Sabon Bayani Kan Shirin YEIDEEP
Sabon Bayani Kan Shirin YEIDEEP
Abin da Ya Kamata Jama’a su Sani
Shirin YEIDEEP ya jawo tambayoyi da dama daga al’umma, musamman kan batun buɗe asusu(Account ) da tsarin gudanar da batches. Wannan sanarwa na zuwa ne domin fayyace yadda tsarin yake, tare da kawar da duk wata rashin fahimta.
Tsarin Shirin – Batch by Batch ne
Batch na Farko:
su ne mutanen da suka fara cike wa aka tura mu su(code) code dinda zai baka damar zuwa ɗaya daga cikin bankuna uku na farko (Keystone, Fidelity, Lotus) domin buɗe account wato ta hanyar link da aka tanada.
Batches na biyu:
Su ne wadanda suka cika ba tare da anturo musu code ba kai tsaye YEIDEEP suka tantance bayanansu sannan suka buɗe musu asusu(account) ta tsarin kwamfuta.
wadanda suka dinga ganin account number ba tare da sun bude account din ba.
Daga Baya kuma An canja tsarin program din gaba daya Saboda yawan mautanen da suka cike program din, da farko Bankunan 3 ne kacal Amma a yanzu bankuna 12 ne
A can farko babu tsarin shigar da BVN amma yanzu Dole sai da BVN, Sunyi hakanan ne Saboda su budewa mutanen account kai tsaye kamar yanda tsari na biyu yake babbancin shi ne; karin bankuna da aka samu 3-12
Me Wannan Ke Nufi ga Masu Nema?
Babu buƙatar ka buɗe wani asusu a wajen shirin, domin ba za a yi amfani da shi ba.
saboda haka idan ba a turo maka account number ba kada ka wani da mu hakan na nufin ba a kai batch ɗinka ba tukuna ba wai an cire ka daga shirin ba.
muhimmin Sako shi ne;
Al’umma, musamman mata, na shiga damuwa suna zuwa banki domin bude account, ko kin bude account da wani bank indai ba ƙarƙashin wannan program na YEIDEP aka bude miki shi ba wanda a halin yanzu ban kuna ba su da damar yin hakan, aikin banza kika yi ko nace kin budewa kanki account ne kawai.
Shi ma biyan kudi kamar yanda suka sanar zai zo ne tsarin batch-batch.
Allah yasa muna da rabo a wannan program.
Alhamdulillah, amma ni ina da code keystone bank sun tura min da Link yadda zan bude account nayi komai har code na saka Toh amma banga account number ba gaskiya.
ReplyDelete