Yadda Za ku Buga Slip ɗin Tantancewa (Screening Slip) na Hukumar CDCFIB
Yadda Za ku Buga Slip ɗin Tantancewa (Screening Slip) na Hukumar CDCFIB
Matakan Buga (Print) Slip ɗin ku:
Application ID (Lambar rajistar da aka ba ku lokacin da kuka cike aiki). Lambar waya ko Imel ɗin da kuka yi amfani da shi.
Idan kuna amfani da Kwamfuta (Desktop/Laptop), danna maballin domin ku buga shi kai tsaye zuwa na'urar Printer. Idan kuna amfani da Waya, za ku iya ajiye shi a matsayin PDF sannan ku kai babban shago (Cyber Café) domin a buga muku (print).
Muhimman Abubuwan Dubawa a Jikin Slip ɗin:
Wurin Jarabawa (Venue): Garin da cibiyar da za ku yi tantancewa. Rana da Lokaci (Date and Time): Tabbatar kun san ranar da aka ware muku. Lambar Jarabawa (Seat Number): Wannan ita ce lambar ku ta zama a wurin jarabawa.
Abubuwan da za ku tafi da su wurin Screening:
Bugaƙƙiyar takardar (Original Printout of Screening Slip). Kofin bayanan ku da kuka cike a baya (Application Form). Asalin takardun karatun ku (Original Credentials). Katin ɗan ƙasa (NIN Slip). Takardar shaidar asali (State of Origin Certificate).
Shawara Ga Masu Nema:
Kada ku tsaya sai gobe jarabawa sannan za ku nemi hanyar buga slip, ku tabbatar kun yi hakan akan lokaci domin gudun samun cunkoso a yanar gizo. Tabbatar kun buga slip ɗin a takarda mai kyau (yawanci ana son Coloured print).
Allah ya ba da sa'a ga dukkan masu nema. Domin samun ƙarin bayani da jagora kowace rana, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.
abubakarshehu798@gmail.com
ReplyDelete