Yadda Zaki Hada Kunun Gyada mai Shinkafa da Kuma Ayaba
Yadda Zaki Hada Kunun Gyada mai Shinkafa da Kuma Ayaba
Assalamu Alaikum,
A yau zan kawo maku hadin kunun gyada guda biyu, yadda zaku hada kunun gyada mai shinkafa da kuma kunun gyada mai ayaba a saukake.
Abubuwan bukata sune kamar haka
Gyada
Shankafa
Tsamiya (option)
Gasaran koko ko flour
Suga
Yadda Zaki Hada;
Da farko dai Za ki sami gyada sai ki soyata sama sama kada ki bari ta kone amma idan kinaso tayi maki kamshi. Bayan ta soyu sai ki sauke ki bazata a tray ki murjeta saboda bayan ya fita sai ki markada gyadarki, zaki iya amfani da engine ko kuma idan kinada blender mai kyau zaki iya nikawa da ita. Bayan kin nika gyadarki tayi laushi sai ki tace ki fitar da dussar da tayi, sai ki sami tukunya ki daura a wuta ki sa ruwa dan kadan ba dayawa ba. Bayan kinyi wannan sai ki wanke shinkafarki kamar rabin gwagwanin peak ki zubata acikin tukunyar da kika daura dan ta fara nuna sai ki zuba ruwan gyadan ya tafasa , daman tsamiyanki ya juku sai ki kawo kullun kunun geron ki ko flour dinki dai dai yanda idankika sa zai yi kauri, sai ki zuba a cikin ruwan gyadanki ki kabarshi ya kwaikwaya yayi kauri, sai a sauke a sa suga. Shikenan kunun gyadarki ta hadu, sai kiyi serving.
2. Kunun Gyada da Ayaba
Abubuwan bukata sune kamar haka;
Gyada
Ayaba
Gero
Sugar
madara
Yadda zaki hada;
Da farko zaki gyara gyadarki kisoyata sama sama yadda zata yi maki kamshi, sai ki wanketa kisamu manyan ayabarki ki maikyau ki markadesu. Bayan kin markadesu sun niku da kyau sai kidora akan wuta kibarta dahu idantafara fitarda kumfa sai kidauko garin nikakkiyar gyadarki cokali biyu kixuba acikin kunun gyadar ki, sai ki dauko kullun kunun ki na gero ko kuma garin flour kamar cokali uku haka kidamashi da ruwa kizuba acikin tukunyarki zakiga ya Jade jikinshi yadanyi kauri, sai kisauke. Shikenan kunun gyadarki ki ya kammala sai kiyi serving ki saka sugar idan kinaso ki hada da madara. Asha Lpy
0 Response to "Yadda Zaki Hada Kunun Gyada mai Shinkafa da Kuma Ayaba"
Post a Comment