-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Ya Ake Zama da Kishiya 2023

Ya Ake Zama da Kishiya 2023

Ya Ake Zama da Kishiya 2023

   Kishi wata halitta ce da Allah ya halitta acikin zukatan bani Adam, Mata da maza.

   Sai kuma Allah (s w t) ya bawa maxa cikakkiyar dama da zasu hada mata har guda hudu duk da kishin da ya halitta musu.

   A matsayinki na mace musulma  kishinki bazai hana mijinki kara aure ba, domin wannan umarnin Allah ne kuma sunnar ma'aiki ne.

    Saboda haka kiyi riko da wadannan shawari da zan baki a matsayinki na uwar gida, don samun saukin zamantakewa da salama tareda kishiyarki .

     Shawarin sune kamar haka:

 1-kokarin mallake mijinki, ta hanyar rubanya kyautatawarki gareshi fiye da yadda kikeyi a baya.

2-ki dauketa abokiyar shawara idan zakiyi wani abinda ya shafi rayuwarki, wannan ba karamin tasiri yakeda shi ba a wajen mallake kishiyarki da sauki.

3- Kada ki kuskura kibari tasan abubuwanda suke bata miki rayuwa (Jan girma)

4- Kada ki shiga hakkinta ko ta wace hanya.

5- Ki yawaita kudurtawa azuciyarki cewa auren da kikeyi fa ibada ne, kuma hanya ce ta tsira gobe kiyama idan har keyi kokarin kiyaye haqqokin da suke wuyanki.

6-Kiyi mata marhaban da kuma sake mata fuska a farkon haduwarku, tayadda koda an samu wata matsala baza'a zargeki bah.

7-Ki kware wajen iya girki, iya saka sutura da kuma tsabtar jiki da mihalli, ta yadda kishiyarki zata dauki darasi a wurinki.

8- Ki akidance a zuciyarki cewa mijinki kike aure ba kishiyarki ba

 Hakika wannan na daga cikin manyan abubuwan da ke janyo zaman kishi mai dadi.

Wannan kadan kenan daga cikin abubuwan da ke sa uwargida ta iya zama da kishiyarta lafiya da ikon Allah.

Da fatar Allah ya nuna muna daidai yakuma bamu ikon bin daidai.

0 Response to "Ya Ake Zama da Kishiya 2023"

Post a Comment