-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE HADA YORGHURT DA WAKEN SOYA

YADDA AKE HADA YORGHURT DA WAKEN SOYA

YADDA AKE HADA YORGHURT DA WAKEN SOYA

Assalamu alaikum, a yau zan koya muku yadda zakuyi yoghurt da waken suya batare da wani wahala ba. 

Abubuwan bukata;

Waken suya

Pure milk flavor

Lux essense milk flavour

Banana powder flavour

Coconut flavour

Suga

Salt

Yadda zaki hada;

Da farko dai zaki Samu waken suya, ki cire datti sannan ki jika kibarshi ya dau tsawon zuwa awa takwas ko fiye da haka. Bayan ya jiku sai ki wanke ki cire tsakuwa  sannan kibayar a markada miki ita a tsaftataccen engine ko kuma kina iya amfani da blender ki nika abunki. Bayan an markadata sai ki sa ruwa iya yawan soya beans dinki a tukunya, Bayan nan sai ki Bari ya tafasa ki dauko markadan ki zuba ruwa a ciki yayi ruwa ruwa Amma ba ruwa sosai ba, sai ki zuba cikin ruwan zafi ki barshi ya tafasa inya Fara tafasowa zai dinga tashi ka fin ya taso ki ta juyawa kina juyawa har ya daina tasowa. Bayan ya daina tasowa kuma ya daina kumfa ki sai ki bari ya kara minti goma Sha biyar sai ki sauke ki Bari ya huce, idan ya huce sai ki tace.

Yadda zaki race;

Da farko zaki samu abin tacewa da roba ki sa abin tacewa cikin roba sai ki zuba yourghurt dinki a ciki sai ki tace. Bayan kin tac sai dauko dusan kisa ruwa kmr litre biyu cikin dusan Sai ki matse. Idan kin gama sai ki rufe yourghurt dinki da marfi da zai rufe ko'ina ki barshi yayi kamar awa goma zuwa goma sha biyar sannan ki bude. Bayan kin bude sai ki dauko ludayi ki bude yourghurt din kamar wuri hudu sai ki barshi zuwa minti biyar Zaki ga ruwa na fitowa sai ki kwashe da ludayin, haka zakiyi ta kwashewa har sai ruwan ya kare, idan kina da mixer kisa kiyi mixing dashi in kuma Baki da shi kiyi amfani da maburgagi ki kada yourghurt dinki yayi laushi sai kisa flavors dinki.

Yadda zaki saka flavours dinki;

Zaki iya samun flavors din yorghurt a wurin masu saida kayan zobo;

Da farko zaki saka pure milk flavor dinki babban cokali 2 a mudu daya sannan a yi mixing, sai ki dauko flavor na biyu shine lux essence milk flavor shikuma ana saka shi babban cokali hudu a mudu daya Shima a yi mixing. Daga nan flavor na uku shine banana powder flavor Shima cokali uku a mudu daya sannan a yi mixing sai coconut flavor sachet uku. Bayan kin saka flavours dinki sai ki dauko suga shima a mudu daya kina iya sa gwangwani takwas ko fiyada Haka yanda dai kikeso sai ki sa gishiri cokali daya, a cikin suga Zaki sa ki hada da gishirin sai ki zuba.

Shikenan yoghurt dinki ya hadu sai serving, asha lpy

1 Response to "YADDA AKE HADA YORGHURT DA WAKEN SOYA"

  1. Jazakallahu bikhair naji dadin bayanin nan, inshallah nasamu sana'a

    ReplyDelete