Abubuwanda yadace kiyi lokacinda kike da ciki
Abubuwanda yadace kiyi lokacinda kike da ciki
Daga lokacinda kika samu ciki wato junabiyu yakamata kisani cewa baashan magun guna barkatai kodakuwa faracitimol na saidai in likita yace kisha ,kuma kisani cewa duk wani lemu mai gas saikinbarshi domin kuwa zai iya bararmiki da ciki dakuma duk wani abu maidaci .
saikuma abubuwanda yakamata kici wato abincinki yakasance mae gina jiki abubuwan kuwa sune , lemu, kankana,ayaba,dadai sauran yayan itatuw madara,kwai,kifi dasauran su.
sannan yakamata kidinga zuwa asiti lokaci bayan lokaci domin surika duba lafiyarki da ta
jariri tayadda koda bakida jini kokuma kinada wani ciyo wanda kilake bakisan dashiba, kega tananna zasusan yadda zasu karejaririnki idan cutar wadda zaiiyadaukata,inda zasubaki maganinda zakisha domin kiyaye lafiyarki data jariri sannan kisani magungunanda akabasuwa wajan awoke sunada amfani sosai gareki don karki ajiye, sannan kidinga hadawa da addua kina neman sauki ga Allah.
To daga lokacinda Allah yasa cikinki yakai wata tara to lokacinne zakifara shirin haihuwa idan mijinki maibarin kihaihu asibitina walillahilhamdu kayanda zakije dasu kawai zakitanada.
kayankuwa sune kamar haka:-
1, zannuwa hudu
2,kayan jarairai wayanda maza nasawa mata nasawa(unisef).
3,Roba babba
4,Beby oil
Idankuma bamae bukatar zuwa asibiti bane zaki bukaci harda reza sabuwa dazare bayan wayancen kayan.
Sannan idan lokacin haihuwa yazo wato idan kinacikin halin nakuda anabukatar kikaranta ayatulkursiyu acikin ruwan zam zam kisha sannan kikaranta wannan addua kamar haka:-
_ yahayyu yakayyimu birahamatika astagisu
Lailahaillalahu azimunhalim
Lailahaillalahu rabbussamawati wal'ardi warabul'arshilkarim
Allahumma rahmatika arjun walatakilni ilanafsi darfata aini, waaslihli shanikullalah Lailahailla'anta,
Allahumma lasahala illamajaaltahusahla waanta tajaalalhuzna izashi'ita sahala,Allahu,Allahu, Allahu rabbi laushshirikabihi shaiah,Lailahaillalaha illa'anta subihanaka innikutuminazalumin.
_Bayan kinkaranta wannan addua zaki'iya rokon duk abinda kikeso zaa baki insha Allah.
0 Response to "Abubuwanda yadace kiyi lokacinda kike da ciki"
Post a Comment