-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Abubuwanda Yadace Kiyi Bayan Haihuwa

Abubuwanda Yadace Kiyi Bayan Haihuwa

Abubuwanda Yadace Kiyi Bayan Haihuwa

Ita dai haihuwa abace wadda Allah subhanahu wataala ke azurtawa ga ma'aurata a lokacinda yaso kuma yaga dama domin komai a hannunsa yake shine mai ikon komai. Allah ya azrtamu da samun zuria mai albarka ameen.

Abubuwan da Mace ya dace tayi bayan Haihuwa sunada yawa. Da farko dai idan mace ta haihu Allah ya sauketa lafiya ana bukatar tasamu hutu domin samun damar shayar da jinjirinta cikin aminci baaso daga haihuwa ki dinga yin ayyuka masu wahala idan da hali kisamo almajiri haka ko Yar aiki wadda zata dinga tayaki yan ayyukan gida na yau da gobe kafin ki samu sauki ki warware domin ita haihuwa ba karamin abu bace mutane kanyi kirari kan cewa haihuwa yakin mata tabbas haka dan mutum akwai wuyar cin riba idan kin haihu anaso ki dinga wanka da ruwan zafi masu zafi harna tsawon kwana arbain domin jikinki yayi kwari sosai  kuma ki dinga Zama acikin ruwan zafi domin samun lafiyar jikinki anaso kisamu bagaruwa ki tafasa ta a kullum kina Zama acikin ruwan nata dakika tafasa kuma kina mai watsa dettol acikin ruwan wankanki shi ruwan zafi yanada matukar muhimman a lokacin da Mace ta haihu domin idan bakya wanka dasu to b shakka bazakiji karfi a jikinki b abu na gaba shine anaso mace bayan ta haihu tasamu abinci mai kyau mai zafi wanda zai kara mata karfi da lafiya ta rika ci kuma anaso tasamu nama ko na rago ko na kaji kowa meye wanda ya sawwaka tanaci Yana kara lafiyarta da ta jaririnta sannan kuma zata dinga Shan kunu mai zafi ko normal kunu ko kunun sabara Amma gaskiya anfi bukatar na sabara saboda wannan sabarar itace zata kara mata ruwan nono yaro yasamu lafiya kuma ana hadawa da kunun kanwa duk Yana kara ma mamanki ruwa.

Idan tayi kwana arbain zata cigaba da gudanar da rayuwarta Kamar Yanda ta saba taci gaba da kula da abunda ta Haifa tana shayar dashi har na tsawon shekara biyu sannan bawai komai bane kika gani zakice Zaki ci b domin dole zakiyi hakurin cin wasu abubuwa musamman na kwalama domin lafiyar yaronki zakiga kinci wani abu da bai gamsu da jinki b shikenan zai bata maki ruwan nono kinga kuwa da yaronki yasha wannan maman shikenan zai taba mishi lafiyar shi more especially abu Kamar su aya, gyada, kunun aya, zobo da dai sauransu su wadannan sukan batawa yaro cikin sa idan kika Sha ko kuma su saka mishi kuraje a jiki Amma ya danganta wani baya saka shi komai idan ma yasha Amma akasari wadanda yake yiwa illa ga yayansu sunfi yawa it depends on how strong your blood is wani jininshi zai iya zurewa wani kuwa sabanin hakan.

Allah yasa mu dace

0 Response to "Abubuwanda Yadace Kiyi Bayan Haihuwa"

Post a Comment