Yadda Ake Alalen doya, Alalen dankali, Alalen plantain, Alalen Fulawa, Alalen kabeji, Alalen Nama da kwai
HADIN ALALA KALA BIYAR DA YA KAMATA KI IYA
Yadda Ake Alalen doya, Alalen dankali, Alalen plantain, Alalen Fulawa, Alalen kabeji, Alalen Nama da kwai
1. Alalen doya
Abubuwan bukata;
Kwai
Doya
Curry
Hanta
Magi
Attarugu
Da farko zaki wanke doyarki ki yanka ta daidai yadda zaki iya rikewa, sai ki goge ta da abun goge kubewa. Bayan kingama gogeta sai ki yi blending dinta tare da attarugu da albasa yayi kauri kamar yanda ake kullun wake. Daga nan sai ki kawo magi, da curry kadan ba’aso yafito sai ki saka a ciki, , sai ki kawo yankakkiyar dafaffen hanta ki saka shima aciki. Bayan kinyi wannan sai ki dauko dafaffen kwanki ki yankata kanana sosai sai ki sakata aciki, idan kuma baki bukatar dafaffen kwai zaki iya saka danye bayan kin kadashi. Bayan kin gama hadin ki sai ki kullashi kamar yadda akeyin Alalen wake, sai ki dafashi. Idan ya dahu ki sauke shikenan alalen ki ya yi sai kiyi serving. Zaki iya cinshi haka nan ko kuma ki hadashi da miya.
2. Alalen dankali
Abubuwan bukata;
Dankali
Nama
Kwai
Attarugu
Albasa
Curry
Maggi
Gishiri
Mai
Da farko zaki dafa dankalinki ki marmasa shi ko kuma ki daka. Bayan kinyi wannan sai ki tafasa namanki ki daka kizuba shi akan hadin ki na dankali, sai ki jajjaga attarugu da albasa kizuba akai. Daga nan sai kisa maggi, curry, gishiri da mai, sai kuma ki fasa kwai kizuba akai ki juya sosai ya hade jiki, sai ki zuba a leda ko gwangwani ki dafa. Shikenan alalarki ta dahu sai ayi serving.
3. Alalen plantain
Abubuwan bukata;
Plantain
Garin plantain
Cray fish
Busashen kifi
Attarugu da Albasa
Curry
Manja
Da farko zaki bare plantain iya yawan da kikeso sai ki yayyanka ta kanana ki markadata a blender. Bayan kin markadeta sai ki zuba garin plantain kofi daya da rabi akan plantain din dakika nika, sai ki saka busasshen kifinki da dakakken cray fish akai, kisa maggi, gishiri, attarugu, albasa da mai akan gadinki sai ki juya. Idan yayi kauri sai ki kara ruwa yazama kamar kullin Alale, sai ki dauko gwangwani ko ledarki ki saka aciki sai ki dafa. Idan ya dahu sai ki sauke ayi serving.
4. Alalen Fulawa
Abubuwan bukata;
Fulawa
Kwai
Nama
Danyen kifi
Nikakken kayan miya
Albasa
Attarugu
Curry
Gishiri
Magi
Dafarko dai zaki tafasa kifinki sai ki bare ki fitarda kaya ki bar tsokarki sai ki kwaba fulawa da kauri kamar kwabin Alale, sai ki fasa kwai akan hadinki na fulawa. Daga nan sai ki zuba kifin da kika murmusa ki yanka namanki shima kanana ki zuba, sai ki zuba markadadden kayan miyarki bada yawa ba ki yanka albasa da attarugu, kisa curry, gishiri da magi. Bayan kinyi wannan sai ki zuba mai gwangwani daya ki juya hadinki sosai, sai ki shafa mai a gwangwanayen da kika tanada ki zuzzuba ko ki kulla a leda ki dafa. Idan ya dahu sai a sauke.
5. Alalen kabeji
Abubuwan bukata;
Kabeji
Wake
Hanta
Kwai
Kifi
Attarugu da Albasa
Maggi, Curry da Gishiri
Manja ko Man gyada
Yadda zaki hada;
Da farko zaki surfa Wake gwamgwani hudu ki zuba attarugu da albasa ki bayar a markada miki ko Kuma idan kinada blender mai kyau sai ki nika dashi yayi laushi sosai, sai ki yanka kabejinki kanana mai dan yawa ki zuba akai, ki yanka dafaffen kwai kizuba akai, sai kisa maggi, curry, da gishiri sai ki juya sosai, kisa mai gwangwani daya sai ki kara juyawa ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa. Idan ya dahu sai a sauke ayi serving.
6. Alalen Nama da kwai
Abubuwan bukata;
Kwai
Nama
Hanta
Albasa
Attarugu
Magi da gishiri
Curry
Mai
Yadda zaki hada;
Da farko zaki tafasa nama da hantarki da tafarnuwa da maggi da gishiri, ki yanka namar kanana, sai ki dauko hantarki itama ki daka ta ki hada su guri daya. Sai ki jajjaga albasarki da attarugu ki zuba a kai ki fasa danyen kwai ki zuba akai, kisa maggi, gishiri, curry da mai ki juya sosai yadda zai hade jiki sai ki zuba a leda ko gwangwani ki dafa. Idan ya dahu sai a sauke.
0 Response to "Yadda Ake Alalen doya, Alalen dankali, Alalen plantain, Alalen Fulawa, Alalen kabeji, Alalen Nama da kwai"
Post a Comment