-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

MEKE FARUWA Hausa Novel

MEKE FARUWA Hausa Novel

MEKE FARUWA Hausa NovelYana kwance cikin tafkeken bahon wankan da ke cikin tsfkeken bayin, Sam bai yi kama da bayi ba, domin yana da girma kwarai. Bahon kato ne haka nan daga inda bahon kana iya kallon TV manne jikin bango can daga nesa kadan ga gurin da zaka zauna don yin bahaya (toilet) tsararre ne mai tsafta. 

Kwance cikin baho Modibbo ne, daga in da yake cikin bahon da ya cika da ruwan dumi da kuma ruwan sabulu mai shegen kamshi yake canza tashar da yake kallo zuwa (CNN) daga inda yake yana jiyo karan kawankawasa  kofar bayin. Shin wanene? Ya tambayi kanshi amma ci gaba yayi da kallonshi. Da ya tuna duk Wanda ya matsu ya jira shi kusan rabin sa'a sannan ya soma cuda jikinshi, ya cire abin da ya toshe rariyar da ruwan ya tsiyaye sannan ya kunna wani dake zubowa daga inda aka rataye su ya rufa a jikinshi sannan ya dauki karami yana goge sumar kanshi. Bayan yazura lallausan silifas a kafarshi zama yayi kan wata kujera duk dai nan cikin bayin ya shafe jikinshi da mai mai kamashi tare da turaruka ya gyara sumarshi tare da shafa mata nata kalolin.

[8:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 02 馃彽


 Modibbo yana kashe ma kanshi kudi fiye da zaton mai tunani,mikewa yayi cikin tafiyarshi ta kasaita ya nufi dakin barcinshi don saka tufafi ya kalli kofar da zata kaishi falo sai ya tuna ana jiranshi, din taski yaja sannan ya rufe kofar (bedroom) din shi bayan ya shige tare da fadin ko ma waye zai tafi ne don yanzun lokacinan na kar2 ne. Shirayawa yayi cikin wandon {jeans blue} da rigarsahi mai dogon hannu ya isa kan durowa ya kwashi takardu tare da wayoyinshi ya zuba su cikin aljihu, takalmanshi sawu ciki ne ya saka sannan ya fita.

  Vicky ce zaune a falon tana jiranshi,ji yayi tamkar bai ganta ba duk da tsananin son da yake yi mata. Ya nufi hanyar fita, ta taso da sauri tana kiran shi. 


Darling prince D P

Ci gaba yayi da tafiya, ta soma gudun sassarfa ta cinma shi ta dafa kafadarshi tana cewa cikin turanci. 

Duban ta yayi tamkar ba zai magana ba sannan yace amma kin yi saurin hucowa. Ya taba baki" ina zaton kin manta ni wanene shi yasa kike yi min fushi, bani da lokacin lallashin ya mace duk da son da nake musu. Ki gane bani Yarima Modibbo ke bin mata ba, ni suke bi. Je ki ci gaba da fushi dan kin ganni da wata. " yaci gaba da tafiya yana sake fadin Yanzu lokacin kar2 ne ba na surutu ba. 


Ta tsaya ranta a bace,hawaye ya soma zubo mata tana tunanin yaushe ne zata daina kuka saboda prince? Yaron da take matukar so, yaron da mata suke rububinshi, yaron da yake ma mata jan-aji, yaro mai kyau da kwarjini, ta zube ta soma kuka. 

 Kafin ke dubin ki sun yi Vicky . 

Yarima Al-amin kenan. Kenan dan sarki Ismail jikan Abdullahi mai mulkin yankin Bauchi. Matashin yaro dan shekara ashirin da biyu  Wanda aka fi sani da YARIMA MODIBBO A malesiya gurin kar2 ake CE mi shi prince


A ZARIA FA? 

 

Katon gida ne ginin kasa mai dauke da sassa kusan goma sha biyu, gida ne ginin kasa tun na da wato ginin gargajiya. Kafatanin 'yan gidan dangin juna ne in ka dauke Fatima'yar mutanen Bauchi da aure ya kawo ta gidan. Yanzun da haka fatimar ce zaune tana tuka tuwon dawa, Bilkisu ta yi sallama ta shigo jikinta sanye da atamfa java, ta rataya jaka kana ganinta kasan daga makaranta take. Bilkisu kyakkyawa ce ta bugawa a Mujalla, domin idan har za'a zuba gasar kyau ta shiga ciki babu abin da zai hana ta lashe gasar 'yar kimanin shekara ashirin da biyu CE. Ta isa gurin mahaifyarta Fatima tana fadin.


Mamarmu sannu da gida Ta dube tace da kulawa duk da kasancewarta'yar fari ta ce "yauwa sannu maigado. { shi ne sunan da ake kiranta da shi } ma'ana mai gadon zinar. Kirarin maisuna Bilkisu. 

   Yau kin dawo da wuri. Ta ce " Eh, Mamarmu wata kawar mu muka je dubawa da tuni na dawo. Ta ce Allah sarki, bata da lafiya ne? 

 Zazzabin cizon sauro ne, nan sabon gari suke. 

 Allah ya bata lafiya. In ji mamar. Amin . Bilkisu ta amsa. Sannan ta nufi dakin mamansu duk da gajiyar dake tattare da ita sai da ta share dakin fes tare da gyara shi. Sannan ta fito ta share tsakar gidan duk da cewa ba'a siminte yake ba, yakan ba da sha'awa in an share . 


Asma'u Auta ta shigo da sallama, ta dawo daga Islamiyya tace, Sannu Mamarmu, sannu Aunty Maigado. Bilkisu ta harare ta da sauri ta gano laifinta ta ce, Na manta ne, yi hakuri. Tana yar dariya . Bilkisu ta ce ban son Aunty ki ce min Bilkisu kawai don bana son maigado . Ranar da ki ka kara fada sai na fasa miki baki. Mama ma ta ce. To ai sai a hankali zata saba, mu dai ai ba yanda za ai damu.

[8:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 03馃彽

Ta dubi Asma'u. 

Auta amso min kwanukan mutanan gidannan in kwashe tuwon nan. Dakuna uku duk da na su hudu sashen Babansu malam mamman kenan matanshi hudu ya'aya ashirin da takwas, don haka kwanukan da Asma'u ta baje gaban Maman mu sai ke ce za'a kaima gidajan layin gaba daya ne, yawancin kwanukan duk sunyi tsatsa da kuma lamba, haka Mamanmu ta ci gaba da kwashe tuwon nan tana zuba ma kowane. Bilkisu ta fito daga daki tana cewa, Mamanmu bari in debo ruwa in kin gama sai na dora ina son na yi wanka. 

 

Tace, ai fa ke kam ko kwado ya San da zamanki gurin wanks. Dariya tayi sannan ta dauki bokiti zuwa gurin rijiya. Kananan yara sun kai hudu suna wasa da kasa a bakin rijiyar, maza uku mace daya macen mai suna Safiya tana zaune tsakiyar tabon da suka kwaba, rigarta duk koko haka nan fuskarta, kanta rabi a tsefe rabi da kitso. Tsaki Bilkisu taja sannan ta ce da su. Kai Ku ta shi a nan kazaman yara kawai."  Bala dan babba a cikin su ya kalle ta. 

To ina ruwanki dama za ki ce mu ta shi? 

Ta samu kanshi ta dan buga dai dai da shigowar mahaifinsu Malam Mamman. Yace ke ke ke kar ki sake ki duke shi, ki shafa mishi bakin jininki

  Ta dakata. Me yayi miki? Ko zalinci da mugun Abu za ki nakasa min da namiji gashi ke uwarki bata iya haihuwar ya'ya maza ba. Ya ja tsaki kai Bala. { hahahah wai bala dama bala sunane?} Idi, kuzo muje ciki domin zata iya jefa Ku cikin rijiyar nan yan ubanci ba karya ba ne.  Allah ya kyau ta. 

Bilkisu hawaye suka zubo mata, ita dai tana matukar mamakin irin tasanar da dukkan dangin mahaifinta 'yan dai-dai-ku suke yi mata ta dibo ruwan ta dawo, yanda taga fuskar Mamanmu tasan cewa ta ji duk me baba yace mata, don haka ta ce kiyi hakuri Mai gado wata rana sai labari .

Da daddare kwance take kan gadonta, gefenta Asma'u ce tana ta shara barcinta, ita kam ta zurfafa cikin tunanin cukurdaddan al'amarinta, kullum tana tambayar kanta shin me ke faruwa da ita ne? Tana da kyau na gani afada, tana da hankali ta sani domin mutane suna fada, tana da ilimi duka biyu wato islama da na boko. Natsuwa da kamun kai kuwa ba a magana, amma me ya hana ta burge maza? Me yasa ba ta da saurayi?me ya hana wani yace yana son ta? Kuka ya kufce mata Wanda ya zama dan kullum. A fili tace. Meke faruwa ne da nine? Wa zai bani amasar tambayata?  Shin ko Ubangiji bai kaddaro ni cikin wadanda zasu yi aure ba ne? Allah kai kadai ne mafi sani......... Ta daga hannuwanta  Ya Allah Ya Ubangiji halitta kai ne majibancin al'amurana, kafi ni sanin halin da nake ciki, Allah ka zaba min mafi alkairi. Ta maida kai ta kwanta ta soma tuno ita wacece? 

 Uhm sai an jima.


 GIDAN MARINA, shi ne sunan da ake kiran gidanmu a unguwarmu, wato Ojo saboda 'yan gidanmu ita ce sana'an da suka gada daga kakanninsu, kuma ita ce har yau yayanmu suke yinta wato rini. Gidanmu katon gida ne mai dauke da sassa sama da goma. Asalin maigidan shi ne Malam salisu, shi ne mahaifin su Babanmu. Yana da mata hudu 'ya'yanshi talatin da bakwai maza guda goma sha biyar sauran duk mata ne, mahaifinmu yana cikin ya'yan Goggo Amarya shi ne da na uku a gurin ta yana bin mata biyu, kakanmu malam salisu mai rini mutumin kirki da sanin ya kamata, ya rasu tuntuni lokacin ma ba'a haife ni ba, uwargida ma lantana Allah ya yi mata rasuwa, yanzu saura mata uku. Tun rasuwar malam salisu gidan ya lalace rigingimu tare da matsaloli sukayi ma gidan yawa. Gidanmu ba'a cika auran bare ba sai dai dan wannan daki ya auri 'yar wancan daki, suma su ja na su sasan ko kuma cikin dangi na wani gu ya auro kuma dangi na wata unguwar ya auri yar gun, haka suka ke yi har zuwa kan mahaifinmu, wanda suka yi bikin wani abokinsu aka kawo Amarya daga Bauchi, cikin kawayan Amarya idon shi ya kyallo Fatima yar mutanan Bauchi daya daga cikin kawayan Amarya, nan ya birkice kun san bazazzagi da mace. Nan fa ya shiga zarya tsakinin Bauchi da zariya, Fati ta yarda itama tana son Muhammadu, wanda yan gidan basu goyi baya ba, saboda tuni yasan da hatun ladiyo yar kanin mahaifinshi baba isa dake jushi, hakan yasa duk yan gidan kin amin cewa da batun har da mahaifiyarshi goggo Amarya .

 

Goggonsa ce kurum ta ce ai hakuri ba a san rabo ba, tasa'ya'yanta su shige mishi gaba gurin neman auran, bayan kai-kawo aka biya sadaki sai bikin, ya gina sanshi kamar sauran'yan gidan ginin kasa ciki da falo, aka kawo Fatima dakinta, zaman nasu ba laifi sai dai bata jin dadi'yan gidan sai Goggon sa kurum.

[8:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 04馃彽


 Bayan'yan watanni sai rayuwa ta canza tun da gara ta kare shi kenan mataloli suka kunno kai cikin zaman nasu, farko ya sakar mata sayan su sabulu, man shafawa, daga baya suturar a shekara dama yake mata itama ya daina, daga baya ma sai ya zama abinci in ya kawo masara ko dawa ko kuma doya to batun cefane can ta gane, cikin haka dangi suka soma tsegumin shekara biyu babu haihuwa gaskiya sai dai ya sake aure, haka ce ta faru. Ladiyo tana jiranshi nan ko aka soma shirin biki Fatima ta zuba ido domin sabon shafi ne na wulakanci ya bude tsakaninta da dangin mijin da kuma shi kanshi maigidan saukin ta daya goggon sasa tana yin kuli to sai tana bata mirji da suya tana biyanta a haka Goggo ladiyo ta shigo cike da gadara da jin kai har zama yayi zama kafin wata biyu ladiyo ciki ya bayyana. 


 Nan dangin miji suka sakota gaba ko yaransu suka hana ta aika, sukan ce ta abr musu'ya'yansu in taga dama ta haifi nata, ya zama sai dai in tana son aike sai taje, ko kuma ta fita makota ta aika yaransu. Duk wannan ba shi ne tashin hankalinta ba irin yanda Ladiyo ta tsiro tsirfar bata son warin tuyar kuli kuma in taga tunkuzar kuli tana sakata yin amai, kenan'yar sana'ar tata ta barta a halin da ita ne take samu tana rufa ma kanta asiri.  

 Tabbbas nufin Ladiyo ta samu ta raba ta da sana'arta, maigidan kam ya ce baya son ya kuma ganin kuli ko tunkuza, ta ce amma kasan cewar da wannan sana'ar na dogara ko?  Nan take ya fusato, kenan ke kike ci da kanki? Ta ce menene marabar dambe da fada? In ka kawo min hatsi ko doya shi kenan, ba kudin cefane ba na nika ko na ice, sabulu, man shafawa duk a jikina suke fita, ya ce to koma menene dai a daina min kuli, tace gaskiya ba zata yiwu ba, ni kenan kullum sai dai dangi su taimaka min? Ya ce kanki aka soma?  ai ba kanki mata suka fara cefane ba, don haka ki canza sana'a, ta ce amma ai ita Ladiyo kana bata ba dan baka dashi ba ne kake hana ni, saboda haka yanzun na soma yin kuli in ba'a so in yi sai a tsare min komai, " ya fita tare da fadin To bismilla, kiyi ki gani, haka ko washegari ta amso aikinta ta shiga yi,  Ladiyo ta fito shi ne kike kulin dan ki ga bana son warin so kike cikina ya zube ne tun da ke ba ki iya samun cikin ko? Bata tanka ba ta ci gaba da aikinta, makira mijin na shigowa da gudu ta shige daki ta hau gado tana ta burgima tare da kakarin amai. Yana ko karasowa ya shiga masifa har da zaginta, a karshe ma dukanta yaso yayi ta shige daki. Washe gari kam ta ce ta gaji gida zata tun da tana da gatanta hakuri kuma ba hauka ba ne. Wannan tsiya, yau miji ya maka gobe mutan gida, uwarmiji sai ta shigo har sasansu ta zage ta tas tana cikin wannan tunanin tana hada kaya, taji muryar Goggo Amarya.

 Ina kike 'yar mulki da iko da an ce ki daina aikin kuli saboda mai cikin haihuwa ke naki cikin ban da kashi ba ya iya daukar komai shi ne za ki bar gidan, itama mai baki aikin ai munafunci ne ga mata da yawa kowane sashe ta mika aiki ai yi zasu yi amma dan gulma ta fi son ta ba ki shi yasa bata ciniki to mai farar kafa ta taba ba dole yayi kwantai ba?


 Fatima kam shiru ta yi tamkar bata nan, Goggo ta gama masifarta ta fita,itama ta dauko kayanta da saka su cikin garin yayi zafi ta fita a waje yayyan maigidan ne su biyu sani da Rabi'u suka ce ina za ki? Ta ce zan yi tafiya ne, suka ce in dai yaji ne kiyi hakuri, ta ce kai ita ta gaji gara taje garin su. 


Daf da magriba ta iso Bauchi, sanda ta shiga gidan su mahaifiyarta tana alwala ta ce lafiya kuwa? Murmushi taye tare da fadin lafiya kalau bayan sun yi sallah sun ci abinci nan ta shiga zayyano ma Umma abin da ya faru tare da halin da take ciki. Umma ta ce bari Malam ya shigo. 


Iyayanta suna da mutunci tare da sanin ya kamata, suna son Fatima sosai, saboda ita kadai ce ya mace a cikin 'ya'yansu maza guda biyu. Aminu da Abubakar wadanda suke kasuwancinsu a nan babbar kasuwar Bauchi, kuma suna da iyalansu suna matukar kula da iyayansu da kuma Fatima. 


Sun hada mahaifinsu da yayyanta sun yanke shawarar in yazo biko za'a ja mishi kunne sannan ta koma, ta ce ita in so samu ne a raba Auren amma sai mahaifinta ya ce ba zai yiwu su kashe mata aure ba, ta je ta ci gaba da hakuri. Satin ta daya sannan 'yan uwanshi suka zo shima sakamakon yanda 'yan uwanshi suka matsa mishi da magana har da makota sannan ya yarda yazo bikon tare da'yan uwan nashi. 

An ja mishi kunne 'yan uwanta sun hada mata jari tare da dunkuna sun ce taje ta sayi fridge ko ruwan sanyi ne tana saidawa,  ta dawo dakinta ta ci gaba da hakuri tare da yan sana'o'inta haka nan ta sai fridge din tana kuma samun alhairi haka Ladiyo ta haihu suka yi ta rawar Kansu har aka yi suna hankalinta kawance, tunda tana sana'arta. Cikin watan ya sake ta da wani dakin yana gamawa ya rigimo Auren karima bazawara ce daga unguwan kaura aka sha biki itama tabi sahun yin cefane da kanta, wankau ta ke yi, shekarara danta sunusi daya ta kuma samun ciki sai fa suka soma gasar haihuwa ita da karima Fatima ta da dai zuba ido ya'yansu maza suke Haifa.

[8:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 05馃彽


 Kamar wasa ya kuma tada daki ashe zai cika ne wannan karon 'yar yarinya ya dauko musu daga kauyan Turunku Mara kunya nan suka hada kai su uku suna mata habaici wai juya su kam sai zazzaga haihuwa suke, cikin ikon Allah sai ga Fatima itama ta wayi gari da ciki. Kwanci tashi har haihuwa tazo, komai na gama da ciki don kayan yara duk ita ta siya, domin da ta tambaye shi cewa yayi shi dama bai taba sayan kayan jarirai ba kuma kanta ba zai fara ba. Suko sauran kishiyoyin nata sai zundenta suke wai ba saban ba su wance anyi ciki.


Bisa ga yardar Ubangiji ta haifi'yarta ita daya kuma cikin dare, maigidan dama dakin Amarya yake, ita ce ta yanke cibi da kanta dama tana da sabuwar rezarta, sannan in ta zaga sasan Goggo sasa takan tambaye ta yanda zata yanke cibi saboda ko zata haihu cikin dare, ba zata samu mai kira mata Goggo ba. Ta nade' yarta cikin zani da ta huta ta tashi ta kwashe jinin. Da Asubahi Allah ya kara mata karfin jiki ta fito ta dora ruwan wanka, ta wanke 'yarta mai matukar kyau sunusi babban yaron maigidan nasa dan gidan Ladiyo ya leko wai in ji Goggo salame ( amaryarsu kenan) ta ce ki bata kwanon koko, ta ce babanka fa? Ya ce ta yana dakinta ta ce kaje ga kwanonin ka kai sannan ka ce babanku yazo na haihu, da murna yaron ya tafi kun San yara da dokin haihuwa, sai ko gashi ya shigo ba yabo babu fallasa fuskarshi ya dauki yarinyar ya gani ba ko addu'a ya aje ta kilama bai iya addu'ar ba ta ce don Allah ka siyo min dan kayanta mana? Ya dube ta ke Fatima dube ni ba kanki na soma haihuwa ba, bare ki min tsurfa in za ki sha kunu kisha duk sauran kunu ake dama musu.

Ta ce to yanzu wa zai je ya fado ma'yan Bauchi? Ya ce wannan kuma ya rage naki, ni dai bani da kudi haihuwar nan ma ki samu ko masarar fate in Samar miki kada ki sa rai zan yi wata karya dan bani da hali. Ta dube shi cikin takaici tare da da na sanin auranshi. Ta ce duk matan ka ka fifita su kai na, domin ganin idona kana sai musu kayan (shayi) sannan ka musu ragon suna har ma da dan dinkin suna, ban sani ba ko sun fini yi maka biyayya ne?  Tsaki yayi sannan yayi waje, tayi ta tashi wani dan saurayi jikan Goggon sasa ta mishi kwatance ya tafi Bauchi don shaida ma iyayanta.


Washe gari kanwar Umma ta biyo dan aike suka dawo ta ci gaba da kula da ita a zaman Inna hausi ta tabbatar Fatima tana matukar hakuri domin komai da kanta take saye don abincin gidan nasu baya ciyo ga Inna hausi sai daiu su yi yar miyarsu haka ake har suna tun ana gobe yan Bauchi suka zo, masara kurum ya miko ko gishiri bai bada ba ita ce ta yi komai, dangi sun hada mata shatara ta arziki, ya kuwa ta ce suna Bilkisu mai gadon zinari. Tubarkalla Masha Allah haka kowa ya ke cewa in ya ga Bilkisu shi ko ubanta ko kaza bai yanka mata ba bare rago amma ta zuba ido kuma ta bar ma Allah.


Haka Bilkisu ta taso cikin sha'awa da kuma birgewa amma gurin uwarta domin mahaifinta bai taba mata ko da wasa ba daga nesa bare ya dauke ta, a haka ta kuma samun cikin Sakina sannan Maryam sunnan Umma ne don haka suke kiran ta momy, sai Ku Asma'u lokacin tana goyon Asma'u abubuwa sun mata yawa ga yara maigidan baya biya musu bukatun 'ya'yansu cima ba dadi, in kana son ci da dan galmi sai ka bude bakin jakarka yara babu karatu su sun usima da suke maiya ya dai saka su amma ya bar iyayan da siyan takarda da biyan dan kudin jarabawa, don haka suka hana yaran zuwa makaranta kowacce ta kama Sana'a tana dora ma ya'yanta suke nan da yake son su bare Fatima wadda ita da ban za duk daya, gidan Hajara ta shiga wato aminiyarta, suka shawarta tace hajara shawara na kawo miki, ta ce ina jin ki Fatima, tace kina dai kallon rayuwar da muke yi a gidanmu. Ba cin kirki sai gasar haihuwa, to ba zan iya ba so nake don Allah ki ma Malam maigidan ki magana ya taimaka min da wani dan taimako haihuwar nan ta tsaya in samu in ji da tarbiyar wadannan ma balle ni mai'ya'ya mata ta ce kin yi tunani zan ko gaya mishi haka ko aka yi rubutu yayi mata haihuwar ta tsaya ta samu ta saka Bilkisu firamare..

[8:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 06 馃彽


 Sana'o'i ta ringa yi sbulu, omo, manja,mangyada, lallai ana shan wahala da rayuwa,haka nan tayi ta kula da yaranta har suka soma tasawa. wata karamar sallah tazo nan ta shirya ita da yaranta, don zuwa bauchi, Bilkisu yarinya mai kyau da shiga zuci, lokacin shekarunta biyar, kawunta Aminu ya tafi da ita kallon hawan sallah, tana sha'awar kallon hawa ko a zariya tana son zuwa amma Mamanmu bata bari haka suke ce ma fatima, ba wanda ya burge Bilkisu gurin kallon hawan nan kamar wani dan yaron sarki ba zai fi shekara biyar ba tsaran ta kenan, an mishi nadi shima cikin wata alkyabba bayan shi runduna ce guda, yaron yana ta daga ma mutane hannu, itama sai daga hannu take tana mishi bye-bye, ai ko kullum bata da labari sai na Yarima. haka kawunta ya ce mata sunanshi har suka bar bauchi suka dawo zariya lbrin yarima take yi haka nan kuma sai ta shiga yin mafarkin yarima. kullum ta kwanta sai tace tayi mafarki sun wasa da yarima har abin ya ishi mamanmu tace kada in kuma jin zance yariman nan,

 don haka ko tayi sai tayi shiru. kowane sassa zundenta suke wai ta ki dora ma yara talla gata da ya'ya mata, in ta tashi aurar da su saga ni me zata kai ma ya'ya daki? sam wannan bai damu mamanmu ba ita dai burinta shine taga 'ya'yanta sun samu tarbiya tare da kulawa. Bilkisu yarinya ce mai tsananin hakuri da zurfin ciki, tana da kwazon karatu da son karatu, sabanin Sakina mai fada da kin raini don haka duk kishiyoyin mamanmu ta tsane su matuka, Maryam ko sai dai fushi da miskilanci. Asma'u auta itama akwai tsiwa tun tana karamarta, yanda yayyinu suk dukan Bilkisu sai dai ta yi kuka. Asma'u kam bata raga ma abokan goyonta shi yasa rigima kullum. Salame ta shiga dakin karima tana fadin ke 'yar gari king uwar mata? Me tayi? In ji karima bayan ta bada dukkan hnkalinta, Yau kuma takalma silifas sababbi ta sai musu. kan ta yi magana sai ga Ladiyo, kunga uwar mata? A gindinsu zata kare an siyo musu silifa. Karima taja tsaki ai ta haifar ma kanta wahala mata kai ta musu bauta ko gidan Miji suka je ba ka huta ba, mu ko masu mazan da farko in sun kawo karfi sai dai mu kwanta su mana su ma kannansu matan. salame ta ce ai Allah ya taimake mu da muka fara da maza. Ladiyo ta ce ni duk ba wannan ya dame ni ba, irin in ma kalli Bilkisun nan yarinya kyau tamkar aljana? salame ta ce kuma tafi sonta ba, tsorona daya kada wani mai halin ya aure t. Ladiyo tace kada nima ina wannan tunanin amma ga shawara ta rada musu wata magana a kunnuwansu, suka saki dariya tare da fadin kin kawo shawara. Bilkisu da kannanta cikin kayan islamiya suka nufi islamiyya, sai da ta raka kannanta kofar ajinsu Sakina da mami, sannan ta tafi ajinsu, duk malaman makarantar sun son Bilkisu saboda kokarinta tare da hazaka ga ladabi ga kuma tsafta duk da cewa kayan makarantar tasu sun tsufa amma tsaf suke a wanke. ta shiga suka soma karatu, basu dade ba wani malami ya shiga da wata yarinya sabuwar zuwa ce, duk ba zata fi Bilkisu ba, ta shigo tana yan kalle-kalle alamun bakunta Bilkisu ta kalle ta cike da murmushi,

[8:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 07 馃彽 


 don haka sai ta je ta zauna kusa da bilkisu.  Bayan sun tashi sun fita bilkisu tace yaya sununki? Ta ce Mansura Sadik, ke fa? Ta ce ni sunana B M S, da fatan zamu zama kawaye? Mansura cikin murna ta ce. Insha Allahu. Ta debo kannanta itama da kaninta Abba ta dakko shi daga ajin da aka kaishi suka jero suna hira. Gidan su Mansura ba shi da nisa da islamiya, don haka Mansura ta roki Bilkisu ta shigo ta gaida Ummanta, jikin Bilkisu yayi sanyi da ganin daular da su Mansura suke ciki, lallai Mansura ba abokiyar yinta bace, domin an ce kwarya ta bi kwary. hajiya mero mahaifyar mansura nurse ce mahaifinta kuwa ma'aikaci ne a {G T Bank} da ke kaduna.

 makarantar bokonsu ta kudi ce mai tsada, haka ne yasa Bilkisu dan Jan jiki da Mansura, amma Mansura sai ta kara shige ma Bilkisu ta ki sai wata rana bata da lafiya don haka bata samu zuwa islamiyya ba hankalin Mansura ya tashi don haka kuwa ana tashi ta bi su Sakina don ta dubo Bilkisu. Sam Mansura bata damu da yanda taga gidan su Bilkisu ba, har ma da ta samu Mamanmu ta gama tuwo sai da taci, hakan ya sanyaya zuciyar Bilkisu don tana son Mansura musamman ma da ya ke Mansura iyayanta sun kasance yan gombe, tana ganin gombe da Bauchi kamar daya ne gunta  tana son yan Bauchi dangin uwa masu sonta, tana ganin kamar bata da masu sonta sai yan Bauchi shi yasa duk inda ta ga yan Bauchi tana girmamamasu, Mansura tana da son tuwo don haka sai ta samu gurin zuwa.


