-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI

ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI

ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI

Da Farko Dai Aikin Gwamnati Wani Garkuwa ne Ga 'Ya Mace Acikin Gidanta Haka Kuma Shari'a ta Bada Damar Yin Aikin Gwamnati Ga Mace Idan Har Kai Mijin nata ka Aminta

Idan Har kanada mata ma'aikaciyar gwamnati a matsayinka Na mijin ta Yanada Kyau Ka San Ya Halayyar Mutanen Da take Aikin tare dasu take, sannan suwaye tafi mu'amala tare dasu Domin a wajen aiki ana daukar Wasu halaye Daban-Daban marasa wadanda baza ka iya juresu ba wata rana ma sai ka dawo kana Da Na Sani. Kayi kokari tun kamin alakarsu tayi nisa ka dakatar Da huldar da suke a tare musamman Wasu mata sai kaga hadda sirrin mazajen su suna bayyanawa Acikin kawayensu da suke aiki tare dasu, to idan ka raba ta dasu zaka Samu matar ka kamar yadda kuke zama tare da ita ba tare da ta canza ba.


Haka Kuma ba Dole bane ace a wajen da matarka take aiki duka Mutane ba! Zaka iya tarar Da maza sun kasa matan kashi uku Kuma daga cikin su akwai bata gari Wasu ma zasu iya Kokarin kulla wata mummunar alaka ta aikata Alfasha Da ita, A matsayinka Na Mijinta kayi Kokarin sanin masu irin wadannan halayen Domin ka tabbatar mata Da cewa bayan Hulda ta gaisawa banso wata alaka ta hadaki da wadannan Mutanen bata gari. Idan Har ka Sanar da ita wadannan Mutanen Kuma kayi mata gargadi idan har batada bukata da yin rayuwa irin tasu zaka ga ko lambobin wayar irin wadannan abokanin Aikin baza ka Samu a gareta ba. 


A Bangaren kai mijin nata; Da Yawa Wasu idan suka auri Mace ma'aikaciyar gwamnati sun raja'a da cewa suyi musu bukatun yau da kullun Na cikin gida kamar cefane, biyan kudin makaranta ga Yara, yima Kansu sutura, biyama Kansu kudin kitso Da lalle da dai sauransu, To hakan ba dai dai bane Kuma ka budewa kanka hanyar reni Da rashin bin umurnin Da kayimata Acikin gida Kuma yaranka zasu taso su raina ka. Yanada kyau kayi Kokarin daukar duk wata lalura da aka Dora maka Har idan ta Taimaka ma shike nan akasin haka Kuma sai kayi hakuri tunda dama ba dole bane amma kaima duk abinda zaka yimata idan Har babu Taimakon da take maka kada kayi abinda zai zo shi wahalda kai Har takai ga Al'ummar Da kake tare dasu kowa Na binka bashi Domin faranta ma matarka rayuwar ta.


A Bangaren mace Kuma Zaka ga Wata mace mai Aikin gwamnati daga gidanta zuwa wajen Aikin nata akwai tazara sosai kamin ta isa wajen Aikin nata wata rana ma sai ta isa a makare kamin ta Samu mai adaidaita sahu ko Dan achaba. Wasu matan Kuma mazajen su Nada ababen hawa kamar mota, Babur amma ba zasu iya daukar dawainiyar kaisu wajen Aikin ba saidai su nemi achaba amma idan kai Na miji kanada halin kaita to ka dauki dawainiyar kaita kullun idan lokaci yayi Kuma sai ka koma ka dauko ta a wajen Aikin nata Domin mata rauni ne dasu Kuma amana ce a wajen maza. Ke Kuma a Matsayin ki Na mace kiyi Kokarin yima mijin naki ihsani koda bai kai ki wajen Aikin hakan zaisa yaji bari ya kama kai ki yana zuwa ya dawo dake.


Wasu iyayen idan 'yar su Mace Na Aikin gwamnati zaka ga sun dogara gareta komi basu iya yi koda sunada rufin asiri sai kaga da abunda take Dashi suke biyan bukatunsu. Idan ka Fahimci haka a Matsayin ka Na Mijinta ka kara Kokarin kauda kai ga duk wani abinda take tarawa kanta Domin duk abinda take ajewa a asusun ajjiyar ta suna sane Dashi. Ko lalura gareka kada ka nemi rance gareta Yi Kokarin zuwa wajen Wasu daga cikin abokanin ka masu hali ka nemi taimakon su Domin ka nema ma kan ka mafita Amma ba ka nemi rance ta wurinta ba. Dalili shine da Sun nemi su karbi abinda take Dashi da yayi gaira ga abinda suka Sani zasu tambayeta ina sauran kudaden? Daga nan zata gaya musu kai ta ranta ma. Shike nan sai su kama tunanin cewa Kaine ke karbe duk abinda ta nema Kuma ka dogara ga Abin 'Yar su.


Wata uwa mace ma ita ke Dora diyar ta akan Layin da Kada ta yadda kai Mijinta ka San sirrin abinda ke gareta Kuma kada ta kuskura kiyi masa hidima da abinda kike Dashi Domin wata rana da Abinki zai hada shi kara aure daga nan ke kin fita wajen Aikin naki sai ya dawo gida shi da amaryar sa suna cin soyayyar su a tare.


Kai Na miji idan ka Fahimci cewa matarka bata son Taimaka ma kan harkokin yau Da kullun Kuma tana Aikin gwamnati, Yi Kokarin Kara kawar Da kai daga duk abinda take Samu idan Da hali ka manta Da Aikin gwamnati ma take yi Ka Dauki dawainiyar gidanka Daidai gwargwado daman Shari'a kai ta dorawa dawainiyar gida. Kuma ka kai zuciyarka nesa ina tabbata maka cewa wata rana idan Allah ya Baka Abin kara aure idan ka auro wadda take Kokarin Taimakon ka koda ita ba ma'aikaciyar gwamnati bace Zaka ga tayi wurgi Da waccen hudubat da aka jima ana yimata ta fara Taimakon ka Da yaranka Wanda sai kayi Namaki. Daga nan sai kaga ana competition (gasa) Na Taimaka ma Tsakaninta da abokiyar zamanta😄😄


Daga wannan lokacin ma zata fara planning (tsara) yadda zata yima yaranta garkuwa da wannan Abin da take Samu Kuma ta fara tuntubar ka shawarwari game Da rayuwar yau Da kullun. 


Wannan shine bayanin yadda ake zama Da Ma'aikaciyar Gwamnati tare Da yin rayuwa cikin mutunci

0 Response to "ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI"

Post a Comment