SABUWAR DAMAR AIKI: Gidauniyar Women in Global Health Nigeria Na Neman Masu Tattara Bayanai (Data Enumerators) da Alawus Mai Tsoka
SABUWAR DAMAR AIKI: Gidauniyar Women in Global Health Nigeria Na Neman Masu Tattara Bayanai (Data Enumerators) da Alawus Mai Tsoka
Ana sanar da masu sha’awar neman aiki a fannin bincike da tattara bayanai cewa gidauniyar Women in Global Health Nigeria (WGH Nigeria) ta buɗe shafin ɗaukar masu aikin Data Enumerators na shekarar 2026.
Wannan aiki yana cikin wani babban bincike na ƙasa da ƙasa mai taken Gender Inclusion in Digital Health Campaigns, wanda aka tsara domin inganta daidaito da shigar da kowa cikin shirye-shiryen kiwon lafiya na zamani a Najeriya.
Game da Gidauniyar WGH Nigeria
Gidauniyar Women in Global Health ƙungiya ce da ke fafutukar tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata a ɓangaren kiwon lafiya, tare da ƙarfafa mata wajen samun damar shugabanci da yanke shawara a harkokin lafiya.
Jihohin da Ake Buƙatar Masu Aiki
Ana buƙatar masu nema su kasance suna zaune a ɗaya daga cikin waɗannan jihohi 12:
Arewa maso Yamma
Kano
Kaduna
Arewa maso Gabas
Bauchi
Adamawa
Arewa ta Tsakiya
Abuja (FCT)
Kwara
Kudu maso Yamma
Lagos
Oyo
Kudu maso Gabas
Enugu
Anambra
Kudu maso Kudu
Edo
Cross River
Abubuwan da Ake Buƙata
Samun aƙalla OND, HND, ko Digiri (Bachelor’s Degree).
Samun gogewa a tattara bayanai (Quantitative da Qualitative Research).
Ƙwarewa wajen amfani da manhajojin tattara bayanai kamar KoboToolbox.
Iya magana da harshen yankin da mutum yake zaune.
Mambobin WGH za su samu ƙarin fifiko.
Ayyukan da Za a Gudanar
Gudanar da hira da binciken gidaje ta amfani da wayoyin zamani.
Taimakawa wajen gudanar da tattaunawar rukuni (Focus Group Discussions).
Tabbatar da cewa bayanan da aka tattara sun cika kuma ba su da kuskure.
Tura bayanan da aka tattara kowace rana zuwa tsarin adana bayanai.
Albashi da Nau’in Aiki
Nau’in Aiki: Na ɗan gajeren lokaci (Project-based Contract)
Alawus: Ana bayar da alawus mai tsoka na aikin fili
Yadda Za a Cike
Masu sha’awar wannan dama su aika da:
Sabunta CV
Cover Letter
Zuƙa wannan adireshin imel:
📧 Imel: wghnigeria@womeningh.org
Muhimmi: Dole ne a rubuta sunan jihar da mutum yake zaune a matsayin Subject na imel.
Misali: Data Enumerator Application – Kano
Ranar Rufewa
29 ga watan Mayu, 2026.
Wannan babbar dama ce ga masu sha’awar samun gogewa a manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma fannin bincike.
Allah ya ba da sa’a ga dukkan masu nema. Domin samun sabbin guraben aiki a kullum, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.
0 Response to "SABUWAR DAMAR AIKI: Gidauniyar Women in Global Health Nigeria Na Neman Masu Tattara Bayanai (Data Enumerators) da Alawus Mai Tsoka"
Post a Comment