Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ancelotti, Mbappe, Rodriguez, McGregor da Johnson, Bayan PSG tayiwa Mbappe tayin karin albashi
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ancelotti, Mbappe, Rodriguez, McGregor da Johnson, Bayan PSG tayiwa Mbappe tayin karin albashi
Paris Saint-Germain ta shirya bai wa ɗan wasan ƙungiyar mai shekara 23 Kylian Mbappe sabon kwantiragi kan fam 799,000 a duk mako domin ya zauna, inda ita ma Real Madrid ta ce tana son sayen ɗan wasan na Faransa. (Le Parisian, via Star)
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Everton da Colombia James Rodriguez mai shekara 30, ya sa tsohon kulob ɗin nasa na Everton ya zama cikin shiri bayan ya nuna alamun yiwuwar komawarsa daga Qatar. (Express)
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti mai shekara 62, ya bayar da mamaki bayan ya shiga cikin jerin waɗanda ake sa ran za a zaɓa domin zama kocin Manchester United na gaba. (Times - subscription required)
Bayern Munich da Tottenham da Arsenal duka na son sayen ɗan wasan bayan Middlesbrough ɗan ƙasar Ingila mai shekara 21 Djed Spencer wanda a halin yanzu ya tafi aro Nottingham Forest. (Sky Sports)
Sai dai duka Tottenham ɗin da Arsenal tare da Liverpool na son su taya ɗan wasan bayan Torino ɗan ƙasar Ivory Coast mai shekara 21 wato Wilfired Singo wanda ake sa ran sayar da shi kan fam miliyan 15. (Football London)
Barcelona na sa ran shawo kan ɗan wasan bayan Chelsea da Denmark wato Andreas Christensen mai shekara 25 da kuma Cesar Azpilicueta na ƙasar Sifaniya domin su koma kulob din a kyauta a ƙarshen wannan kaka.
Kocin Nottingham Forest Steve Cooper ya bayyana cewa ba za a kawar da hankalin ɗan wasan gaban kulob ɗin ba Brennan Johnson mai shekara 20 ba da batun tattaunawa kan kwantiragi ko batun komawa wani kulob da ke buga gasar Premier. (Mirror)
Shahararren ɗan damben duniyar nan Conor McGregor mai shekara 33 ya nuna sha'awarsa ta sayen Chelsea bayan mai kulob ɗin Roman Abramovich ya ce yana da niyyar sayar da kulob din. (Twitter)
0 Response to "Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ancelotti, Mbappe, Rodriguez, McGregor da Johnson, Bayan PSG tayiwa Mbappe tayin karin albashi"
Post a Comment