ya’yansu karbar muhimman rigakafi guda hudu, wato:

  • Rigakafin BCG (na tarin fuka)

  • Rigakafin Penta (na diphtheria, tetanus, tari mai tsanani, hepatitis B da Hib)

  • Rigakafin PCV (na cutar huhu)

  • Rigakafin MCV (na kyanda)

Wadannan rigakafi na cikin jadawalin rigakafin jarirai a Najeriya kuma ana bayar da su kyauta a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati. Baya ga haka, shirin na hada kai da hukumomin gwamnati domin kara yawan wadatar rigakafi da wayar da kan al’umma kan muhimmancin yin rigakafi.

Wannan babbar dama ce ga matasa da masu neman aiki domin shiga cikin shiri mai anfani ga al’umma.

Ayyukan da Aka Bude

Ga jerin guraben ayyukan da ake nema a New Incentives:

  1. Field Officers (Entry-Level) – Bauchi State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/d0d0e6ea8f4f-field-officers-entry-level-bauchi-state

  2. Field Officers (Entry-Level) – Gombe State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/b40b6daffe50-field-officers-entry-level-gombe-state

  3. Field Officers (Entry-Level) – Jigawa / Katsina / Zamfara
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/bb0007be7436-field-officers-entry-level

  4. Field Officers (Entry-Level) – Kaduna State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/0e32c25552de-field-officers-entry-level-kaduna-state

  5. Field Officers – Kano State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/83533afe0983-field-officers-kano-state

  6. Field Officers (Entry-Level) – Kebbi State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/70c858cc3eca-field-officers-entry-level-kebbi-state

  7. Field Officers (Entry-Level) – Niger State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/0221d5cbdf11-field-officers-entry-level-niger-state

  8. Field Officers (Entry-Level) – Sokoto State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/6957042fec69-field-officers-entry-level-sokoto-state

  9. Field Officers (Entry-Level) – Yobe State
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/4529bc0085d4-field-officers-entry-level-yobe-state

  10. Accountant (Remote – Worldwide)
    Domin cikewa latsa nan: https://new-incentives.breezy.hr/p/d134b50a341a-accountant

Yadda Za Ku Cike

Domin neman wadannan gurabe, ku latsa mahaɗin (link) da ke karkashin aikin da kuke sha’awa, ku cike bayananku daidai kamar yadda aka bukata.

Allah Ya ba da sa’a.

0 Response to "An Bude Daukar Ma’aikata a Gidauniyar New Incentives – Dama Ga Masu SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, MSc da Ph.D"

Post a Comment