Ko Bilkisu bata nan Mansura tana zuwa gurin Mamanmu jin ta take tamkar mahifiyarta waton Ummanta suka niyan gidan sai suka tsiri sakin habaici, Bilkisu ma nan ta saki jiki da Umma Umma da Mamanmu suka zama kawaye, haka ya sosa ran su Ladiyo musamman da suka ga tana basu kayan sawa zuwa dan abin marmari.


Bilkisu tana zaune ciki wani ciyayi mai kama da cafet guri sanyi da iska yanda yake Kore fatau ya bata sha'awa ga fararan tattabaru suna tashi wasu suna sauka. Can daga nesa sosai take hango dan matashin yaron tasaranta bisa kan doki yana isowa gurinta ya tsaya cike jin kai. Yace ke wa ya kawo ki gonata? 


Ta dube shi nan ne gonarka? Kafin ya bata amsa sai ga wasu mutane su biyu suka kama mishi linzamin doki ya sauka, sannan ya isa wata kujera dake can gefe irin ta sarakannan ya zauna sai ga wasu mutane cikin jaja yan kaya sun tsaya a bayanshi, can kuma sai yace na sallame Ku. Suna tafiya ya dawo gurin Bilkisu ya zauna kusa da ita ke yar sakin wane lardi ne? Ta dube shi ba ni da alaka da sarauta. Ta bashi amsa, yace kin sanni? Ta dube shi cike da mamaki kai ba ka da gane mutane so nawa muna wasa da kai? Firgigita ta farka daga bacci yau mafarkinta ba irin na sauran ranaku ba ne, domin sauran ranakun tafi mafarkin suna wasan kwallon kafa, ko na raga koma na tebur, suna hira sosai, amma ya kan nuna bai ma Santa ba ne, tayi murmushi, tun tana yar shekara shidda take mafarkin Yarima gashi yanzun tana shekarar karshe a primary shekarar haihuwa kuwa sha daya su Bilkisu an soma zama yammata, kyanta kullum karuwa yake yi.

Hankalin mamanmu ya tashi domin ba ta da kudin da zata yi ma Bilkisu hidima dan zuwa secondary, duk da cewa ta ci domin makarantun gwamantin ma wannan zamanin sai kana da hali. Da kanta taje makarantar da Bilkisun ta ci sun mata lissafin tun daga rijista zuwa uniform da takardu dubu takwas har da dori. Hankalinta ya tashi bata da inda zata samo kudin nan, gidan hajara kawarta ta shiga don yin shawara, hajara ta bata shawarar me zai hana Bilkisu ta yi aikin gida ko na wata uku ne, in yaso sai ta shiga a zango na biyu tun da an amso form. Mamanmu jarumar uwa ce wacce samun kamarta sai an tona, tsamaranta cewa zata zamar wa ya'yanta uwa kuma uba, don haka ta ce ma hajara ni zan yi aikin da kaina wa ki ke ganin zan samu ya nemo min aiki? Hajara ta ce kada ki damu akwai mata masu hali da suke zuwa gurin malam zan dinga musu magana har a dace, shin maigidan naku zai barki?

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 08 馃彽 


 Ta ce tunda ba bani zai yi ba ai batun hanawa ma bata taso ba, shi fa yanda na kula koma menene kije kiyi amma kada ki tambaye shi, sukansu kishiyoyin nawa da yake sonsu baya musu komai, amma don rashin tunani suna nan suna ta zabga gasar haihuwa,yaran bacin kirki bare sutura, karatu kuwa sai dai na zagi ashar kam, kwando-kwando za ki ga dan karamin yaro yana saukewa, gaskiya 'yan gidanmu su ne suke bata ma zage zagi suna, shin haka kowane gida suke yi? Hajara tace a'a akwai dai masu yin amma ba duka ba.. Cike da farin ciki  tabar gidan hajara, ta samu Bilkisu da yan kannanta a cikin daki, tana koya musu darasin lissafi, nan ta zayyane ma Bilkisu komai, Bilki ta ce mamanmu ki bari ni nayi aikin in an samu, ta ce a'a nafi soe ni in yi bana son kije ki bata ma masu gidan har su sallame ki, bukatarmu ya zama bata biya ba. tace mamanmu amma kinsan bana fada ko? tace na sani maigado, amma ki bari sai dai an samu din kisan ke yarinya ce ba kowane abu ne zaki iya yin shi ba. Sallamar Mansura ta katse su, suka amsa ta shigo kusa da mamanmu ta zauna sannan tce mamanmu ina kwana? Suja gaisa ta dubi Bilkisu tace "Bily ya dai, yaushe zaki fara shiga school ni dai on monday zan fara zuwa. Bilki tace ni kam ba rana Mansu, kila ma sai second term. Mansura tace akan me? Tace kudi, mamanmu tace kin san ko mai yanzu sai da kudi ana cewa ne dai makarantar gwamnati amma suma duk shegiyar darin ce ga kudin motan zuwa makaranta kullum mansura tace bari Abbanmu yazo week end zan gaya masa. Bilki har suna hada baki da mamanmu, a'a kar ki yi masa magana shima yana ji da nasa iyalin. Mansura tayi shiru, amma a ranta ta raya sai ta fada mashi... Haka kuwa yana dawowa ta gaya mishi, ya tambaye ta ko njawa suke nema? Ta ce ya basu kowanne ita dai bata sani ba, kuma ta san ko ta tambaye su ba zasu fada ba. Dubu goma ya bata yace, gashi ki basu." sai da ta kai kudin mamanmu da yaranta suka je suyi godiya,Bilki kuwa sai da tayi kukan murna, sannan tana ta mamakin dama da gaske ne akwai iyaye masu yiwa 'ya'yansu hidima? Ba sabanin iyayansu mata da wahala?  Cikin nasara ta shiga j.s.1 mansura kullum in za su je makaranta sai ta saka direbansu ya biyo sun dauki Bily, sunan da ta ke kiran bilkisu kenan, ita kuma Bilki tace  Mansu, wani abin da yake kara ba Bilkisu mamaki shi ne, yanda mafarkin  Yarima ke kara yawaita a gare ta, ko gyangyadi take sai ta yi bare barcin dare. saboda sabon da suka yi har ta saka mishi Yarima aboki, shi ko yana kiranta Beauty, tana son sanar da mamanmu amma tasan mamanmu zata ce shirme ne, shi yasa take bar ma cikinta don ko mansu bata taba ba wa lbri ba. cikin haka hajara tazo ta ce, an samu aiki. Mamanmu tace ai ko zan yi,

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 09 馃彽 


Suka je gidan hajara inda hajiyar da za a yiwa aikin take jiransu.Bayan sun gaisa tadubi mamanmu tayaba da tsaftarta don haka tace girki nake so zaki iya? Mamanmu tace me zai hana.Nan suka sasanta ita da hajiya kilishi, gidanta na nan tudun wada, sun sasanta kan dubu uku, kuma za'a dinga zuwa ana daukarta haka nan za'a dawo da ita ko da ta samu maigidan nasu da batun sai yace,shi ina ruwan shi,ta dai sani dole ran girkinta tazo shima ta mishi,dama tasan haka zai ce,tunda shi dama baya son ma mace tace ko da bani kudin kamu,wani lokaci takan zauna tana tunani, anya maigidansu yana son lahirarshi ta mishi kyau?In'yan abinshi suja motsa haka zai je ya nado tsiranshi yazo ya zauna gaban'ya'yanshi yana ci ba zai sammusu ba in ma yaga suna kallonshi sai yace kai daina kallona ka da ka saka ni in kware.Ko ya fita bakin titi da yamma ya sayi doyarshi da kwai ya zauna yana ci in an ce yara suzo suce yaba da kudin cefane sai yace kai zauna nan kayi wasan ka shareta,kuma fa in yaron nan ya zauna haka zai cinye ya hana yaron, halin wannan mutum sai shi hakika baici sunnanshi ba.  Cikin sa'a Mamanmu ta soma aiki tana tafiya da safe in yaranta sun tafi makaranta da sha biyu suke maidota gida, in ta gama musu abincin rana domin tana son ta zo ta sallam yaranta. hajiya kilishi kan ce Dibar musu ki kai musu. Sannan karfe hudu zata koma tayi na dare, in ranar girkinta ne kuma sai shida take tafiya don ta samu ta gama na gida. Su kam su ladiyo, nan suka soma nuna hassada tare da canza mata suna daga uwar mata zuwa boyi. Su yi ta mata habaici tare da maganganu marasa dadi, kafin wani lokaci mamanmu da 'ya'yanta sun canza,sunyi kyau, saboda cima ta canza in ta kawo abincin takan dibar musu ta mika ma ladiyo tace su ba wa yara, suna zaginta suna komai haka zaki ga suna kason su sai kace daukin nama su da ya'yan suna ci tandar harshe. Hajiya kilishi tana da yara mata kusan sa'annin su Bilkisu don haka suna samun kaya. Rayuwa dai ta canza yanzu har da sabulu mai kamshi suke wanka.  Cikin haka suka shiga J.S 2 lokacin alamun girma ya soma shigar ma Bilkisu, kyanta ya soma bayyana, duk layin kowa sai zancenta yake yi, sun kuma kara shakuwa da mansura duk in da kaga zara za ka ga wata.Bilkisu tana da kulafucin karatu don haka bata da lokacin komai sai na karatu. Azumi ya matso gashi, lokacin ana fama da rashin kudi a gari, 'yar doyar da maigidan ya kawo buhu daya ce, nan ya kasata gida hudu yace kowa ya kwasa sannan kada wacce tai mishi zancan geron kunu domin ba shi dashi, cikin haka Azumi ya kama. Saboda rashin hankalin su ladiyo sai suka ce ma maigidan su fa kowa tayi girkinta kenan suna kyashin taimakon juna, maigida yace wannan lalurarsu. Mamanmu ta ji dadin hakan domin ya'yanta hudu ne,kuma dama aiki yana mata yawa,ranar girkinta yanzu kam hajiya kilishi tace ki dinga hada girkin tare da yaranki,dama ga alale da kunun tsamiya na sadaka da ake yi ana bai wa al'ummar Annabi sai kurum ta huta da yin girki biyu,in ma dakinta yake sai ta dibi nashi cikin kwano samira da kunu a kofi. Bilkisu taje ta amso, wataran ta roki direban ya kawo nan zaka ga malam maman an baza tabarma tsakar gida ana kwasar gara, cefanan wani kai ka kasa, haka matan ke ce mishi,in sunga yana rawar kan cin abinci ran girkin mamanmu,haka nan mijinta da yayi rabon kayan azumi shinkafa, masara,gero,da kuma suga sai daya ba mamanmu kowanne buhu,jikin kishiyoyinta ya dauki bari bakin cikinsu ya kasa boyuwa ita kam kowa sai da ta dibar mishi har 'yan sauran sassan da su rukarta su goggon sasa tare da matan yayyin maigidan nasu da na kannai. Wato mamanmu mace ce mai rama alkairi ga duk wanda ya mata sharri, tana da matukar hakuri tare da sanin ya kamata, in ban da haka yanda kishiyoyin nan nata suke mata kai har shi kanshi maigidan yafi mata wulakanci akan sauran kishiyoyin nata, amma hakan bai sa tayi tunanin cin zarafinshi ko kishiyoyin ta ba sai ma kyautata musun da take yi, shi yasa kullum cikin ci gaba take. Hatta abincin sadaka ko nata in tayi sai ta basu..

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 10馃彽


 Bilkisu tana tafe amma duk wanda yasan ta in ya ganta yanzu zai fahimci tana cikin damuwa,duk da cewa dama ita ba mai son hayaniya ba ce, ko yawan dariya akan hanya,ta tsaya kofar gidan su mansura tace Sakina shiga kice ma Mansu in ta shirya tazo mu tafi,mun yi latti. Sakina na saka kai Mansura na fitowa,tace "ashe kun iso?Nima naga shiru nace bari naje gidan na gani shin lafiya?Bilkisu ta dan yi tsaki sannan tace, to lafiya,suka soma lafiya mansu tana korin cewa. Gaskiya bily ban yarda lafiya ba,idanunki kamar kin yi kuka.Tace kawai bana jin dadi ne.Ko a islamiya bilkisu babu kwanciyar hankali duk malamin da ya shigo sai ya gane,saboda zazzakar muryarta mai kayata karatun nasu in suna yi yau adusashe take,haka nan kyakkyawar Fuskarta yau kam a daure take tam.Mansu ma duk ta damu suna tashi bata shiga gida ba sai kannanta tace ma ku shiga gida ku ce ma umma zan gaida mamanmu in dawo, Bilkisu ta dubeta mamanmu tana gidan aiki,mansura ta kada kai na sani ina so ne muyi wata magana,suka nufo gidansu bily.

 Sai da suka zauna sannan mansura tace wai me yake damunki ne bily? Bilki tace ba komai  Mansura. Ta daga mata hannu alamar tayi shiru, ina baza ki fada min ba to in tafi gidanmu kawai bana son dogon labari. Bilkisu tace to ni ban san ta ina zan soma ba, abinne kamar tatsuniya kin gane! Tun ina karama ne muka taba zuwa sallah bauchi,shi kenan kawuna yaje dani kallon hawan sallah, naga dan sarki, shima yayi hawan, dan yaro ne tamkar ni a wancan lokacin shi ne fa tun daga nan kullum ina cikin mafarkinshi har yanzun. Mansura tace ban gane ba? Bilki tace ai ba zaki gane din ba.donni ma da bani ce ke yi ba zan karyata ne. Mansura tace wane irin mafarki ne haka kullum kina mafarkinshi ya kara girma ko yana nan kamar da? Sannan shi ne sanadin bacin ranki yau? Bilki tace, yana girma nasan zaki sha mamaki in na gaya miki tun daga randa na ganshi, nake mafarkinshi har yau din nan ko gyangyadi ne ya dan sace ni sai nayi mafarkin shi,sunan shi Yarima modibbo, yana da kyau kuma dan kwalisa ne komai nashi da ka'idarshi Komai da lokacinshi, misali baya cin abinci a lokacin karatu,kin gane irin abun yana ce min wasan da yake zuwa muna yi lokacin wasan kenan, awa daya da rabi muke yi sai ya tafi, wai baya son shiga lokacin wani abin, kuma shi ma'abocin son girma ne, baya son raini ni fa da shi har fada muke yace ya girme ni, ni kuma in ce karya ne yanzun nan zaki ga yayi fushi ya tafi nesa dani kafin lokacin tafiyar shi yaya. Mansura taja tsaki, ni don Allah ki gaya min damuwar yau. Bilki tace kin cika garaje baza ki gane ba ne hn ban miki dalla-dalla ba. Haka muka taso tare dashi cikin mafarkina shima yanzun js3 zai je, kin gane ai jiya kuma ita ce ranar da nayi mafarki mafi muni kin aji, wai sai na isa gurin da muka saba wasa, yau ma na riga shi zuwa kamar sauran lokutan, sai dai har lokaci yayi nisa bai iso ba, na soma damuwa ga hadari har an soma yayyafi, dan tsumman riga da siket din da ke jikina suka jike dama sun sha jiki sai suka matse min a jiki iska ta shiga kada min shi, ni kadai a filin Allah,


Kamar daga sama sai naji an dafa ni ta baya ina juyowa sai nagaYarima tsaye,yana sanye ne da riga da wando na farin shara-sharan yadin shi ma din duk ya jike,nace zan tafi dubi duk na jike,ya dubi kirjina,don kirgan dangin daya soma nuna yake kallo,nace zan fa tafi fa,in gaya miski mansu sai jina nayi a jikinshi,na soma kai mishi duk ina cewa,bani son iskanci an ce maka ni yar iska ce?Yace ke wawuya ce beauty wani wasa Zan koya miki In dai takaita miki wai sai gani ni da shi muna...Mansura ta rufe mata baki ita kuma ta fashe da kuka,mansu tace shi ne to na damuwa ba a cikin mafarki ba ne?Nace bara fa kiji tashi nayi na ganni cikin jini...Jini? In ji mansura,bilkisu tace eh shiyasa narasa yanda zan yi,kuma na kasa yaya ma mamanmu tsorona daya kada ace ina da ciki mansura tace gaskiya ne kin sani yanzun muje mu samu.Ummarmu tunda ita tana aikin asibiti ne zata sani,da sauri bilki ta mike.Sun same ta tana sallah suma suka yo alwala har zasu tada salla,mansura tace kin mata malam yace,inda jini jikin mutum bazaiyi salla ba Bilkisu tace ai yace jinin haila ni ko wannan ba haila bace bana ma yin wannan, wannan fa kin ji yanda aka yi jinin fa yazo, basu ji shigowar umma ba sai suka ji tana cewa wane irin jini ne? Tsuru-tsuru suka ji tace da ku nake fa, kuka bilki ta soma yayin da mansura ta soma magana cikin in-ina, gaya mata dai. In ji mansura, cikin kuka bilkisu ta shiga bai wa umma labarinta da Yarima har zuwa jiya, a karshen lbrin ta dora da cewa ni tsorona kada ace ina da ciki. Tamkar umma ta kwashe da dariya, amma sai ta boye tace kin san haila ko? Bilkisu tace malamin fikihunmu yana mana bayani amma ban santa ba, umma tace to haila ce ta same ki, batun mafarki kuwa sai dai na kiya ya dan tsoratani, yanda ki kace tun kina karama, Allah yasa ba aljanu bane suka fake da Yariman da ki ka gani? Kin san suma shu'umai ne, amma zan yi batun da mamanku.

 Sannan ta dube su tace, yanzu abin da zan ce muku shi ne dake da ki ka balaga da ita din da bata soma ba na sani tana kan hanya, ku kula. ta dai ja musu kunne.ta fita sai gata da part ta nuna mata yanda zata yi amfani da shi, umma ta samu mamanmu sun zanta kan batun mafarkin Bilkisu, mama tace bana zaton maigado tana da aijanu, kinsan in ka kallafa abu a rai dole ne kayi mafarkinshi, tun tana karama da taga dan sarkin garinmu shi kenan bata da zance sai nashi.  Umma tace to bilkisu tana da nutsuwa sai dai ki kara ja mata kunne ko in ce nasiha, tunda yanzun ta girma sai da saka ido, dan yau sai Allah. Mamanmu tace Insha Allah komai zai zo da sauki,Allah dai ya shirya mana daukacin ya'yan musulmi.Umma tace.Amin,yau din ce tayi wuya,sai ki ga yarinya ta tashi da hankali da nutsuwa,ki daga ki yi mata tarbiyar kwarai daga baya sai kiga samari ko wasu kawaye sun rusa komai. Mamanmu tace kwarai dole ne mu sanya ido kan ya'yanmu, wadannan irin kawaye ne suke tare dasu,haka nan kar mu yarda da samarin banza.

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 11馃彽


Da wannan hirar suka yi bankwana.Tun daga wannan lokacin take tsoran maza sam bata son wata hulda ta shiga tsakaninta da kowane namiji,balle da mamanmu ta kara nuna mata cewa kar ta yarda da 'yan kananan samarin nana masu bata yara suna kai su suna barowa.Mamanmu tace ki lura don shi da namiji duk abin da yayi ado ne,  ke kam mace ce duk in ki ka yarda aka bar miki abin kunya shi kenan rayuwarki ta lalace,koda ba ai miki ciki ba da an kau miki da budurcinki shi kenan,duk mijin da kika aura baki da wata daraja ko mutunci a gunshi in me kawaici ne zai daure ya barki da Allah,in ko mai zafin kishi ko in ce wanda ba zai iya hakurin bane kisha magana gori har yaranki suta so yana miki don haka ki kula. Bilkisu yarinya ce amma akwai zurfin tunani, domin tun daga nan tasa ma kanta da nazari kan maza ana ta ganin maza sun cika son kansu musamman in tayh duba ga mazan gidansu tun daga kan yayun da kannai na mahaifinta tare da shi kanshi mahaifin nata mazan gidansu daidai gwargwado suna samun kudi da irin sana'ar da sukeyi. Amma sam ba sa biyama iyalansu bukatu, ya'yansu babu boko babu islamiyya, sai yawon talla, kusan duk matan gidan su ke ci da kansu da kuma ya'yansu,ba sutura, amma abin da yake bata mamaki yanda su kuma matan ke faman gasar haihuwa tare da fada da kishi mai tsananin a junansu, saboda mijin da bai san darajarsu ba, ita kam ta gode Allah da yasa mama ta kasance uwa agare su don ta tsaya musu da tarbiya da ganin sunyi karatu sun zama yaran kwarai, kuma insha Allah baza su bata kunya ba, sannan su zama rahama gare ta ba kamar yanda yan gida da suke cewa  wahala bashi yasa ko cikin mafarkinta yanzun bata sakar ma Yarima fuska sannan ta dage da addu'a kan Allah ya yaye mata mafarkin Yariman nan. Haka nan hasashen umma na cewa, ko Bilkisu tana da aljani ne ya saka mamanmu cikin tunani don haka ta samu mijin Aminiyarta Hajara tai ma malam mudi bayani, shima da ya yi Istihara ya gano bata da aljanin kowa, don haka yace da mamanmu rudin ne kurum irin na mafarki kada ta damu don haka sai ta kwantar da hankalinta.

 tare da ci gaba da neman na rufin asirinta gurin Allah


 Yau da gobe asarar mai rai in ji yan' magana gashi Bilkisu har an shiga ss1 lokacin tana  da shekaru sha shidda, daukacin unguwar Oja da kewayenta labarin kyawun ta ake ita har mamaki take yi idan taga mutane sun shagala da kallonta,  farinta irin farin nanne fes jikinta na dauke da lafiyayyar fata me laushi sumul- sumul suma kwance jikin fatar sai ka zata cikin AC take kwana doguwa ce amma ba can ba, dirin jikinta irin mai wahalar samu din nanne danko ta keru, farin da jikin duk na mahaifiyarta ne, 


Ko mace'yar uwarta kan shagala gurin kallonta, gefen kumatunta ya kan lotsa ko da magana zata yi shi yasa duk sanda ta fita sai taga jama'a na kallon ta sai dai abin mamaki bata taba samun ko da wasa wani da namiji Yazo yace yana sonta ba, hakan bai dame taba nata ganin rashin sakin fuskar da take yi ne in zata fita da kuma tsoron da ta kema mazan, dama bata bukatarsu tunda ana ta ganin sun cika zalunci tare da dan nema mata hakkinsu shi yasa basu ne a gabanta ba, amma ga mamanmu tana son taga cewa Bilkisu tana da tsayayye kafin ta kare secondary in yaso taci gaba a dakinta, sai ga shi mansura samari sun mata Caa! Haka Sakina da Maryam kannan Bilkisu wadanda ke j.s 2 yanzun haka, sannan'ya'yan su ladiyo duk ba Sufi sha biyu sha uku ba amma duk suna da samari yan cikin gidan yayaran yayin mahaifinsu.


Malam mamman ya shiga dakin mama tana zaune kan dardumar da ta idar da sallar isha'i, ta amsa sallamar da yayi tare da fadin sannu da zuwa, yace yauwa. Ya zauna " Dama nazo ne kan batun Bilkisu , don na kula yarinyar bata da mutunci shi ne ma dalilin da yasa ban taba ganin saurayi yayi kiranta ba, sai dai kannanta, kila tana nufin sai me mota ne ko? To ba zan yarda da zamanta ba, ba ruwana da wata bokon baza can, ke da ki ke daure mata to ki gaya mata na ce aure zan mata, mama ta sanyaya murya sannan tace to kayi hakuri amma ma yarinya take da za ka daga hankalinka? 


Yace ke Fatima ban San zancan wofi su suwaiba ba kannanta ba ne? Tani da Amina duk sun sasanta dasu Jibrin, don haka ba ruwana da wani lokaci , su ladiyo sun Fiki tunani, tunda suka sa  'ya'yansu suka fito da miji sai kece oho na fahimci gaskiyar su ladiyo ne da suka ce kin ce ke'yarki sai mai kudi ko? 


Zaku ga kudin in nayi sada ka da ita kuma almajiri zan ba sadaka, ya fita yana mai ci gaba da fada har zuwa gurin mahaifiyar shi wato goggo amarya nan ya shaida mata nufinshi na sadakar da Bilkisu ta ce jeka ba da ta in ma mahaukaci zaka ba shi, uwarsu ta ci dogon buri akan su bari ka ji in shaida maka in har ka sakar ma wannan matar taka fuska to zaka yi da ka sani , tunda ta daure ma ya'yan ta mata suna wannan bokon na san cewa tana da mugun kuduri nufinta ta tarasa suyi mana gandan- gandan a cikin gidanka, ya zama kai ba da kayi bata karba saboda ka jibge balagaggu cikin gidanka, tashi kaje duk nufinta ni na sani burinta kenan sai mai kudi....


 Yan rigingimu sun faru cikin yan kwanaki in da su ladiyo tare da sauran dangin na maigidan suka yi ta zuga shi yana zuba wa mama da ya'yanta wulakanc.  Bilkisu tana zune ta ma kasa cin abinci,saboda hankalinta yana tashe ne, yan kwanakin mansura tana zaune gefenta tana lallashinta, can cikin daki kuma mamanmu ta tasa su Sakina tana musu nasiha kan cewa ba su isa kula samari ba, shekarunsu ko sha biyar basu kai ba sakina tana sha hudu maryam sha uku maigidan ya shigo da fada yana cewa ina Bilkin ne? Da sauri ta mike tana matukar jin tsoro shi, yace fita maza ga bakon ki can waje shi ne mijinki shi na baki, saboda bakin jininmu,na idar da sallar la'asar na tashi ina cewa ina da 'ya duk mai bukata na bashi amma na rasa mai so sai da na toho hanya sannanna ci karo da wannan dan garuwan shima sai da na roke shi arziki da kyar ya yarda sauran ki mishi wulakanci, cikin kuka ta fita yana tsaye jikin gidansu riga daban wando ma haka, kuma duk na shadda, kodaddu sun jike, ta isa gurinshi tace sannu da zuwa.

