YADDA ZAKU GUJI RASHIN CANCANTA (DISQUALIFICATION) A SHIRIN NAMP
ƘARIN HASKE KAN SHIRIN NATIONAL AGRICULTURAL MECHANISATION PROGRAMME (NAMP)
Ta hanyar saƙonnin da nake samu a manhajar WhatsApp, na lura cewa mutane da dama ba sa samun nasara (ana disqualifying ɗinsu) saboda rashin fahimtar yadda ake amsa tambayoyin da ke cikin tsarin tantancewar.
Don haka, ga waɗanda suka samu saƙo ta imel (email), ga ɗan ƙarin bayani domin fahimtar manufofin shirin National Agricultural Mechanisation Programme (NAMP):
Menene NAMP?
Shiri ne na musamman na Gwamnatin Tarayya wanda aka ƙirƙira domin inganta harkar noma ta hanyar amfani da injuna da kayan aikin zamani (Mechanisation).
Haɗin Gwiwa:
Shirin yana da alaƙa ta kusa da Bankin Noma (Bank of Agriculture - BOA), kuma yana ɗaya daga cikin manyan manufofin ajandar "Renewed Hope" ta Shugaban Ƙasa domin bunƙasa tattalin arziki da samar da wadataccen abinci.
Shawarwari:
Idan kuna amsa tambayoyin tantancewar, ku tabbatar kun mayar da hankali kan yadda kuke son bunƙasa nomanku ta hanyar amfani da injuna, domin wannan ita ce babbar manufar shirin
0 Response to "Yadda Za Ku Guji Rashin Cancanta (Disqualification) A Shirin NAMP"
Post a Comment