-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE

YADDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE

YADDA ZAKI MALLAKE MIJINKI

 Dafarko dai wanene miji?

Miji  shine wanda ALLAH ya hadaku ya zama abokin rayuwarki a duniya wanda muke fatan har lahira,  yazama abokin rayuwarki sannan Kuma Allah ya sanya soyayya da tausayi a tsakaninku.kuma shike ciyar dake ya baki abinsha ya miki sutura ya baki wurin  kwana inbaki da lafiya ya nema miki magani,ya dauki dawainiyar makarantar ki data ya'yan ki.


YADDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE

1.Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga mijinki dakuma Mahaifiyar mijinki kidauki mahaifiyar mijinki tamkar mahaifiyarki karki walakantata karki cutar da ita kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.

Duk yanda kikeson mijinki in bakison mahaifiyarsa kinyi aikin banza Kuma shine matakin farko na zubarwa da kanki qima a idon mijinki da Yan uwansa .


2. Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.


3. Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.


4.kizama kwarriya wurin tsaftar jikinki da tsaftar muhallinki karki kuskura mijinki ya gano wani Abu na kazanta acikin gidanki ko a jikinki ko a abincinki 

Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.


5.Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.


6.Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki Duk abinda yazo dashi ya baki ki karba kiyi godiya Kuma kiyi masa addu a kinuna kinji dadi sosai


7.Ki saita kanki abisa gyaran kanki, kitso, lalle, wanke kai, wankin kaya, da kuma gyara jikin ki ta kowacce ɓangare, dai-dai gwargwado Yadda ALLAH yayi muku wadata, komi kiyi sa abisa dai-dai karfin ku.


8.Kada ki raina kanki a gaban shi, menene raina kai ki zamo mara tsari, mara gyara, za ki sanya masa bakin ciki a zuciyar sa duk son da yake miki, ki zamo kin kare martabar ki ta YA'MACE, ki kasance wacce yake samun nutsuwa da ita ki gyara harkar ibadar auren ki dai-dai gwargwado ta hanyar ciye ciyen abu masu amfani gare ki, soyayya, da kuma dabaru.


Idan kika fadi anan, duk ilmin ki addini ko kudi da sauran su, duk soyayyar da ke tsakanin ku, za ki rasa daraja ta YA'MACE, kuma za ki rasa farin cikin gidan ki, za ki rasa walwalar miji da wasa da dariyar sa, domin ba shi da natsuwa, zai riqa cutuwa.


9.Kada ki ba da wata kafa da za'a raina mijin ki, ko da ma kuwa wanene,  Duk yanda mijinki yake mijinkine Kuma bakida Wanda yafishi ki rike sirrin gidan auren ki, ki maishe da mijin ki aboki mafi girma.


10.Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin aikin alheri.

Daga  karshe Duk matar da takeso ta MALLAKE MIJINTA CIKIN SAUKI dole ta  kasance mace mai kyautatawa mijinta ,ta kyautatawa iyayensa, ta nuna masa tsantsan  so da kauna ta kaunaci abinda yakeso ta guji Duk abinda baya so matukar Bai sabawa shari a ba ta tarairayeshi ta tausaya masa ta kasance  dashi cikin halin farin ciki ko kunci.

Allah yasa mudace.

0 Response to "YADDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE"

Post a Comment