-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sakonnin Soyayya Masu Janyo Ra'ayin Budurwa

Sakonnin Soyayya Masu Janyo Ra'ayin Budurwa

Sakonnin Soyayya Masu Janyo Ra'ayin Budurwa

Idan Na Tuna Dake a gareni Kin Xarce Lailah Da Ashwarya a Fagen Iya Tsara Kwalliya Da Kyawun Fasali Sakamakon Kin Xamo Tamkar Gajimare Saboda Tsawon Gashinki Har Izuwa Gadon

Baya. Amincin allah yatabbta agareki hadaddiya hamshakiyar sanssanyar iska wacce take busawa a sararin samaniya maidauke da kamshin furanni tareda fatan kina lpy Inaso namiki gaisuwa tsaftacciya kuma tabbatacciya zuwaga mace  ingantacce kamarki. 

Dunbin soyayya da aminci da yarda da murna da farin ciki marasa karewa agareki mace daya tamkar dubu,hakika kece wanda nabawa mulkin zuciyata kece wanda 6acin ranki ke girgizani kuma kece wanda hawayanki kan zamto tamkar ruwan zafi agareni.

musamman lokacinda naji wani wadda kikeso yayi fatali dake nasan kinsha kuka,hakan yasa zuciyata tamkar garwashi acikinta. 

Sannan ina mika shimfidaddadiyar murnata mai dauke da dauwamammiyar kauna tareda goyon baya cikin soyayyarmu.

Ya wanda sautin muryarta take rikitar dani takuma gigitani saboda tsananin ƙaunarki danake mai sona. Ina so infadamiki irin ribar danaci sakamakon haduwa ta

dake Bari nadakata anan domin naga kamar ranki bayaso Dan kinsan naki jinin 6acin Ranki. zan rikeki amana bazan yada keba har abada inshaallah.  

Naturo maki sakon gaisuwane kafin muyi waya,kuma ina mai jaddadamaki cewa ina alfahari dake abin kaunata.

QALBI NA Samun ki a rayuwata ya bani k’warin guiwar tunkarar matsalata da samun nasara a kan dukkan abun da na sa a gaba. 

Kulawarki a kaina na k’ara min jarumta, soyayyarki a gare ni na sanyawa na ji ni a matsayin cikakken mutum. Nagode mosoyiyata, ina alfahari da samun ki a rayuwata.

A gare ki nake samun bargo, a dukkan lokacin da sanyi ya  rufe ni. Ina samun tsaro, a dukkan lokacin da hatsari ya tinkaro ni Ina samun farin ciki, a dukkan lokacin da damuwa ta lilliɓe ni fatana da burina mu mutu tare mu tashi tare mu rayu tare a gidan Aljanna ina Son Ki Mai sona Fiye Da Yadda Nake Son Kaina.

1 Response to "Sakonnin Soyayya Masu Janyo Ra'ayin Budurwa"