-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

LABARI MAI DAƊI: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shirin Tallafin Koyon Sana'o'i Kyauta Ga 'Yan Najeriya Miliyan 10 (Free Upskilling 2026)

LABARI MAI DAƊI: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shirin Tallafin Koyon Sana'o'i Kyauta Ga 'Yan Najeriya Miliyan 10 (Free Upskilling 2026)

LABARI MAI DAƊI: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shirin Tallafin Koyon Sana'o'i Kyauta Ga 'Yan Najeriya Miliyan 10 (Free Upskilling 2026)

Daga Taskar HaskeNews

Wata gagarumar dama ta sake kunno kai ga matasa da mata a faɗin Najeriya domin su samu kwarewa a sana’o’in zamani da za su ba su damar dogaro da kansu. Gwamnatin Tarayya, ƙarkashin ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, ta ƙaddamar da shirin "Free Upskilling Programme 2026".

Wannan shiri yana nufin horar da mutane miliyan goma (10 Million) a fannoni daban-daban domin rage raɗadin rashin aiki da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar fasaha da sana'o'in hannu.

Fannonin Da Za A Bayar Da Horon:
Masu sha'awa za su iya zaɓar koyon sana'a a waɗannan fannoni:

  • Fasahar Zamani (Digital Skills): Computer, Coding, da sauran su.

  • Kasuwanci (Business & Entrepreneurship): Yadda ake gudanar da sana'o'i.

  • Sana'o'in Hannu (Trades & Engineering): Kanikanci, walda, da gyaran injina.

  • Kiwon Lafiya (Healthcare): Ilimin kiwon lafiya da kula da kai.

  • Zane-zane (Creative Arts & Design): Fashion design da sauran fasahohi.

Waɗanda Za Su Iya Nema?
Wannan shiri na kowa ne, ciki har da:

  • Ɗalibai da waɗanda suka kammala karatu (Graduates).

  • Masu neman aiki (Job seekers).

  • Mata masu zaman gida (Homemakers).

  • Ma'aikata da masu sana'o'in hannu (Artisans).

Fa'idodin Shirin:

  1. Kyauta Ne: Ba za ka biya ko sisi ba, gwamnati ce za ta ɗauki nauyin komai.

  2. Koyon A Wayar Hannu: Za ka iya yin karatun ta wayarka cikin sauƙi.

  3. Takardar Shaida (Certificate): Bayan ka kammala, za a ba ka takardar shaida da duniya ta amince da ita.

  4. Kwarewa: Za ka samu dabarun da za su taimaka maka wajen samun kuɗi ko samun aiki.

Abubuwan Da Ake Buƙata Wajen Cikewa:
Yayin da kake cike fom ɗin a dandalin WAWUAfrica, za a buƙaci waɗannan:

  • Cikakken suna da shekaru.

  • Lambar NIN ko BVN (Domin tantancewa).

  • Bayanan karatu da irin burin da kake da shi.

  • Dora hoton shaidar kanka (ID Card).

Yadda Za A Cike (Method of Application):
Idan kana da sha’awar shiga wannan shiri na Gwamnatin Tarayya, danna mahadar (link) dake ƙasa domin fara rijista kai tsaye:

👉 Danna Nan Domin Cikewa: https://wawuafrica.com/onboarding

Muhimmi:
Ka tabbata bayanan da za ka bayar sun dace da waɗanda ke jikin takardunka na hukuma (NIN ko BVN). Wannan babbar dama ce da bai kamata ta wuce ka ba.

Hanzarta cike naka yanzu, sannan ka tura wa 'yan uwa da abokai domin kowa ya amfana!

0 Response to "LABARI MAI DAƊI: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shirin Tallafin Koyon Sana'o'i Kyauta Ga 'Yan Najeriya Miliyan 10 (Free Upskilling 2026)"

Post a Comment