-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA ZAKI HADA FANKASO

YADDA ZAKI HADA FANKASO

YADDA ZAKI HADA FANKASO

Abubuwan bukata;

Alkama

Filawarki 

Ruwan tsamiya 

Yeast

Sikari

Ruwan kanwa

Mansuya 

Yadda  zaki hada;

Dafarko za ki samu roba mai zurfi da kuma marfinshi sai ki zuba suga,  yeast da kuma ruwan tsamiya kanwa ki rufe ki barsu su jiko, sai ki dauko filawarki ki hadata da garin alkama. Idan yeast dinki ya narke kijuye filawarki ki kwabata sosai kada kibari tayi gudaji (kolallai) kuma kada ki bari kwabin yayi ruwa karkuma yayi karfi sosai, saiki rufe ya samu kamar awa daya zakiga ya tashi. Bayan nan sai ki dora man suyarki, anaso kisaka mai yaji sosai saboda fankasau baya son karancin mai, sai ki barshi yayi zafi sosai. Idan yayi zafi sai ki dauko kwabin ki kara mulkashi sosai zakiga ya koma ya kwanta kuma kuma ya saki, saiki sami farantinki watau tire ki shafe shi da ruwa kirika gutsurar kullin kina sawa akan dan farantin ki huda tsakiya saiki saka acikin mai zakiga yana tasowa a cikin mai a hankali sai ki barshi ya soyu kada kiyi saurin juyawa saboda funkaso bayason yawan juyawa. Idan kinga kasan ya soyu saiki juya saman shima ya soyu. Ana sanya tsamiya a funkaso ne saboda ya rage shan mai kuma yasa suyarki tai ja tayi kyau. Shikenan bayan ta soyu sai ki tsameta daga cikin mai, ayi serving.

0 Response to "YADDA ZAKI HADA FANKASO"

Post a Comment