-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sakonnin Soyayya Masu Saka Kauna Tsakanin Masoya

Sakonnin Soyayya Masu Saka Kauna Tsakanin Masoya

Sakonnin Soyayya Masu Saka Kauna Tsakanin Masoya

Ina son ki kuma zan cigaba da son ki na tsawon rayuwata mai sona. Ni da ke tamkar k’ashi ne mai k’warin da bana fatan ganin ranar da zai yi targaɗe balle har ya kai ga ya karye. 

Ina Son Ki. Daga cikin biliyoyi da Miliyoyin yammata na zaɓo ɗaya tamkar da dubu. Tabbas na yi nasara na samun ki a matsayin mosoyiyata abun alfaharina. A tsawon lokacin da zan rayu ina numfashi, ina son ki so mara iyaka.

saƙon murmushi zuwa ga wacce zuciyata keda burin mallaka akoda yaushe, saƙon farin ciki nake isarwa zuwa ga wacce dake da isa mafi isa daga cikin masu isa afadar zuciyata, me kyau nakasa misalta irin yanda nakejin sonki acikin jijiyar dake aika jini dukkan sassan jikinah,  a kowane lokaci da kowani yanayi kece abar tinanin kwakwalwata, me kyau soyayarki daɗa ƙaruwa take akowanni sa'a na agogo, kin kasance wani bangare daga cikin jikina wanda yafi komai muhimmanci shiyasa baki da tamka ackinta, na mallaka miki zuciyata da dukkan soyayyata domin kece wacce kikapi chanchanta dana mallakawa, ina mutukar alfahari dake, kuma ina fatan zaki kuladani kuma kikulaman da kanki sarauniyata,  

Dear Hubbina kisanar da zuciyar ki cewa ina gaisheta, sannan ki sanar da ita cewa a ko yaushe bani da burin da yawuce na ƙosar da ita da kalamai waɗanda zasu ratsa duk jiki da jinin jikin ki. 

domin ki samu tabbaci kuma kiji a jikin ki cewa kina dani a duniyar masoya abar kaunata, zuciyata takamu da kaunarki matuka masoyiyata. 

Ana gane kyawun shuka ne idan har an gama ta da taki Tayaya za a gane sama idan har babu ‘kasa? Kamar haka ne, farin-cikina zai yi wuyar bayyanuwa matu’kar ba ma tare da juna. 

Na kan shiga damuwa a dukkan lokacin da na duba gefena ban gan ki ba. Yau rana ce ta farin-ciki gare ni da kuma ke da sauran danginmu.

abar qaunata, tauraruwar dake haskakamin zuciya ta,ina Alfahari dake dare ko rana Sonki ba zaitaba gushewa azuciyata ba.Ganinki cikin farin ciki shine burina,kasan cewar ki cikin annushuwa shine fatana. Dawwamar sonki azuciyata shine roqon danake har kullum agurin Allah (S.W.A).

Aduniyar masoya kinciri tuta domin kece kadai kike da hasken idaniya annurin fuska dakuma sautin murya mai dadin saurara. Zuciyata tana tare dake sarauniyar mata ma'abociyar soyayya Wacce Sonta ya zama tamkar jinin ji kina, tunanin ki yazama abokin rayuwata. 

Tabbas da da abin da yafi Kalmar so da qauna dasu zanfada agareki,soyayya rmu dake wata baiwace daga Allah kuma ni'imace agaremu.

0 Response to "Sakonnin Soyayya Masu Saka Kauna Tsakanin Masoya"

Post a Comment