Baki ya saki yana kallonta,cikin in-ina yace ke ce kece babanki ya bani?Ta daga kai yace,tab gaskiya kin fi karfina,wannan rike ki ai sai gwamnatin tarayayya,karamar hukuma ma kam ba zata iya ba.Ya tafi yana waiwayanta yana cewa kaga mutum zai cuce ni? gida ta koma cikin jin dadi tana gaya masu mansura da su mamanmu abin da ke faruwa.Muryar babansu taji ya kwala mata kira, da sauri ta fita.Ya dube ta kun gama magana ko?Tace ya dai tafi ne.Yace kina nufin baku daidaita ba?Ta daga kai alamar eh.Yace ki dai ce kin koreshi,yau ko kyaci ubank.Ya ciro igiyar guga ya shiga dukanta,mama sarkin hakuri tana jiyo su kuma zuciyarta na zafi amma haka ta daure bata fito ba,sauran matan sai dariya suke ba wadda tace ai hakuri,jina-jina yayi mata ya fita yana zage-zage,ru mansura suka kamata suna kuka suka shige daki.Tun daga nan kullum cikin turo mata maza yake,amma kamar hadin baki duk wanda yazo sai yace tafi karfinshi hakan nan shima bai fasa dukanta ba,har bikin su suwaiba yazo aka yi biki aka watse Sannan Bilki ta dan sama sauki sai dai sun sha habaici ranar bikin, wannan bai dame su Bilkisu ba. Maryam zo ki jawo min ruwan wanke wanke. Cewar Bilkisu, tace Allah sarki Anty Bilkisu dazun fa nice na ja miki na wanki ga Sakina can Allah bata komai. Sakina ta fito tana cewa, sannu da cewa bana komai wa ke gyaran daki? Bilki tace maryam ja min ruwa sakina je ki karasa gyaran dakin, ladiyo ta dubi karima tace. Allah mun huta su tani ana can dakin kai, salame ta cafe ai yafi musu ni in bar 'yata gwansame duk wanda ya shigo ya kasa gane waye uwa wacece yar. Karima ta kalli Bilkisu, sannan ta kalli su Salame, Ya'yan namu sun da farin jini ne, amma wasu zaki ga ga dai kyau sai a rasa ma shinshini. Ladiyo tace kin kaita da nisa, kin manta da wadda uwar ke fita yawo boyi gidan masu dashi, ya'yan na gantalin boko, amma babu mashinshini. Karima tace babu ya babbar kullum sai uban ya kima, su kasa dariya,daidai sanda Sakina tazo tana ce ma Bilkisu.Anti Bilki ina abin kwashe shararmu

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 12馃彽


 Kafin ta bata amsa sai ta ji karima tana cewa don tsabar bakin jini irin na o'o sadaka ma an rasa mai so, duk yanda maza ke son mata amma an rasa mai sonta.Sakina tace,aikin banza sa'idawa.Salame ta mike ke mara kunya waye mai saka idon? Bilki tace ke sakina kin hauka ne? Su karima suka soma masifa amma sakina bata yi shiru ba,fadi take toni da ku nake? Kuna maganarku,nima tawa nake yi. Bilki tace wuce daki bana son rashin kunya.Ladiyo tace yi min shiru munafuka ke kike sata bata son hayaniya don haka sai ta mike ta nufi dakinsu.Cikin haka har suka shiga ss3. Lokacin 'yammatan duk sun kawo,hatta Asma'u auta an soma girma, ga malam mamman kullun cikin fada yake kan cewa ya gaji da ganinsu sannan duk cikin dangin su ya cigita koda wanda yake so amma sun ce sam saboda tsana, cikin haka suka soma jarabawar sauka mansura da bilkisu sunfito daga gidan su mansura zasu zo gidansu Bilkisu a kofar ghda suka ga Sakina tare da wane dan yaro suna hira....

 Mansura tace Bily gaskiya ki masu sakina magana su daina kula kananan yarannan ba fa aure za su yi ba, sai dai bata yara. Bilkisu tace kin san sakina da shegen musu in na musu magana sai suce wallahi ba samarin su bane 'yan makarantar sune bari zanyi maganin su yau sun samu mama tana cin abinci suka zauna mansura tace mamanmu zan ci tuwon nima, ta turo mata kular gashi nan ki saka gamiyar can cikin tukunya wata nayi kin san yau ladiyo ce ta yi girkin mansu tace. A'a mamanmu ba an raba girkin ba? Bilkisu tace kin san matan gidan sai dai shirin Allah sun kuma cewa sai dai a hada,Mansura ta ture kular tare da cewa ba zan ci tuwon wannan kazamar ladiyon ba. Bilkisu tace yauwa. Mamanmu, gaskiya kima su sakina magana su daina kula kananan yaran nan, ga masu sonsu 'yan mutunci, ai gara ma su fitar da mazan saboda fadan baba ko yaya ki ka gani tunda suna j.s.s3 ne sun ci gaba can dan fadan baba yana daga min hankali ta soma hawaye duk dana tsani maza da ace na samu mai sona ko yaya yake Allah zan yi aure ne..

 Ko dan ke ma ki huta da gorin'yan gidan nan, mansura tace haka ne tunda suna da manema, cikin tausayi mamanmu  tace maigado kena ke tunani bana son su riga ki aure,gashi naso suma suyi karatu mai dan zurfi.Bilki tace kada ki damu aure da mutuwa duka na Allah ne,kema zaki samu saukin fadan baba in kin rage biyun,suna cikin tattaunawa ne maryam ta shigo mama tace mamina daga ina?Tace banace miki Ibrahim ya iko kirana ba?Tace yauwa dama ina son in ji shin da gaske ne auran ki zai yi?Maryam ta sunkuyar da kai kasa tace tun tuni fa yake cewa zai turo na ce mishi a'a saboda ga antinmu nan bata yi ba.    Bilkisu tace kin ji shirme,to dama in yazo kice mishi ya turo tunda ba boyayye ba ne,kowa yasan gidansu akwai mutunci,mansura ta duki kafadar bilki tace kai su Bily akwai shegen manyace,suka sa dariya bily tace Allah kuwa na sakina ne wannan Abdul din nake ganin sai an dan yi bincke kanshi,saboda don kano ne Mansura tace shin kece za ki bincika?Bilkisu tace,to hakkin baba ne kema kuma kin san ba zai yi ba amma a san yanda za'ayi ko Mamanmu? Ta ce dole kam.


Bayan binciken da Mamanmu ta saka aka mata kan mai son sakina ta hanyar mijin hajara suka gamsu da maneman sannan ta basu dama suka fito aka sa rana. Walimar saukar su Bilkisu tazo inda aka yi a cikin harabar makarantar tasu.  Bilkisu ta amshi kyaututtuka, kamar su'ya mai ladabi ta daya, tsafta tare da taimakon malamai, wato in ba malami sai a sata ta koyar da yaran. Mamanmu sai da tayi kukan murna, yayi da labari ya karade unguwar, Umma ta shirya musu walima ta musamman tare da buga musu kalanda da sauran abubuwa, wai! Nan Abu ya ba su Ladiyo haushi in da suke ta yar da habaici.


Washe garin walimar, wai a banza tunda ba walimar aure bace, shi kan shi baban su kanshi kato yake duk Wanda ya mishi murna, sai ya yi ta fadi 'yarshi tayi sauka amma bai taba basu koda biyar din fensir ba. 


A gida kuma cika ya shiga yi yana cewa bata da ladan komai dan ta sauka tundaba aure tayi ba, ga Bilkisu duk ba wannan ne a gabanta ba, mafarkin Yarima da ya zame matan masifa shi ne matsalarta, ko gyangyadi ta yi sai ta ganshi, ga rashin mashinshini ta rasa me ke faruwa da ita. 


Duk abin da aka sama rana ai yazo, sai ga Bilkisu Sakina yazo,  'yan Bauchi sun zo tun sauran kwana uku biki, ranar ce kuma aka kawo a kwatunanan da ket suka kawo, kaya masu tsada da kyau Ibrahim yana aiki ne a zonal office Kaduna, don haka ma can za'a kai ta, yayin da Sakina zata yi kano  Abdul dan kasuwa ne in ji  ' yan magana suna cewa, Dan kasuwa mai kamar wani sarki.


Su Ladiyo sai zunburar baki da jin haushin maigidan ga zaton su duk abin da ake facaka dashi tun kafin ranar daurin aure shi yayi, basu San ma daga in ake da shi ba, ya kawo kudin sadakin da ya amsa naira dubu ishirin- ishirin ayi amfani da kudin ba, da kyar ya ba da dubu ishirin yace ya dauki dubu goma-goma cikin sadakin kowaccensu, cewarshi zai ci da su ne a banza?  Mamar tace sadakin hakkin yara ne amma tunda ka ce haka shi kenan yaje ya dauki ladan tuwon ko kuma kudin hatsin da ya ba su. 


Hajiya Kilishi uwar dakinta, hakika ta taimaka sosai, domin ita ce ta yiwa yaran kayan kicin, baban Mansura shi ne ya yi musu gara,  yan Bauchi kawunan amare tare da sauran dangi kudi suka kawo,  akwai da shin da tayi gidan hajara nan ta hada aka je kasuwa aka hado musu kaya na gani da fada, Umma ita ce ta sai musu zannuwan gado da labulaye, sadkain su kuma a hannunsu mama tace aba su, amma su kace sun bata. 


Biki yayi kyau komai cikin tsari dangin uba kam ba wata gudunmawa sai dai su cika gida sunata Jan girki tare da yiwa Bilkisu shaguben tayi abin kunya kannanta sunyi aure sun barta, abokan wasanta kam sun fake da wasa sun cacaccaba mata magana . har da cewa kyau bai ji rana ba. Tun da ba mshinshni kyan Dan maciji batun ya bata ran Bilkisu amma Mansu tace kada ki damu Bily wani jinkirin alkairi ne, amma ba mutane duka ba ne suka San haka ba. Bilkisu ta ce don tani ban damu ba surutun ne bana so kawai, amma nima basa gabana.

[4/21, 01:44] A~PROF: 40. Biki ya tashi lafiya, kowa na sambarka, gudunmawar da ta samu na kudi daga abokan arziki tace da Umman su mansura ta aje mata saboda komai gada,Allah zai fito mata da nata,Bilkisu sun gama zana jarabawarsu cikin sa'a sun riga su mansu da kwana biyu suma suka gama mamanmu ta ce maigado ki shirya kije ki ma ummata kwana biyu mana,tunda baki shiga sana wayyar ba mana? Cikin murna tace kamar kin shiga raina mamanma,Asma'u auta tace zan je Aunty maigado.Bilkisu ta harare ta auta zan fa duke ki in har ki ka kuma ce min maigadon nan, tace na daina to zanje Aunty Bilki?Tace a'a ke kam ki na da islamiyya.   Mansura ta dube ta,Bily ba zaki bari sai week end in Abbanmu yazo mu tafi tare ba?Saboda nima zan je gombe ne. Bilki tace,nan da kwana hudu zan fi kowa son muje tare,amma zaman nan da zan yi na kwana hudu zan sha gori da habaicin 'yan gidanmu, kan cewa na rasa mai sona."ta dafa kafadarta, kada ki damu mansu, zan tafi goben in yaso in zaku je gombe sai na baki adireshin kizo nima ba sai naje na gaida yan gombe ba

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 13馃彽


Mansura tace to shikenan muje ki rubuta min adires din, kuma zan zo da safen na raka ki tasha Bily tace to Mansu.suna tafiya a hanyar sun rike jakar su biyu kowa ya rike hannu daya,Bilkisu tana zayyane ma mansu abin da ya faru yanzu, waton abin da mahaifinta tare da kishiyoyin mama suka mata,mansura tana tsananin son bilkisu, don haka itama taji haushi tare da takaici amma sai ta ce kiyi hakuri, ba komai ke damunsu ba sai hassada,bilki ta dube ta kin sani ne mansu? Taci gaba. Wallahi duk da tsanar dana ma maza saboda wannan abin da ake min yasa nima yanzun nake jin na kosa in yi aurannan, tsaki mansu tayi tare da cewa, duk ma nawaki ke?Don Allah kada ki saka kanki cikin damuwa. Haka taci gaba da lallasinta tare da bata hakuri har suka kai gurin mashin, tace ki koma sai na ganki tace a'a sai  naga tashin motarki, haka kuma har gareji ta raka. Bilkisu sai da motar ta tashi sannan mansu ta koma cike da kewar aminiyarta kamar yarda ta bar Bilkisun cikin tunaninta, suna son juna fiye da zaton mai karatu,

 Ba ma kmar mansu, tana tsananin son Bily, sukan su iyayanta sun san haka, don tun suna yara ko dinki ne aka mata in ba ama Bily ba sam bazata saka ba komai sai dai ai musu tare,shi yasa ko mamanmu ma in ta dauki albashinta in har zata sai ma Bilkisu wani abu tare take saye.  Umman mama taji dadin zuwan Bilkisu don duk cikin jikokinta tafi son ta domin tana da hankali, sannan tana koya mata karatu tare da addu'o'i. Bata manta wani hutu da tazo ta koya mata zikirorin sallah,gasu nan har yau tana yinsu. Adda wata yar dattijuwa ce da su kawu Aminu suka daukarwa umma suna biyanta tana tayata yan aikace-aikace,don ma umma akwai ta da juriya tare da kazar-kazar.Bilkisu tana son bauchi tana jin dadin zama da umma tun jumma'a ta damu yan gidan da labrin zuwan mansu,umma ma ta damu tana son taga mansura nan dai,ga tsarabar mansu da tasha,sai dai har lahadi ba mansu duk ta damu. Monday gidan kawu Aminu ta kwana,ta tatara ta wuce gidan kawu Abubakar ko'ina taje sonta suke su da ya'yansu.

 Ran Jumma'a tana kwance kan gado umma ta tafi masallacin jumma'a adda tana wanke-wanke sai kawai taji sallama muryar mansunta ce da gudu ta fito tana fadin oyoyo mansuna.nan ta yar da jaka suka rungume juna,sai yau ki kazo? mansu na shiga damuwa,tace bari ke dai Bily,Abbanmu ne ya kwafsa min,tare da shi ma muke yana waje,da sauri Bilki ta dauko hijabi ta debi ruwa suka fita,suna cikin gaisuwa sai ga umma ta dawo,nan tace ya shigo ciki,ya shhiga suka gaisa nan kuma yayi mata sha tara ta arziki yace shi zai wuce kaduna ne,shima satin shi daya a gombe suka mishi rakiya ya tafi. Da dare suna kwance kan gado barci yaki zuwa sai hirarsu suke yi, mansura tana ba bilki lbrin tun wancan satin suna gombe,tace har kuka na yiwa Abba akan ya kawo ni nan amma ya ce sai ya tashi tafiya. Bilki tace nima haka nan duk na damu,mansu tace albishirinki?Bilki tace goro kwarya goma sukayi dariya,tace.Abba yace kafin mu dawo zai saya mana form na jamb,murna bilkisu ta somayi domin da har ta debe tsammani da karatu tunda abin na kudine

 

Suna tafe a kan hanya suka ji anata horn bayan su amma duk suka share 

 Ganin basu da niyyar tsayawa ya saka shi fitowa ya biyosu, assalamu alaikum yace musu,suka tsaya mansura ta jujo yayin da Bilkisu ta sha mur tare da kin juyowa,don Allah zan iya magana daku ko da na yan mintina ne? Mansu tace muna jin ka, yace nagode gaskiya ni dai na ganki ne nake sonki,mansu tace wa ni?Yace kwarai,tace gaskiya an min miji,sai dai wannan Bily ta dube su cikin daure fuska tace,ni matar aure ce, ita ce budurwa,dan kyakkyawan saurayi yace,ai ke kam nasan kin fi karfina shi yasa ma banzo nan ba jama'a na kaini  inda Allah bai kai ni ba,kalmar nan ta kinfi karfina tana ba su Bilkisu mamaki,shin dama mace tana fin karfin namiji?Bilkisu ta daure tace,na gode da ka gane haka,yanzu dai na baka kawata,domin na ganka da alamu na masu hankali,yace nagode sosai,ni sunana Umar Faruk Sulaiman ni mutumin gombe ne,nazo gaida kanwar mamana ne a nan bauchi,sannan ina aiki a kaduna ne, tare da bankin PHB, ku fa?Bilkisu tace mu yan zaria ne,

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 14馃彽


Amma batun dogon bayani sai mun sake haduwa,yace a ina? Kuma yaya sunan kawar taki?Tace sunanta Mansura,ta nuno mishi gidan su umma daga nesa ga gidan kakarmu can in ka samu lokaci a nan zaka ji sauran batu, taja mansura dake tsaye tamkar wawiya tana jin su,yace nagode ko zan rage muku hanya?A'a mungode,cewar Bily Gidan uncle suka kwana,kani ne gurin umman mansu,adaran farooq yazo nemansu basa nan,sai da yamma suka soma shirin dawowa,anty salma matar uncle itama tana ta yaba kyan Bily,haka sanda suka taho kowa sai ya tsaya yana ta kallonta,ta saba ko zaria haka take fama da kallon nan,kullum mutane suna ganinta amma tana fitowa sun dinga kallon ta kenan. Sun idar da sallar isha'i umma tana basu lbrin zuwan bakonsu,sai ga dan aiken mansu tace,Bily ba ki kyauta min ba,meyasa ne zaki jona ni da mutum?Ko sauraran mansu bata yi ba,tace da yaron kace tana zuwa.Wasa wasa saida mansu taga bacin ran Bily sannan ta fita gurin farook,sunyi hira kuma yaji komai dangane da mansu sun yarda dajuna da suka ji  yangari daya ne

Mansu tana son farooq sai dai tana tunanin Bily bata son tayi aure,ta barta don haka tayi mata shawara su aure shi tare mana? Hkan ya kusan kawo musu rigima sai dai umma ta tsawata sannan mansurta hakura.Satin mansu biyu ita kuma Bilkisu hudu Abba yazo yace zai wuce gombe ne,jibi zai zo su tafi saboda monday zasu soma zana jarabawa,don haka su shirya ran jajibarin tafiyarsu.Sun yi sallama da kowa kawunan Bilkisu sun musu dinke-dinke tare da tsarabobi, umma tace gaskiya ya kamata kuje gomben ne don haka kawu Abubakar ya saka su cikin mota yayi gombe da su sun ji dadin ganinsu Abba ma yace shi kenan ya huta tsayawa.Daren ranar ne Bilkisu cikin mafarkintan nan na fama,Yarima ke ce mata,kiyi kokarin sanin wanene Yarima kafin ki bar bauchi da safe kam suka dauko hnyar zuwa gida, zuciyarta cike da tunanin wanene Yarima?Meke faruwa tsakaninsu? Umma da mamanmu sunyi farin ciki da ganin yayansu Bilkisu har wani kyau ta kara tare da yar kiba duk da cewa ba wani jiki ne da su ba.

Sun zana jarabawa cikin sa'a duk su haye,Abba ne tsaye kan komai har suka samu shigewa Bilkisu ta samu fannin da take so na yayinda Mansura ta hakura da gefen lissafin don bashi ta nema ba,baba ya tambayi mamanmu shin wani sabon karatun ta kama?Mama tace to Allah bai kawo miji ba,ai sai aci gaba da karatun ana cikin yi in mijin yazo ai dole ne ayi auren, yace ba wani,na lura Fatima akwai burin daki kaci akan yarinyar nan, amma nasan maganin abin ya fita yana zage-zagenshi,mama ko cewa tayi Allah ya kyauta. Haka rayuwa taci gaba abubuwa na faruwa yau sauki gobe tsanane  shekararsu ta farko, lokacin ne farooq ya matsa kan batun auran su da mansu.Tun dama ita ce mai jan lokaci wai ko Bilkisu itama zata samu ko da cikin school din su ne amma duk son mata irin na yan jami'a babu wanda ya taya Bilkisu,sai dai kallo wasu har tuntube suke yi in suna tafe suna kallonta,bisa ga wannan dalilin ne yasa mansura ta jira yi zuwan farooq wannan satin da yake kaduna yake aiki shi yasa duk sati yake zuwa shima yazo..

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 15馃彽

Da tashi damuwar tason ya turo magabatanshi zaman gaurantaka ya ishe shi, yana bukatar mace a kusa dashi. Don kada yaki yarda da batun yasa tasha kunu kafin ta bude motar ta shiga ganin yanayin tane ya fadar mishi da gaba saboda nan duniya ya tsani yaga mansura cikin damuwa,yace meya tasani yaga mansura cikin damuwa,yace meyafaru.Sweetyna?ta sake daure fuska gaskiya ni ina ganin zai yi wuya muyi aure. Cikin tsoro yace,saboda mene?Tace saboda Bily,gaskiya farooq ba zan iya aure in bar Bily ba,sai dai ka zaba cikin biyu,ko dai ka aure mu tare,ko kuma mu hakura da juna zan jira ta in ta samu sai muyi tare,baki ya saki tare da bin ta da ido,dariya ma ta bashi yana dariya yace kuruciya kenan,kowa da irin tasa,haushi ya kama ta,tace dariya kake min? Kuma nice kuruciya shekara ashirin shine kuruciya ko?Ta juya zata fita,ya riko ta haba mansura,me yasa kike irin wannan magana?   Yaya ma zaki ce in auri Bily?Gaskiya bazai yiwu ba.Bily tafi karfina, bani da halin da kera gidan da zan sakata. Cike da mamaki ta kalle shi kana nufin sai me hali ne zai aure ta, ka kalli gidan su mana. yace ke baza ki gane bane,kuma nima ban san yanda zan miki bayanin yanda nake ganhnta bane,so mu bar maganar.tace to shikenan,Allah ya hada kowa da rabon shi,zata fita yace ban fa gane nufinki ba?Tace ai zabi na baka,kuma kace mu bar zancan cewa zaka aureta,wanda haka yana nufin ni da kai sai bankwana.Ta fice ta bar shi zaune.Mamakinta yake yi yasan takan komai in ta kafe sai dai ya hakura ko kuma ya hada tada Bily,don haka sai ya tashi motarshi sai gidan su Bily,dai dai wannan lokacin tana kwance cikin daki bisa gado jikinta rinkif da zazzabi.Asma'u auta taje ta siyo mata magani,mama tana kofar dakinta yayin da su ladiyo suke zaune a gindin murhu, suna cin tuwo hira suke yi kasa-kasa ba a jin me suke fadi sai dai ajiyo dariyarsu,yaro ya shigo yace wai an ce ana kiran Bilkisu,nan take suka katse dariyarsu,kuma suka shiga kallon-kallo, mama ma taji daban don ba a taba hakan ba,tace in ji wa?

 Yar yace in ji wai farooq,mama tace kace tana zuwa,ta shiga daki tace ke maigado ki zo saurayin mansura yana kira, ta sauko tana tunanin anya lfy?Don ko yaushe yazo tare da mansu suke zuwa, sai ta shigo su fita tare tana fita ladiyo ta kwala ma yarta Basira kira,tace zo nan Basira,suka yi mata rada ta fita da gudu,jim kadan ta dawo da gudu tana tsugumawa a gabansu tace wani ne a mota na ganta,a gidan gaba ta zauna,karime tace kin ji ko?Gaskiya gobe zamu koma kusfan na kada mlm yayi mana haka?Salame tace na ma kasa mgana,saboda ko kwanan nan nawa muka bashi? Ladiyo tace niga bashi ma da ake bina ban biya ba,na kuma ciyo wani muka hada muka bashi haka nan suka ci gaba da tattaunawa tare da shirya yanda zasu yi.A cikin mota farooq ya rattafo ma Bilkisu yanda suka yi da mansura, amma sai yace mata shi ne nazo in ji naki ra'ayin. Ran Bilki ya baci tace muje gidan,a fusace ta shiga dakin mansura, bakin gado ta same ta ta zuba tagumi cike da takaici ta dube ta,nagode mansu tallat ma ki ke yi,.

ki sani koda Farooq ya amince ni ba zan yarda ba,kuma in har kina son mu shirya dake gara ma ki fito ku sasanta,in kuma kika ki ni dake zamu hakura da zumuncin haka nan,wanda muka yi baya Allah ya bamu lada,tafita da gudu mansu ta biyo tazo kiji Bily,daf da kofar fita ghdan ta rike ta wallahi  Bily ba wai ina tallarki bane,ya matsa min da zancan zai turo ni kuma gaskiya bazan iya aure na barki ba,Bilkisu ta girgiza kai tare da rike hannun mansura,kada ki manta mansu kannaina da muke ciki daya sunyi aure,yanzun haka duk suna da tsohon ciki ne,ki sani aure yana gaba da komai a gurin mace, Allah bai ce wani ya jira wani ba,kin sani ko ni bana daga cikin matan da zasu yi aure a duniya?Ta numfasa muje gurin shi,da kyar suka shawo kanta ta yarda ya turo daran ranar,Bilkisu bata yi bacci ba yau ce rana ta farko da ta soma zubar da hawaye,saboda rashin masoyi,wani kunci ta samu kanta ciki. Gurin binciken wanene farooq su Abba suka gano ashe mahaifin shi abokin Abbane, zamanin suna secondary wannan yasa suka tsaida

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 16馃彽


Tsaida bikin watan may,wata biyu kenan, shirin bikin suka kama saboda babu lokaci ishasshe,Mansu dai rigima suke tasha da farooq,duk da irin lallashin da yake mata. Ana sauran sati biyu bikin yace za'a kawo akwatuna,nan tasa mishi rigimar in dai bai yi ma Bilkisu komai da yayi mata na akwatin ba,wallahi ba zata taba saka kayan ba,kallonta ya tsaya yi yana tunanin kanta daya kuwa?Yace kin san nawa na kashe mansura?Tace ni ina ruwana ko gida bana saka kaya in har bata da irinshi in ma kasan  baka da halin yi mata tun kan a kawo kaje ka raba mana wanda ba iri daya ba ne ka canzo ta fitittike taki sauraronshi kan dole yaje ya sayo zannuwan da ta kalman zuwa gyalulluka,kayan shafa da akwatuna ne bai sa yaba da 'yan kunne,yaje ya aje,randa aka kawo akwatuna suna makaranta amma sun san da zuwan 'yan kawo kayan,tunda yan gombe ne zasu amsa daganan sai suka hadu da danginAbba da na farooq su kawo zaria, kawayen,umma ne suka tari yan kawo kayan kaya ne na ban mamaki, da suka dawo daga mkrnta gidansu Bilkisu suka zame

 Mamanmu tana basu labarin kaya,Bilki duk ta matsu suje su gani, masha Allah in ji bilkis time da ta gama duba kayan,umma farooq yayi kokari,mansu kam kosawa tayi yazo ran sati don ta ji ina na sahibarta? Ya kam iso da kayan cikin katuwar akwati guda daya ko rufuwa bata yi, amma sai mansu tace ita kam sai ya sayi set din akwatin,yace haba mansu wlh account dina yanzun ba ko naira,yakike son in yi? Tace to gaskiya zan je in ciro 2 ka hada mata da wannan ni  sai na dauki biyu da ket,yana mamakin wane irin so ne wannan mansu take ma Bily?Suna cikin haka sai ga bilkisun, da fara'arta ta kwankwasa glass din motar a tare suka fito tace brother kasha kamshi fa,yace kanwata ya gari da shirye-shirye? Tace mungode Allah,ya naku? Bata jira amsar shi ba, ta dubi mansura dake cika tana batsewa,tace yaya ne mansu any problem?Mansura ta dan daga kafadunta alamar babu dan bata son tasan maganar. Farooq yace akwai ya koro mata komai, kasa magana bily tayi kallon mansu kurum take yi...

