-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Maryam Musa Waziri (Maryam Waziri)

Tarihin Jaruma Maryam Musa Waziri (Maryam Waziri)

 Jaruma Maryam Musa Waziri (Maryam Waziri)

An haifi Maryam Musa Waziri a ranar 9 ga Nuwamba, 1992 a Jihar Gombe, jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya. Ta girma a jihar Gombe kuma ta yi karatun firamare da sakandare. Jaruma Maryam Waziri ta yi digiri daga Jami'ar Maiduguri (UNIMAID)

Maryam Musa Waziri na daya daga cikin kyawawan jarumai a masana’antar fina -finan ta Kannywood. An fi saninta da Maryam Waziri. Maryam Waziri tayi Karatun firamare da na sakandare duk a jihar Gombe, inda aka haife ta.

Jaruma Maryam Waziri ta fito a fina -finan Hausa da dama, kuma a halin yanzu rahotonni sun nuna cewa tana daya daga cikin jarumai masu tsada a masana'antar fina-finanai ta Kannywood.

Maryam ta fito a fina -finai sama da 40 tun lokacin da ta samu kanta a matsayin Jarumaa, Maryam Waziri ta fito a shirin fim inta na farko a shekarar 2015. Wasu daga cikin fina -finanta a masana'antar Kannywood sun hada da:- Yakin Mata, Yan Zamani, Amina Juna, Muguwar Mace, Yakin Mata, Labarina, da Dan Halak 

Wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Maryam Waziri


0 Response to "Tarihin Jaruma Maryam Musa Waziri (Maryam Waziri)"

Post a Comment