-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Sabon Shirin Tallafi Ga Masu Ƙanana Da Matsakaitan Sana'o'i (MSMEs) a faɗin Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Sabon Shirin Tallafi Ga Masu Ƙanana Da Matsakaitan Sana'o'i (MSMEs) a faɗin Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Sabon Shirin Tallafi Ga Masu Ƙanana Da Matsakaitan Sana'o'i (MSMEs) a faɗin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani babban shiri na tallafin kuɗi har naira biliyan ɗaya (₦1 Billion) domin tallafa wa ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa (MSMEs) a faɗin Najeriya.

Wannan babbar dama ce, musamman ga waɗanda ke ɓangaren Noma (Agriculture)—wanda yake ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan tattalin arzikin kowace ƙasa, domin idan babu noma, babu abinci.

Muhimman Ranaku:

  • Ranar Buɗe Shafin: 7 ga Afrilu, 2026

  • Ranar Rufewa: 7 ga Mayu, 2026

  • Ranar Ba da Kyautar: 27 ga Yuni, 2026 (Ranar MSME ta Duniya)

  • Adadin Tallafin: Za a raba naira biliyan ɗaya tsakanin ƙwararrun 'yan kasuwa (MSMEs) guda 100 da aka zaɓa.

Yadda Za a Cike:

Kuna iya cike wannan tallafi ta yanar gizo a nan:
👉 msmeclinics.gov.ng/award-apply/

Muhimman Bayanai:

  1. Ba a yarda mutum ɗaya ya cike fom ɗin fiye da sau ɗaya ba.

  2. Waɗanda suka taɓa samun wannan tallafin a baya ba za su iya sake nema ba.

Abubuwan da Ake Buƙata Wajen Cikewa:

  • Cikakken suna, jinsi (mace/namiji), imel, da lambar waya.

  • Sunan kasuwancin (MSME Business Name).

  • Jiha da Ƙaramar Hukuma (LGA).

  • Rukunin tallafin da kake nema (Zaɓi Agriculture idan na noma ne).

  • Lambar Shaidar Haraji (TIN).

  • Ɗora gajeren bidiyo na mintuna biyu (2 mins) yana bayanin kasuwancinka (Kada girmansa ya wuce 30MB; a tsarin mp4, 3gp, ko MOV).

  • Ɗora takardar shaidar rajistar CAC (a tsarin PDF ko hoto; kada ya wuce 5MB).

  • Ɗora sauran wasu takardun shaidar da suka dace (PDF ko hoto; kada ya wuce 5MB).

1 Response to "Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Sabon Shirin Tallafi Ga Masu Ƙanana Da Matsakaitan Sana'o'i (MSMEs) a faɗin Najeriya"