Kafin daga baya tace laifin kane farooq daka ki sanar dani harka biye mata kasiyo kayan yanzun kuma zaka juya da sune ka mai da bana so kuma na lura mansu bata son mu rabu lfyne, ni da ita,shawarar da zan baka kai namiji ne,kuma sai yanda tace zaka sha wahala don bata da hankali kasa ni kai ne mai bada umarni da hani suna gurinka,so be carefull,kaya kuma nagode bana so ko ka kara mata ko kuma ka maida ka amshi kudinka.ta juya ta koma gida tana mamakin son da mansura take mata, nan ta kara shiga damuwa dama tana tare da tunanin yanda zata kasance in mansu tayi aure tunda yanzun ma gidan take kwana,amma taji mamanmu tana cewa zata sa atoshe uwar dakinta abude ma Bilkisun kofa ita da Asma'u,mkrnt tare ko ina tare,Umma suka kaima kayan itama sai da tayima farooq fadan biyewa mansuran sannan tayi godiya ta kira mamanmu ta bata, mama ma kin karba tayi sai da Abba yasa baki yace kayan mansura na Bilkisu ne,haka nan kayan Bilkisu na mansura ne shi ko daya baiga laifin mansura don tace mijinta yayi ma Bilki kayaba Bilkisu taki ayi wasu bidi'o'i a bikin tace walima kurum zasu yi in da zasu gayyato mlmai dan su yi wa'azi haka ko akayi,dama daurin auren can gomben aka yi sun soma walimar bayan sallar la'asar,inda malama sa'adiya tayi wa'azi akan hakkin aure wato miji akan matarsa Bilkisu wace suke zaune kusa  da juna ita da mansu tace kin dai ji ko?Mansu kam jikinta ne yayi sanyi,dayake gombe za akaita can ma akayi jeren in hutun shi ya kare sai ya samar mata gida nanzaria saboda karatu shi kuma zai na zuwa mata hutun karshen mako.washe gari suka dauki hanyar gombe kuka mansu keyi tun daga zariya har gombe haka nan bilkisu sai ma washe gari randa zasu dawo a wannan rana mansu da bily sun sha kuka,da kyar suka rabu har ma wasu sun taya su kukan, aure kenan, tun a mota bilkisu ta soma kewar mansu, dashi ke su mamanmu ne suka je jere gomben basu je kai amarya ba,mama ma a talauce dubu biyar taba umma da kyar ma ta amsa.

 Bilkisu kam itama mamanmuce ta bata dubu bakwai tayi ma mansu yar sayayya ba dan sun ishe ta ba,sai don bata dashi amma tasha alwashin in ta gama karatu tana kama aiki zata kula da mansu fiye da kanta,ba don mansu bata da shi ba,sai donta kwanta,hakanan Bilkisu taci gaba da zuwa makaranta ita daya, amma kullum sai tasha kukan rashin mansu. Can ma gombe ango yakasa gano kan amaryarshi,duk da lallashi gami da ban bakin da yake mata,har dan hutun nashi na sati hudu ya kare,kafin nan yasamu dan madaidaicin gida,suka dawo sunyi murna da ganin juna ita da mansura suka ci gaba da zuwa mkarnta. Wannan satin ko nace Friday farooq yazo dawuri lokacin suna makaranta shi ne yaje yazo da su bayan ya kira mansura cikin new phone din ta nokia.cewa gashi nan zuwa nan take ta canza fuska har Bily ta gane, tace bakiso zuwanshi ba ne?Tace a'a nadai gaji ne.Bily taso su sauke ta gida amma sai farooq yace yana son magana da ita,agidansu ne yake cewa na sani be dace in miki zancan nan ba sbda ke ba matar aure bace kuma irin zancan nan..

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 17馃彽


bai dace ya hada mu ba sai dai dole ne in mikishi dan nasan kece zaki iya min mganin abin da yardar Allah mansura dai tun da muka yi aure sam taki yarda dani yau sati biyar kenan sai kace wata yar karamar yariya.na mata wa'azin nayi fadan nagaji tana cutar dani,batun yayi ma Bily nauyi har ma ta kasa kallon farooq,amma duk da haka tace kayi hakuri ka yafe mata tayi kuskure bazata kara ba,taja hannun mansu cikin dakinta,suka zauna gefen gado ta dube ta cikin yanayin damuwa, kin san masifar dakike ciki kuwa?Kin san zunubin da kike diba? Koda yake nasan kin sani tunda tare muka yi karatu nace malami daya ya koyar damu,..nan dai Bily Tai tayi mata fada da nasiha..!Cikin hawaye take ma bilkisu wlh bily,tsoro nake ji,dariya ma ta ba bilkisu, jibe ki wai tsoro ta mike ina son gobe labari ya canza in ba haka ba wlh- wlh kinemi wata bilyn bani ba,ta fita mansu ta biyo ta tana kira,kin tsayawa tayi farooq ya biyota shine ya sauke ta gida lokacin Babansu yana nan zaune awaje tare da wasu yan uwansu,kallo yabita dashi.Baba tsalha wan shine yadube shi.

 Yace toga shaida kana gani? Amma zan dauki mataki,gara dai cewar baba tsalha. washi gari tun misalin bakwai saura sai ga farooq yayi sallama da Bilkisu, suka gaisa yace ta taimaka suje gida ta lallasar mashi mansura tana can tana ta kuka ko kula shi taki tayi Bily tayi maza ta shirya ta bishi suna shiga gidan mansu tayi saurin fadawa jikin mansu ta kara fashewa da kuka tana Allah farooq baya sona baya tausayi na mansu tayi saurin rufe mata baki tana lallashin ta nan ta wuni tana kula da ita sai dare ta tafi.


Baba tsalha yakalli mamman sannan yace,ina jinka mamman, kace Inusa ya shirya aure?Mamman yace, haka nace.Baba tsalha yace,ban da kai mamman wanne mahaukacin uba ne zai ba Inusa auren 'yarsa? Yaron da bai san ciwon kansa ba,sai shaye-shaye da bin kwararo yana damke kajin mutane da agwaginsu ba sana'a. Malam mamman yace to nina bashi Bilkisu tunda ita shegen bakin jini yayi mata yawa,Baba tsalha yace to ni fa  ba ruwana kuma bani da kudin masa aure, mamman yace dama ai sadaka zan bashi,kuma da zaka ce babu ruwanka ka sani ko sanadin auren ya shiryu?Baba tsalha yace shi kenan zan mishi bayani.Abin ban mamaki,Inusa ma da tsohonshi baba tsalha yakira shi yayi mishi zancan Bilkisu cewa yayi a'a tafi karfinsa.Babansu bilki tare da baba tsalhan ne suka tasa shi suna rokonshi ya yarda,yace zai dai yi tunani. Yayi sallama kofar mamanmu tana ninke kayanta yayin da Bilkisu ke cin tuwo,fuskarshi sam babu annuri gaban bilkisu ya fadi dama duk sanda ta ganshi sai gabanta yayi muguwar faduwa,balle yanzun da ya shigo afusace,ya dube ta ke Bilkisu daga yau naba inusa ke tunda abin naki ya zama iyashege,haba dole mana maza suyi ta gudunki,kowa yana tsoron ciwon kanjamau, ashe maza kike bi, su ladiyo sun sha gaya min amma na kasa yarda sai yanzun da na gane ma idona,dan tsabar iskanci kam har kofar gida ake zuwa daukarki to na kawo kasrhen abin inusa shi ne na bawa ke,ido ta zuba mishi cike da mamaki tana kallonshi, yanzu ne ta kara yarda mahaifinta baya kaunarta,domin duk uban da yake son yarshi bazai taba yarda ya kwatanta ta da auren yaro irin inusa ba yaron da babu arabi balle boko, sai shaye-shaye,kullum cikin datti tamkar mahaukaci,ga satar tsiya ba sana'a tana cikin tunani ya katse ta,kin tsare ni da ido ba neman shawara nake yiba,umarni na bada dama ai nine musulunci ya bawa damar in zaba miki miji,bata san sanda tace amma baba Inusa baya daya daga cikin mazajan da musulunci ya yarda a basu aure, saukar mari taji sannan yace sai ki gaya min Wanda musuluncin ya yarda a bashi ke da kike  rainawa yanzun haka ya ki sai lallashin shi ake yi ya rufa miki asiri har kina da ta cewa? Ya dube mama wadda ta tsananin bakin ciki da mamaki ya hanata magana yace kece ke zugata na jima da sanin haka to ki sani kan wannan Auren kema naki Auren yana siradin karshe, in kin tafi gidanku kuma in daura Auren ya fice fuu...... Kuka mai karfi Bilkisu ta saki sannan ta juya tana kallon Mamanmu cikin kuka take fadin Allah Mamanmu wannan karon bazan yarda ba ni ba zan aure inusa ba, shi baba baya kaunata Sam ta matsa ta kama kafafun mamanmu tana cewa me yasa baya sona? Me na mishi? Ko dai ni din ba yarsa bace?


Kuka da mama ke makewa shi ne ya kwace cikin kuka take cewa nima wannan karan na gaji ai ba akan shi kike ba. Hakkinki da Allah ya dora mishi matsayinshi na uba bai kula dasu ba, sai yanzun ne zai ce hakkin shi ne ya zaba miki miji? 


Zamu ji mugani, yan kwanakin nan rigingimu sun kankama cikin dan lokaci. Mutane kalilan ne suke cewa bai dace a aura ma inusa Bilkisu ba, tunda shi ba nutsattse ba ne, sauran kam sun ce an cuci Inusa, mahaifiyar Inusa ma tsalle ta daka tace sai da yar tayi kwantai sannan za a lika ma danta? 


Har sassan su ta shigo cike da masifa ta samu mama tana wanka sai Bilkisu zaune ta tasa abinci ta kasa ci, saratu uwar Inusa ta dubi Bilkisu ta ce, ke ina uwarki gunta nazo, in kuma bata nan bari na baki sako ki gaya mata, ki ce nace hadin bai hadu ba kin gantsare kin rasa mai so za a maka wa dana? Har fa masallatai an kai cigiyar mai sonki an rasa, anyi yawo da hotunanki an gaji, ga bin maza ki je ki saka mishi ciwon zamani. 


Mama ta aje bokitin wanka ta dubi saratu tace ke saro ki dube ni da kyau, in kina zaton nima na amince a hada min 'ya Da mahaukaci ne ki ka zo nan ki yi rashin mutunci to ki sake sabon tunani Inusa mutun ne? ina tambayarki? Don kunga ina muku shiru ba yana nufin tsoro bane kuma ba kasawa bane, duka nawa megadon take shekara 20 da yan watanni ne kuke mata wannan surutun, Ku shiga cikin unguwar nan Ku duba in babu wadanda suka girmeta . don haka daina daga jijiyar wuyanki nima ba zan yarda a dauki zukekiyar yarinya kamar maigado a ba Inusan da ko gabas bai sani ba bare yanda ake sallah,. Saratu cikin sanyin jiki tace oho dai na dai gaya miki kar a makalawa yarona, kila da ciwo ehe, mama tace ba gara kowane ciwo ba da ciwon dake jikinshi na jahilci, baki in yasan abin da zai fada bai San Wanda za a maida mishi ba, haka ce ta samu saratu ta tafi cike da kunya yayin da su Ladiyo dake gefe suna kallon suka ji haushin saratu yanda ta tsaya matar nan tayi mata ta tas. 


Bilkisu ta ji dadin yanda mama ta gaggaya wa saratu magana, domin sun raina musu hankali a gidan rigima ta kasa karewa babansu Bilkisu da baba tsalha sun matsa ma Inusa randa ya amsa musu da dare cewa ya yarda washe gari da asubahi ya tattara yanashi- yanashi ya gudu don ba zai iya Auren Bilkisu ba, kuma shi kanshi ya rasa dalilin gudun Inusa yasa rigima ta tsananta uwarshi tace ba zata yarda ba kila asiri ne mama suka ma danta ya bar gari, su Ladiyo ma haka suka ce ma maigidan kuma ya hau kai ya zuna ya samu Mamanmu yana ta masifa fadi yake gara ma taje ta karya asirin tun kafin abu yayi nisa banza tai musu suka yi ta surutun su suka gaji suka yi shiru dama ance watan kwaram daya ne da ya wuce shi kenan. Sai dai ita kuma bilkisu tana mamakin akan kinta ne Inusa ya bar gari?In ko haka ne,da mamaki meke faruwa  kenan?Lallai bakin jininta ya bunkasa, cikin dan tsakanin sakina ta haihu 'yarta mace, anyi suna da sati uku maryam ma ta haihu danta faisal yayin da yar sakina taci sunnan maman Abdul,Amina. suna kiranta da mimi, mansu ma anyi ciki shagwaba ta karu ga laulayi dole Bilkisu ta koma gidan saboda farooq kaduna yake in yazo Friday sai ta dawo gida.Haka rayuwar ta ci gaba da juyawa,Bilkisu tana zuwa makaranta har mansu ta haihu, dan yaronta mai kyau yaci sunnan baban farooq, suna kiran shi dady. Bilkisu tayi juyi yau shekara duka nawa ta sani ba  wai tayi girman da za'a ce gashi gashi ba ne amma surutun mutane ya isheta,ita kanta tana so tayi aure yanzun..   Sai kuma gobe. 


 Yarima kwance kan wata kujera jikinshi sanye cikin gajeran fari tas din wando da yan singilet din ta, gefenshi Vicky ce sanye da da brezzier da pant wasannin su na yau da kullum suke tana da kusan rabi na abin da yake so a gurin mace, sun yi nisa cikin shagala Sam bai ji sallamar ba bare ya amsa,sai da mai sallamar ya shigo kai tsaye kuma ya rufe kofar da karfi da sauri ya zare bakin shi daga na Vicky wace ta soma fita daga hayyacinta, magajin Malam ne ya ce maza ka tashi tare da mai martaba....... Sallamar mai martaba ce ta katse magajin Malam daga maganar da yake, tsoro da faragaba tare da kunya ne suka rufe Yarima, Vicky kuwa tsawa magajin Malam ya mata, ta mike ta fita, Yarima yana zaune akan kafet ya dukar da Kan shi bai ji dadin wannan ziyara ta ba zata da da mahaifinshi ya kawo mishi ba, wannan shi ne karo na biyu da ya kamasa da mace wancan zuwan ya samu ya kare kanshi da cewa abokiyar karatunshi ce, duk da mai Martaban ya gansu ne suna kissing din juna, kuma bai ce ma Yariman kala ba shi ne dai yake ta borin kunyan shi to yau fa?


Da me zai kare kanshi? Dubi kayan jikinshi dubi nata, gara ma wancan karon duk da kaya a jinkinsu.


Magajin Malam ne ya soma magana afuwa Yarima yake nema Allah ya taya maka a yafe mishi. Mai martaba ya daga ma magajin Malam hannu alamar yayi shiru, sannan cikin magana irin ta manya yace, Modibbo dama saudiya zan shige na ratso domin in ganka, kuma na same ka lafiya duk muna waya kullum, yaya karatun naka? Cikin in-ina yace Alhamdulillah ranka ya dade, yaya su Umma? Ummar ka lafiya shin ko kana da matsalar kudi? Ya dan shafa kai I to ba dai sosai ba, mai martaba yace in da matsala ka fada, yace eh akwai bayan wannan fa? ya ce babu ranka shi dade, ita kenan, ya mike ya nufi kitchen yazo da ruwa da lemunkan sha, ya dire ma magajin Malam don yasan mai martaba ba zai sha ba, ya shiga daki ya saka kaya har lokacin jikinshi a sanyaye yake , yasan halin mahaifinshi sarai shirun da ya mishi ba yana nufin ya bar shi bane ya sani zai hukunta shi ta in da baya zato, don shi baya fada bare zagi, yanzun shi dai zai saurari hukuncin daza a yi masa Allah yasa kada ya maida shi gida nigeria da karatun shi dan ba ya son karatu can kuma matan can basa burge shi duk kyan ya mace .

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 18馃彽


 kwanan mai martaba biyu a malaysia kafin ya wuce Saudi  yayi kwanakin ne a wani shahararren masaukin baki dake cikin birnin na malaysia. Yarima sam bai yi mamakin shirun da mahaifin nashi yayi mishi ba. Domin yasan zai yi maganin abin, wani Abu da yaba magajin Malam mamaki, gidan Yarima yake kwana kuma ganin da mai martaba ya mishi bai sa Yarima ya daina kwana da mata guda biyu a shimfidarshi ba, don haka magajin Malam yake kwanciya a falo ko dayan dakin Yarima, magajin malam dai shine babban abokin Yarima kuma shi da ne ga waziri, mai martaba yana son shi tamkar Yarima. Shi yana karatun injiniya, yayin da Yarima ke karatun likita mai martaba yazo da shi don yaga abokinshi ya juya gida shi kuma ya wuce Saudi, bayan sun ga tashin mai martaba suka dawo gida, kai tsaye fridge magajin Malam ya nufa a kitchen ya dauko robar ruwa, kusa da Yarima ya zauna da yake kokarin kiran Ummarshi, 


Layin ya ki shiga, ya dubi Yarima yana son yin magana amma yasan halin yan kayan shi, don haka sai yayi nufin share zancan amma kasancewar Yarima mai matukar saurin fahimta sai yace um'hum ina jin ka, magajin Malam yace ban yi magana ba. 

  

Yarima ya dube shi cike da kasaita irin ta yayan sarakuna, sannan yace kana so yin maganar ne ai, magajin Malam yace nasan halinka ne zaka iya cewa yanzun ba time din amsa ba ne, Yarima yace tambaya zaka yi kenan? 

 Magajin Malam yace tun shekaran jiya nake son yin tambayar, Yarima yace bata dame ka ba ne da kayi ta koda ba zaka samu amsa ba.


Magajin Malam yace zan iya tambayar yanzun ko? Yarima ya tabe baki tare da fadin in kaso ba, magajin Malam ya gyara zama, dama ina son jin me yasa kaci ka son mata? Kuma me yasa ka canza daga silent din ka zuwa mara jin magana? Yarima ya ajiye wayar a gefenshi sannan ya ce na kasa samun Umma din ma ya kalli magajin Malam wacce zan amsa maka? Duka in har zan samu, ya ce to mata abin so ne don su ne nishadi na karshe, duk cikakken namiji mai lafiya yana son mata, sai dai kowa da nashi salon son, sannan ban canza ba har yau ina nan a silent dina, magajin Malam yace ka canza domin a da in har mai martaba ya hane ka da yin wani Abu ka bar shi har abada, amma yanzu ba ka damuwa da hakan. Yarima yace me ka gani? Ya ce in daina ban daina ba?  watannin baya mun zonan dashi mun sameka da mace. Sai kuma gashi wannan zuwan ma gara wancan cikin sutura kuke wannan karon ba Ku da maraba da tsurara, sannan kuna cikin halin sumbatar Juna, kilama damun jima ba mu shigo ba mu same Ku cikin wani halin. Yarima ya zuba mishi ido babu wani hali da zaku same mu da ya wuce wannan domin ni kamar yanda ka sani komai da lokacin shi, wannan lokacin ne na wasanni kuma duk nacin mace ba zan wuce mata haka ba ka fahimta? 


Sannan kai ma zan tambaye ka wancan zuwan da Ku ka yi ka ji mai martaba yace kar na kara? Hasalima bai ce min kala ba. Haka nan wannan zuwan kaji ya yi min magana ? Magajin Malam yace amma kasan hausawa sun ce shiru ma magana CE, ta ishi mai hankali ko? Sannan kana ganin shirun da ya yi maka yana nufin ya ji dadin abin da ka aikata ne? Yarima gairgiza kai ko kusa nasan ba haka ba ne, INA cike da sanin zai dauki mataki kaina, sai dai ina tsoron irin hukuncin da zai yanke min, magajin Malam yayi dariya tare da fadin, ai na san ka shirya daukar kowane hukunci ne tunda ka kasa daina hulda da matan duk da yana garin ka ci gaba da kwana da mata har biyu kasan ko matanka ne na sunna addininka bai amince maka ka kwana da su, su biyu ba ko? 


Magajin Malam yace wane hukunci ka ke ganin mai martaba zai yanke maka? Yarima yace sai Allah shi ne ya sani sai kuma shi. da na zace zai CE zai mai da ni Nigeria in yi karatu a ga ban shi yanzun kam na bari wannan tunanin tunda a gabanka ya kara min kudi, magajin Malam yace ni ko sai INA tunanin kila ya yi maka aure........ Da sauri Yarima ya tashi zaune au! What? Yayi yar dariya kada ka manta am 22 fa yaushe aka haife ni, da har zan yi aure? Please bar wannan zancan ban isa aure ba, magajin Malam yace kai ko ka isa har ko  ka zarta tunda da mata biyu kake kwana. Yarima yace tab da ko ya yanke min hukunci mafi muni, ni fa aure nayi da wuri in yi shi nan fa shekara goma masu zuwa, kana da garantin kaiwa wannan lokacin! Cewar magajin Malam Yarima ya mike tare da fadin, in na biye maka sai in shiga time din wanka na, ya nufi dakin shi magajin Malam ya bi shi da kallo yana kuma mamakin Yarima, yaro mai shiru shiru da kamun kai, yana da natsuwa ta karshe shi yasa yake samun girmamawa gurin al'lummar Bauchi, shi kanshi ban da ya gane ma idon shi abin da Yarima yake yi zai musa, yana da girmama lokacin shi yasa yake da cika alkawari in har ya dauka.

 kwankwasa kofa aka yi tare da neman izinin shigowa, magajin Malam da ke zaune yaba su izinin suka shigo, turawa ne mace da namiji, sun gaisa sannan suka tambayi prince ya gaya musu cewa yana wanka, suka dubi a gogon da ke manne a bangon falon sannan suka jira shi yayi musu izinin zama, jefi-jefi suke  hira suna kallon fim din da suka samu magajin Malam yana kallo, Yarima ya fito cikin bakin jeans tare da shirt mai dogon hannu tare da layi-layin baki da fari takalminshi mai shegen kyau tare da tsada shima baki ne, sumar kanshi irin ta asalin fillo tasha gyar tana ta sheki, kamshin turaren matador yana tashi a jikinshi, Dora ta kalli M, tace He's handsome guy, ta mike ta isa gurin shi cikin kasaita ya kalle ta tare da fadin ya take? 


Gefen kunnashi ta sumbata sannan ta rike mishi hannu ya dubi magajin Malam wanda haushi ya hana shi magana, yace abokina bari mu shiga school da kai magajin Malam ya amsa suka fita yaja tsaki Allah yasa mai martaba ya yiwa Yarima hukuncin barin wannan kasa da lalcewa tayi mata yawa.


Mai martaba Alhaji Isma'il Abdullah ya kammala umrarshi lfy, kuma ya matsu ya dawo gida saboda matsalar dan shi Yarima, Al'amin yayi addu'o' masu yawa kan Allah ya shirya mishi nutsattsen yaron nashi sai dai wasu lokutan yafi ganin laifin shi da ya dauko shi ya kawo shi wata kasa masu wata irin tarbiya babu mai saka ido babu mai tsawatar wa ya kama mishi gida mai tsadar gaske sannan ya cika mishi account da kudi lallai yace mishi je kayi yanda kake so, duk da cewa ya halasta mutum yaje ko ina ne dan neman ilmi shi yasa duk abin da Muslim ya tsara mana in munce zamu bar shi sai mun gaba dai dai ba, wannan shi ne dalilin da yasa aka ce in danka ya balaga kai mishi aure, mai martaba ma yace wannan ne ya dace da Yarima wato aure, kuma yasaha alwashin da ya sauka gida zai yi shawara da mutum daya, ya san tsohon zai taimaka mishi.


Cikin bacci taji ana girgizata, Aunty in ji Mamanmu, ta yi mika tare da hamma sannan ta sakko jikinta a mace zuciyarta cike da tunanin mafarkinta Yarima ne a mafarkin yake matsa mata da son ta nemo labarin shi, har ma suka yi rigima don tace me sanin labarin shi zai kareta da shi? Yayi fushi ya tafi yace mata ba ya kara zuwa sai randa ta samo labarin shi, ta mike tana tunanin dama ta huta don itama ta gaji da mafarkin shi....

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 19馃彽


Bilkisu ta dubi Mansu, kizo muje tare, ta saba dady a kafada maimakon nonon da take bashi, tayi gaba zo muje, gurin shirya abincin. Shagala abokan farooq suka yi da kallon wannan baiwar Allah, tsarki ya tabbata ga  Ubangijin da ya kagi wannan yar tahalika, basu kara tsinkewa ba sai da ta soma gaida su da wannan zazzakar muryar tata, cikin in ina suka amsa mata har ma taji nauyin hakan ta koma falo in da su Sakina suka shagala da kallon wani Nigerian film, a tashar African magic, Mansur  ne ya soma magana, abokina ina ka samo wannan zukekiyar yarinyar kaman tasha hatimin Aninabi Yusufa don kyau? 


Sani ya amshe iya gane ganena ban taba ganin mace mai kyaun ta ba, farooq yace wanene zai shiga a cikin Ku? Sani yace tab ni wannan tasha gabana, sai dai ko su mansur ko Aminu, Aminu ya ce ni ba Ku ji ban tan ka ba? Dan nasan wannan daga gidan sarauta, sai ko gidan wani shugaba ko na jiha ko na kasa, duk tadin da suke yi Mansu tana jin su wannan Abu yana daure mata kai, farooq yace yaya za Ku ce mata, yarinya ce mai hankali, ko ilimi, da saukin kai, mansur ya ce barni dai wannan ka kalle ta da kyau kuwa? Firgita ni take yi da kwarjininta mai ban al'ajabi, in har na aure wannan tuni zan zama zauna nan, duk suka sa dariya, Mansu ta damu tana son sanin MEKE faruwa ne kowanne namiji ke fadin tafi karfinshi...? 


Sai yamma suka baro gidan Mansu, ta cika yaran su Sakina da Maryam da kudi tare da kayan shafa. Bily ko kaya ne kala hudu na salla da farooq yayi mata, kanta amsa sai da suka hau sama da Mansura, don tace sun yi yawa ba zata karba, kuma sun yi wahala da ita da yawa, yaushe ne itama zata samu ta kwatana musu? Mansu tace wannan kuma na Allah ne shi ne mai yanda yaso ke dai ki dauka, Allah ya bar mana zumunci.


************************

 magajin Malam ya dubi Yarima, prince don Allah ka sake  hali ni zan tafi kaga har mutane sun soma shiga jirgi, please Yarima be a  Muslim, Yarima ya kalle shi yanzo ni ba Muslim ba ne? To ka zama cikakke. I will do my best, magajin Malam yace ni fa har mamaki na ke ji, gaba daya ka canza Yarima ya dafa shi na sani kana tsoro ne kada nazo Niger in yi abin da zai zubar da mutuncin gidanmu ne I'll never do it kada ka damu zan kula, Yarima yana kallon magajin Malam har ya shige jirgin don zuwa gida.


Mai martaba ya sauka lfy jerin gwanon motoci ne suka zo filin jirgin don daukar yallabai, ya kashingida bisa kafet ya dafa tuf-tuf dan hutawa, gefenshi kuma uwargida ce sarautar mata ta jera mishi kayan shaye- shaye da ciye- ciye. Hajiya salma kenan mace mai mutunci da sanin ya kamata, gata da son addini tare da tausayin na kasa, gefenshi ta zauna tana tare da cewa yako lbrin autana? 


Cike da sakin fuska ya ce autanki, lfy lau, ya kara girma tare da zama namiji sosai, Hakika kasar ta amshe shi tamkar balaraben kasar misra suka yi dariya, tace shekara biyu kawai da ban ganshi ba shi ne ya zama duk wannan? Yace zaki ganshi zan shirya miki zuwa tace shifa ba zai zo Hutu ba ne? Ya dube ta zai ci gaba da zuwa hutunshi a Saudi ne, duk da cewa ina tunanin nan gaba kadan wani sanadi zai kawo shi nan gida, hira suke yi yana cin abincinshi, taso ya sanar da ita ko menene zai yi sanadin zuwan Yarima, amma sai yace ta bari in lokaci ya yi zata sani.

kamar ko yaushe in har zai je gurin dattijon sirikin nashi yafi son ya fita shi daya kuma yaja motar da kanshi kamar yanzu kenan, karfe tara na dare ne yaja motar dan zuwa gun surukin nashi ne  shiga dakin Modibbon ya sanar mishi da cewa ga mai martaba.


