-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shirin Tallafin TVET: Ga waɗanda suka sami irin wannan saƙon

Shirin Tallafin TVET: Ga waɗanda suka sami irin wannan saƙon

Shirin Tallafin TVET: Ga waɗanda suka sami irin wannan saƙon

Ga waɗanda suka sami irin wannan saƙon, hakan na nufin an soke sunayensu daga cikin waɗanda za su amfana da shirin TVET Initiative.

Duk wanda ya sami wannan saƙon, ana shawartarsa da ya tuntuɓi cibiyar horarwa (training center) da aka tura shi, domin a taimaka masa wajen gyara matsayin (status) dashboard ɗinsa daga 'Approved' zuwa 'Registered'. Insha Allahu, idan aka gyara, za su ci gaba da amfana da shirin.

Mafi yawancin waɗanda aka tura wa wannan saƙon su ne waɗanda ba sa halartar horo (training), ko kuma waɗanda ba su kai rahoto (report) a wuraren da aka tura su koyon sana'a ba.

Haka kuma, za a sake buɗe shafin yin rajista domin ɗaukar sabbin masu amfana da shirin TVET Initiative (Rukunin na Biyu/Second Batch) a ranar 8 ga watan Afrilu, Insha Allahu. 

0 Response to "Shirin Tallafin TVET: Ga waɗanda suka sami irin wannan saƙon"

Post a Comment