Gidauniyar Grow Strong Foundation (GSF), wadda take daya daga cikin manyan kungiyoyin dake tallafawa mata, matasa, da kananan yara a Arewa maso Gabashin Najeriya, ta sanar da bude shafin daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2026.
Wannan aiki ne na kwantiragi na tsawon watanni 12 (shekara daya), kuma za a gudanar da shi ne a jihohin Borno da Yobe tare da hadin gwiwar hukumomin UNICEF da NHF OCHA.
Wadanda Za Su Iya Nema:
Ana neman mutanen da ke da wadannan matakan karatu:
Masters Degree
Bachelors Degree / HND
NCE
Diploma
SSCE (Kwalin Sakandare)
Jerin Guraben Ayyukan Da Aka Bude:
Akwai guraben aiki da dama, ciki har da:
Case Worker / Case Management Officer (CMO)
PSS Facilitator / CFS Animators
Community Mobilizers (Masu wayar da kan al'umma)
Protection Monitors
Project Coordinator / Child Protection Officer
GBV Officer (Jami'in kare cin zarafi)
MHPSS Officer / Nutrition Officer
ICT Officer / Accountability Officer / MEAL Officer
Traditional Justice Officer / Inclusion Officer
Finance Officer / Procurement Officer
Logistics & Security Officer / Auditor
Abubuwan Da Ake Bukata:
Kasancewa da kwarewa a fannin aikin da kake nema (shekara 1 zuwa 5).
Iya amfani da kwamfuta (Microsoft Word, Excel, da Powerpoint).
Dole ne ka kasance kana zaune a jihar da kake nema (Borno ko Yobe).
Dole ne ka hada CV dinka da Takardar Neman Aiki (Cover Letter) a matsayin takarda guda daya ta PDF.
Yadda Za A Cike (How to Apply):
Idan kana da sha’awar wannan aiki kuma ka cika sharuddan, zaka iya cike fom din neman aikin kai tsaye ta wannan mahadar (link) dake kasa:
👉 Danna Nan Domin Cikewa:
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLScG1mlugdQxDyiFkNVsPZCQAuEP6py6dYpLwEKehQP0mM-mWw/viewform
(Tabbatar ka yi amfani da wannan Link din a matsayin hanyar shiga fom din)
0 Response to "Gidauniyar GSF Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata Masu SSCE, NCE, Diploma Zuwa Masters"
Post a Comment