Bayan ya zauna suka gaisa da tsohon mai tarin shekaru masani ne na Qur'an and hadisai, Allah ya yi mishi baiwar sanin abubuwa da dama, shi ba mishiriki ba ne, baya duba ko bugun kasa, tsoho ne mai bautar Allah tare da takawa,  shekarunshi dari babu uku amma in ka ganshi zaka zata bai fi saba'in ba, wasu suna gani tamkar waliyi ne Allah dai ya bar ma kansa sani cike da girmamawa mai martaba ya gaida Modibbo tsohon mai daraja ya amsa cikin sakin fuska da kulawa ya tambaye hanyar da kuma abokinshi wato takwaranshi Yarima Modibbo mai martaba yace yana lfy yace a gaishe ka, 


Ya gyara zama, yanzu ma matsalarshi ce ta kawo ni, tsohon ya tattaro hankalinshi gurin mai martaba sannan yace gaba, zuwa na biyu ina samunshi da mace hankalina ya yi matuka gurin tashi, yanzu da na yanke shawarar in yi mishi aure, sai a tura mishi matar can, ko yaya ka gani?  Tsohon yayi shiru tamkar mai nazari, sannan yace haka ne yafi dacewa domin saboda gudun wannan matsalar shi yasa musulunci ya yi horo da ya'yanku sun balaga to Ku musu aure, 


Mai martaba ya ce haka ne, kwarai na yi mamakin canzawar yaron lokaci guda, tsohon yace babu wanda zai gagara daga shaidan, don shi ba rago ba ne, yanzu kaje gida akwai istihara da zan yi game da al'amarin shi idan Ubangiji yaso sai musan ta in da za'a bullo, mai martaba ya shiga godiya tare da yin sallama da tsohon wanda ya yunkura ya tashi ya yo ma sirikin nashi rakiya zuwa gurin mota.

Yarima zaune kan wani dan dakali karkashin wata bishiya mai sanyi cikin makaranta, yana nazarin littafan biology, dago kan shin da zai ya sai ko ya sauke idanunshi kan wata yarinya  'yar mutanan China tana sanye da gajeran siket wanda iyakarshi tsakiyar cinyarta, rigar jikinta kuwa singileti ce mai dan siririn hannu,


Ta cikin gilashin idonshi yake kare mata kallo nan zuciyar shi ta kwadaitu da lafiyayyar fatar ta, da takusa in da yake sai ya yi tamkar bai ganta ba, a nata gefen yau ne gani na uku da ta mishi gayen ya tsaya mata a rai, tayi niyya yau zata kula shi ta tsaya gefenshi cikin harshen turanci take CE mishi sannu da hutawa kasaitar tashi ta motsa, yi yayi tamkar bai ji ta ba, sai da ta sake maimaitawa sannan ya amsa ba tare da ya dube ta ba, tace zata iya zama kusa dashi?  


Yace in taso haka zata iya, ta zauna tana satar kallon shi, ta dan yi gyaran murya, sannan tace shin zata iya tambayarshi? Hannu ya daga mata kafin yace yanzu ba time din tambaya ba ne, shiru tayi na dan lokaci sannan ta ce to zai iya taimakon ta? Ko yanzun ba lokacin taimako ba ne? Ya bata amsa dace wa in taimakon ya shafi kar2 ne zai iya in ko wani Abu ne daban to ba a yin shi cikin makaranta ya tambaye ta shin ta fahimta? Tace eh ta gane, nan ta soma mishi tambayoyi akan abubuwan da suka yi mata duhu shi ko ya shiga bata amsa yanda zata fahimta har zuwa lokacin sallar la'asar ya mike ta ce ina zai je ne? Yace ya fita lokacin kar2 ya shiga na sallah don haka yanzu sallah zai je.

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 20馃彽

 Mamanmu ta dubi Bilkisu ta ce maigado ki daure kiyi amfani da maganin nan ga na turaren nan wannan kuma wanka zaki yi da shi, Bilkisu ta dube ta Mamanmu kada ki shiga cikin mata masu shiga gurin malamai saboda gudun shirka, aure lokaci ne. Mama tace maigado ba zan kauce hanya ba, wannan da ki ka gani Ummana ta ai ko dashi wannan na iskokai ne, abin nan yana bani tsoro, na rasa gane me ke faruwa? Bilkisu cikin sanyin murya tace kada ki damu Mamanmu, In'sha Allah, Allah zai kawo min mafi alkairi, wata rana sai labari, 


yanzun su Bilkisu sun shiga shekara ta uku a jami'a { A.B.U} mass comm. Take karanta wa, tana sha'awar zama yar jarida duk da kasancewarta ba mai yawan surutu ba amman tana so ta zama cikin yan media, karatunta ta saka a gaba in da Mamanmu ta hana kanta ci da sha ta dage dan ganin burin maigado ya cika, duk da Abban Mansura yana taimaka mata sosai to karatun jami'a ya wuce wasa wasa, dan gane da mahaifinta sai abin da ya karu na tsana, da kuma tsangwama.

 

***************************

Jumma'ar yau kam Modibbo tsohon nan daga masallacin jumma'a ya nufi fada dan ganawa da mai martaba, cikin wani daki na musamman suka kebe duk suna zaune ne kan dar duma bayan gaisawa da suka yi Dattijon ya soma magana. Abu na farko da na fara gani cikin al'amarin Yarima na ganshi mai yawan fitsari ne in na ce mai yawan fitsari ina nufin yana da matsananciyar sha'awa, game da batun aure kuma ba da gaggawa kamar yadda ka ke nufi ba, amma zai yi aure ba da jimawa sosai ba, saboda matar tashi ba yar yankin nan jihar ba ce, sannan tana da matsala, haduwarsu da Yarima zai kawo abubuwa da dama, a cikin binciken nawa na ga al'amura da yawa, amma Allah shi ne mafi sani haka nan yafi mu sanin komai game da abin da zai faru, anan gaba. Sai dai za a iya nema mishi Auren daga wasu jihohi yazo yaga wadda zasu sasanta ko Allah zai sa tana ciki, haka ne in ji mai martaba, za a nemo mishi hotuna nan su sai in sa a kai mishi ya zaba in yaso sai ayi bikin a tura mishi can, dattijon yace to madalla haka din ma ya yi zamu bisu da addu'a, bayan tattaunawa suka yi sallama.


Yarima yana cikin bahon wankan mai cike da kanshin sabulai kaloli masu sa santsin jiki da laushin fata, kwance yake ciki ya yi lamo zuciyarshi dam da sha'awar yarinyar yar mutanen China, yau sati daya da haduwarsu kullum sai ta neme shi da yawa tana son shiga harkarshi musamman da ta San in yana makaranta to karatu yazo abin da bata sani ba makaranta tana cike ne da yammatanshi sai dai sun san baza ya kula su a school ba in kin matsu isko shi gidan shi sau biyu suna rigima da Vicky.

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 21馃彽


 Bilkisu sun shiga shekara ta karshe a makaranta , da kyar da sidin goshin da taimakon su Abban Mansura ta gama Degree na farko, ta samu damar zama yar jarida, suna gida sai jiran bautar kasa, cikin yardar Ubangiji da sa'a Kaduna aka tura ta, farooq kam yace ba wata bautar kasa da Mansu zata yi saboda tsohon cikin dake gare ta tuni ma ya tafi da ita Kaduna gidanshi na can, don haka gidan su Mansu take son zama kamar yanda suka yi da Mansu, ta waya, 


Dama cikin shekara hudun nan Mansu a shiririta take karatun, course din da aka bata ba shi ta nema ba, gidan farooq ya kama a malali na sani same road, ya yi kusa da sakatariyarsu, Bilkisu duk da cewa sai ka hau mashin, ranar da ta soma saka kayan NYSC zaku ganin tamkar tafi kowace mace sa'a Mansura ta ce kin yi kyau wlh Bily, ta dubi Mansu, ina tunanin yaya zanyi na fita da wando? Zan dinga saka after dress idan zan fita in naje zan cire.

zaune kofar gidan Yarima, magajin Malam ne tunda ya sauka ya iso gidan a kulle,ya sani kamar wannan lokacin Yarima yana makaranta, zaman kusan awa uku sai ga Yarima shi da yar mutanan China, hannuwansu rike cikin na juna, magajin Malam yace toh! Abu ya kara gaba, tunda yanzu har cikin gari yana yawo rike da mace, abin damuwa ba ne, ya tsaya cike da matukar mamaki ganin magajin Malam ya iso yana cewa, abokina tun yaushe ka ke a nan? Magajin Malam ya mike Yana dan karkade rigarshi, nafi awa biyu ina jiranka fa, suka yi musabiha rike da hannun juna suka nufi cikin gida, tana biye da su Yarima, ya ce jiki na fa ya yi sanyi da ganinka, Allah yasa ba hukuncin mai martaba ba ne zan fuskanta, magajin Malam yace barin na huta nayi sallah, to yi bari na amso mana take away suka fita shi da chelen don yanzu ta zamar mishi jaka, ko ina tana manne dashi ga tsinannan kishi, dama tana yawan gaya mishi  su a dokar kasarsu mutum ba zai yi mata biyu ba. 


Yarima kam ya ce mata shi sai dai tayi hakuri da shi, soyayyah zai yi da mata da yawa, amma macen aurenshi daya ce, ta kan ce ita ce? Sai yace mata ba zai iya sani ba, zaune suke tsakiyar falon Yarima da magajin Malam, yan ciye ciye suke yi tare da yan hirarraki ya matsu yasan Dalilin zuwan magajin Malam shi ko magajin Malam sai ja mishi rai yake yi, tare da tsokanarshi, Yarima don Allah magajin Malam yi min bayani mana, mikewa ya yi ya shiga bedroom din Yarima Ya dauko jakarshi irin wacce ake ratayawa , yazo ya zauna ya zage ta ya ciro envelop ya mika ma Yarima gashi in ji mai martaba sakon kenan yace lallai ka duba in je mishi da amsa, ya mike rike da jakarashi duba ina zuwa bari na maida jakar.


Daya bayan daya yake bin hotunan da kallo, ya'ya ne na sarakuna da na manyan attajirai, kuma yan juhohi daban- daban, domin ya gani a bayan hoton magajin Malam ya dawo ya zauna kusa dashi cike da tashin hankali mai tsanani Yarima ya dubi magajin Malam, wai martaba yana nufin in zabi mata? Ina zaton haka ne in ji magajin Malam, Yarima Ya ce gaskiya ba amin a dalci ba, 24 years shi ne zan yi aure? Gaskiya ba zan iya ba, kwana kadan mutum ya tsufa, ya tara yara magajin Malam yace to yanzu ya zaka yi? 


Nasan dai ba zaka yi gangancin fada mishi wadannan magananun ba? Yarima zufa yake yi, ya dubi magajin Malam ni gaskiya ko da aure zan yi ban sha'awar matanmu na nigeria, musamman. 'Yan arewarmu kauyawa ne, ya watso ma magajin Malam hotuna duba fa ka gani, kalle su bana son irin mutanan gaskiya ni kuma bana da sha'awar Auren mata da yawa, mata daya jal zan yi dan bana son a cika min gida da yara yanda mazan hausawa suke yi, kallon shi kawai magajin Malam ke yi cike da mamaki.

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 22馃彽


Yace Modibbo kana bani mamaki in na ce ka canza kana min musu yanzu har da haihuwar ce ba ka so? Yace eh bana so ko ka taba ganina na dauki wani yaro iya tsawon rayuwarka? Shin ko wasa kaga ina ma yara? Magajin Malam yace to tunda ka ce baka son matan nigerian sai yan wace kasar, yan China? Cikin gatse ya tambaye shi. Yarima yaja tsaki ni yanzu kawai ka ce mishi cikin su babu wadda ta min, kallon hotunan magajin Malam ke yi cike da mamakin yarima, yanmata ne kyawawa, ya dube shi matan sauran kasashin farar fata ba su fi namu kyau da cikar halitta ba,farin ne kurum amma matan arewa sune matan da ya dace mu aura sabo..... Yarima ya katse shi, please wannan ra'ayinka ne ni basu min ba, magajin Malam yace ni ko kaga akwai yarinya da nake so amma ina shakkar tunkararta. Yarima ya dube shi, wannan wace yarinya ce har da zata daga maka hankali? Magajin Malam yace sumayya yar gidan Umman gombe, tsaki Yarima yaja, sannan yace kai dai soko ne, yanzu dama wannan yar yarinya ce har kake wani kana shakkar ta? Kada ka bani kunya mana, ni nan shi yasa na ke matukar burge kaina, duk yanda mace ta kai da tsaruwa tayi kadan in tsaya ina wani binta ko in lallabata ba ayi ta ba, kuma ba za'a yi ta ba, in da na gagara kenan, magajin Malam yace ai matan sun fi son irin Ku masu wulakantasu, ni dai zan kai kaina gurin sumayya da naso ne in jira yi zuwan ka sai ka ja min gora muje, da sauri Yarima ya kalle shi muje INA? Gidan su can gomben cewar magajin Malam, god forbid, ba zan iya zuwa gidan su da sunan na raka ka tadi ba, sai dai in gaida Umman gombe naje kai ni fa ko matan nan da suke da daraja a idona sai dai su biyo ni, ba dai ni na biyo su ba, ni suke ya yi ba su nake ya yi ba.magajin Malam yace ba zaka gane ba ne, matanmu na arewa suna da kamun kai natsuwa da kuma kunya ba za su taba binka ba,sai dai in an dace da masu ra'ayinka su daban ne, tsaki Yarima yaja sannan yace ba a wata mace da zan so ta ba, kaf Nigeria, na fada da babbar murya, magajin Malam ya yi dariya sannan yace daina zafafawa shi Allah ba yanda bai iya ba, in yaso sai ya dauko wuyan ka ya mika ma yar nigerian ta yi ta juyi da kai son ranta, Yarima ya mike tare da fadin wannan kam tatsuniya ce irin ta mutanen da, ko cikin mafarki bana zaton zai yiwu bare a gaske, kai dai kai mishi hotuna ka ce basu yi ba, shi kenan magajin Malam yace in kuma shi yaga wadda ta yi ya zaba maka da kan shi fa? Murmushin takaici Yarima ya yi sannan ya shiga bedroom din shi don yin wanka.


***************************


Cikin sa'a Bilkisu ta soma aikin bautawa kasa, an fi turata gidan radio station na Kaduna, fannoni daban daban duk tana tabawa, wani sa'in ma har gefen TV sukan turata, yau kan news zata yi a dauka duk ta kasa sukuni saboda zata yi wani Abu ne da bata taba zaton zai zo kanta ba, duk da tana sha'awar hakan. Mansu ita da farooq dinta suna ta karfafa mata gwiwa tun a gida, sai da aka dora mata kyamara ta yi addu'a samun nutsuwa nan take natsuwa tazo mata, ta shiga karanto cikakkun labarai cikin harshen turancinta din nan dan gaske, Masha Allah haka duk wadanda suka kalli labaran litinin din yau suke cewa, saboda ganin kyau tare da zazzakar muryarta tana dawowa, Mansu ta rungume ta tana cewa kin ganki kuwa? Tamkar dama kin dade kina yi kina karantowa kina dago kai tare da juya kyawawan idanuwanki, Bilkisu ta ce har ma da sharri wane juya ido kuma? Abokan aikinta ma sun sha mamaki tare da al'ajabin kwazonta cewa suke Allah kin yi kokari Bilkisu Muhammad Salis. 


A Zaria kuwa babansu haushin mama yake ji nashi ganin ta tura ya karuwancine a Kaduna, in ma ta sake ta debo ciwon zamani ba dai gidan shi ba,su Ladiyo ma haka suke cewa, ta tafi yawon dandi suna zuga shi yana faman fada. Goggo Amarya kuwa cewa ta yi Allah ya isa tsakaninta da Fatima kuma tayi bakin cikin hada zuri'a da ita, auduga Mamanmu ta sa ta toshe kunnenta tana yiwa 'yarta fatan alkairi ne ta tsaya tsayin daka dan yiwa 'yar tata addu'a saboda Allah yana saurin karbar addu'ar iyaye ga ya'ayansu. 


***************************

Lokacin rakiyar magajin Malam filin jirgi ne suke tattaunawa a mota, Yarima yana me kara jaddada ma magajin Malam sakonshi gurin mai martaba, fadi yake yi don Allah kace mishi duk cikin su babu wadda ta yi min, yar dariya magajin Malam ya yi kafin yace wlh ba zan iya cewa mai martaba haka ba, jin ka kawai nake yi, dama shiru na maka in na shiga jirgi in duba hotunan wadda ta kwanta min a rai sai na ce mishi ga zabinka, Yarima yace tab ka ce kaso dai ka kulla min tsiya? Magajin Malam yace tabbas domin kuwa ina fada sai a shiga biki, sai dai kaji an  gama.Yarima ya yi parking gefen titi yace da ka cuce ni yanzu to yaya zan yi ne ma? Magajin Malam yace oho, ni dai ba zan iya yiwa mai martaba rashin kunya ba, domin wannan rashin kunya ne, kai ka kira wayarshi ka sanar dashi cewa babu wace tayi maka. Yarima yace kasan ko da wasa ba zan iya ba, to shi ne ni ka ke son in je gaban shi in gaya mishi haka, kimarshi ta wuce nan a gurina, ni kawai ka kai ni kada lokaci ya kure, jirgi ya barni a tasha, wayarshi, ya shiga Neman layin mai martaba, a zuciyar shi kuma yana kisima me zai CE mishi? Yarima yayi sallama lokacin da ya ji an dauka, mai martaba ba ya amsa sannan ya soma gaishe da mahaifin nashi cikin girmamawa, mai martaba yace ina fata kuna lafiya? Lfy lau in ji Yarima sannan yace am dama shi kenan dai dama zan gaishe ka ne, mai martaba yace kayi magana Modibbo nasan akwai abin da ka ke son cewa Aa ba komai ranka ya dade, yace shikenan kaga sakon gurin magaji ko? Yace na gani ka zabe ne? Mai martaba ya jeho mishi tambaya, eh am...Aa ban amma dai kawai Ku zabar min don ni banga wadda ta kwanta min ba.


Yarima ka duba sosai kuwa? Cewar mai martaba, na duba amma Ku duba min duk wadda kuka ga ta yi shi kenan, ni nawa bi ne In'sha Allah, to ko dai auran ne ba ka so? Ina nufin ya yi wuri? Aa in ji Yarima, ni duk yanda kuka yi shikenan zan bi, shirun dan lokaci sannan mai martaba yace shi kenan tunda ba su yi ba za a duba maka wasu sai dai ina maka nasiha da cewa kazama na kirki a duk in da ka ke ka guji zina saboda ita babban zunubi ce ka sani in ka yi da yar wani sai anyi da taka in ko da matar wani kayi haka nan za'a yi da taka, ka zama na gari wannan shi ne yace to na gode Allah ya kara maka nasara, magajin Malam yana nan zuwa yanzu zai taso yace Allah ya kawo shi lfy.


Ya dubi magaji cike da fara'a na ci nasara, kai mugu har kana min dariya, suka tafa ya kai shi filin jirgi suka tashi ya juyo gida cike da nishadi prince kenan.


 Watanni shida kenan da fara service din Bilkisu, sallah ce ta zo babba, sun samu dan Hutu na kwana uku su Mansura gombe zasu je sallah sun matsa mata da cewa lallai da ita za suje tace bari in munje zariya kila in je, haka ne kuwa, Allah yasa tana da rabon zuwa, Mamanmu ta ce kuje mana ba zai yiwa ba ma in hana ki zuwa, suna zaune a falon Mansura na gidansu a can gomben tsarar rangida ne da a ka ganshi cikin family house din su farooq an sauke su da kalolin abinci masu dadi dangin farooq suna matukar son Mansura,

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 23 馃彽


Yammatan gidan su hudu ne kannan farooq, sumayya ce kurum suke ciki daya dashi,sauran duk uban su daya amma kansu hade yake.Suna girmama mansura sun shiga dakin su suna labarin kyan Bilkisu.Da dare suna zaune dakin hajiyar farooq wadda take matukar jin nauyin mansura,da Bilkisu kadai take hira itama jefi jefi tace,yar nan na zata kin yi aure?Bilkisu tayi murmushi tace  Allah bai kawo lokacin ba,ta dube ta cike da kulawa,to Allah ya kawo na alkairi kada ki yi ruwan ido ko ki ce sai wane kin ji ko?Bilkisu tace to hajiya,ni dai ma ban samu bane in na samu mai so yaushe ma zan tsaya cewa sai wane? Haka kawai ta ji hajiyan farooq ta kwanta mata a rai har ma tana sha'awar ta gaya mata matsalarta,hajiya ta gyara zama,me ke faruwa ne da ke 'yar nan? Bilkisu tace wlh ban sani ba hajiya,ni dai tunda na taso da sunan wasa ban taba 脿samun wanda yace ina sonki Bilkisu ba. Al'ajabi ne ya cika hajiya tare da tausayinta,tace ke ko da za ku jima ne ai da kun je bauchi in kai ki gurin mahaifinmu,shi malami ne waliyin Allah,

 In'sha Allah matsalarki tazo karshe, mansura dake gefe tana jin su,da farko har ta ji haushin Bily menene na tona ma kanta asiri? Amma jin haka sai tace hajiya zamu je don batun aiki kiyi waya ki ce baki jin dadi, nima farooq yasha gaya min ko zamu je gurin kakansu a bauchi, in na gaya mata sai tace mu bar komai hannun Allah hajiya tace to sai ya kai ku in'sha Allah za'a warware matsalar kada ki damu,godiya suka yi sannan suka ci gaba da dan tattaunawa, ran jajibari suka zo gombe washe gari ranar idi suka dauki hanyar bauchi, gidan Modibbo Al'amin Dattijo mai ran karfe nan suka sauka, gida ne na alfarma ginin zamani da 'ya'yanshi suka tsara mishi,farkon gidan,shi ne a sasan farko mai dauke da tafkeken falo da dakunan bacci guda biyu,daga ciki dan autan shi ne jafar tare da iyalinshi tsohon yana da yara kusan guda 16, shidanne maza yayin da goman suke mata, ya'yanshi duk suna da rufin asiri matan kuma duk suna auran masu rufin asiri. Farooq ne yayi musu jagora zuwa falon Modibbo yana zaune kan wata lallausar darduma kan kafet, tsohon mai yawan shekaru ba yada rudu sam tuni matanshi sun jima da rasuwa,farooq ya zauna kusa dashi  yana cewa,barka da war haka Akaramakallahu,ka ko shaida mu?Su mansura duk suka zauna gefe,ya dago ido ya kalle shi sannan ya kalle su?Yayi dan murmushi,Ummmarul faruku duk da baka zuwa gaishe ni ai ba zan manta ka ba,wadannan dai su ne ban san su ba, kila iyalinka ne,cikin yar dariya suka gaishe shi, farooq yakara shige mishi sannan yace ka min uzuri saboda nisan garin da nake aiki, amma ai ina yo maka aike ko?Aiken ka baya damuna nafi son kazo ka gaishe ni fiye da sakon ka,yace to zan kula,ni kaina ina son zuwa ka dinga sa min albarka,yanuna mansura ga mai dakin na nan,ya tashi yadauko dady,yana bacci ma yadora mishi akan cinya,ga kuma danka nan tsohon ya rungume shi masha Allah,yayi girma to ka kai su ciki gurin kawun naka,ya mike ko mu shiga ciki mace mai kirki da son mutane ta sauke su cikin farin ciki 

da la'asar Farooq yana son ganawa da tsohon amma mutane sun mishi yawa,da yawa 'yan gaisuwar sallah ne, manyan attajirai ne tare  da malamai,farooq ya shiga cikin gidan yace ku shirya muje mu gaida umman gidan mai martaba,hajiya fati tace gaskiya ne suma dai nasan gidan yau yan gaisuwar sallah sun yi yawa, amma gara yau akan gobe,tunda gobe hawa gaban bilkisu ya fadi tace a ranta dama farooq suna da dangantaka da gidan sarki?gidan su yarima kenan,sun shirya bilkisu cikin jallabiyya baka ta zagaya dan gyale tamkar yanda larabwa suke yi,takalmin ma baki ne.Hajiya fati ta yi ta yabon kyan bilkisu da tsarinta, mansura cikin shadda galila suka sha anko ita da farooq suka nufi kofar fada. Tsararran gida ne ginin zamani duk da girman gidan harabar cike da motoci na alfarma suka yi parking sannan suka fito me yasa gaban bilkisu yake faduwa? Sun shiga kofafi faluka kashi-kashi, kafin su ka shiga wani tafkeken falo, yana shimfide da carpet kirar china me shegen laushi,

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 24馃彽


Ga kujeru na alfarma kusan gefe uku kowacce da kalarta kuma ta dace da gefen da aka jera su, wata Dattijuwa ta nufo su da fara'a tana cewa Aa umar farooq kune a gidan ina gajiya?yace babu gajiya hajjo umma tana ciki kuwa?Tana nan bari ayi muku iso,ta fito tace gata nan zuwa, sai nan ta shiga gyara mata inda zata zauna,ma'ana ta shiga kakakabe kujerar duk da ba ko kura akanta,kyakkyawar mace ta fito sanye cikin wani leshi na alfarma, gwala-gwalai ne suke kyalli a yatsunta a hannun da na kafa, zuwa wuyanta. Tunda ta fito take kallon bilkisu a zuciyarta kuwa fadi take masha Allah, ta zauna kan kujerar ta dubi farooq da suka zube kan carpet tace idonka kenan ko farooq?Yayi murmushi yace ayimin afuwa umma, ta dubi su mansura tabe to wace ce matar taka cikinsu ko dukansu ne?Yana 'yar dariya ya nuna mansura sannan ya mika mata dady,kiyi hakuri umma ko gombe ma ina dadewa ban zo ba,saboda yanayin aiki wannan karon ma dan hutu ne muka samu,shi ne muka zo gaishe ku, tace to mungode Allah yayi albarka,

.ta nuna Bikisu wadda kanta ke sunkuye tace wannan fa?Bata san me yasa yarinyar ta tsaya mata a zuciya ba,farooq ne yayi magana,kawar mansura ce itama ta biyo mune tayi gaisuwa,umma tace mungode kwarai amma tana da aure ne?Yace tukunna dai tace to Allah yabaki miji na gari,shi da mansu suka ce amin, tace umman taka fa? Tana gaishe ki su sumayya ma ina ga yau za su zo,yaya gurin su anty salma su Aisha?Ta ce duk suna lfy sai gobe zasu zo gaida mai martaba,yace sai dai a gaishe su dan gobe zamu juya Modibbo ma mutane sun mishi yawa bai san ma munzo nan ba,tace yau kam Modibbo ai har dare amsar gaisuwa zai dinga yi.yanzun nan ma nake ma takwaranshi magana yazo yaje ya gaida shi  tunda kwana uku zuwa hudu zai yi ya tafi farooq yace Al'amin yazo ne? Tace jiya me martaba yace mishi yazo gida yayi salla farooq yace ya fito ne?Yaushe rabon da mu hadu anfi shekara7,Umma tace kai dashi duk ba masu son zumunci bane bari in kira muku shi ku gaisa,

Dai dai nan wasu 'yanmata su biyu suka soma jere kayan ciye-ciye da shaye-shaye a gaban su mansura da farooq. Bilkisu gabanta ya tsananta  faduwa kanta kuma yana kasa wasa take da zoben dake karamin yatsanta, umma ta kira layin Yarima tace babana ga yayanka ummar faruk kazo ku gaisa yace to su dan jira shi zai yi wanka, tace babana  kayi sauri na sanka fa,yace to su ka ci gaba da hira tare da 'yan ciye-ciye, bilkisu kam kasa cin komai tayi kuma sai ta samu kanta da matsanancin jin nauyin umma,kula da hakan da umman tayi na kin ki cin komai da bilkisun tayi ne yasa tace ke kin ki cin komai saboda me?Ta dubi  umman cikin jin kunya tare da dan murmushi,ta ce na koshi ne.Umma tace ka'idar gidan nan in ka shigo sai kaci abincin gidan,tasa hannu ta dauki yankakken apple ta  saka abaki,tana taunawa a hankali idanun umma na kanta yarinyar sha'awa take bata,ta dubi mansura, yaya sunan kawar taki ne?Mansura tace sunanta bilkisu a ranta tace ta ci sunanta,Bilkisu maigadon zinari..


