Me Yakamata Nayi Lokacinda Nakeda Juna Biyu (Ciki)
Me Yakamata Nayi Lokacinda Nakeda Juna Biyu (Ciki)
Juna Biyu:Da farko dai daga zarar ciki yashiga mace zata samu wasu Alamomi dabatasaba jinsu ba(ma'ana Alamomin juna Biyu kenan): daga Cikin wadannan Alamomin akwai:
1:daukewar jinin al'ada na wata
2:tashin zuciya
3:amai
4:Karin girman nono
5kwadayi
6:yawan fitsari
Da dai sauransu.
Saidai duk abubuwan bazai tabbatar da mace tana dauke da juna Biyu ba face sai tayi gwajin jini ko fitsari. Domin tabbatarwa.
Hanyoyin da mace zatabi domin Zama Cikin koshin lafiya:
Da farko Indai mace tayi ciki yaron da yake cikinta Yana tsukar jinintane saboda shine abincinsa wannan dalilin yasa Mata masu ciki suna Samun Karacin jini a jikinsu,
Shiyasa yakamata mace Mai juna Biyu ta samu nau'in abincin dakeda sinadarin Gina jiki:kamarsu kayan lambu dakuma kayan marmari;
Wake
Kifi
Nama
Kwai da dai sauransu
Dakuma kayan lambu da kayan itatuwa kamarsu:
Kankana
Alayyahu
Cabbage
Zogale
Tuffa(apple)
Lemo da dai sauransu
CIN abinci Mai lafiyayye Yana karawa yaron da ke Cikin kaifin basira da kuma lafiya
Rayuwar yau da kullum na Mai ciki zai banbata Dana sauran jama'a
a:mace Mai juna Biyu Bai kamata tana aikin wahala kodayausheba anfiso tadinga Samun Hutu ko wacce Rana
b:mace Mai juna Biyu in batada lafiya dole taje asibiti gudun kartaje tasha maganin dazai zamar mata matsala kokuma abunda ke cikinta
c:tsaftar muhalli GA Mai juna Biyu yanada muhimmanci domin gudun kamuwa da wasu cututukan
d
:Zuwa awo gamai juna Biyu NADA muhimmanci sosai saboda a lokacin ne za'a gane Yadda kwanciyar yaro yake,Sannan ta hanyar awo ne Ake gano wasu matsalolin kamarsu:
Hawan jini
Ciwon sugar na masu juna Biyu
Kanjamau
Zazzabin cizon sauro
Da dai sauransu.
Sannan motsa jiki:motsa jiki Yana taka muhimmiyar tawa wajen nakuda sosai kuma Yana Hana ciwon Baya da kumburin Kafa,da sauransu,
Ba'aso mace Mai juna Biyu tadinga Saka matsatsun Kaya ajikinta kamar rigar mama da sauransu Sannan yayin motsa jiki Kar a dinga tsayawa wuri guda saboda jini zai iya taruwa ya daskare.
0 Response to "Me Yakamata Nayi Lokacinda Nakeda Juna Biyu (Ciki)"
Post a Comment