-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Hafsat Ahmad Idiris (Hafsat Idris)

Tarihin Jaruma Hafsat Ahmad Idiris (Hafsat Idris)

Jaruma Hafsat Ahmad Idiris (Hafsat Idris)

Hafsat Ahmad Idiris wacce akafi sani da Hafsa Idris, na daya daga cikin shahararun Yan wasan Hausa na Kannywood.

An haifi Hafsat Idris, ranar 14 ga watan Julin shakarar alib 1987 a garin Shagamu dake jihar Ogun a Najeriaya. Iyayen Hafsa Idris “yan asalin Jihar Kano ne dake Najeriya.

Kafin zama daya daga cikin jaruman Hausa, Jaruma Hafsat Idris “yar kasuwa ce yayin da take gudanar da kasuwancinta a Oshogbo zuwa Kano, kasancewar samun nasarar ta a kasuwancin ta sai Jaruma Hafsa Idris taji sha’awar shiga cikin harkar fim.

Hafsat Ahmad Idris ta fara fim ne a shekarar 2016 a cikin fim mai suna Barauniya, da bannan Darakta Ali Nuhu. Ta shiga masana'antar kannywood bayan da ta gwada hannun ta a harkar kasuwanci, ta yi tafiye-tafiye mafi yawan lokuta daga Oshogbo zuwa Kano saboda kasuwanci. Duk da haka, duk da yin kyakkyawan aiki a kasuwancin, sha'awar Hafsat ta karkata zuwa zama 'yar wasan kwaikwayo. Hafsat ta mallaki wani film samarwa kamfanin da aka fi sani da Ramlat Investment, ta ya samar lambobi na fina-finai a shekarar 2019, ciki har da blockbuster movie kira Kawaye a cikin abin da gabatar da taurari, kamar Ali Nuhu, Sani Musa Danja da kuma kanta

Hafsat Idris ta fara shirin fim din Hausa a 2016 yayinda aka fara haska ta a wani fim mai suna Barauniya da Makaryaciya da wasu fina finan dayawa tare da da Jarumi Ali Nuhu.

Hafsat Idris ta mallaki kamfanin samar da finafinan Hausa mai suna Ramlat Investment, kuma ansamar da fina finai masu yawa ciki harda wani fim mai suna Tagwaye tare da Jarumai irinsu Ali Nuhu, Sani Danja dakuma kanta.

Hafsat Idris tasamu kyaututtuka da dama cikin harkar fina finan Hausa.

Shekara Kyauta Nau'i Sakamakon

2017 Kyaututtukan Nishaɗar City Mafi yawan 'yan wasan kwaikwayo Ayyanawa

2018 Kyaututtukan Nishaɗar City Mafi shahararren dan wasan kwaikwayo Lashewa

2019 Kyaututtukan Nishaɗar City Mafi kyawun actress Lashewa

2019 Kyaututtukan Nishaɗar City Fuskar Kannywood Lashewa


Wasu daga cikin fina finan Jaruma Hafsat Idris

Biki Buduri, Furuci, Labarina, Barauniya, Makaryaci, Abdallah, Ta Faru Ta Kare, Rumana, Da Ban Ganshi Ba, Dan Almajiri, Haske Biyu, Maimunatu, Mace Mai Hannun Maza 2016, Wazir, Gimbiya Sailuba , Matar Mamman, Risala, Igiyar Zato, Wata Ruga, Rariya, Wacece Sarauniya, Zan Rayu Da Ke, Namijin Kishi, Rigar Aro, Yar Fim, Dan Kurma,

Mata Da Miji,  Kawayen Amarya , Dr Surayya, Alqibila, Ana Dara Ga Dare Yayi da kuka shahararran shirinnan mai dogon zango Labarina Series 1,2, da kuma 3.


Wasu dagaaga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Hafsat Idris

2 Responses to "Tarihin Jaruma Hafsat Ahmad Idiris (Hafsat Idris)"