 Kamshin data ji ne yasa gabanta ya tsananta faduwa menene take jine kodai mafarkin tane na yau da kullum?Muryar nan ta Yarima ta jiyo mai cike da kasaita da son girma, ya dubi farooq cike da sakin fuska yace,yayana sannu da zuwa,ashe da rabon zamu gaisa ne, farooq ya mike tare da mika mishi hannu,suka yi musabaha yana tambayar farooq iyali ya nuna mansura yace gata nan,ya dubi dady dake wasa kusa da umma, yaronka ne wannan? Yace eh Yarima ya tsugunna kusa da daddy yace Hello handsome, mansura tace ina yini, ya zuba manyan idanunshi kan fuskarta, yace lafiya yaya boy da yayana tace lfy,Bilkisu kam ta kasa dago ido ta kalli Yarima ganinta irin mafarkin da ta saba yi ne,mansu ta tabata tare da yi mata alama da ido wai su gaisa da Yarima, ta dago ta dube shi dai dai sanda ya zubo nashi idon kanta miyan bakinta ya kafe,ta kasa motsa lebanta ma bare ta iya furta wani abu,shi dai ya kauda kanshi amma zuciyarshi cike da mamaki,kyawunta tafi kama  da larabawan gabas ta tsakiya,

 Fiye da yan nigeria ta kuma kallonshi tana son ta  tabbatar da cewa ba mafarki take yi ba,don haka tace Yarima! Ya kalle ta da sauri tayi  dan murmushi har yanzun baka huce ba kenan?Cikin mamaki ya dube ta,a ina ki ka sanni ni?Ta dubi mansura sai kuma tayi shiru. Farooq yace cikin mamaki,kin san shi ne Bily?Tace tunda bai gane ni ba bar shi kawai,shiru Yariman yayi yana son tuna inda ya santa,umma cikin dan murmushi tace babana baka santa ba? Ya mike tare da fadin ban taba ganinta bafa, cike da rainin wayo ya fada,har ma su mansura da umma basu ji dadin yanda yayi ba,musamman mansura da tasan cewa Bilkisu ba ta da son magana da maza to ko shi ne Yariman mafarkinta?Shi ko ciki ya koma bilkisu ta bishi da kallo,Yariman mafarkinta ne tabbas, meyasa bai gane taba? Shin ko shi ba ya mafarkinta ne?Abokin wasanta tun suna yara? Suyi fada suyi wasa.

[8:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 25馃彽


Har suka koma gidan Modibbo mamakin Yarima tayi tana kwance a kan katifa a masaukinsu, Mansura ta dafata Bily a ina ki ka San Yarima? Cike da nadamar yi mishi magana ta ce shi ne Yariman mafarkina, tun muna yara amma dubi yanda yayi min, ba laifinshi ba ne ni ce da na mishi magana, Mansura ta dan yi murmushi kin manta ne cikin mafarki ne? Kin manta cewa mafarki ba gaskiya ba ne? Sam Bilkisu ta manta da wannan batun har ma ta ji haushin kanta game da maganar da ta mishi, tayi data sani sannan ta cika da al'ajabin ganin Yarima yanda ta San shi a mafarki haka yake.


Farooq ne zaune gaban tsohon suna tattaunawa cikin nisan dare, ya sanar mishi da Abu buwa masu yawa game da Bilkisu kuma tsohon ya yi mishi alkawarin ganawa da ita, da safe bayan yayi istihara kan lamarinta, hakan ce ta kasance da safe inda ya gana da Bilkisu ya yi mata yan tambayoyi domin yaga Lamari da yawa cikin al'amuranta, ya dube ta jikata ki kanyi mafarki ne haka ko na ruwa ko na gini ko na wani mutum? Tace eh to na kan yi mafarkin wani tun ina yarinya kuma har yanzu ina yi sai dai in ban kwanta ba, ya dube ta kamar ya ya kike yi? Tace ina mafarkin shi wani dan sarki ne, muna wasa kuma yana yawan ce min in je in nemi tarihinsa, tsohon ya kalle ta na tsawon lokaci tamkar me son ya karanci wani Abu a fuskarta, sannan yace Bilkisu In'sha Allah za ki yi aure, kuma a yanda na fahimci al'amaran mijin naki zai kasance wani ne ma'ana babban mutum ne, kuma lokacin ya kusa sai dai naga rigingimu da yawa kici gaba da addu'a nima zan taya ki, kanta a kasa tace In'sha Allah zan dinga yi zuciyar ta kam tab da tunanin wai ta kusa aure? Kuma mijin dan babban gida ne?


Yanzu zan ba ki wasu addu'a zaki dinga yin su a lokutan sallah da kuma bacci, duk da cewa na lura ke din mai tsayawa ce akan addininta, Allah ya yi miki albarka, tace na gode kwarai, In'sha Allah zan kiyaye, Mansura ko da ta ji labarinn da suka yi da tsohon daga bakin Bily murna ta hau yiwa aminiyarta ta kusa aure, tace da yace mijin da za ki aura dan babban gida ne sai na raya Yarima, Bilkisu ta kalle ta cikin sauri ki ka raya Yarima! Mansura ta ce sosai ma, Bilkisu taja  dogon tsaki don Allah ki bar yi min mugun fata,ni fa Yarima nan ba wai ina sonshi ba be, ko cikin mafarkina aboki na dauke shi tunda shekarunmu daya, sannan ma sabonmu cikin mafarki ne tunda dibi wulakancin da yayi min gabanki Mansura ta ce Aa ba zamu shirya ba, ni fa bani da burin Auren yaro karami , Yariman nan fa na girme shi, Allah ya tsare ni da auran karamin yaro ko da Modibbo yace babba ne zan aura ina zaton yana nufin babba mai shekaru, shi ne kuma ya dace dani, Mansura ta ce ba wani ke dai kin cika ra'ayi kuma In'sha Allah shi ne mijin ki, fita Bilkisu tayi har ga Allah cikin ranta ta tsani zancan Yarima. suna cikin shiri sai gombe yau, kuma sai Kaduna, sun gama shiri tana cikin wani Jan yadi mai ratsin baki, tayi kyau sosai Mansura ta ce don Allah kiyi kwalliya ki dan yi shafe shafe zaki yi tamkar balarabiya, tace Aa bana so yar hodannan ta ishe ni tana magana tana fesa turare ta dauki karamin kum tana taje gashin ta zuwa baya farooq suka shigo shi da Yarima da kuma magajin Malam, da saure ta dauke dan kwalinta ta rufe kanta amma duk da haka Yarima ya gani, magajin Malam kam cewa yayi Masha Allah ya dubi Yarima ya mishi rada, kaga hurul inin duniya? Yi yayi tamkar bai ji ba kuma yaki kallon inda take tun da ya kalle ta sau daya, kan kujeru suka zauna Mansura ta gaishe su, suka amsa farooq yace Mansura babu rabon ku kalle hawa yau zamu tafi su kuma yau zasu fara, Mansura ta kalle Bilkisu, Bily ko mu tsaya ne? Ta yatsina fuska, A'a aikina Ku ku tsaya ni kam zani koma bakin aikina Yarima ya saci kallon ta wannan ya kula tana da gadara, shi zata ma gadara? Yaji bata iya ta gaishe shi ba don ma rainin wayo jiya har da nuna tasan shi ? Gashi yanzu ma ko ta gaida su magajin Malam yace ina kwana Malama? Ta dube shi lafiya, ya ya sallah ? Ya ce Alhamdulillah, jin muryarta ta saka magajin Malam rudewa yayin da Yarima yayi tsam da ranshi yana sauraronta, suna hira ne jefi jefi Yarima yace ma farooq mu zamu tafi dama mun zo gaida tsohon nan ne nima gobe ko jibi zan koma in ban zo yau ba maybe ba zan samu zuwa ba farooq yace to kun gaisa ne? Yarima yace kasan shi da mutane, mun zo yana da baki ya dubi magajin Malam duba mana tsohon nan ko bakin sun tafi, 


A ran Bilkisu fadi take wannan dan rainin wayo ne,ban da haka mene nashi na Aiken wannan, shi kuma har da zuwa tashi tayi ta fita ta shiga gurin hajiya Fati, ta same ta tana shafa ma yarta mai,yar kyakkyawar yarta mai gashi, ta zauna tare da fadin baby zo nan in shafa miki man, dama gata da son yara. Hajiya tace kuna ta shiri ko? Tace wlh dan ma wannan Yarima ne ko wanene? Ya zo yana jiran Modibbo su gama da baki da yanzun mun dauki hanya, tace Aa Yarima yazo kenan? Tace ina jin shi din ne taci gaba da shafa ma Aisha mai tana sama yarinyar kaya sai ga Yarima ya shigo tare da sallama hajiya tace Aa mutanen wacan kasa yaushe a gari? Yace shekaran jiya nazo, gobe nake tunanin tafiya suka gaisa da yar hira Bilkisu tana jin su ta taje ma Aisha gashin ta sai nan ta dago kai ta dubi hajiya tace, hajiya ina ribbon din ta? Ta jeho mata sai ta dan kalle Yarima cikin sa'a suka hada ido ita ce ta soma kauda kai shi kuma ya mike bari naga dan takwarkwasasshen tsohon nan da ya ki mutuwa, hajiya Fati ta ce lallai haka ma zaka ce? Albarkarshi fa kake ci ya tafi.

Hajiya fati tace Yarima kenan,tsohon nan naka yana matukar ji da kai,kai ko tsiya ka ke mishi,Bilkisu kan ta duk adaure tun jiya tana son sanin wani abu da Yarima,tace shima yana da dangantaka da Dattijon nan ne?Ta dubi  Bilkisu baki bude sannan tayi murimushi jikan shi ne kuma shine jika mafi soyuwa agurin shi, kenan suna da dangantaka da farooq? Cewar Bilkisu kanta bata amsa sai ga mansura ta shigo ki zo ga wayarki ta amsa ta fita tana amsa call din sa'adatu sani abokiyar aikinta ce, farooq ya cekuzo mu tafi fa,bilkisu tace to bayan ta gama amsa waya. Yarima zaune gaban kakanshi bayan sun gaisa ya dan mishi tsokana irin ta kaka da jika,sannan yace Aminu ana can ana ta shirmen ko?Ya shafa keyarshi tare da fadin a haba dai muna karatu ne ba shirme ba,yace to yaya batun aure kuma ina fata ka soma shirin yi?Ya dubi tsohon haba wane aure?Ai ba yanzu ba,sai yaushe?Sai na gama karatuna na fara aikina nahuta,yace nan da yaushe kenan? Yarima cikin jin dadi ya gyara zama domin yasan cewa in tsohon ya daure mishi

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKE FARUWA 26馃彽

In tsohon ya daure mishi gindi ba zai yi ba,to dole ne mai martaba ya hakura, ya soma lissafi, shekara 7 zan yi zuwa 8 yanzu nayi 4 ina cikin na5 , saura 3 da yan watanni, in fara aiki duk dai da komai mu barshi nan da shekara 7 ,lokacin shekaruna sun kai 31 kenan.


In soma neman Auren zuwa yin Auren kila ya kai shekara ko biyu haka in an hada tare kenan, tsohon yayi dan murmushi yace haka ne, to Allah ya taimaka, ya dauko wani Kofi ya juye ruwan zam-zam a ciki, sannan yayi wata addu'a ko nace ya tofa addu'a sannan ya mika mishi, 


Yarima ya saka hannu biyu ya karba ya kafa kai ya shanye tare da addu'a nasan zaka zo kafin ka tafi ko? Yace eh to zan zo kila gobe ne fa tafiyar, yace to kayi kokari ka zo din dan zan baka wasu addu'o'i su farooq suka yi sallama suka shiga falon dan yiwa tsohon sallama, kusa da Yarima farooq ya zauna, su Mansura suna gefe Bilkisu a ranta du'a'i take yi Allah yasa kada tsohon yayi maganar matsalar ta a gaban wannan sarkin girman kan, farooq yace mu zamu tafi, tsohon ya ce to Ummarul Faruku, Allah yashi albarka, kawun ka ya yi min bayanin tsaraba, Allah ya kara budi mun gode da zumunci, to Ku tashi na sallame Ku har kai Aminu, ya nuna Bilkisu ke kuma jikata bari in dan ganki.


Ya dubi Dady dan zo nan, dady yaje gunsa ya shafa kansa Allah ya yi maka albarka, Mansura ta ce mun tafi sai wata rana, ya ce to ki kula da zumunci kada ki biye wa mijinki, suka yi dariya tare da mikewa, Yarima kam dama ranman gim kuma ya riga su fita, bayan duk sun fita ya dubi Bilkisu zaki samu dawo wa nan kusa? Tayi shiru sannan ta ce matsala ta yana yin aikina, amma da na samu dan Hutu zan zo, yace shi kenan amma ki rike addu'o'in nan da kyau, tace na gode, Ya ce zan ci gaba da addu'a nima a nan, tashi kije Allah ya yi miki albarka, ta tashi tana godiya suna sallama da Yarima Bilkisu ta fito, ya bita da kallo a ranshi yana tunanin shin KO dai yar uwarsu CE?  


Menene hadin ta da.  Kakanshi? Ya dan kalle ta yana jin mamakin kyan da cikar halittarta yake yi sai dai kuma kauyanci irin na matan arewa ya hanata ta nuna kyaunta, ya shiga motar bayan shima ya yi sallama da farooq. 


Mansura duk murna ta cika ta son surukarta ya kara shigarta, haka nan Bilkisu ji take tamkar mahaifiyarta CE,ta zayyane mata yanda suka yi da tsohon, itama taji dadin jin hakan ta kuma yi fatan alkairi taso su biya gurin Umman Mamanmu amma suna sauri ne jiya da suka je Bauchi, zariya suka  tsaya Mamanmu tasha murana jin batun da tazo dashi washe gari da sassafe suka nufi Kaduna ta koma bakin aikinta.


Yarima yana kwance a dakin shi can malesia, ya rasa dalilin da yasa zuciyar shi ta cika da son ya tuno inda ya san yarinyar wadda zuciyar tashi ta mata lakabi da beauty, amma ya kasa, ya sani bashi da saurin mantuwa da sun taba haduwa kyanta ba mai saurin gushewa a rai ba ne da zai tuna, wata zuciyar tace meyasa ka damu kanka da tunanin inda kasan wannan yar kauyen? Tsaki yaja sannan ya mike yana ayyanawa a zuciyar shi, cewa cikin lokutan da ya tsara bai cire na tunanin kowa ba,saboda bai ga macen da ta isa ya tsaya tunaninta ba, can haka ya tashi ya nufi kicin don kora wani abin mai dan sanyi. 


Dattijon ya maida hankali ne kan rokon Ubangiji ya karkato hankalin jikanshi ga aure, duk addu'o'in da ya yi mishi cikin ruwa da wadanda zai dinga karanta wa duk saboda hakan ne.


kwana uku tsakani zuciyar Yarima ta tsumu da sha'awar yarinyar da zuciyar shi tasa mata suna beauty, in suna kwance da chelen sai ya dinga rayo beauty, in su Vicky ma yanzu ana dai harka ne kawai, a tsarin shi baya son ya nemi yar arewa don baya son raini, su din basu waye ba, bayan haka ma baya son ya samu zubar da darajar gidansu, to meyasa ya samu kanshi da jin sha'awar yarinyar, ya tuno cikar kirjinta da yanda mazaunanta suke juyawa, lokacin da zata fita daga cikin masaukinsu na gidan kakanshi, tunanin yanda yarinyar take yaji irinta ta yaya, zai kai ga samun haka? Duk da ya kula sai saka yake yana warwarewa, kafin daga karshe ya yanke shawarar neman farooq, bayan sun gaisa ne farooq yace, lallai yau za'ayi ruwa da kankara Yarima yayi murmushi yace dan dai da ba ka da number ta ne shi yasa bana gaisuwa.


yace, haka ne kam dama ina son in tambaye wannan yarinyar ne wani Abu shin kana da number din ta? Farooq yace wace kenan? Yarima yace, wadda Ku ka zo tare din nan,. Ya ce OK kana nufin Bilkisu ba? Yarima yace, kila ita din ce, kawar dai matarka. Farooq yace kana sonta ne? 


Ko kusa, zan dai tambaye ta ne wani Abu.farooq dai ya tura mishi number. Yarima ya soma tunanin yanda za ta dauki abin da zai gaya mata, amma sai yace bari ma dai ya fara sanin ina ta san shi? Kuma yaya suke? Ma'ana shi da ita

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 27馃彽


Ta dan watsa ruwa don taji iska kamar yanda ta saba yi kullum in zata kwanta, ta shafa humra mai hade da wani turare mai dan karan kanshi, ta saka rigar baccinta haye gado. Mansu ta shigo tana cewa. Bily ga dan gidan ki wai yau ma nan zai kwana.


 Ta jawo shi ta kwantar a bayan ta tace. Ai dama dadyna dan rigima nasan nan zaka kwana ko? 

Yace, eh momy. Haka yake kiran su su duka. Momy Bilkisun ma yace momy mansu tace bari in je in kwanta kamshinki yana rinjayata. Bily tace kija mana kofa sai da safe.


 Cikin bacci taji wayarta, cike da mamaki ta dauko ta daga saman kanta ba ko shakka kuskuren numba ne tunda ita ban da mansu da mijinta sai kannanta su Sakina sai ko abokan aikinta bata da mai kiranta amma duk da haka sai ta dauka cikin yana yin bacci tayi sallama daga can gefen ya amsa a kasaice, sannan yace.


A ina ne ki ka san Yarima? 


Nan ta wartsake, haushin shi ne ya cikata tace rai a bace. 


 Wanene kuma Yarima? Ni ban san wani Yarima ba, kai Malam. Yayi shiru maganar ta matukar ba shi takaici,amma ya dake.


Kada ki damu please sanar dani. 

Tace kai ni fa ban san shi ba.

 Dole ne kin san shima don in da ba ki san shi ba ai baza ki nuna mishi sani ba,amma tunda kin ce haka menene dangantarki da Modibbo family? 


Wadannan tambayoyin fa sun ishe ni haka, ta ce da shi.

Dole ne kuma ki amsa su. Shima yace a fusace.

 Tsaki tayi sannan ta kashe wayar, ta kwanta zuciyar ta tam takaici. 


A nashi gefen kam yafi ta bakin ciki sosai, bai taba zaton wata mace zata yi mishi wulakanci haka ba, wai macen ma yar Nigeria kuma yar arewa bakauyiya. Ya girgiza kai. 

Alkawari ne sai na rama ko ta halin yaya ne. Ya yi niyyar share ta amma sai ya fasa. Kuma kiranta yayi

 ta dauka, wai lafiya? 

Amsa min tambaya ta, yace da ita sai ka zo ka shake ni na amsa maka din.

In kin fi son haka za ki samu.


Tace toh bismilla, ina jiran ka. Ta kuma kashewa. 

Ya mike tsaye, ba a taba cin mutuncinshi haka ba,mace ce ma tayi mishi haka kai shi ko namiji ma bai taba mishi wannan cin kashin ba, bare Mace wadda bai dauke ta komai ba sai abin nishadi ya na bata daraja ta wannan fanni amma baya daukar raini, kwana yayi yana da na sanin kiranta kuma yanzun in ya barta haka taci nasara akan shi kai sai ya yagata.


Washe gari da safe yana kwance cikin bahon wanka tunani ne ya ci kanshi Sam ya kasa yin komai saboda takaici yana son ya samu mafita amma ya rasa sai dai zuciyar shi tafi tafiya kan Abu daya, ya yi soyayyan karya da ita ma'ana ya daure yace yana sonta sai ta shiga tarkon shi sannan ya yagata, ya gama wanka ya fito bai tsaya gurin shafe shafe ba, kai tsaye ya wuce bedroom din shi waya ya dauka sannan ya zauna kan wata kujera dake gaban dogon madubin nashi, ya soma kiran layinta dai dai suna karyawa ita da dady tana sauri ta fita ta dauki wayar tana dubawa shi din ne,dama ta zargi haka,ta dauka a dake yace.


Ki sanar dani in da ki ka sanni.

In an kifa?

Tace a fusace.

Zaki yarda ma,ba kamar ma in kin shirya yin aure? Dan nasan shi ne kawai zai yi maganin rashin kunyar ki.


A tsaye zancan yazo mata a ranta tace wannan kanshi daya kuwa? Amma a fili sai ta ce 


Ba ka isa ka aure ni ba ka min kankanta ka min yaro, nasan kuruciyarka nasan yarintarka don haka ka min kadan kai kanin bayana ne don haka.....

Ya katse ta.

Ke!!! Kina hauka ne? Ni ki ke gaya ma haka ? Ki sani ban taba samun macen da taci min mutun ci irin haka ba,zan nuna miki ni yaro ne sai na aure ki kuma sai na ganar dake kurenki I promise za ki San wanene YARIMA

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 28馃彽


Duk yanda Bily taso kada tasa

abin aranta sai da hakan ya faskara,domin kwana

tayi tana tunanin dalilin Yarima na cewa lallai sai

yasan inda ta sansa,bayan tun farko shine ya

dauko hanyar da bazai yiwu ya sani ba,domin

daya saurareta lokacin data nuna tasansa hakika

daya ji cewa cikin mafarki ne.Sai yanzun yana

nuna shi fa dole ne ma ta sanar dashi saboda

wannan dalilin shine har yake ikirarin aurenta

saboda ya wulakanta ta.Da safe bayan sunyi

wanka da Dady tana shafa masa mai,Mansu ta

shigo Dady yace Good morning Momy,tace How

are you my boy,Bily ta saka dariya tare da cewa

Iye! Yaron yayi hankali.Mansu tace waya koya

maka gaisuwa ne?Ya nuna Bily tare da fadin

Momy din nan ce tace inna gaida Momy da

Abbana zan shiga gidan aljanna,wai haka tace ni

Musulmi ne?Dariya suka kama sakawa,Bily ta

soma saka masa uniform Mamansa tana cewa

yaron nan Bily ya baci da surutu.Bily tace,barshi

yayi zaifi daukan karatu,Mansu tace to ina kwana

ko gaisawa bamuyi ba,Bily ta amsa lafiya

lau,yaya twins?Mansu tace,daina min fatansu,ni

yanzun ma dayan na kosa yayo waje,ciki tuntuni

ya fita watan haihuwarsa?Bily cikin tausayawa

tace,gurin Allah ne lokacin da saura.Daya cika

zaki haihu mu samu yaro ko Dady?Dady yace eh

mana,Abba ma haka yace,Momy zata je asibiti ta

siyo mana yarinya,suka fito a tare suna

dariya.Faruk ya fito sanye cikin suit

bakake,Mansu tace har ka fito baban Dady?Yace

naso in makara ma,yakamata yanzu ina office,Bily

ta dubeshi antashi lafiya yayana?Yace lafiya lau

sister,hakan take ce masa tun kafin ayi bikinsu da

Mansu,ya tafi Mansu tana biye dashi,Bily ta bisu

da kallo.Gaskiya lamarin Mansu yana son

gyara,ace kullum mijinka baya karyawa yake fita?

Duk da an san yanzun da ciki,to tun kafin cikin

ma haka take yi,amma bari ta haihu lafiya zasu

zauna dole ta sake tsari.

PRINCE Modibbo kwance cikin kwamin wanka,zuciyarsa tam da takaici tare da tunanin yanda zai bullo ma matsalarshi,yana sha鈥榓war yarinyar,yana jin haushinta cikin ranshi yana raya zai iya komai dan ya muzguna mata ciki harda aurenta,wata zuciyar tace masa,kai da baka son aure yanzu amma ka yarda ka aureta?Yaba kansa amsa da cewa,zan aureta ne don in nuna mata cewa ni da ita ba tsararraki bane,kamar yanda ta zata,kuma ta sanar dani labarin kuruciyata kamar yanda take tutiya,sai nayi Teaching din ta lesson,I promise.Hannu ya kai kan wayarsa dake gefen bahon wanka ya dauka,layin Bily ya soma nema duk da bai tanadi abinda zai gaya mata ba,shi dai burinsa ya bata mata rai da safennan don yasan yanzu su safiya ne a Nigeria.Suna karyawa daidai wannan lokacin wayar Bily ta shiga ruri,haka kurum taji gabanta yayi wani mugun faduwa,ta jawo wayar ta tsura ma number din ido(+)din data gani shine ya tabbatar mata cewa Yarima ne,domin bata da wanda zai kirata daga kasar waje sai shi,tsaki taja sannan ta ajiye wayar,ki dauka mana Bily,inji Mansu ko baki san number din bane?Kamar ta share sai kuma ta dauka domin in taki dauka Mansu zata so jin dalili,kuma bata shirya bata labarin rigimarsu yanzu ba,domin Mansu tana bukatar hutu da akwantar mata da hankali,tare da guje yin wata magana da zata saka ranta ya baci. Tana daga wayar ta saka akunne ba tare da tace kala ba,fuskantar da yayi an daga wayar shine ya saka sa ya soma magana. Ina son sanin abinda kike takama dashi da har kike gaya min magana son ranki? Me kike takama dashi nace? Wanene ya tsaya miki? Ke 鈥榶ar wanene? In sarauta ce ke 鈥榶ar wane sarki ne? Ko mulki kike takama dashi wane Gwamna ne ya haife ki? Ko ke 鈥榶ar shugaban kasa ce? Ko 鈥榶ar wani mashahurin malami ce? Dan kasuwa sananne ya haife ki? Bani amsa dawa kike takama?

Duk maganganun da yakeyi tana jinsa afuskarta ko wani murmushi ne irin na bakin cikin nan takeyi bata son Mansu tasan halin da take ciki don haka sai ta mike ta nufi dakinta,Mansu ta bita da kallo aranta ko addu鈥榓 takeyi Allah yasa aminiyarta ta samu mai so ne.Bily ta zauna bakin gado daidai sanda yake cewa,ki sani ban taba samun mutumin daya bata min rai ba irinki,ko namiji dan uwana sai ke mace,macen ma bakauyiya.Ki sani sai na saki cikin damuwa fiye da yanda kika sakani,in har ki.....鈥渒ai! Ta katse sa da tsawa,saurara min.Taci gaba da magana da kakkausar murya,kai ba kowa bane,kuma kai ba komai bane,duk abinda kake takama dashi shirme ne,kuma ni na wuce da tunaninka,wanda ya tsaya min ya wuce da tunanin,wanda ya tsaya maka bama kai ba.Don sanin ko ni 鈥榶ar wanene sai ka saka cigiya,aure ne dai nace baka min ba,yaushe ma kashinka yayi kwari?Yaushe aka daina yi maka tsarki....?鈥淗ee!鈥淵a katseta you are very stupid,kin san me kike fada?Bari ma na gaya miki,kada kiyi zaton nima sonki ne yasa nace zan aureki,a鈥榓 zan aureki ne on my own baki san ta hanyar aure ne kurum zan gasaki yanda naso ba tare da mutane sun zargi wani abu ba,domin ni nan ina gudun abinda zai bata sunan Masarautarmu,zaki gane kin maida ma prince magana.Ya kashe wayarsa tare da dauraye jikinsa ya fita daga bahon.Bily ta tsura ma wayarta ido tamkar Yarima yana jiki ne,bakin cikin maganganun daya gaya mata takeyi,amma sai ta danne tare da kudurin inta fita zata sayi layin (zain)don ta samu ta huta,ta mayar da (mtn)din.Lokacin data fito,Mansu ta nemi jin wanda ya kira Bilyn,sai ta shara mata karya da cewa,abokiyar aikinta ce take shaida mata cewa ta fito karfe goma domin yau wani gidan buga jarida za a tura su.

