-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zama Da Attajirin Miji

Yadda Ake Zama Da Attajirin Miji

Yadda Ake Zama Da Attajirin Miji

Zama da Attajirin Miji yanada matukar Dadi sosai saboda Zaki samu duk biyan bukata ta bangaren rayuwa game da kudi har dai idan ya kasance mai bayarwa wane a koda yaushe abin nufi a nan shine wato hannunshi a bude yake kowane lokaci domin kuwa sometimes akan samu mijin da gashi da dukiyar Amma iyalansa suna neman kudin da zasuyi lalurorinsu sun rasa saboda baya bayarwa ko cikin attajiran kala kala ne akwai wanda ke bayarwa akwai wanda baya bayarwa. 

Idan akace mutum attajiri ne ana nufin Allah ya azurtashi da dukiya mai tarin yawa wanda kuma idan bai sa tunaninsa ba na sanin Yanda yakamata yayi da ita zata kaishi ga fadawa halaka kuma tayi sanadiyar shigarsa wuta gobe kiyama. Idan Allah ya baka dukiya bawai zaka dinga kashe kudi bane anyhow Yanda kaga dama aa zaka dubi hanyoyi mafi amfanuwa da inganci gareka da kuma alumma baki daya sai ka sarrafa su ta hanyar da ya dace.

Uwargida idan Allah ya baki miji attajiri ki zauna ki nutsu kici arziki keda 'yayanki sannan kuma ki dorashi akan hanyar da zai kashe dukiyar domin samun tsira gobe kiyama  domin Allah ne ya bashi kuma a ranar lahira zai yi bayani a gaban ubangiji da naira daya daya a duk hanyar da ya kashe su don haka ki jajirce ki kulaa sosai wajen ganin cewa bai bata dukiyarshi ta hanya Mara kyau ba. Ke kuma uwargida bawai dan Allah yabashi dukiya ba kuma Yana baki a koda yaushe Zaki dinga karba b moderate dai so that bazai ga kin cika bani bani ba a koda yaushe domin shi namiji koda yanada shi bayason kullum ace ya bada kedai kawai ki dinga yin irin kisisinar mu irin ta mata hankalinsa ya dawo kanki tor ina tabbatar miki Zaki samu kome kikeso batare da ma kin tambaya ba sannan kada ki ji haushi ko ki nuna bacin ranki idan ya dauki kudi ya bawa wani ko yayi kyauta da wani abu ki nuna masa farincikin ki nayin hakan ki zamanto mai karfafa masa guiwa wajen kyautatawa mutane da kuma yan uwansa.

Watarana zakiga ya dauki kudi masu yawa ko wani abu mai tsada ya bawa yan uwansa ko kuma mahaifiyarsa to kada kiji haushi ko ki nuna masa bakiji Dadi b domin akwai matan dake hakanan su ji takaicin abunda miji ke yiwa yan uwansa wanda haksn bai dace b to idan bai yi musu b tunda yanadashi wa zai yi musu ki tuna fa babu wanda yakaiki keda yayanki cin arzikin shi to don ya dibi wani abu daga ciki ya bawa yan uwanshi menene aciki  kafin suci guda sai kin ci goma ko fiye keda yaranki so anaso ki godewa Allah sai Allah ya kara miki ki zamanto mai Kulawa da dukiyarsa da yayansa idan bayanan koma yananan din kuma kina mai masa addua a koda yaushe dacewa Allah ya sakawa dukiyarsa albarka domin idan b albarka aciki tamkar shara ce da batada amfani. Ki Zama mai rike amana da gaskiya a koda yaushe kuma kada ya ajiye kudi ki dauka ko ki taba bai baki ba a tunaninki ke ai kudin sunada yawa ko kin diba bazai gane ba idan bai baki ba kinci haram kuma ki tuna idan baya ganinki Allah Yana ganin ki ...da zarar kin sa wadatar zuci tor Zaki zauna lafiya qalau keda Mijinki kuma ki samu biyan bukata a koda yaushe ki zamo mai nuna masa soyayya da qauna a koda yaushe sai kuji dadin rayuwa kuda yaranku.

Idan ki bi wadannan hanyoyin haka ne zaki zauna da Attajirin mijinki lafiya qalau ba fargaba kuma kici arziki ki more keda iyalinki da yan uwanki kowa zai amfana...sannan idan kinga akwai abubuwan da yadace yayi na taimakon alumma ko yan uwansa baiyi ba saiki zaunar dashi cikin sanyi ki bashi shawara  dacewa ai yakamata ayi kazaa baayi ba shine nace ko manta kayi shine nake tunamaka ko kuma ai wane ya can canci ayi mishi wani abu ko abashi wani abu irin ku fahimci juna hakan zaisa ya kara sonki kuma ya kyautata miki akan irin shawarwari da kike bashi da kuma Kulawa dakike da shi da kuma danginsa.

Zama da Attajirin miji duniya ce uwar gida Zaki gane hakan kadai idan kin san abunda ya kamata kuma kuma kinada ilimi na addini dana zamani kuma idan  kinbi abunda Allah da manzonsa sukace shikenan kin kwashe komai shi Zama da zarar ka saka Allah aciki shikenan ka gama komai kuma kisa a ranki duk abunda zakiyi domin Allah kikeyi kuma da neman aljannarki sai kiji dadin zama

Allah yasa mu dace amen

0 Response to "Yadda Ake Zama Da Attajirin Miji"

Post a Comment