-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Zaki Hada Garin Sabaya A Saukake

Yadda Zaki Hada Garin Sabaya A Saukake

Yadda Zaki Hada Garin Sabaya A Saukake

A koda yaushe burin kowace ‘ya mace shine ta kasance abin sha’awa a wurin mijinta, tayi kyau yadda zata amsa sunanta na ‘ya mace. A yau zan kawo muku wani sirri wanda ba kowa ya sani ba, wasu kuwa sun san dashi amma basusan yadda zasu hada shi a gida ba. Wannan hadin da kuke gani malamai sunyi Magana akan ingancinshi bama a wurin ‘ya mace kawai ba, wannan hadin kowa na iya shanshi domin yana kara lafiya sosai musammam ga masu shayarwa. Yana karawa uwa ruwan nono, kiga yaronki ya kara samun kuzari da kuma lafiya, yayi bulbul gwanin sha’awa. Ke kanki uwa sai kiga kinyi kyau fatarki na sheki abun burgewa. 

Saudayawa mutane na alakanta samun kiba da sabaya, wanda abun ba haka yake ba, saidai ya kara gyara maki fatarki ya kuma sa ki cicciko.

Abubuwan da zaki bukata sune kamar haka;

 1. Farar shinkafa

 2. Alkama

 3. Gero

 4. Aya

 5. Waken suya

 6. Gyada mai kampala

 7. Ridi

 8. Kwaka(idan kinaso)

 9. Karas

 10. Dabino

 11. Garin hulba

 12. Mazarkwaila.

Da farko zaki samu farar shinkafarki, alkama, gero, aya, waken suya da kuma ridi ki gyara su da kyau ki cire tsakuwa, sai ki wankesu. Bayan kin wankesu da kyau sai ki tsame ki shanyasu a rana. Bayan wannan sai ki dauko dabinon ki ki cire diyan dake cikinshi ki wanke da kyau saboda dattin da ya kwaso, shima sai ki shanya a rana. Sai ki dauko kwakwarki da Karas ki gurza su da abun gurza kubewa, sai ki shanyasu a rana su bushe. Daga nan sai ki dauko gyadarki itama ki gyarata da kyau, ki soya ta sama sama kada ki barta ta kone, Sai ki dauko mazarkwailarki ki  daddatsata. 

Bayan kin gama wannan, sai ki dauko ridi, aya da waken suyarki da suka bushe suma ki soyasu sama sama yadda kikayiwa gyadarki ba tareda kin barsu sun kone ba. Bayan kin gama wannan sai ki dauko sauran kayayyakin da kika busar ki hadesu da kayanki da kika soya da kuma hulbarki da mazarkwailar da kika daatsa, sai ki bayar akai maki nikarsu ko kuma idan kinada abun nika sai ki nikasu duka. 

Amma wasu sukan nikasu daban daban saboda su kara nikuwa da kyau kuma dan kada su cure wuri daya yayin nikawar. Bayan kin gama nikarki sai ki tankade su gabaki daya idan kinason yayi laushi sosai idan kuma baki bukatar hakan basai kin tankade su ba. Sai kisamu wurin ki adana garinki.

Anason wannan hadin ki kiyaye shanshi safiya da maraice, idan da hali anason ki dinga sanya madara a duk lokacin da zaki shashi kuma kina iya sanya Zuma ko suga idan kinaso. Wannan hadi idan mace ta rike shi ya isheta amfani wurin gyaran Jikinta. Sannan wannan hadin ba lallai kawai sai matar aure zatayi ba, kowa na iya shansa daga kan yara, budurwa, harda maza ma.

Ku biyo ni a wani shafin domin samun wasu sirrika na ban mamaki.

Nagode.0 Response to "Yadda Zaki Hada Garin Sabaya A Saukake"

Post a Comment