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKEl FARUWA 29馃彽

Shi ko Yarima bai kara kulewa ba sai da ya gama shirinsa tsaf,don shiga school sai yaga karfe biyu har ma da rabi.Shi da zai shiga Lecture karfe daya,ya shiga wanka sha biyu da rabi ya tsara duk shirinsa zai gama komai zuwa daya don ya bata lokacin wankan sa ne afalo zaune yana tunanin mafita,har lokaci ya wuce.Ya shiga wanka da nufin yayi sauri ya fito,nan ma yarinyar ta masa sanadin rasa Lecture ya koma ya zauna.Ya rike kai bai taba tunanin akwai wata rana da zata zo ya shiga damuwar da zai shagala har haka ba  a fili yana cewa dole ne ya dauki matakin gaggawa kan yarinyar nan koya samu nutsuwa karatunsa yana bukatar nutsuwa tare da kwantar da hankali.Cikin dare Mansu ta soma nakuda,Faruk ya buga ma Bily kofa duk sukayi asibiti har dady tunda gidan babu kowa,tasha wuya sannan Faruk ya saka hannu don ai mata aiki.Anyi nasarar ciro mata 鈥榶arta katuwa mai matukar kama da Faruk,satinsu daya suka dawo,鈥榶an Zaria da 鈥榶an Gombe kam gasu nan,sai da sati ya zagayo sannan akayi suna inda jaririya taci sunan Umman Bauchi,Mamansu Yarima kenan.Wannan kara ta jama 鈥榶ar farin jini gurin daukacin family din mai martaba,don duk yayyan Yarima sai da suka zo suna tare da sha tara ta arziki,ga kuma na Umman Bauchin sannan gana mai martaba,dankareriyar sarka da 鈥榶ankunne na gwal kirar Dubai.Kowa ina ka saka ina ka aje yake da yarinyar mai suna Sa鈥榓datu.Lallai tayi sa鈥榓,bayan an watse duk sun koma sai kannan Faruk,鈥榶ammatan su uku Sumayya,Fauziyya da Safina.Bily tana kula dasu tare da duk hirar da sukeyi,kusan duka su ukun basu da labari sai na Yarima.Kamar yanzun data shigo ta samesu,Sumayya ce kwance tana zuba masu Fauziyya labarin Yarima tana fadi,kunsan Allah Safina?Nasha alwashin wannan hutun indai yazo ko na kwana daya ne sai naje zan kuma masa magana ince ina sonsa ko in fada ma Ummansa.Safina tace da kin more,ni kaina sonsa nake,Fauziyya kuwa cewa tayi,ai ke Sumayya banza ce,da nice na samu dama irin taki mahaifiyata da tasa ciki daya,ai koda burauba ma sai na auresa.

Bily tace 鈥淎ssha! Ke ko Fauziyya menene na zunduma ashar haka?Babu kyau,don Allah ki daina鈥�.Duk suka hada baki gurin cewa,don baki ga gayen bane anty Bily,yana da kyau ga aji,dan kwalisa ne na karshe.Bily ta zauna bakin gado tana cewa,ni dai inda zan baku shawara ku dauka,dana ce karku yarda kuce da namiji kuna sonsa, don su maza ba a musu haka,Sumayya tace anty don baki gansa bane,kuma ina bala鈥榠n sonsa,duk hakurina ya kare,zan tunkaresa ne kawai.Safina ma tace Allah yasa ki iya,ya cika kwarjini ne da yawa.Bily ta kalleta aranta ko tausaya mata takeyi don Yarima da take magana bamai mutunci bane,ta sake cewa addini bai hana mace tace tana son namiji ba,amma Sumayya alkunya tana da kyau ko?Tamkar zatayi kuka tace,anty Bily nayi alkunyar bai ma san inayi ba,don haka ni zan gaya masa.Bily ta mike tana cewa,bari naje naga sahibata,na tsaya ina biye ma shirmenku.Safina tace,ba shirme bane anty,kema in kin gansa sai kin soshi,Bily tace Allah ya tsare ni.Fauziyya tace,kila kuma ita bazata soshi ba,tunda itama tana da kyau.Sumayya tace,mai kyaune kuma da mai kyau,anty Bily kuna kama da yaya Modibbo.Bily ta fita tana dariyan shirmensu.Ya sake kallon agogo,karfe takwas,yasan yanzu a Nigeria zai zama biyun dare kenan,tunda awa shidda ne tsakaninsu da Malesia.Bari dai ya bari sai yamma sannan,nan su rana tayi,wata zuciyar tace masa kafin yamma haka zakayi ta zama?Ka tuna fa yanda yarinyar nan taci maka mutunci,me zai hana kasan wanda take ikrarin ya tsaya mata din?Tuna hakan daya yi ya sakasa daukar waya ba shiri ya soma neman layin Magaji zuciyarsa tana kara tuno masa maganganu na batancin da yarinyar ta masa wanda yayi sanadin tsayawar al鈥榓muransa ciki harda karatunsa tare da holewarsa da mata ababen sonsa,bai taba zato akwai wata damuwa da zata shigar masa cikin huldarsa da mata tayi dumu-dumu ba hatta Chelen duk yanda taso taja shi bata iyawa saboda bacin rai.

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 30馃彽


Wayar ta katse ba鈥榓 dauka ba yaja tsaki sannan ya sake neman layin,ringing na uku Magaji ya daga wayar.Yarima yace,haba Magaji adinga rage bacci ana nafila mana,wannan bacci kamar ka mutu?Magaji yace,gara ma ni bacci nake,shima ibada ne wani ma ba鈥榓san ko shi da mata nawa yake ba,Yarima yace,na gode.Yanzu dai duk ba wannan ba,me kasani game da wannan yarinyar?Magaji yace,wacce kenan?Yarima yace,yarinyar da muka hadu gidansu Modibbo kawar matar Faruk din Umman Gombe?Magaji yayi 鈥榶ar dariya tare da cewa,nasan dama wata rana sai ka min zancan yarinyar,domin irin taku ce.Ya dan saurara kafin ya cigaba,gaskiya bansan komai kanta ba,ni da farko ma na zata kun hada iri can cikin dangi.Tsaki Yarima yaja,sannan yace kada ka bani haushi fa Magaji?Tunda kace baka san komai kanta ba,na baka awa sittin da shida daga yanzun,ina son sanin who is she?Ya kashe wayar ba tare da ya jira jin me Magaji zai ce masa ba.Tun misalin goma na safe Magaji ya soma neman sanin Bily,da farko gidan Modibbo ya nufa gurin Hajiya Fati don son sanin wacece Bily?Don nan ya soma ganinta gurin Modibbo ya soma shiga suka gaisa,baice ma Modibbo komai ba game da bukatar Yarima na son sanin Bilyn ba.Sun dan taba hira har ma Modibbo yake cewa,ina labarin abokinka ne?Magaji yace,yana lafiya sannan yace,bari ya shiga su gaisa da kawu.Modibbo yace,kawunku yana Yola,na aikesa sai dai mai dakin tana nan ciki,yace to bari mu gaisa dama nazo gaisheku ne.Sun gaisa da Hajiya,sannan yace dama Hajia ina so in tambayeki ne shin ko kin san Bily kawar matar Faruk din Gombe?Haj.Fati tace,ikon Allah nifa nayi mamakin ganinka da safe tunda kuka zo Yarima na nan ba wani zuwa kuke ba sai sa鈥榓.Tayi 鈥榶ar dariya sannna tace,wallahi ni ban santa ba,daga ita har matar Faruk din.Nima karo na farko kenan da fara ganinsu.Nan dai sukayi sallama ya fito,cikin mota ya soma tunanin wazai tunkara da wannan bukata?Yana ganin abinda sauki ashe duk ya wuce nan.Yayi tunanin to ko Faruk zai kira?Sai kuma yace,kai da Yarima yana son Faruk ya sani da shine mutum na farko da zai fara nema.

Nan Sumayya ta fado masa yarinyar da yake mutuwar so,yace bari ya kirata yau dai yaji muryarta tunda ya shiga ya fita da kyar ya samu number din ta gurin yaya Salma ya kasa kiranta,amma yanzu zai kira kila ma ya samu labarin daya fito nema.Dafda zata yanke Sumayya ta daga wayar duk da cewa wayar tana hannunta,haka nan bata gane ko number din wanene ba.Cike da yanga tace,hello! Ya lumshe ido don jin muryar da yake matukar so,sannan yace,Assalamu alaikum,Sumayya tace ,Wa鈥榓laikassalam,wanene please?Yace au baki gane ni ba?Tace,a鈥榓.Yace,to Magaji ne daga Bauchi,tayi 鈥榶ar dariya.Oh,Magaji ban gane kaba,koda yake bamu taba waya ba,yaya Bauchi? Yace,Bauchi lafiya duk suna gaisheki tace,ina amsawa,yaya Yaya Modibbo?Yace lafiya,dama wani taimako nake so ko zan samu?Tace in baifi karfi na ba,ai bazai gagara ba,yace kin san kawar matar Faruk dinku?Tace anty Bily kenan,nasanta jiyannan muka dawo daga gurinsu.Yace,yauwa don Allah menene labarinta?Kamar ya?Ta bukata,yace,ina nufin kinsan tarihinta?Ta girgiza kai tamkar tana gabansa bansan komai kanta ba,face nasan ita 鈥榶ar Zaria ce kuma ta gama karatu bansan me ta karanta ba,amma yanzu tana bautar kasa ne,yace to na gode,kina da number dinta ne?Tace,eh,amma sabuwar number dinta ne nace ta bani don ina sonta,kai ne zaka shiga?Yace ni wane ni,wani abokina ne.Da sauri tace,Yarima?Yace,a鈥榓.Tayi ajiyar zuciya har abin ya bashi mamaki,yace shikenan kiyi min text din number dinta,tace to.Da taso ta rokesa ya shigar da ita gurin Yarima,sai dai ta fasa,shiko zuciyarsa ta shiga rudu,kada dai Sumayya tana son yarima ne. Zuwa washegari,Magaji duk ya gama bige-bigensa shi dai bai gano komai ba game da Bilkisu,dole sai ya hada da zuwa Zariya.


Kwance agaban gidansa,cikin wani dan gado Yarima ne,daga gefensa Chelen ce tana sanye da Bra da pant,wasa takeyi da gashin kirjnshi,idanunsa lumshe zuciyarsa tana masa nacin me yasa yaba Magaji kwana uku?Ya matsu yasan ita wannan yarinyar 鈥榶ar uban wanene Ita ko Bily daidai wannan lokacin hankalinta kwance,tunda ta cire(mtn)ta saka(zain)sai dai bata yarda ba kamar yanda tasoyi da,saboda numbers din dake kan(sim)din,tana son ta ba Mansu labari sai sun zauna tukunna.Magaji ya shigo Zaria kai tsaye unguwar T/wada ya nufa gurin wani abokinsa da sukayi karatu a (University)nan Bauchi.Ibrahim dan Zaria ne,a unguwar T/wada.Da kwatance ya iso T/ wadan,nan kuma ya shiga kiran number din Ibrahim amma is switch off.Tun safe yake neman wayar taki shiga,nan ya shiga nemansa ta hanyar tambaya duk ba sa鈥榓,yayi parking nan kusa da wani Masallaci da nufin yayi magriba,zaije ya nemi masauki.Amma cikin yardar Allah yana sahun gaba sai kawai yaga Ibrahim a sahun gabansa.Don haka suna idar da sallah sai yasa hannu ya dafa shi,nan suka fita wajen Masallacin,Ibrahim yana ta mamaki.A dakin matar Ibrahim suna cin abinci,Magaji yana fada masa dalilin zuwansa Zaria,yace na shigo garinku ne don neman labarin wata yarinya Bilkisu.Ibrahim yace,ikon Allah!鈥榶ar wace unguwa ce?Magaji ya kafa kofin ruwa yana sha,sai daya gama sannan yace,nan fa daya,wallahi bansan komai kan yarinyar ba,hasalima sau daya na taba ganinta.Ibrahim yace,to kai batayi maka kwatance bane?Magaji yace,nifa Bauchi muka ganta.Yarima ne ke sonta shine duk ya daga min hankali,yanzu haka gobe yake son jin ko ita wacece.Ibrahim yace,gaskiya ya baka aiki,Zaria tana da yawa,ta ina zaka soma nemanta?Magaji yace,shi yasa na biyo ta kanka tunda kaine dan gari.Babban misalin dazan iya badawa na yarinyar kawai shine,kyawunta nasan saboda tsabar kyanta bazata bata a unguwar da take ba.Ibrahim yace,to kafin a gano unguwar da take fa?Magaji yace to bari dai in mukayi Isha鈥榠 sai mu soma tun yau.Haka kuwa,suna idar da salla suka shiga gari.Da G.R.A suka soma don zaton Magaji na ko 鈥榶ar wani mai halince,gida-gida suka dinga bi cikin G.R.A sune har sha daya da rabi.Washegari ko suka soma da T/Wada,S/ Gari,haka sukayi ta yawon neman inda zasuji labarin Bily,amma shiru.Bayan sunyi sallar La鈥榓sar,suka shiga Ojo da har zasu wuce amma MGJ yace su shiga.

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 31馃彽


La'asar, suka shiga ojo da har za su wuce amma magajin yace su shiga anguwar.

Kai tsaye kusa da wasu samari suka yi dayan ko sai rantsuwa yake yi. Ibrahim yayi musu sallama suka amsa. In ban da dayan da yake ta zuba bai ma san ana sallama ba. Ibrahim yace, bayin Allah muna tambaya ne ko Allah yasa kun sani? Biyu suka hada baki gurin cewa,to magaji ya matso don Allah cikin ku ko akwai Wanda yasan wata Bilkisu? Yaci gaba. Yarinyar tana da kyau na ban mamaki. Samarin suka ringa kallon magaji kamar sunga wani sauna. Dariya ma ya basu, inda dayan yace Malam, Bilkisu suna da yawa a unguwar nan, kuma akasarin su kyawawa ne.Magaji ya yi shiru, can yace ita fa kyanta dabanne, kuma ta gama makaranta. Gaba dayan su suka sa mishi dariya har ma ya ji haushi zai tafi, sai daya daga cikin masu musun kwallon nan mai surutun tsiyan yace, Aa ko dai yana nufin Bilkisun gidan marina? Nan take samarin suka ce ita ce ma, don duk unguwar nan ita ce best a kyau. Magajin Malam da jin haka sai ya dawo yana cewa, don Allah yaro zo mu muje ka gwada min gidansu.Yace,to Magaji ya saka hannu cikin aljihu ya debo kudi 鈥榶an naira ishirin ya mika musu ba tare da ya kirga ba,yace na gode fa,suma suna ta godiya.Ibrahim yace,bari na zauna baya shi ya shiga gaba saboda zai dinga yi maka kwatancen inda zaka bi.Magaji yaji dadin haka,don yana son ya yiwa yaron tambayoyi musamman ma da yaga yaron zaiyi surutu.Ya dubi yaron,sannan yaci gaba da tuki,yace abokina kusa kuke dasu kenan? Yaron yace,E,gida biyu ne tsakaninmu dasu.Amma gurinta zaka?Magaji yace,eh,yaron mai suna Sule,yace ai ina ganin fa bata nan tana Kaduna,aikin gidan TV takeyi,ko bauta ma kasa naji 鈥榶an gidanmu suna cewa, suna zuwa yace da Sule ya shiga ya tambaya ko tana nan.Bayan fitar yaron ne Ibrahim yace da Magaji abokina zaka iya samun labarinta gurin yaron nan,don naga yana da surutu.Magaji yace nima na lura.Sule ya dawo da sakon cewa tana KD.Magaji yace,amma ka tabbata nan ne gidansu?Sule yace,nan ne,ko ba wata doguwa ba?Fara mai kyau?Magaji yace,itace,nan ne gidansu nan yaro ya labarta ma magaji labarin bilkisu

Bayan sun gama magaji ya kawo kudi ya bashi suka maida shi inda suka dauko shi suka tafi yana mamakin inda take zaune dan shi in ta tashi ne diyar wani hamshaki ce dan shi a zaton sa in ba'a samu gidan su a GRA ba toh cikin dai shahararrun unguwannin masu kudi take

Magajin Malam da ya gama ba Yarima labarin Bilkisu kamar yadda yaji sai Yarima yace,ka bincika sosai ko?Magaji yace duk wanda ka saka ba zai zo maka da sama da wannan labarin ba,sannan ga number dinta nan zan turo maka,wane saurayi ke nemanta?Bata dashi.Yarima yayi wani murmushi aransa kuma fadi yake,yarinyar nan ta cuce sa data ce ta sansa har kuma ta mammaida masa da maganganu.Layinta ya soma kira,amma sai aka ce ba zai je ba,nan take ya soma kiran sabon layin da Magaji ya tura masa,wayar ta soma ringing lokacin Bily tana tsaka da yin nafila,bata kalli wayar ba sai data idar ta sallame sannan ta dauko wayar cike da mamaki tace,to wanene wannan?Domin tasan ba kowa bane yasan layin,kuma wane mahaukaci ne da kiranta cikin dare haka?Tana dauko wayar ana sake kira,bata gane number din ba don shima bada wancan layin ya kira ta ba,sannan duk da(+)din data gani batayi tunanin cewa Yarima bane,duk da tasan cewa bata da wanda zai kirata daga wata kasa.Cikin mamaki ta saka wayar akunnenta,kafin tayi magana ya soma cewa,ke!鈥榶ar gidan masu rinin tsumma,鈥榶ar kauyen kayau,鈥榶ar talakawa tilis,鈥榶ar gidan ginin kasa.Kin cuceni da kika ce kin sanni,sai na saka brush na wanke bakina sosai saboda furtawa da nayi na cewa zan aureki.Wanene kike ikrarin kina dashi wadda mahaifinki Malam Mamman ke rini,uwarki ke aikatau?.....kai jahili! Ta katsesa da zafin rai,tana huci tace,kai jakin ina ne?Da baka san talaka da mai kudi da mai sarauta duk Allah ne ya halicce su ba?Kuma babu wanda Allah yafi so face wanda yafi bauta masa,kana zaton wayonka ne yasa Allah ya sakoka cikin gidan sarauta?Je ka shiga Islamiya,kana da bukatar sanin ilmin Tauhidi.Na biyu kuma duk da talaucinmu ba muzo roko gidanku ba,sannan Ubangijina shine wanda ya tsaya min,dashi nake takama,sannan baka san hakkin dan Adam ba da zaka min waya cikin dare.....ya katseta ni kika kira jahili?Tace ,eh.Zaki ga aikin jahilci,zan baki mamaki donni na wuce da tunaninki 鈥榶ar matsiyata kawai.Ya kashe wayarsa duk su biyun sun batawa juna rai,sun gaya ma juna maganganu masu zafi. 


Yarima saboda shi namiji ne zufa ya shiga yi tare da yin jifa da wayarsa,yayinda ita kuma ta hau kan gado ta dora hannu akai ta saki kukan bakin ciki,bata iya fada ba,bata taba fada ba,don haka sai abin duk ya zamar mata sabo,don haka kwana tayi tana kuka,kafin gari ya waye fuskarta ta kumbura suntum,haka nan da ciwon kai ta farka,da kyar tayi sallah.Shirun da Mansu taji shiyasa ta fitowa,tasan babu lafiya don tasan Bily da yanzun tana kitchen.Ganinta cikin bargo yasa ta karasawa gaban gadon da sauri taga yanayin da bilyn take ciki hankali tashe tace Billy baki lfy ne ta daga kai kawai ta kamata zuwa jikinta tana mata sannu tace bari toh na kawo maki wani abu ki taba sai muje ko asibiti tace sam ita ba zata ci komai ba mansu Tai banza da ita ta tafi ta hado mata abincin amma sam billy sam taki ci sai kuka take tayi lallashin har ta rasa ya zata yi mata


Mansu ta kalli Faruk tace,baban dady na rasa yanda zanyi da Bily,dama so nake ka gama cin abinci in shaida maka yau ko fita batayi ba,bata ci komai ba sai kuka nayi tambayar duniyar nan taki ta gaya min damuwarta.Ya mike da sauri zo muje,tana zaune ta hada tagumi suka sameta,sannan duk da zafin da akeyi tasha rigar sanyi.Faruk ya jawo kujerar gaban madubi ya zauna agabanta,Mansu kuma ta zauna kusa da ita,ta dafa ta tare da cewa,Bily tunda ni kinki sanar dani damuwarki,ga yayanki nan sai ki gaya masa domin tun kafin in haihu nasan kina da matsala,boye min kawai kikeyi.Kada ki manta fa ni dake ko 鈥榶an biyun da suka fito ciki daya alokaci daya basu kaimu shakuwa ba,ga zatonki bansan kina da damuwa ba?Bily ta kalleta da idanunta da sukayi jajir suka kumbura,sannan ta kalli Faruk tayi wani dan guntun murmushi wanda yayi sanadiyar zubowar hawayen da take kokarin makalewa.Muryarta tana rawa tace kada ku damu,ba wani dogon abu bane ya faru.Ta saka hannu ta kama hancinta ta dan ja iska,sannan taci gaba kun san wani lokaci abu kalilan ne yake bata ma mutum rai,domin zagin da Yarima yayi min wallahi anyi min gomansa amma ban damu ba,sai nasa.Faruk suka kalli juna shida Mansu,sai suka ji zancan wani banbarakwai,Faruk ne ya soma magana,wane Yarima?Ta nuna sa Yarima naka,taci gaba saboda Yarima na canza layi,amma bansan inda ya kuma samun layina ba ya kirani jiya yayi min tatas,harda gorin talauci.Babu abinda yayi min ciwo irin yanda ya zagi uwata.Faruk har suna hada baki da Mansu gurin cewa zagi?Tace zagi dai,Faruk yace tun dama menene ya hada ku?Bata boye ba,nan ta warware masa komai game da mafarkinta da Yarima zuwa ganin data masa,ta masa magana har zuwa sa-in-sar da sukayi dare jiya.Abin yayi matukar bata ran Mansu,Faruk ko cewa yayi sai ya kirasa yaci masa mutunci,nan Bily ta jajirce kan cewa kada ya kirasa,ya kyalesa in halinsa ne zai hadu da daidai shi.Mansu ko kallon Faruk tayi sannan tace,wai shin shi Yarima wanene shi?.

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 32馃彽


YARIMA MODIBBO cikakken sunansa shine Al鈥榓min Isma鈥榠l Abdullah,shine da daya tilo namiji da iyayensa suka mallaka bayan sun haifi 鈥榶aya mata ishirin da biyu.Sarki Isma鈥榠l ya gaji sarauta ne gurin Babansa Abdullah tun yana da rai ya sauka yaba dan nasa Isma鈥榠l mulki.Modibbo shahararren Malami ne mai tarin ilmi,su aminan junane shida mai martaba sarki Abdullah,tare suka taso wannan dalili ne yasa daya baya aiwatar da komai sai da shawarar daya,don haka lokacin daya kawo masa shawarar sauka daga kan mulki,Modibbo ya amince tare kuma da bashi shawarar yayi wa dannasa aure hadi da nadin sarauta.Sarki Abdullah yace shima nufinsa kenan,kuma yana so ne ya hadasa da 鈥榶ar wajenka Sa鈥榓.Modibbo yace,wannan dama tasa donna gani cikin lamarin aurensa danayi istihara.Shekara daya jal da auren hadi da nadin sarautar ta sintilo 鈥榶arta mai kyau inda taci sunan matar Modibbo mahaifiyarsu Sa鈥榓,wato Salma.A takaice sai datayi mata shida sannan ya auri 鈥榶ar sarkin yankin Katsina,itama 鈥榶aya hudu duk mata.Lokacinne sarki Abdullah,Allah yayi masa rasuwa,Wazirinsa shima tsakaninsu sati daya,sai dan Wazirin mai suna Hafiz shima ya gaji mahaifinsa bayannan ya kara mata biyu jere banda sadaka ga kuma kwarkwarori bakin abinda Allah ya halatta masa,duk babu wadda tayi koda barin namiji.Al鈥榓marin daya daga masa hankali kenan,saboda yasan mace ba zatayi mulki ba yana son magaji,haka yake kullum cikin damuwa har girma ya fara shiga,domin da yawa 鈥榶ayan nasa ya aurar dasu.Umma mai babban daki haka suke kiran Haj.Sa鈥榓,tana tausayawa mijinta kullum tana addu鈥榓r Allah yabawa mijinta da namiji koda ba agurinta ba,ko gurin sauran kishiyoyinta ne.Lokaci yayi nisa,haihuwa ma harta tsaitsaya musu,ba wai sun tsufa bane,Allah ne kurum ya tsaida musu ita.Kwatsam!Sai ga ciki jikin Umma mai babban daki,batayi saurin sanarda mai martaba ba saboda tasan tana sanar dashi yanzun nan zai daga hankalisa,sannan ya hana idanunsa bacci yana rokon Allah yasa da namiji ne.Cikin hakane wani dare takai ziyara gurin mahaifinta Modibbo take sanar masa cikin dake gareta.Modibbo yace,na ganki cikin mafarki kina shayarda wani yaro namiji,sai dai ba yana nufin lallai namiji zaki haifa ba,domin mafarkin Annabawane kurum yake zama gaskiya.Murna ta cika ta tace,a taya mu da addu鈥榓,sannan bana son mai martaba yasan da cikin nan.Modibbo ya dubeta yace,saboda me?Tace zaya damu ne,yace wannan ba dalili bane,ki sanar dashi.Sai dai kada ki sanar dashi game da mafarkina,domin karya saka rai.Umma tace,to Modibbo na gode,Allah ya kara lafiya da nisan kwana,sukayi sallama ta dawo gida.Cikin satinne matar waziri Hafiz ta haifi danta namiji,mai martaba yayi murna tamkar shine aka haifamawa.Inda waziri yayi kara yasa ma yaro sunan mahaifin mai martaba,wato Abdullah.Da yake anfi kiran mai martaba Abdullah da Malam,saboda yana da ilmi na addini,don haka sai ake kiransa Magajin Malam,wato jaririn da aka haifa.Wannan yasa mai martaba kara son yaron,Umma mai babban daki ta sanar da mai martaba cewa tana da ciki,murna sosai ya shiga yi tare kuma da rokon Allah.Gefe daya kuma zuciyarsa tana cikin damuwa inya tuna shi bashi da kwan da zai samar da namiji kamar yanda wasu Likitocin suka shaida masa lokacin daya  shiga neman taimakonsu.Amma ya dai mikama Allah lamuransa,ya kan tuna kalaman Modibbo da yake cewa,lallai kada ya zama daga cikin bayi masu cire rai daga rahamar Ubangiji.Haka dai ciki yayi ta girma har zuwa lokacin da aka haife sa.Ranar wata Juma鈥榓 an tafi masallaci,an haifesa ne awani asibitin kudi dake nan cikin garin Bauchi bayan Umma tasha wahala.Mai martaba yana Fada Jakadiya ta iso masa da albishir,zancen daya saka mai martaba farin cikin da Fadawa suka jima basu gani ba,nan take yace da Jakadiya ya bata kujerar Makka.Kafin mai jego ta dawo gida labari ya karade garin Bauchi da kewaye.Yanda asibitin ya cika shine dalilin sallamarsu zuwa gida.Tun ranar ake shagalin yanke-yanke har zuwa ranar suna,inda mai martaba ya saka sunan Modibbo yace tunda waziri yayi masa kara ya saka Magajin Malam Sai dai yana fatan inya sake samun wani namijin ya saka masa Abdullah,ko kuma in Modibbo ya girma yayi aure to yana fatan Allah ya barsa da rai yaga ya saka masa sunan Abdullah.Faruk ya dubi su Mansu yace,bazan iya sanar daku gatan da Yarima ya samu ba,duk abinda yakeso shi zaiyi shi zai ci,haka nan shi zai sa,banda yayi sa鈥榓r iyaye masu tarbiya da ilmi hadi da sanin yakamata,to ko daba karamar shagwaba zaiyi ba,ko ince daya lalace,tun yana karami yake zuwa Fada,mai martaba yasa ake kawosa.Wannan abin yasasa girman kai ganin yanda ake zubewa gabansu.Yarima wani yaro ne dan kwalisa mai tsananin tsafta tun yana karaminsa,ga manyance tare da son girma,yana da matukar wahala kaga y shiga harkar wani,haka nan baya son ashiga tasa,halayensa rabi na Turawa ne,ko ince na tsarin Musulunci ne,misali;yana da cika alkawari,in har yayi maka alkawarin abu tabbas ne babu go nd come,sannan ko kai waye karya ne ya zageka abayan idanunka shi dan karara ne ko kaji dadi ko kada kaji bashi da yawan hayaniya,shiyasa nayi mamakin sa- insarku.Ya dan dakata kafin yaci gaba,ya taso shi wani tauraro ne cikin kafatanin 鈥榶an gidansu,haka nan gurin Kakanmu Modibbo bai hadasa da kowa ba,to haka yake cikin dangi kowa yana sonsa.Yayi karatun Nursery da Primary a (C.N.I)wata makaranta ce mafi tsada a Bauchi.Secondary yayi tane akasar Spain,yanzu kuma yana Malesia yana karatun Likita ne fannin mata.Bansan yanda zan gaya muku halin Yarima ba,shi dai dabanne komai nasa dabanne,bansan yanda zanyi muku bayaninsa ba,yana da tsattsauran ra鈥榓yi,haka nan baya son duk wani abu da zaya zubarda mutuncin gidansu,yana da alheri.Kada kuce ina yabonsa hakane halinsa.Bily tace,niko baban dady banga haka ba,Faruk yace ni kaina nasha mamakin lamarinku,shi ba mai shiga cikin lamarin wani bane,baisan fa bacin rai ba.Bily tace,shidai ya sani.Mansu tace,kadai gaya masa ya kiyayeta,ai talaucin ba bawa yake dorama kansa ba,haka nan don kana da kudi ba yana nufin Allah yafi sonka bane ya baka,wani kudinma in mai su baiyi hankali ba sai su kaisa wuta.Yace zan kirasa.

