
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Shirin TVET Don Horas da Matasa da Rage Rashin Aikin Yi - Tare da Tallafin ₦22,500 Ga Dalibai (da Kayan Farawa) da ₦30,000 Kan Kowane Dalibi Ga Masu Koyarwa
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Shirin TVET Don Horas da Matasa da Rage Rashin Aikin Yi - Tare da Tallafin ₦22,500 Ga Dalibai (da Kayan Farawa) da ₦30,000 Kan Kowane Dalibi Ga Masu Koyarwa
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin horar da matasa a fannoni na fasaha da sana'o’i (TVET) domin rage rashin aikin yi da kuma gina ƙwararrun ma’aikata. Dr. Maruf Alausa ya bayyana cewa shirin zai gudana na tsawon shekaru 3, ko kuma za a iya zaɓar tsawon watanni 6 ko 12. Za a ba da takardar shaidar kammala daga NABTEB da wasu hukumomi.
Dalibai za su karɓi ₦22,500 a kowane wata tare da kayan farawa, yayin da masu koyarwa za su karɓi ₦30,000 kan kowane dalibi. Shirin ya haɗa da sana’o’i kamar walda, gyaran wuta, ICT, gini da sauransu. Za a gudanar da shi ta hanyar makarantu da cibiyoyin horo masu lasisi.
Za a yi amfani da NIN da fasahar geofencing domin sa ido. Ana gudanar da biyan kuɗi ta dandalin NELFUND. Bankin Masana'antu zai ba da rance mai sauƙi da kuma tallafin kasuwanci.
Minista Suwaiba ta bayyana TVET a matsayin tushe ga ci gaban ƙasa. Ana buƙatar matasa su ci moriyar wannan dama.
👉 Yi rijista yanzu a: https://www.tvet.education.gov.ng
0 Response to "Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Shirin TVET Don Horas da Matasa da Rage Rashin Aikin Yi - Tare da Tallafin ₦22,500 Ga Dalibai (da Kayan Farawa) da ₦30,000 Kan Kowane Dalibi Ga Masu Koyarwa"
Post a Comment