Kalaman Soyayya Ayau
Kalaman Soyayya Ayau
Kyan Alqawari Cikawa masoya ga na biyun na kawo muk
Bari kaji yadda abin yake........
A matakin farko kana bukatar ka san abinda yake burge 'yan mata da kuma abinda suke so tukuna....... Ah' ah ha ! Kwantar da hankalin ka kaji mana ! Kaa ga! duk ba maganar kokarin ka a makaranta bane, ko sai Mahaifin ka ya zama wani sannan a soka.
Wohoho ! Dadina da kai gajen hakuri ! Nace maka ba sai kayi quru ka sayi Mashin ko Mota ba.To waima bari in tambaye ka. Gayu nawa kasha gani basu da ko sisi amma 'yan mata sun makale musu????? Ah toh! Ka ganima ko! Ai na fada maka babu mummuna a Maza !!! Bari kaji sirrin ...
Abinda zakayi tashin farko da ka hangeta shine ... Amma kafin ka tunkare ta ya kamata kasan wadannan sharuddan kamar haka:
Mace bata son matsoraci ko wanda ya cika fariya ko mai girman kai.
Mata basa son namiji mai yanga duk sai yabi ya gundure ta , ah ' eh mana ,kana yanga tana yanga me kenan akayi?
Mace tafi son wanda baya jin kunyar fada mata duk wani motsin sonta dake zuciyar sa.
Mata basa son hauragiya da harigido, saboda haka ka natsu ka fuskance ta, a yayin da kake bayyana ra'ayinka gareta.
Mace tana son namijin da yasan darajar mata, kaga kenan kar ka kuskura ka bata labarin cewa wai mata dayawa suna sonka amma ka wulakanta su saboda ita da zarar taji haka to kashin ka ya bushe (k'amas ma kuwa) koda ta amsa tana sonka kuwa.
Sannan kar kaje kai tsaye kace ''INA SONKI'' a karon farko eh mana, ai sai ka firgitata, ana bukatar abinnan da turawa suke kira 'Introduction' kaga zaka tanadi wasu bayanai kenan amma fa masu ma'ana, wad'anda suka dace da ita, domin ba sakin baki zakayi ka rinka zuba kamar kanyar ba, kana wani soki burutsu ba.
Kuma ka nuna mata kasan darajar kanka ,don haka kar ka kuskura ka rok'e ta wai.... ta soka ai sai ta rainaka ta raina wayonka ko kuma ta ja maka aji sosai kafin...... Hmm... idan kaci sa'a ta amince kenan ma, idan kuma ba'ayi sa'a ba tam...... abindai ba'a cewa komai.
Mata suna son mutum mai saikin fuska da barkwanchi (ban dariya) koda kuwa ita ba haka take ba.
Akwai abubuwa da dama bayan wadan nan amma zanso mu fara jarraba wad'an nan tukuna, don musan inda muka dosa....... Ku sani dai so gamon jini ne ba gamun gambiza ba.
0 Response to "Kalaman Soyayya Ayau"
Post a Comment