DAN GANE DA ZAMAN TAKEWA NA MA AURATA
DAN GANE DA ZAMAN TAKEWA NA MA AURATA, Ga wasu baiwa dake tattare ga mata.
Ya kamata maza su fahimci zaman takewar su tsakaninsu da matansu,
Kasani cewa idan ka mutunta matarka zata baka dukkanin soyaiyar ta gareka,
Idan ka mata murmushi kuma ita kuwa zata kyakyata da dariyar da zai saka farinciki,
Idan ka bata zuciyarka ita kuma zata baka rayuwarta,
Idan kai mata dakin kwana zata Maka gidan zama,
Idan kazo mata da shawara zata zo maka da mafuta,
Idan ka dauketa sarauniya zata maidaka sarki,
Idan ka bata soyaiyar da take bukata zata sadaukar maka da dukkanin rayuwarta,
Haka kuma idan ka nemi cin mutuncinta zata iya balbalta rayuwarka.
Ga wata shawara dangane da samari masu neman aure, sam kada ka yadda da wanan macen mayaudariya ce ba auranka zatai ba,
1 yarinyar da bataso kana gaisawa da iyayenta
2 yarinyar da bataso kazo kofar gidansu seda kaji tana mu hadu a bayan layi
3 yarinyar da kullum take yawan zo maka da bukata, samin kati, samin data, aduk rana, da za kace baka dashi seta fara fushi dakai, alama abinka take so ba kaiba,
4 yarinyar da bata da lokacinka, aduk lokacin daka bukaci ganinta ko waya da ita, seta kawo maka uziri mara tushe,
5 yarinya mai yawan karya akan abu daya, misali zata iya cewa tana gida anjima kuma kaji tace maka taje aika ko tana wurin biki.
6 yarinya mai yawan kule kule, tace wanan class mate dinane wancan dan unguwarmu ne, wanan aboki nane, da zaka bincika seka tarar duk samarinta ne,
Dalilai gamsassau game da nisantar macen da nuna bata sonka, kayi hakuri dan uwana ka kyale macen da tace bata sonka ko ta nuna bata sonka,
Akwai banbanci tsakanin dabi ar mace da dabi ar na miji game da soyaiya, Ita mace soyaiya da tausayi hade suke acikin zuciyar ta yawanci basu rabuwa, idan mace tana sonka to tana tausayinka gwargwadon soyaiyar da take maka gwargwadon tausaya maka da zata rika yi, idan tana sonka da gaske bazata taba daga maka hankali ba, kota dora maka abinda ze wahalar dakai, zata saukaka maka wahalar rayuwane, zata temaka maka cikin duka lamuranka, amma idan bata sonka to bata tausayinka ko abin birgewa kai mata haushi zaka bata, kuma ba zaka taba burgeta ba, wata macenma ko mutuwa zakai ba zataji tausayinka acikin ranta ba, irin wannan macen aka aura maka ita idan bata da tsoron Allah zata iya hallaka ka ba tareda da an sani ba, ko abayyane kowa ma yasani, ana haka da yawa.
Sabanin namiji, shi soyaiyar da tausayi abubuwa ne biyu mabanbanta acikin zuciyarshi, namiji ze iya tausayin macen da baya so, wanima tausayinne ze karkato da zuciyarsa ya fara soyaiya da wacca baya so, namiji ze iya auran macen da yake tausayi koda baya sonta, kuma ze iya son mace alhalin baya tausayinta,
Akwai mazajen da sun daina jin kaunar matansu, amma tausayi yake sanya su cigaba da zama dasu, mace kuma ba haka bane idan ta daina sonka to ta daina tausayinka idan kaga ta cigaba da zama dakai to ta lissafa taga idan ta futa batada madafa ne amma da zarar ta hango madafa zata futa, zama da macen data nuna bata sonka wasa da rayuwarka ne, da wanan zaku kara fahimtar wasiyyar Annabi (s a w) da yace "Ku auri matan dake haihuwa masu soyaiya gareku"
Rashin sanin fahimtar banbancin dabi a tsakanin maza da mata yana temakawa sosai wajen kawo sabani tsakanin jinsin biyu, da bukatar mu kara fahimtar junanmu da kanmu, domin samun maslaha atsakanin junanmu.Allah yasa mudace
7 yarinya da bata son maganar aure, idan kayi mata maganar zatai kokarin kawar da maganar ko tace maka kadan jira,
8 yarinyar data rainaka, musamman taga kana sonta sosai, maimakon ta girmamaka seta fara wulakanta ka tana rainaka.
Shawara anan shine, ka nemi yarinya mai tsoron Allah da tarbiya, wadda tasan mutuncinka kuma take sonka da gaskiya tsakani da Allah,dan uwana kada Ka bari soyaiya ta rufema idanuwa har ka fada tarkon mace, Allah yayi mana zabi na gari.
0 Response to "DAN GANE DA ZAMAN TAKEWA NA MA AURATA"
Post a Comment