Ana kira ga masu neman aiki da su ƙara haƙuri, sannan su ci gaba da duba sabbin bayanai a dandalinsu (dashboard) na neman aikin.
Akwai labari mai daɗi ga masu neman aikin, domin an fara tura saƙonnin gayyatar rukunin na gaba don yin hira (interview). Kwamitin ɗaukar ma’aikata yana gudanar da aikin ne mataki-mataki (phases), domin kauce wa cunkoso da kuma rikicewa a wuraren hirar.
Ya zuwa yanzu, saƙon gayyatar bai kai ga mutum 700 ba, daga cikin guraben aiki 5,669 da ake da su. Idan har yanzu ba ka sami naka saƙon ba, kada ka damu; haƙuri yana da matuƙar muhimmanci.
Ana tura saƙonnin ne a hankali, don haka duk wanda ya cancanta zai sami nasa a lokaci mai zuwa. Ana ba ku shawarar ku riƙa duba dashboard ɗinku akai-akai domin kada ku rasa damarku.
Ga waɗanda suka riga suka kammala hira (interview), su ma aikin bai ƙare ba tukuna. Ku ci gaba da shiga (login) shafinku (portal) lokaci zuwa lokaci. Idan kun yi nasara, za a tura muku fom na CSC kai tsaye a dashboard ɗinku domin ku cike, sannan ku tura (submit).
Allah ya sa mu dace.
0 Response to "SABON BAYANI GAME DA ƊAUKAR MA’AIKATA A JIHAR BAUCHI"
Post a Comment