-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

TALLAFIN KUƊI: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Shirin 'Renewed Hope Ward Development Project

TALLAFIN KUƊI: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Shirin 'Renewed Hope Ward Development Project

TALLAFIN KUƊI: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Shirin 'Renewed Hope Ward Development Project

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shirin tallafi na musamman mai suna RENEWED HOPE WARD DEVELOPMENT PROJECT. Wannan shiri ne da aka tsara domin kawo ci gaba da kuma tallafawa al'umma kai-tsaye har zuwa matakin mazabu.

Ga muhimman bayanai da ya kamata kowa ya sani:

1. Babu Link ɗin Cikewa a Yanar Gizo:
Ku sani cewa wannan shirin ba irin na sauran ba ne da ake ba mutane link su cike a wayoyinsu. An nada jami’ai (coordinators) na musamman a dukkan ƙananan hukumomi (774 Local Governments) da ke faɗin Nijeriya domin kula da aikin.

2. Tsarin Rajista:
A halin yanzu, ana gudanar da rijistar ne mazaba-mazaba (Ward by Ward). Jami’an da aka ware suna raba takardun neman tallafin (Forms), sannan bayan kun cike za su tattara su domin tura bayanan ku a na’ura mai ƙwakwalwa (Computer).

3. Kyauta Ne, Kar Ku Biya Kuɗi:
Muna jan kunnen jama’a: Wannan rijista ana yin ta ne kyauta. Kada ku yarda ku bai wa kowa ko sisi da sunan zai cike muku ko ya sa muku suna.

4. Gargadi Ga Masu Ba Wa Scammers Kuɗi:
Abin takaici ne yadda wasu suke haɗa kuɗi suna bai wa ’yan damfara (scammers). Muna jaddada cewa duk wanda ya yarda aka damfare shi saboda rashin bincike, kada ya zo mana da ƙorafi daga baya. Mu guji garaje, mu bi matakan da aka shimfiɗa.

Abin Da Za Ku Yi Yanzu:
Ku gaggauta tuntuɓar ofisoshin ƙananan hukumominku (Local Government) ko kuma jami’an da ke kula da mazabun ku domin tabbatar da an ba ku fom ɗin ku cike.

Kada ku bari wannan damar ta wuce ku. Allah ya ba da sa'a!

0 Response to "TALLAFIN KUƊI: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Shirin 'Renewed Hope Ward Development Project"

Post a Comment