-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Bidiyon Jawabin Sarkin Musulmai akan Ganin Watan Shekarar 1442/2021

Bidiyon Jawabin Sarkin Musulmai akan Ganin Watan Shekarar 1442/2021

Bidiyon Jawabin Sarkin Musulmai akan Ganin Watan Shekarar 1442/2021Sarkin Musulmai

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin jinjirin Watan Ramadan a Najeriya.


A wani jawabi da ya gabatar, Sarkin Musulmin ya ce an ga jinjirin watan na Ramadana a daren Litinin, inda ya ce Litinin din 12 ga watan Afirlun 2021 ce ranar karshe ta watan Sha'aban na Shekarar Hijira ta 1442.


Sannan ya ce Talata 13 ga watan Afrilun 2021 ce ranar farko ta watan Ramadana na Shekarar Hijira ta 1442.


"Ƴan uwa al'ummar Musulmi, bisa ga sharuddan Musulunci, muna sanar da ku cewa yau Litinin 29 ga watan Sha'aban shekara ta 1442 bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 12 ga watan Afrilun shekarar 2021, an kawo karshen watan Sha'aban na shekara ta 1442," in ji Sarkin Musulmi.


"Mun samu tabbacin ganin Watan Ramadan daga kungiyoyi da shugabannin Musulmi daga koina a cikin kasar nan, kwamitocin tantance ganin wata na kasa da na jihohi sun tantance kuma mun tabbatar."


Sarkin Musulmi ya kuma shawarci jama'a da su kiyaye dokokin da aka kafa na annobar korona, tabbatar da ba da tazara da kuma sanya takunkumi yayin sallolin dare.


Ya roki al'ummar Musulmi da su yi wa Najeriya addu'a yayin azumin kan matsalar tsaro da ta a'ddabi kasar baki daya.


Sultan Sa'ad Abubakar III ya roki masu arziki da su rika taimakawa marasa karfi domin tabbatar da soyayya da kaunar juna.


Kamar Najeriya, haka ma kasashen Musulmai da dama, da suka hada da Saudiyya sun sanar da ganin Watan Ramadana din a ranar Litinin.


A wannan karon dai al'ummar Musulman duniya za su fara azumin ne bayan da aka sassauta dokokin kullen hana yaɗuwar annobar cutar korona a duniya, ba kamar a bara da aka yi baki ɗayan azumin cikin matuƙar kullen ba.


Yawanci duk shekara, batun ganin watan Ramadan na janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya, amma a shekarun baya-bayan nan an samu raguwar hakan. Sai dai ana yawan samun sabanin fara azumi tsakanin Najeriya da makwabciyarta Nijar.


Azumin watan Ramadana na daya da cikin shika-shikan Musulunci. Ana kwashe kwanaki ashirin da tara ko talatin ana yin azumin.


Kuma Musulmai kan kaurace wa ci da sha da kuma saduwa da iyali daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.Ramadana wata ne mai alfarma da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga Mahalicci.


0 Response to "Bidiyon Jawabin Sarkin Musulmai akan Ganin Watan Shekarar 1442/2021"

Post a Comment