-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Ɗaukan Malaman Makaranta Aiki: Hukumar Kula Da Malamai Ta Jihar Gombe Ta Fara Gudanar Da Jarrabawa Ga Masu Sha'awar Aikin Koyarwa

Ɗaukan Malaman Makaranta Aiki: Hukumar Kula Da Malamai Ta Jihar Gombe Ta Fara Gudanar Da Jarrabawa Ga Masu Sha'awar Aikin Koyarwa

Ɗaukan Malaman Makaranta Aiki: Hukumar Kula Da Malamai Ta Jihar Gombe Ta Fara Gudanar Da Jarrabawa Ga Masu Sha'awar Aikin Koyarwa

Hukumar Kula Da Malamai Ta Jihar Gombe TSC, ta fara gudanar da jarrabawar gwaji ga masu sha'awar aikin koyarwa kimanin dubu biyar don ɗaukar malamai dubu ɗaya  waɗanda suka yi nasarar jarrabawar a matsayin sabin malamai, bayan da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da hakan.

A cewar shugabar hukumar ta TSC Mrs. Na'omi Philip Maiguwa, jarrabawar wacce ake yi ta na'ura mai ƙwaƙwalwa a Jami'a Mallakar Jiha (GSU) za a shafe kwanaki biyar ne ana yin ta, daga ranar Litinin 25 zuwa Juma'a 29 ga wannan wata.

Tace dole ne masu rubuta jarrabawar daga ƙananan hukumomin jihar 11 su gabatar da fom ɗin su na neman aikin da suka cika ta yanar gizo, da shaidar kammala digiri dana hidimar ƙasa wato certificates na digiri da NYSC da kuma shaidar zama ƴan asalin kananan hukumomin jihar kafin a basu damar rubuta jarrabawar. An kuma yi tanadi na musamman ga masu buƙata ta musamman wato naƙasassu.

Idan za a iya tunawa dai, a watan Afirilun wannar shekara ce Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Maje Gombe), ya umarci hukumar kula da malaman ta jihar ta ci gaba da shirye-shiryen ɗaukan sabin malaman wadda aka faro tun watan Janairun bana, don ɗaukar sabin malamai dubu ɗaya da sauyawa wassu 288 wuraren aiki daga Hukumar Samar Da Ilimin Bai Ɗaya Daga Tushe Ta Jiha SUBEB zuwa manyan makarantun sakandare da kolejojin fasaha na jihar. Tun watan Yunin daya gabata ne dai hukumar ta kammala sauya guraben aikin wa waɗannan malamai ya zuwa ma'aikatar ilimi don maida hankali ga ɗaukan sabin malaman dubu ɗaya.

Tace "Abun farin ciki ne ganin yadda mai girma gwamna bisa karimci da hangen nesan sa, a farkon watan Yulin nan ya bawa hukumar mu ta TSC umarnin ta ƙarƙare aikin ɗaukan sabin malaman dubu ɗaya data faro".

Mrs Maiguwa sai ta bayyana kwarin gwiwar cewa kafin fara sabon zangon shekarar karatu ta gaba, duk sabin malaman da waɗanda aka sauyawa guraben

0 Response to "Ɗaukan Malaman Makaranta Aiki: Hukumar Kula Da Malamai Ta Jihar Gombe Ta Fara Gudanar Da Jarrabawa Ga Masu Sha'awar Aikin Koyarwa"

Post a Comment