-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zaman Zawarci

Yadda Ake Zaman Zawarci

Yadda Ake Zaman Zawarci

Dafarko dai menene zawarci

ZAWARCI yana nufin zaman wanda ya taɓa Aure na wani lokaci babu Aure.

A lura cewa ba dukkan Macen da ta zama bazawara shi kenan a rinƙa ganin ta wulaƙantacciya ba, zawarci ba aibi bane, wata ta zama bazawara ce saboda rashin dace da tayi a zamantakewar aure, wata ta auri mijin da bai cancanta ta zauna da shi ba ko a addinance, wata kuwa mijinta ne ya rasu dalilin haka ta zama bazawara, duk da kasancewar akwai gurɓatattu ɓata gari da sunan zawarci hakan bazai sanya duk a rinƙa musu kuɗin goro ba.


Zawarci Yana Da Daci A Zukatan Zawarawa.

A Gidajen Talakawa Kuncin Rayuwar Zawarci Shike Jefa Dayawa Daga Zawarawa Fadawa Cikin Karuwanci Don Nema Ma Kansu Abin Biyan Buqatar Rayuwa.


A Lokacin Da Mace Takasance Bazawara A

Cikin GidanSu Kannenta Zasu Rinqa Yimata

Kallon Hadarin Kaji,

Kuma alokachin damace tazama bazawara awannan lokacin kowane kareda doki sai sufara nemanta dafasiqanci atunaninsu tinda tasan namiji ada zaiwahala ta iya tsallake tayinsu na fasiqanci

Dada ma wasu basutaba zinaba kafin auransu nafarko saibayan fara zawarcinsu

Kuma Ta Samu Incin

Yawo Guri-Guri Domin A Lokacin Ba Kowa Bane Zai Iya Tsawata Mata Ba.

Shin meke kawo fadawa cikin zawarci

1.Rashin Bincike Kafin Aure:

2. Wasu  Mutuwace Ke Yanke

Kaunar.

3.Wasu  Mazanne Masu Auri Saki.

4.Wata Rashin son zama da Kishiya

5.wata matsalar dangin miji ko danginta

Wasu daga ILLAR ZAWARCI

-Rashin kame kai daga Alfasha ga wasu zawaran koda kuwa suna ƴan mata basu taɓa yawon ta zubar ba,hakan yana faruwa ga maza da mata,a inda wasu kuma a lokacin suke sake kamewa saboda tsoron Allah da tsoron faɗawa halaka da kuma gudun zargin Duniya,suyi haquri da halin da suka riski kansu a ciki.

-A wasu gidajan daidai da sabulun wanka ko

 wanki iyaye basa siyawa BAZAWARAR ƴarsu,idan tana da abin yi ko sana'ah ta sharewa kanta hawayen matsalolinta,wata kuma sai dai ta fara Gantali don samun kuɗaɗen shiga idan bata da tsoron Allah sosai

-Gori daga yayyyunta da qannanta wasu harma da iyaye.

-wasu idan wahala ce ta fito dasu daga gidan mazajensu basa son a sake yi musu zancen Aure,sunfi son abarsu su rayu a haka kawai.

Wadannan dama wasu ILLOLIN duk suna cikin rayuwar ZAWARCI.

Ina baku shawara, wallahi kusan waya dace Ku aura, Ku rage buri, ku ringa hangen nesa a rayuwar Aure, Arziki na Allah ne. 

Idan ki Kaga Namiji yana da hankali da abun yi da tausayi, kiyi kokari ku fahimci juna, Ku rufawa kanku asiri kuyi aure. Ku karasa rayuwar ku cikin Aminci da bautar Allah. 

Kunga a wannan lokacin Bazawara mai ‘ya’ya bata auruwa, matukar ba kud’i ne da ita ba, ko mijin ta ya mutu yabar mata dukiya. Ko mahaifinta yana da kud’i ba. 

Amma maganar gaskiya zaman zawarci bashi da dad’i, ko kina da kud’i dole akwai abinda kika rasa, wanda da yawa yake kaisu ga halaka. 

Balle Kuma azo maganar abinda Kuka haifa, wanda koda kin yi auren ba kowanne namiji yake yarda aje masa da agola gida ba. 

Sannan yaran yanzu kana tare da su, ya tarbiyyar su ta kare Balle baka nan.

Allah yasa mudace

0 Response to "Yadda Ake Zaman Zawarci"

Post a Comment