-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE ZAMAN BUDURCI (Kashi na biyu)

YADDA AKE ZAMAN BUDURCI (Kashi na biyu)

YADDA AKE ZAMAN BUDURCI (Kashi na biyu)

       Kamar yadda bayani ya gabata gameda saninin minene budurci, da kuma sanin wacece budurwa , yanzu kuma zamu kawo wadansu matakai da kuma hanyoyin kiyaye budurci.

   Hanyoyin da akebi wajen kare martabar budurci sune kamar haka :

1-Rage yawan yin daiyar makoshi( kahkahatu)

2-Rage yawan tsallake-tsallake

3-Rashin saduwa da namiji kafin aure

   Hakika rashin kiyaye wadannan abubuwa shine abinda yake janyo lalacewar budurci, kokuma rasashi gabadaya

2-BUDURCI NA SIFFA

     Lafiyayyar budurwa itace wacce zata zauna gaban iyayenta cikin mutunci har zuwa lokacin aurenta.

    Yana da kyau a lokacin budurci budurwa ta sami cikakkiyar kulawa wajen iyayen ta, ta yadda bazata nemi wani abin bukata ga wani ba. Domin bincike ya nuna cewa aduk lokacin da 'ya mace ta shiga halin budurci to kwadayin ta yana karuwa .

    Saboda haka yazama wajibi ga iyayenta su bata cikakkiyar kulawa, ta bangaren abincinta,suturar ta da kuma kayan tsabtace jiki. Domin tabbas alokacin da 'ya mace ta kai budurwa tanada bukata da wadannan abubuwan da na lissafo

   Akasin hakan kuwa yakan taimaka wajen tabarbarewar budurcin ta na jikinta dakuma tafiyar da kimarta a matsayin budurwa.

0 Response to "YADDA AKE ZAMAN BUDURCI (Kashi na biyu)"

Post a Comment