-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Bayani Akan Tallafin Karatu na BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA)

Bayani Akan Tallafin Karatu na BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA)

Bayani Akan Tallafin Karatu na BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 

Ma'aikatar Ilimi ta Ƙasa wato Federal Ministry of Education a ƙarƙashin tsarin nan mai suna BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) ta buɗe shafin ta domin ɗaukar ɗaliban da za a tura ƙasashen wajen domin yin Degree na farko da na biyu (Master's Degree) da kuma na uku (PhD) na shekarar 2023/2024.

Ƙasashen da za a tura wanda zasuyi degree na farko, wato undergraduate studies sune: Russia, Morocco, Hungary, Egypt da kuma Venezuela.

Ga kuma courses ɗin da zasu iya cikewa:

Engineering, Geology, Agriculture, Sciences, Mathematics,  Environmental Sciences, Sports, Law, Social Sciences, Biotechnology, Architecture, Medicine (very limited), Pilot Engineering, and Neurologist.

Ƙasashen da za a tura masu degree na biyu dana uku wato Postgraduate studies sune: Russia (ga waɗanda sukayi degreen su na farko a Russia), China, Hungary, Serbia, da kuma Romania.

Masu Master's degree da PhD zasu iya cike kowanne course.

Wanda zaiyi applying na undergraduate dole ne ya zamanto yana da distinction guda bakwai (As&Bs) a WAEC ɗinsa ta shekarar 2021/2022 sannan kada ya gaza shekara 17, kada kuma ya wuce shekara 20.

Post graduates kuma dole ya zamanto kana da First Class ko kuma 2nd  Class Upper a degree na farko.

Dole ka mallaki NYSC discharged certificate and the age limit is 35 years for Masters and 40 years for PhD.

Zasu rufe ranar Juma'a 6th January, 2023.

Links ɗin da za a shiga domin applying shine:

https://fsbn.com.ng/scholarships


0 Response to "Bayani Akan Tallafin Karatu na BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) "

Post a Comment