An Buɗe Shafin Cike Shirin 3MTT Karo na Biyu na Ma’aikatar Sadarwa da Kirkire-Kirkire
An Buɗe Shafin Cike Shirin 3MTT Karo na Biyu na Ma’aikatar Sadarwa da Kirkire-Kirkire
Shirin 3 Million Technical Talent (3MTT) na Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital na Najeriya ya kuduri aniyar haɓaka ƙwarewar fasaha a ƙasa tare da tallafawa hangen nesa na Shugaba Tinubu na samar da ayyukan dijital miliyan 2 zuwa 2025. Shirin zai taimaka wajen tabbatar da Najeriya ta zama jagora a fitar da ƙwararru a duniya.
Mataki na farko ya fara a Disamba 2023 tare da hadin gwiwar NITDA, inda aka horar da mutane 30,000 a dukkan jihohi da Abuja. An haɗa karatun kan layi mai zaman kansa da darussa na fasaha ta zahiri tare da tallafin ƙungiyoyi fiye da 120.
Mataki na biyu zai horar da ƙwararru 270,000 a rukuni uku na 60,000, 90,000, da 120,000. Wannan matakin zai haɗa kai da gwamnatocin jihohi, kungiyoyin ci gaba, da cibiyoyin koyo don cimma nasara mai ma’ana.
Ayyuka da za'a koyar
- AI / Machine Learning
- Animation
- Cloud Computing
- UI/UX Design
- Data Analysis & Visualization
- Data Science
- DevOps
- Game Development
- Product Management
- Quality Assurance
- Software Development
- Cybersecurity
Yadda zaku cike
Domin cikewa ku latsa shafin yanar gizo gizo dake a kasa
Domin Cikewa: https://app.3mtt.training/apply
Domin shiga: https://app.3mtt.training/login
Domin karin bayani: https://3mtt.nitda.gov.ng/
Allah yasa mu dace baki daya
Allah samu dace Ameen
ReplyDelete