-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Ban Dariya a Soyayya

Kalaman Ban Dariya a Soyayya

Kalaman Ban Dariya a Soyayya

Duk sarakunan mata dake mulkin zuciyoyin masoya babu wata zuciya da ta kai tawa samun sarauniya mai adalci kamar ki. kece ruhina, kin zamto farin cikin raina

A kullum bani da burin sauraren wani zance in ba naka ba Zamo na kowa koda kowa bai zamo naka ba. Yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yima fatan sharri, saka dukkanin musulmi acikin addu arka koda babu mai sakaka acikin addu`arsa.

Nufi kowa da alheri koda akwai masu nufarka da sharri. kyautata tsakaninka da Allah kada kadamu da abinda mutane suke cewa akanka. Allah ya kyautata rayuwarmu Amin

Asali zuciyar mace kyakkyawa ce, nagartacciya, wadda babu komai a cikin ta sai haske tare da kyautatawa ga dukkan wanda ya shigo rayuwar ta, bata san cin amana ko ha'inci gami da yaudara ba,

Idan har kaga zuciyar mace ta rikide daga asalinta na kyawu da nagarta zuwa gurbatacciyar da take ha'intar dukkan wanda ya shigo rayuwar ta, to ka duba farkon lamarin, zaka samu namiji ne ya jagoranceta zuwa ga gurbacewa, amman zuciyar mace bata tab'a gurbacewa ba tare da sanya hannun namiji ba.

Kowa ne dare nakan koma gida ina kuka saboda nasan bazan kara ganin kiba har sai gobe Shin rana ce ta fito ko murmushin kine?

Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya, ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dad’i. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.

KUZO MU YABI UBANGIJI! Ya zama wajibi mu bude safiyarmu da fara salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, muyi Tasbihi da Hamdala a wajen gwani wajen iya tsara halitta, gwanin da idan ka kalli halittarsa sai ka rasa ta wanne wuri zaka fara yabo a gareshi, saboda yakai makura wajen kagar halittar da kyawunta ke d'aukar hankalin duk wani me lafiyayyen tunani da idanun gani!

Tabbas Gwanina Allahu, shine Allahu, shine me halittar akwai daga babu, ya samar da kyawu a inda babu shi, ya samar da nagarta a wurin da babu ita, ya samar da daukaka a cikin makaskanta, ya saukar da baiwarsa ta kamala da cikar haiba tare da zunzurutun Kyau akan wanda ya zaba a cikin halitta.

Kyakykyawar zuciyar kice ta bayyana kyawawan halayyar ki, wadanda suke sakamin cikakkiyar nutsuwa a cikin ruhina Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare.

Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki. kasantuwar mu a raye cikin ruhi guda d’aya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna.

Komai na mu ya kasance yana faruwa ne a lokaci guda hatta ba’kin ciki da kuma farin-ciki, wato ruhi d`aya gangar jiki kuma biyu. Farin cikin ki shi ne nawa, ina son ki.

Tabbas Ubangijina ya cancanci yabo ta kowacce fuska, bayan ni'imar rayuwa da ta lafiya da yayi mana, sai kuma ya kara mana da baiwar kasantuwar sanyin idanun mu a cikinmu, wadda muke kalla muji nutsuwa ta sauka a jikinmu, muji tabbas muma wasu mutane ne masu daraja, saboda kasantuwar me daraja a cikin mu.

Barka da kasancewa cikin wannan rana masoyiyata. Dukanin rayuwata na karanta, nayi Mafarkinta, na jirata, nayi kuka don ita,

yanzu haka na gano kece kadai abar kaunata. Tun farkon haduwata dake zuciya ta aminta dake a matsayin mai debe mata kewa. Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.

Nasan burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana. Ina son ki fiye da zinariya.

Wa kafi ƙauna? na ce, wannan da ta ɗauke ni wata tara a cikinta, ta haife ni tana farin ciki, sa'annan ta kyautata tarbiyata....Wannan ita ce soyayya ta har abada, ba ta tsufa balle ta mutu!

Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyoyi masu d’auke da tsintsaye.

Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki. Masoyi k`aine wanda zuciya ta ta aminta da shi.

Ina son ka kara sani cewa babu wani da namiji wanda zuciyata ta gama aminta da dukkan soyayyar sa face kai.

Wandara; itace Ruhin da ta rike Zuciya ta. ❤️ Tsakanin abinda aka furta sannan ba a nuface shi ba, da kuma abinda aka nuface shi sannan ba a furta shi ba. Da yawan soyayya suka ɓace.

Ina Son Ki, ba da Zuciyata ba kuma ba da tunanina ba. Zuciya za ta daina aiki, tunani zai mance. Ina Son Ki da Ruhina ne, saboda Ruhi bai daina aiki, kuma ba ya mantuwa.

Kyakykyawar Zuciya tana rayuwa ne a karkashin inuwar Aminci da Amincewa,

Zuciyar da aka cudanyata da tsarkakakkiyar soyayya tana samar da ingantacciyar lafiya a gangar jikin mamallakin ta shaukinta yakan bi sassan jini dana ruwa domin cigaba da ginin gangar jiki mai`inganci so kalmar datafi komai dadin fade da saurare

shike haifar da zaman lafiya a kowane karni. Keba zinariya ba, keba luuluu ba, ke ba a zurfa ba, amma dukkanin su kinfi su kyau

Ni ne masoyin son ki, wanda ba ya da wani aiki sai wannan, domin ban mallaki komai ba, sai sahalewar ki. Bana neman wata Zuciya, sai ta ki, ina hanzarin zuwa gare ki. Ba na jin ƙamshin wani fure sai na lambunki. Teku ya harɗe da ɗigon ruwa, wa zai iya bambance shi? *

A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba.

Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba. Masoyiyata ina neman alfarmar da ki mallaka min zuciyar ki,

na dad’e da mallaka miki tawa lokuta masu yawa da suka shud’e abokai ma shaida ne, bayan ya kasance kin mallaka min ita ni kuma zan had’a su na d’aure su waje guda da sarkar soyayya mai ‘karfi na jefa makullin a cikin tekun maliya. Ki amince ina son ki wannan shi ne burina. Ki huta lafiya.

Masoyiya ta a duk lokacin da naji muryar ki nakan samu natsuwa a zuciya ta,

Murmushin ki a gare ni yafi aban kyautar duniya, Fiskar ki a kullum haske take kara yi musamman idan kina murmushi,

Idan kikai fushi sannan ne kike dada kara kyan gani. Amincin Allah ya tabbata a gareka masoyina, hasken idaniya na kanyi farin ciki matukar ina tare kai, na kan mata da dukkan wani damuwar nake ciki idan ina tare dakai, barka da safiya

Nabaki rayuwa ta yadda kema kika bani rayuwarki Sautin muryar ki yana sanya ya mini raina, mu kwana lafiya

3 Responses to "Kalaman Ban Dariya a Soyayya"