-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Fatima Abdullahi Washa (Fati Washa)

Tarihin Jaruma Fatima Abdullahi Washa (Fati Washa)

Jaruma Fatima Abdullahi Washa (Fati Washa)

Fatima Abdullahi Washa sananniyar jarumar Kannywood ce. An haife ta ne a ranar 21 ga Fabrairu, 1993, a jihar Bauchi.

Fatima Abdullahi Washa wacce aka fi sani da Fati Washa a wasanin kwaikwayo na Hausa, mai son sana'ar fim ce tun tana ƙarama a lokacin da take karanta littattafai. Zamowar ta mai taimakawa jarumai bai dakushe tauraruwarta ba. Kyakkyawa kuma doguwar jaruman, wadda ta bankara tsakanin manya ake damawa da ita tun farkon shigowarta industiri. Rol din da ta hau a cikin fim din Hindu - An African Extra Vagrant hakika abin yabawa ne.

Fim ne da ta fito a tsakiyar manyan jarumai irinsu Adam A. Zango da Jamila Umar Nagudu. Yanayin yadda ta taka rawa a tsakiyar tamkar ba mace ba ya kayatar da ‘yan kallo. A wasu lokutan ma sai mutum ya manta da cewa mace yake kallo, domin ta yi tsayiwar daka wajen tabbatar da ganin ta bai wa labarin hakkinsa a matsayinta na matsafiya.

Yanzu a shekarar 2021, Fati Washa tana da shekara 28, kuma ba ta da aure. Kasancewar tana da kyakkyawar fata mai haske, Fati Washa ana ɗaukarta ɗaya daga cikin actress na wasan kwaikwayo mata da ake buƙata a Kannywood.

Ayyuka da fina-finai Ta yi wa kanta kwalliya a masana'antar finafinan Hausa wanda hakan ba karamar nasara ba ce ga matashiyar 'yar fim. Fati Washa ta fito a fina-finai da dama da suka hada da:

Na Gaba, Makahon Gida, Make Da Bake, Ya daga Allah, ‘Yar Tasha, Ana Wata ga Wata, Baya da Kura, Fari Da Baki, Farida, Gaba da Gabanta, Hadarin Gabas, Hindu - Anarin Africanarya na Afirka, Hisabi, Jaraba, Karfen Nasara, Makahon Gida, Niqab, Dangin Miji da sauransu.

Kasuwancin Jaruma Fati Washa

Haka zalika batun kasuwa nan ma babu magana, domin tun bayan nuna fim din a Sinima dake titin Zoo a Kano, ‘yan kallo suka nuna maitarsu a fili ta mararin ganin fim din. Har ila yau ta samu yabo daga wajen manyan masana fim irin su Farfesa Abdallah Uba Adamu, Ahmad Gidan.

Wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Fatima Abdullahi Washa

0 Response to "Tarihin Jaruma Fatima Abdullahi Washa (Fati Washa)"

Post a Comment