Wata babbar dama ta kunno kai ga matasan Najeriya masu sha'awar harkar fasaha (Tech) da kudi (Finance). Kamfanin MoMo Payment Service Bank (MoMoPSB), wanda yake karkashin babban kamfanin sadarwa na MTN, ya sanar da bude shirin TechSpark Graduate Programme.
Wannan shiri ne na musamman na tsawon watanni 12 inda za a horar da matasa, a ba su kwarewa a fannin fasaha, sannan duk wanda ya nuna kwazo zai samu aikin din-din-din (Full-time job) a kamfanin MoMo.
Fannonin Da Za A Horar Da Kai:
Idan ka samu nasara, za a koyar da kai abubuwa kamar haka:
Cloud Computing
Artificial Intelligence (AI) da Data Science
Cybersecurity (Kariyar yanar gizo)
Software Engineering (Kera manhaja)
DevOps da Networks & Infrastructure
Wadanda Suka Cancanta Su Nema:
Ilimi: Masu Degree (Bachelor’s) ko Masters a fannin:
Engineering, Computer Science, ko IT.
Mathematics, Physics, Data Science, ko Cybersecurity.
NYSC: Dole ka kammala aikin yi wa kasa (NYSC) ko kuma kana saura kadan ka kammala.
Gogewa: Masu gogewar aiki daga shekara 0 zuwa 2 (Wato sabbin yaye ne).
Sani: Sanin abubuwan da suka shafi programming (kamar Python, Java, SQL) zai taimaka maka sosai.
Me Ya Sa Ya Kamata Ka Nema?
Za ka samu horo daga kwararrun injiniyoyi.
Za ka samu takardar shaida ta kasa-da-kasa (Professional Certification).
Za ka samu damar yin aiki a daya daga cikin manyan kamfanonin kudi a Najeriya.
Wurin Aiki:
Za ka yi aiki a Victoria Island, Legas (Akwai tsarin "Hybrid", wato zaka iya aiki a ofis da kuma daga gida).
Yadda Za A Cike (Method of Application):
Idan ka cika sharuddan, danna wannan mahadar (link) dake kasa domin tura takardunka:
👉 Danna Nan Domin Cikewa: https://ehle.fa.em2.oraclecloud.com/hcmUI/CandidateExperience/en/sites/CX_1/job/7164/
Kada ku bari wannan dama ta wuce ku, musamman matasanmu masu fasaha da kishin gina gobe. Share wannan labarin ga wasu domin su ma su amfana.
0 Response to "Kamfanin MoMo (MTN) Ta Bude Shafin Daukar Sabbin Ma'aikata Masu Degree Da Masters Domin Shirin ‘TechSpark’"
Post a Comment