Aikin Daukar Ma’aikata na Nigeria Agricultural Quarantine Service (NAQS) 2026 Ya Fara
Aikin Daukar Ma’aikata na Nigeria Agricultural Quarantine Service (NAQS) 2026 Ya Fara
Nigeria Agricultural Quarantine Service (NAQS) ta fara daukar sabbin ma’aikata a shekarar 2026 domin cike guraben aiki a sassa daban-daban. Hukumar ta gayyaci ‘yan Najeriya masu cancanta da su gabatar da takardunsu ta yanar gizo.
Mukaman da ake daukar ma’aikata
1. Superintendent Cadre
Chief Superintendent of Quarantine (CSQ) – Ga masu karatun Doctor of Veterinary Medicine (DVM) tare da takardar NYSC.
Deputy Superintendent of Quarantine (DSQ) – Ga masu karatun Law ko MSc daga jami’ar da aka amince da ita.
Assistant Superintendent of Quarantine II (ASQ-II) – Ga masu digiri daga jami’a tare da takardar NYSC.
2. Inspectorate Cadre
Inspector of Quarantine (IQ I–IQ III)
Ana bukatar:
OND ko NCE daga makarantar da aka amince da ita.
3. Assistant Cadre
Quarantine Assistant (QA I–QA III)
Ana bukatar:
SSCE, NECO ko GCE.
A kalla credits 5 ciki har da Turanci da Lissafi a zama biyu ko kasa da haka.
Sharuddan Masu Neman Aiki
Dole mai nema ya:
Kasance dan Najeriya ta haihuwa.
Samu lambar NIN.
Kasance cikin koshin lafiya.
Gabatar da takardar lafiya daga asibitin gwamnati.
Yi nasarar gwajin kwayoyi.
Kasance mai kyakkyawan hali.
Kasance ba shi da laifi a kotu.
Kasance mai iya amfani da kwamfuta.
Tsawon jiki da ake bukata
Maza: akalla mita 1.65
Mata: akalla mita 1.55
Yadda Ake Nema
Masu sha’awar yin rijista su shiga shafin hukuma:
https://recruitment.naqs.gov.ng
A cike fom din neman aiki sannan a tura bayanai kafin ranar rufewa.
Muhimman Ranaku
Fara karbar takardu: 28 ga Yuli, 2026
Ranar rufe neman aiki: 10 ga Agusta, 2026
Fitowar sunayen wadanda aka zaba: 13 ga Agusta, 2026
CBT Screening/Interview: 15 ga Agusta, 2026
Muhimmin Bayani
Neman aikin kyauta ne, babu wani kudin da ake biya. Masu nema su guji masu damfara da ke neman kudi da sunan samun aiki.
Ku kasance tare da Haskenews.com.ng domin samun sabbin labaran ayyukan gwamnati, tallafin karatu da sauran damammaki a Najeriya.
0 Response to "Aikin Daukar Ma’aikata na Nigeria Agricultural Quarantine Service (NAQS) 2026 Ya Fara"
Post a Comment