-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sakonnin Soyayya Masu Daɗi Da Sanyaya Zuciya

Sakonnin Soyayya Masu Daɗi Da Sanyaya Zuciya

Sakonnin Soyayya Masu Daɗi Da Sanyaya Zuciya

Na ilmantu da kyawawan dabi'u irin naki shiyasa na himmantu wajan gyara zama acikin kaunarki.  

Gabi gabanki yar gata karkive dani kin fasa domin idan jikina ya dauka to tabbas zuciyata bazata jure bah Nida naki ne harkullum kauna agareki  babu ranar fashi koda hakan zai zamo karshen numfashi na. 

Taya zan rayu batare dake bah akwai amana tsakanin ruhi da soyayyarki shiyasa komai na rayuwata na sallama miki

Ban tsinci kaina cikin wata sabuwar dauniya bah saida nafara tozali da kyakkyawar fuskarki ma abociyar annuri da murmushi mai laushi. 

Hakika kinada tsanani kwarjini a idanuna shiyasa ban iya zama da tunanin kowace mace a raina inba keba "Xuciyar Da Kika Dauke Mata Duk wani Sansanin Soyayya a Cikinta Itace Take Neman Agaji Da Tallafin Rikon Gaskiya Da Amana a Gareki.

"IYakar Mallakin Matsayi kin Cancanta Da Mallakarsa a Gareni Domin Kin Xame Min Tamkar Mashahurin Hasken Dake Kore Min Duhun Cikin lungu Da SaQon Xuciyata.

 "Babu Dana Sani Ko Nadama a Duk Lokacinda Na Rusuna a Gareki Sakamakon Kece Sarauniya Mai Martaba  Wadda Ke Taka Rawar Gani A Cikin Babban Birnin Xuciyata.

"Kasancewarki Tare Dani Tamkar Ina Cikin Inuwar Dake Bakin Qorama Ne Da Itace Da Korayen Ciyayi, Rashinki Kuma a Gareni Tamkar Ina Cikin Inuwar Gawo Ne a Lokacin Rani Da Iskar Bazara.

 "Lallai Xuciya Ta Mace Akan So Da Qaunar Da Babu Hadi a Cikinta Kuma Kece Sanadi Yayinda Kika Janye Ra'ayina Ta Hanyar Hasken Kwalliyarki Da Murmushin Soyayya. "Wajibine Xuciyata Tayi Alfahari Da Kanta Matsayin Mai Cikakken  "Yancin Da Bashi Da Iyaka,

Tunda Ta Samu Mafakar Da Xata  Yi Walwala a Cikin Taki Xuciyar. Dare Da Rana Farin Ciki Yana Qara Wanzuwa a Tare Dani Sakamakon Samun Damar Mallakar Sarauniya Irinki Ba Qaramar Gagarumar Nasarace Bace Ga Kowanne Masoyin Duniyah.

 "Tunda Har Kika Xamanto Sinadarin Farin Cikina To Ki Rikeni Na Xama Naki Mallakinki Domin Babu Mai Sauya Min Ra'ayina Akan So Da Qaunar Da Xuciyata Take Miki.

Kallonki Shine Muradin Idaniyar Da ta Samu Haske a Lokacinda Xuciya tayi Arba Da Soyayyarki Kece Jinin Jikina Domin Soyayyarki. Tana Xagayawa a Cikin Jini Da 6argon Jiki Shiyasa Farin Ciki Da Kuzari Suke.

 Qara Wanzuwa a Tare Dani Ina Alfahari Dake   Sarauniyar Dake Dauke Damuwa Da Tunanin Xuciyata. Sakamakon Na Kasance Gasgatacce Kuma Amintacce ga Kyakkyawar Zuciyarki.

Farashin So Da Qaunarki Ne Yake Qara Hauhawa a Kasuwar Xuciyata Dan ina da Tabbacin SOyayyarki.

 Annashuwace Da Kwanciyar Hankali a gareni Xuciyarki Farace Da Alkunya Akan Fuskarki Sakamakon Duniyar Nan  Kece Tauraruwar Da Nake Kallo a Matsayin kyakkyawa Nasani Cewa Ma'abocin Haske a Xuciyata Shine Sonki, Domin Shine Madubi Kuma Sinadarin Jindadina.

0 Response to "Sakonnin Soyayya Masu Daɗi Da Sanyaya Zuciya"

Post a Comment