-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Ina Masu Takardun Kammala WASSCE, OND/NCE, HND/BSc, MSc/Ma ko PHD Ana Neman Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) a Jihohi 36 na Najeriya Domin Wani Babban Bincike

Ina Masu Takardun Kammala WASSCE, OND/NCE, HND/BSc, MSc/Ma ko PHD Ana Neman Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) a Jihohi 36 na Najeriya Domin Wani Babban Bincike

Ina Masu Takardun Kammala WASSCE, OND/NCE, HND/BSc, MSc/Ma ko PHD Ana Neman Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) a Jihohi 36 na Najeriya Domin Wani Babban Bincike

Ana neman ƙwararrun ma’aikata masu hazaka domin shiga wani babban bincike na ƙasa baki ɗaya mai taken “Citizen Mobilisation and Alternative Pressure Mechanisms in Political Action.”

An tsara wannan bincike ne domin gano yadda ’yan ƙasa ke shiga harkokin siyasa da gudanar da mulki bayan zaɓe, da kuma yadda suke tabbatar da adalci da riƙon amana a cikin al’umma. Za a gudanar da binciken a dukkan jihohi 36 na Najeriya tare da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).

Wurin Aiki (Location)

  • Jihohi 36 na Najeriya da Abuja (FCT).

  • Za a ɗauki mutum biyu (2) daga kowace jiha domin gudanar da aikin a yankunan birane da karkara.

Abubuwan da Ake Buƙata (Qualifications)

  • Kasancewa da shaidar karatu ta Diploma ko Digiri (Bachelor’s Degree) a fannin da ya dace.

  • Samun gogewa a fannin tattara bayanai da binciken fili.

  • Iya magana da harshen yankin da mutum yake zaune cikin ƙwarewa.

  • Sanin yadda ake amfani da na’urorin tattara bayanai na zamani kamar KoboCollect da Google Forms.

  • Ƙarin fa’ida: Samun takardar shaida (Certificate) a fannin bincike, musamman kwas ɗin UNICEF Agora Primary Data Collection.

Ayyukan da Za a Gudanar

  • Halartar horon da za a bayar kafin fita aikin fili a ranar 16 ga Mayu, 2026.

  • Gudanar da bincike da hirarraki a gidaje (Surveys, KIIs da FGDs).

  • Tattara aƙalla bincike guda 200 (surveys) cikin lokacin da aka kayyade.

  • Tura bayanan da aka tattara kowace rana ta hanyar manhajar da aka amince da ita.

  • Ɗaukar hotunan filin aiki tare da kiyaye sirrin mutanen da aka tuntuɓa.

Muhimman Ranaku

  • Ranar Rufewa: Karfe 10:00 na dare, Juma’a, 15 ga Mayu, 2026.

  • Ranar Horo (Training): Asabar, 16 ga Mayu, 2026.

  • Lokacin Aikin Fili: 18 zuwa 30 ga Mayu, 2026 (kwanaki 10).

Yadda Za a Cike Fom ɗin Neman Aikin (Application Link)

Ga masu sha’awar wannan aikin, ana buƙatar su cike fom ɗin neman aikin ta hanyar latsa adireshin (link) da ke ƙasa:

👉 Hanyar Cikewa:
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLScVc6u76FwCPRRw_zyXCFDGKcU18bndqjkETJV1bMvN7lZ0qg/viewform?pli=1

Shawara ta Musamman

Ana ba masu neman aikin shawara da su fara yin kwas ɗin UNICEF Agora kan tattara bayanai (wanda bai wuce kusan sa’a ɗaya ba), domin samun takardar shaidar zai ƙara musu damar samun aikin. Ga link ɗin kwas ɗin:

https://agora.unicef.org/c/Primary-data-collection

Lura

Waɗanda aka zaɓa kaɗai (shortlisted candidates) ne za a tuntuɓa. Haka kuma, dole ne mutum ya kasance cikin shiri domin gudanar da aikin a duk tsawon kwanakin da aka bayyana.

Domin samun ƙarin rahotannin guraben aiki kowace rana, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.

0 Response to "Ina Masu Takardun Kammala WASSCE, OND/NCE, HND/BSc, MSc/Ma ko PHD Ana Neman Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) a Jihohi 36 na Najeriya Domin Wani Babban Bincike"

Post a Comment