BAYANI GAME DA YADDA AKE ZAMAN AURE
BAYANI GAME DA YADDA AKE ZAMAN AURE
Da Farko Yanada Kyau Mutane Su Fahimci Cewa Aure Wani Mataki Ne Wanda Allah Zai Kai Mutum Da Ake Tunanin Aga Sauyi Daga Rayiwarshi Da Ta Gabata.
Zaman Aure Tsakanin Miji Da Mata Ya Kunshi Kulawa, Hakuri, Biyayya Musamman Ga Mace Tsakaninta Da Mijin ta. Haka Kuma Anason Tausayawa Ga Namiji Zuwa Ga Matar sa Ta Fannin Taimaka mata Wurin aikace_Aikacen Gida, Taya ta Renon Yaro ko Yarinya Idan Allah Ya Albarkace Ku Da Samu.
Haka Kuma Rayuwar Aure Tana Bukatar Saka Hankali Game da Abokin Zamanka Yayin Da Kai Namiji Idan Ka Lura Da Matarka Ta Shiga Wani Yanayi Wanda Kai Baka Santa a irin Wannan Halin Ba Sai Kayi Gaggawar Binciken ta Ta Hanyar Saukar Da Muryarka Cikin Natsuwa tare Da Bata Kwarin Guiwa, Ta wannan Dabarar Zaka Samu Duka Baya nan Da Kake so Kasamu Daga Gareta. Bayan Ka Samu Baya nan a matsayinka Na Mijinta Sai Kayi Kokari Kabi duk Hanyar Da Zaka bi Ka Kwantar Mata Da Hankali Koda Kaine Silar Wannan Shiga Yanayin Nata.
Ta Fannin Mata Kuma Yanada Kyau Ki Fahimci Waye Mijin ki Kuma ya rayuwarsa take. Wani Lokaci Maza ana bata musu rai a waje, Idan Na miji Ya Shigo Gida Kika Fahimci Ya Sauya Ba Kamar Yadda Ya Fita ba a Matsayinki Na Matar sa Zaki Gane. Hakan Na faruwa Sai Kiyi Kokarin Jawo shi a Jikin ki tare Da Tattausa Kalaman Ki zuwa Gareshi Daga Karshe Sai Ki Nuna masa idan Har Wani Abu aka masa Wanda ke Damunshi Sai ki Nuna Masa Kin Fishi Shiga Cikin Yanayin Damuwa Kasancewar sa Mutum mai Matukar Muhimmanci A wurinki. Daga Gano Haka shi Kuma zai Fara Zayyana Miki Duk Abinda Ya Faru Dashi daga karshe ma Shine Zai Rarrashe ki domin kada ki saka wannan abin a ranki Kuma shima Ya wuce a wurin shi. Daga Bisani sai ki kawo masa Abinci a gabansa da sauran abinda kika San yafi Bukata idan Ya Fara cin Abinci Domin Duk wani Magidanci Zaifi Son Komi Na Gabansa Idan ya fara cin abinci; Maza Basu Son ana kawo musu Abinci Ba tare da An hada komai a lokaci Daya ba.
A Fannin Kwanciyar Aure: Yanada Kyau Kowane Namiji Ya Kasance Cikin Tsafta tare Da Sakama Jikinsa Turare Mai Kamshi kamin ya Kusanci Matar shi. Haka Kuma Mace Ana Bukatar Tayi Shiri tare Da Saka Kaya Wadanda Zasu Kara Janyo Ra'ayin Mijinta Yaji Dole Sai ya Kwana Da ita tare Da Saka Turare Na humra mai kamshi ta Yadda Mijin nata bazai Ji Kyamar kusantar ta ba.
Fannin Biyayya Ga Dangin Miji a Bangaren Mace; Kula Da iyayen miji tare da sauran yan uwansa yana Matukar kara tasiri a Zamantakewar Aure Kuma yana Kara ma Mace kima ga dangin Mijinta Wanda Ko bayan rayuwar Mijinta bazata Walakanta a wannan Dangin ba Kuma Diyanta Zasu Zama Abin So ga Kowa Acikin Dangin Mijinta.
Biyayya Ga Na Miji Ta Bangaren Dangin Mace: Biyayya Ga iyayen Mace Na Kara ma Namji daraja a wajen matar sa Misali: idan Abin Kuka ya Samu kayi Gaggawar zuwa gidansu domin jajantawa zuwa Garesu, idan Abin Murna ya Samu babu bukata Da kiran waya ko Kuma aike, Kawai Kaje Da Kanka Domin Ka Taya Murna In Da Hali Ka jima tare dasu ana tayaku murna tare Hakan Kuma Na kara Zama katangar Toshe wani Sheri Na bata Garin Da ke son shiga tsakaninka Da Iyalinka Domin Bazata yadda ta bari a Hada ta da Wanda ke Hidimta mata ba.
Ta fannin taimako a wajen Zamantakewar aure; Zaka ga Wasu Maza Matansu Suna aiki Na gwamnati Kuma basu damu ba. Yanada kyau a Matsayin ki Na mace kiyi Kokarin Taimaka masa akai-akai yadda bazai takura ba Domin kina fita aiki Kuma wannan zaisa Shikara Yimiki kyakkyawan zato a Zamantakewar Aurenku.
Haka shima Na miji Yanada Kyau ko Baka Baiwa matarka kudi akai-akai to kayi Kokarin riko mata guzuri a lokacin Da zaka shigo gida. Hakan Na Matukar Kara dankon aure tare da Burge Mata.
Wannan shine Rayuwar Aure a Bayyane
0 Response to "BAYANI GAME DA YADDA AKE ZAMAN AURE"
Post a Comment