-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Zaki/Zaka Dawo Soyayya Da Tsohuwar Budurwarka/Saurayinki

Yadda Zaki/Zaka Dawo Soyayya Da Tsohuwar Budurwarka/Saurayinki

Yadda Zaki/Zaka Dawo Soyayya Da Tsohuwar Budurwarka/Saurayinki

Wasu mazan suna rabuwa da wacce suke so ne ba domin ransu naso ba sai domin yadda masoyiyar tasa take masa.

Akwai 'yan matan da a koyaushe hankalinsu na wajen namijin da ba aurensu zai yi ba. Sai sun wulakanta mai sonsu na gaskiya sai kuma wannan da suke so ya ware. Daga bisani kuma su soma kame kame na neman wannan ya dawo.

Ga wasu matakan da zaki dauka bayan kinyi kuskuren koran mai sonki na gaskiya.

1: Ki Daurewa Zuciyar Ki Abunda Zaki Ji Ko Zaki Gani Wajen Dawo Da Soyayyar Ki Dashi.

2 : Kada Ki Soma Nuna Masa Bukatar Ki Kai Tsaye Da Farko.

3: Nuna Masa Ba Wai Dole Sai Kun Dawo Kaman Da Ba.

4: Soma Da Tura Masa Sakonnin Gaisuwa Amma Ba Kullum Ba.

5: Nemi Lokacin Da Zaki Iya Ganinsa Kuyi Magana. Amma Kada Ki Takura.

6: Ya Fahimci Cewa Ba A Son Ranki Abunda Ya Faru Ya Faru Ba Samo Wata Karyar Da Zaki Fadamasa Koda Ba Gamsuwa Zai Yi Na Abunda Ya Faru A Baya.

7: Tuna Masa Yadda Kika Nuna Masa So Da Kauna A Baya. Wanda Zai Yi Wuya Ki Cireshi A Ranki.

8: Tuna Masa Alkawuran Da Kuka Yiwa Juna Masu Mahimmanci A Baya.

9: Sanar Dashi Gaskiyar Yadda Kike Ji Tun Bayan Da Kika Gane Kuskurenki.

10: Jawo Hankalinsa Akan Mahimmancin Yafewa Mutumin Da Ya Gane Kurensa Ya Kuma Nemi Tuba.

Duk kuwa da ya danganta ne da yanayin da kuka rabu. Amma shi namiji a inda ya bambamta da mace shine bai kafewa akan kin yarda da sulhu muddin dai akwai soyayyar wanan macen a ransa.

Da farko zai iya miki tutsu akan bukatar taki. Amma da zaran ya fahimci kinyi nadama kuma wata bata maye gurbinki ba, zai sake baki dama.

0 Response to "Yadda Zaki/Zaka Dawo Soyayya Da Tsohuwar Budurwarka/Saurayinki"

Post a Comment