[8:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 33馃彽


Bily tace,a鈥榓 don son Manzon Allah(S.A.W)kada ka masa magana,bana son kace masa kala!Nifa ya wuce agurina,kada ma yaga kamar ma na damu dashi ne koda abinda ya faru,please forget about him,na bar maganar.Faruk yace shikenan. 


Mai martaba ya kalli Umma mai babban daki,sannan yace,Sa鈥榓datu menene na damun kanki don kawai nace mun yanke shawara za鈥榓 nemawa Yarima aure?Ranka ya dade,bawai na damu bane,ina duba karatunsa ne,sannan shekaru ashirin da hudu duka nawa yaron yake?Yayi dan murmushi.To ni banda Modibbo ya tsaidani da tuni ma anyi auren.Amma yanzun ma bazai dauki lokaci ba,Yarima yana bukatar aure.Shiru tayi domin tasan maigidan nata baya zartar da wani al鈥榓mari sai da shawarar mahaifinta masani mai tarin ilimi,haka nan tasan suna da dalilinsu.Ta dubesa sannan tace,ina fata Yarima bawani shirmen yakama ba?Mai martaba yace,a鈥榓 yana da kyau dai muga 鈥榶ayansa in Allah ya nufa zamu ga hakan,tace hakane,a ina ya samu matar?Mai martaba yace,wannan yana ga Modibbo,yace shine zai zabawa takwaran nasa mata.Umma tace,to Allah yasa mu dace,mai martaba yace amin. Duk da takaicin da Yarima yakeji na yarinyar,amma yana jin gara ya yarda kwallon mangwaron ya huta da kuda,don ba zai iya auren yarinyar ba,taje taci sa鈥榓 domin yaso ne ya aureta ya wahalsheta.Yanzu kuma baya jin auren nasu zai yiwu,tunda yaji ita wacece.Sannan ya jinjina ma karfin halinta kasancewarta mace kuma 鈥榶ar talakawa har kuma ta iya ja dashi,tunda ya gano cewa ita din abin tausayi ce to ya barta.Haka Yarima yaci gaba da harkokinsa,ahankali har ya warware ya ma manta da batun wata Bily.


Ga Bily itama tuni ta saka damuwarsa gefe ta shiga harkokinta.Takaicinta daya shine yanda har yau ta kasa yakar mafarkinta,don har yau tana mafarkin Yarima.Kara zage damtse tayi gurin addu鈥榓,Allah ya rabata da mafarkin Yarima,ta tattara komai nata ta barma Allah,ta kuma sha alwashin tabar kara zuwa gurin Modibbo tunda suna da alaka da Yarima,duk da yanda zuciyarta ke son tsohon

Kai ko Faruk sai taji tana jin haushinsa domin tasan dole ne yafi son Yarima da ita,tunda Mamansa da Maman Yarima uwa daya uba daya,wata kusan kuwa ai tafi wata.Wani sashe na zuciyarta ma har yana zargin koma shine ya gaya ma Yarima wacece ita?Amma ta kasa yarda don tasan Faruk bazai mata haka ba. Kawu yayi sallama ya shiga wurin Modibbo,cikin girmamawa ya zauna gaban mahaifin nasa,sannan ya sunkuyar da kai yace,ina yini Modibbo?Lafiya lau,ka dawo lafiya?Yaya kasuwa?Kawu ya amsa da Alhamdulillah.Modibbo yace,to madalla.Ka shiga ciki inka gama harkokinka sai ka fito zan aike ka gidan mai martaba kayo min iso,gobe in muna cikin masu rai zanzo gurinsa.Kawu yace,yanzu bana komai bari naje inna dawo sai na shiga gidan gaba daya.Modibbo yace,to shikenan,in baka gajiba.Amma da kadan huta,kawu yace,ban gaji ba,bari in tafi kawai.Ana shirin tashi daga Fada,kawu ya isa.Ya nemi iso aka shigar dashi Fada.Nan ya isar da sakon Modibbo ya dawo.Mai martaba sam baya son Modibbo yana zuwa da kansa,yafi son ya aiko masa cewa yana nemansa,shiya dauki Modibbo mahaifi ba suruki ba,don haka misalin karfe tara ya fice ta kofar baya inda Magaji ke jiransa cikin mota.Duk gidan babu wanda yasan ya fita,sai ko Magaji da suka fita tare,shima bai san inda zasu je ba,ya dai kirasa awaya yace masa ya amshi mota ya jirasa bakin kofar baya.Sun hau titi sosai,sannan yace Babana gidan Modibbo zamuje,Magaji yana mamakin mai martaba sosai,sam shi bashi da girman kai,sannan duk inda zaije aboye shiya zaba don ya rakashi.Magaji ne ya shiga yayo iso,babu kowa sai Modibbo yana ta jan carbi.Mai martaba ya zauna daura dashi,Modibbo ya mika masa hannu da suyi musabaha kamar koyaushe,mai martaba ya noke hannunsa suka gaisa.Modibbo yace,kai da nace zanzo?Mai martaba yace,Allah gafarta nine yakamata nazo donni danka ne.Modibbo yace,to amma kuma ai kai shugaba ne.Mai martaba yayi murmushi yace,amma Allah gafarta Malam,maganarmu bata shafi mulki ba,don haka in an bar batun mulki an dawo gida ni da ne,kuma duk da nagari dole ne yabi iyayensa Murmushi Modibbo yayi,yasan gaskiya ce mai martaba ya fada.Don haka kai tsaye yaje da fadin dalilin son haduwar tasu game da zancen takwarana ne yace Malam Shehu yazo min da sakamakon binciken dana sa shi.Yaci gaba,Malam Shehu Almajirina ne tunda dadewa,shi dan Zaria ne musamman nasa aka kira minshi awaya na sakasa yayo min bincike menene asalin Bilkisu?Kuma naji komai game da duk wani abu da shari鈥榓 ta nema asali ga mace,sai dai yarinyar ba masu hali bane yace sai muce Alhamdulillah ,don haka sai atashi 鈥榶an neman aure su tafi.Mai martaba yace,to Alhamdulillah, talauci kam sam ba abu bane da zai hana aure ina son zan tura Fadawa zuwa ga mai martaba sarkin Zaria,daga nan sai su nemi dagacin ko hakimin unguwarsu sannan kuma shi sai ya nemi mahaifinta.Modibbo yace,to,Allah ya shige mana gaba,zamu taya ku da addu鈥榓.Kwana uku da wannan magana,mai martaba ya tashi Fadawa da sako zuwa Zaria.Sun samu tarba ta karamci irin na Zage-zagin asali.Sannan suka sanar da sakon mai martaba nan mai martaba yaji dadin wannan batu,sannan yasa aka nemo masa dagacin yankin,ya umarcesa daya nemi mai unguwar Ojo suzo fada gobe.Washegari suka amsa kiran sarki,nan yayi musu bayani,sannan akace su nemo Malam Mamman mai rini,suna dawowa mai unguwa yasa akira masa Malam Mamman.Sakon ya samesa lokacin yana zugama Mamanmu rashin mutuncin nasa,yana cewa karuwancin ya isheshi haka,dole yana son Bily ta dawo gida ya gaji,kilama shi yana tafiya mutane suna nunasa bai sani ba.Shiru ta masa yayinda su Kariman da suka zugosa,suka hada dan dandali suna shewar dariya.Cikin haka ne aka kwada sallama,baiji ba yana sababi sai da aka sake sannan ya shuri takalminsa ya nufi hanyar waje,yana cewa ai wannan yarinyar da haihuwarta gara barinta.Yarinya ta balaga ta balage min agida ta zamar min kaya?Daidai nan ya isa kofar gida,ya mika ma dan sakon me unguwa hannu suka gaisa,dan sakon ya shaida masa cewa mai unguwa yana nemansa.Malam Mamman yace,lafiya dai ko?Lafiya lau,yace dai muzo tare.Suka rankaya gidan mai unguwa.Gefen tabarma suka zauna yayi gaisuwa,mai unguwa yace,Malam Mamman ka samu sakona ko? Mamman yace,kwarai,shine ma dalilin zuwana

[8:48AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 34馃彽


20-Mai unguwa yace,to nima hakimi ne yayo min aike naje,shine yace lallai muzo tare da kai.Idanun Malam Mamman ya shiga zarewa tare da cewa mai girma hakimi kuma ranka ya dade?Mai unguwa yace ,shi don haka yanzu sai kaje ka shirya mu tafi.Jikin Malam Mamman yayi sanyi,yace cikin in-ina,badai wani abu nayi ba ko?Ranka ya dade nifa ko hakimi ma ban sansa ba.Mai unguwa yace,to ina zaton dai kan 鈥榶ar wajenka ce ko Bilkisu ne sunanta?Sai dai munje kaji saboda shima hakimi ina zaton sakon daga samane,can gurin mai martaba sarki,don haka kaje ka canza tufafi.Jiki yana rawa ya nufo gida,yana tafe yana surutai ni wannan yarinya ta zame min bala鈥榠,ni in za鈥榓 kasheni banace ga kamannin dagaci ba,amma yau sanadin wannan 鈥榶ar iskar yarinyar gani wai har gaban sarki zanje,ko wane bala鈥榠n ta jono min?Oho!,yanzu haka labarin karuwancin nata ne yaje kunnansu.Daidai nan ya shiga gida yana tsaki,matan suna gindin murhu suka dubesa har suna hada baki,lafiya malam?Yace ina fa lafiya,waccan 鈥榶ar iskar taja min wai yanzun gidan sarki ake nemana.Suka ce,wace?Yace,Bilkisu mana.Mamanmu dake daki ta jiyo,don haka da sauri tayo waje don jin me Bily taja masa?Ta fito daidai sanda yake cewa kurum zataja min fitina,yanzu haka ma sunji labarin gantalin da takeyi ne shine aka kirani ahukunta ni.Ladiyo tace,a鈥榓 karka yarda malam,ai ba kaine ke karuwancin ba itace ko kaje karka yarda acutar dakai.Salame tace,ko ko sunji har yau ba a mata aure ba ba.Karima ko cewa tayi,nidai da zakaji tawa,da ka ki zuwa saboda ina tsoron kadasu daure ka ba da hakkinka ba,in haka ta faru mu aka cuta masu kananan yara.Ladiyo tace hakane,ya shiga dakin Salame yanasa kaya,yana cewa, wa zaiki zuwa kiran sarakai?Ai sai azo da dogarawa akamaka.Daya fito ya kalli gurin da Mamanmu take,ki shirya kayanki,domin inna dawo da wani cin zarafin kema zaki samu naki rabon.Ya fita nan Salame ta yafa mayafi ta shiga sashen Gwoggo tana hawayen gulma,wai anzo daga gidan sarki an tafi da malam saboda Bily,yawon banzan da take yi yaje kunnansu.Budar bakin Gwaggo sai tace,babu kaico,na mayi murna ga bokon nan,ni nasan dama haka za鈥榓yi.Ta soma masifa da cewa,ni dai abar min dana suzo su kama uwarta don itace ta tsaya mata.Kafin kice haka,labari duk ya kaima sauran sassan,nan da nan gidan ya cika,sassansu Mamanmu suka dungumo inda take zaune bakin gado cikin daki,ta hada kai da gwiwa.Hankalinta atashe,tasan wani sabon sharrinne za鈥榓 kagawa Bily.Masifar Gwaggo ce ta sakata kuka,tana dai ciki bata fito ba,kowa yana ta fadin albarkacin bakinsa,sai tsinuwa tareda zagi suke yiwa Bily wadda bata san hawa ba bata kuma san sauka ba.Suna isa gidan hakimi,babu bata lokaci suka tafi gidan sarki cikin motar hakimin,anyi musu iso suka shiga duk jikin Mamman yayi sanyi,yana dai binsu ne.A zuciyarsa yana Allah ya isa tsakaninsa da Bily.Suka zube sukayi gaisuwa cikin magana irinta manya sarki ya soma bayani,da farko yace ina mahaifin yarinyar?Hakimi ya nuna shi tare da cewa,gashi nan ranka ya dade.Mamman kamar yace bashi bane,sai dai yasan ba鈥榓 katsalandan afada,don haka yayi shiru,sarki ya gabatar da maneman auren Bily,daga masarautar Bauchi.Idanu ya zaro yana kallonsu,nan suka gabatarda bukatarsu,jiki yana rawa Mamman yace,a-an baku.To hakane ai ba komai,hakimi yace,ka nutsu Mamman.Suka bukaci afadi sadaki,Mamman yace,ni dai na bar komai gurinka hakimi,duk yanda kukayi ni me biyayyane,ko sadaka ne ai zan bada ita kunfi karfin wannan ranka shi dade.Nan dai hakimi yace su bada dubu dari,Allah ya sakama abin albarka.Sarki ne ya bada sadakin,yace tasa gudunmuwar.Sun gabatarda kayan na gani ina so,akwati biyar,ga na uwa dana uba,uku-uku ga kuma wani seti can guda hudu,suka soma bayani kansu,wannan sune kayan da zata koma sawa yayin tsareta ga al鈥榓dar gidan sarauta in dan sarki zai auri yarda bata shafi sarauta ba.Ana boye ta na tsawon wata biyu,babu wanda zai ganta sai Yarima,sai ko shakikanta.Sannan zata daina amfani da duk kayanta sai wannan,wayar hannunta za鈥榓 karba abata wannan Yarima ne kawai zai dinga kiranta,sannan tunda an bada sadakinta,ynzu mune ci da shanta.

 yanzun mune ci da shanta har ayi auren. Don haka a kiyaye, kuna da gurin boyeta ne ko mu bada gida! Mai martba yace, ni zan bada guri tare da masu mata hidima har zuwa auren. Hakimi ya matso kusa da mallam mamman yace,to sai zancan tukuici, ana fa badawa. Mlm mamman yace. To.To!Ni me zan ba su? Sai dai sadakin. Hakimi yace Aa,sadaki hakkin yarinya ne.kawai sai suka ji sarkin mai adalci yana cewa a rubuta musu check na dubu dari biyu a buga sterm suje su amsa. in takaita,nan dai suka shirga kaya cike da mota sannan aka kwaso da sharadin cewa gobe za azo a tafi da Bilkisu, ko in ce anuna musu gidan Bilki. Kuji wani lamari.suna isa gidan har yanzu cike yake da yan jaje,don bayan yan sassa har makota sun shigo.

 sai dai suka ji tsayiwar motoci, sannan sai ga Dogarawa suna shiga da akwatuna, jiki yana bari yasa aka shimfida katuwar tabarma aka soma Jere kaya seti- seti, nan mutane suka shiga kallon- kallo kowa yana son jin Karin bayani. Mlm mamman babu baka sai yake yi. Ya Ciro kudi ya ba Dogarai yana godiya suka tafi suna mishi murna, lallai ya iya haihuwa, sun so suga wannan yar tashi suga ya ya take? 


Shi ko nan jama'a suka yo kanshi, uwarshi ta soma da cewa mamman me ka je yi gidan sarki, wannan kayan fa? Cike da doki yace, Goggo ai arziki ne ya kira ni. Ya shiga raba idon ina zai gano Mamanmu cikin matan dake gurin amma bai ganta ba, sai yace INA Fatima ne? Fatima ki zo ga ikon Allah. Tana tsaye daga kofar dakinta amma bata ko kalle shi ba. Ya ce Goggo daga Masarautar Bauchi ake son Bilkisu. Yasa hannu cikin aljihu,ga sadakinta dubu Dari cif haka ya dinga nuna komai yana washe baki jiki yana rawa sai kace a wasan kwaikwayo,


Makota suna ta sambarka yayinda matan gidan suka shiga zare idanu.gwaggo kuwa ko kunya, murna ta shiga yi tana cewa lallai mun haye, sai godiya. Karima tace, ka ko ji da kyau? Salame tace shi ne dai anya ma kuwa zancan nan gaskiya ne? Ladiyo kam kasa magana tayi.

[8:48AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 35馃彽


Mamanmu cewa tayi.

Mlm gaskiya ban yarda da wannan zancan ba,in dai ka saida ita ne ka sanar dani, don nasan dama neman yanda zaka rabu da ita ka ke yi, don haka ni bana neman kai da ita,haka kawai bata ga mutum ba bai ganta ba ace an biya sadakin ta naira dubu dari? To ban yarda ba ka ji na ma gaya maka tun wuri ka maida musu kudinsu.


Ya zaburo ke Fatima ahir dinki, 'yarki CE ko ko 'yata? Dama ina neman wanda zan ba na rasa sai kuma gashi an zo nema har gida? Daina wannan zance, to ni ina ruwana da wani suga juna? In anyi auren sun ga junan. Gwaggo tace, kai barta me kashin tsiya,in bata yarda ba fasawa za'ayi? Kwaso kayan ina yara kai Ku kira almajirai,. Sukai can sassan gwaggo amarya, ita kuwa gwaggon sasa cewa tayi, haba Amarya komai fa yana son bincike, Ku bari a bincika a ga wanene duniya fa ta lalace, da masifa gwaggo Amarya tace, ke rufe min baki bana son bakin ciki,  idan jikarki ce ai ba za ki ce ayi bincike ba, binciken banza? Allah ma ya hana bincike. Gwaggo sasa tace Allah sarki, ni na San in dai mutumin kirki ne ni na ma fiki murna, kema ganin kudi ne ya gama zagin yar da uwarta? Tasa kai ta fita a sasan,

 Mamanmu tace, lallai yanzu ne kasan yarka ko?Ni dai naga yanda za ayi wannan aure.Yace,Oho kya ja da sarakai,danni na riga na amshi sadaki,gara ma kiyi mata waya tazo don gobe zasu zo su tafi da ita.Salame tace,to ko dai har an daura auren ne?Ya fita yana cewa,ke kuma ina ruwanki? Sarakan bakin ciki! Salame tace,ai yau kuma mune yan bakin ciki.?Yace,eh ku ne mana.tamkar wani zautacce ya fita yana cewa,bari in kira yara su kwashe kayan sukai sasanki gwaggo,kada cikin dare a kunna musu wuta.mutane duk suka tafi suna cewa,ko dai mutumin nan ya saida yarsa ne,tunda dama ba sonta yake yi ba?Wasu kuma suna cewa,Aa gaske ne zai aurar da ita ne ga sarakuna don yaga kudi,kilan dai tsoho ne mijin su ko su gwaggo karima da salame da ladiyo dakin ladiyo suka shige suna jajanta ma juna tare da neman mafita. Ladiyo tace,ni duk ji nake yi ma duk zazzabi ya rufe ni, wato mlman nan kudinmu suka yi taci basa komai?Karima tace  A'a dan yifa aiki yayi, tunda ai babu saurayin da ke kula tan kamar yanda muka bukata Amma sai dai muce yanzu dai aikin ya baci an samu akasi,ai bamu makaraba,sai muje a wargaza al'amarin.Salame tace. To ko cikon kudin nan ne da bamu bashi ba yaki mana aikin?Nan take suka yarda cewa haka ne,kuma suka yanke shawarar cewa zasu je goben nan. Dan ma kada su fita yau nd a gane dama gashi lokaci daya mlm ya canza har dayi musu habaici.ta ajiye hijabin sannan ta koma ta zauna tunani yasha kanta.Ta rasa wa zata tunkara.Zaraf ta mike tace bari naje gidan Umman mansura. Mamanmu tayi sallama a gidan,ta shigo daidai sanda umman mansura ta ajiye hijabinta tare da amsawa.ta fito taga mamanmu,tace,Aa dama ke ce?Shigo nima yanzun nan nake cewa kwana biyu ba mu gaisa ba,da safe in zan je aiki zan biya.Mamanmu tace,uhum!Ke dai bari, nima yanzun zuwa nayi ki kira min maigado,kira min lambarta.Umman mansura tace,lafiya? Mama tace,ina fa lfy, babansu ne da rikicinshi kin dai san halinshi, wannan karon kuma dazun fa ina zaune da rana ya same ni cikin daki,wai shi ya gaji da ganin maigado tana yawon karuwanci Yarinya ta zama annoba,menene wanene?Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.Can aka yi sallama dashi yana dawowa kuma sai cewa yayi in hada kayana,gashi nan an aiko nemanshi daga gidan sarki,wai suma sun ji labarin gantalin da maigado take yi. Yana dawowa zanga cin  zarafi.to in dai takaita miki umman mansura, yana dawowa sai gashi da kaya niki-niki da kudin masu yawa wai sadakin maigado ne, akwatuna kashi-kashi, wlh ni sai ma tsoro ya kama ni,na soma tunanin ko dai ya saida ta ne tunda nasan baya kaunarta?Umman mansura tace,ikon Allah to a ina ya samo mata mijin?Mamanmu tace. Oho,ni ko sauraron shi ma ban yi ba,kila ma sun daura auren ne don naji yana cewa wai gobe zasu zo su tafi da ita. Umma tace,Ikon Allah. Ina zuwa bari in kira Abban su mansura muje mu same shi a ji kan zancen.amma ai ba akira Bilkisu yanzun ba a ruda ta,gashi kin san ta bata iya rudewa ba.yana gida ko?Mamanmu tace, yana nan kofar gida ya tara makota da yan uwansa mazan sai lbrin yake basu,sai ka ce wani zararre.. Umma tace,kije gida in anyi sallar isha'i zamu zo yanzun insha Allah. Mlm Mamman ko ana idar da sallar isha'i ya shigo dakin mamanmu tana zaune kan abin sallah,tayi tagumi ya zauna yana 'yar dariya. Abin al'ajabi wai yau malam ne yake min fara'a cikin zuciyar mama kenan take sakawa.yace fatima cire tagumi ai kin daina tagumi,ki kwantar da hankalinki muyi magana,sallamar umman mansura ne ya tsaida shi ya amsa tare da cewa,ku shigo.Tace yauwa kana ciki ba? Nima ni da maigidan ne dama gurinka muka zo, yace bismillah ku shigo, shimfida tabarma fatima. Umma tace bari in kira shi to. Sun zauna bayan gaishe-gaishe,sannan Abbansu mansura ya soma da cewa,mlm mamman,mai dakinka ce tazo mana da wani batu na game da yarinyar nan Bilkisu,shin me yake faruwa ne?Mlm mamman ya gyara zama,ya shiga rattafo musu yanda abin ya faru,daki-daki.cikin jin dadin shi gashi lbrin baya gundirar shi,hakan baya gajiya daba lbrn. Babu wanda ya katse shi sai da ya kai aya. Abban su mansura yayi gyaran murya sannan yace  Maman Bilkisu in dai abin da ya fada haka ne, to wannan abin farin ciki ne da murna, ki kwantar da hankalinki, zan yi waya gidan su mansura yanzu, kuma zan sa a darennan shi mijin mansuran ya bincika min ta hanyar buga waya mu ji gaskiya lamarin, tunda ai Yariman da ake magana kani ne a gurinsa, dole zai San komai, mlm mamman yace, ita dai ta sani ni fa na riga na bada 'ya, ke ko dan wa'yancan sakarkarun matan masu nuna bakin ciki ba kya ware asha daula ba. Mamanmu ta ce, kai dai ka sani kun fi kusa da su. A yau ne kasan sakarkaru ne? Umman mansura dariya ma ya bata,a ranta tace, namiji kenan.


Lalubawar farko Abba ya samu farooq, lokacin yana kwance ya dora 'yar bebynsu sa'adatu a kirji, Mansura ta saka kanta a cinyoyinshi, ya dauki wayar ya duba.yace, kai Abba ne ya tashi zaune tare da dora babyn akan katifa, yace salamu alaikum, Abba ina yini? Suka gaisa. Abba yace, kana da lbrin Yarima dan uwanka zai yi aure? Farooq yace Aa ai baya nan ma.Abba yace, to yi waya ka min bincike yanzu-yanzu, farooq yace, to Mansura da ta tsura mishi idanu tace, meyace? Ya daga mata hannu, inda zuwa, layin magajin Malam ya nema yasan shi ne zai San komai, bayan sun gaisa ya ce magaji shin gaske ne Yarima zai yi aure? Magajin Malam yace, haka ne, har ma an bashi matar a Zaria, kawar matar ka ko? Cike da mamaki yace, Oh dama Bilkisu CE?  Magajin Malam yace ita CE mana, yanzu haka an biya sadaki farooq yace, Yarima ya sani? Aa in ji magaji, bai ma san za ai masa aure ba, kuma mai martaba yace kada a sanar dashi. Farooq yace shi kenan, mun gode. Ya kira Abban Mansura yace eh Abba zai yi aure wai Bilkisu ce ma, Abba yace, to shikenan, ina so tunda gobe Sunday kana gida ka zo min da Bilkisun, amma kada kace mata komai ko ta sani? Farooq yace Aa yace kar ka sanar da ita sai kun zo. Ya kashe wayar.....

[8:48AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 36馃彽


Cike da mamaki farooq ya zuba ma waya idanu, Mansura a tsorace ta zaro idanu itama, tana kallon shi tare da cewa, wai menene Baban dady? Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce wai Yarima ne zai yi aure. Ta dan ja tsaki, to in Yarima zai yi aure me ya kawo Abba ciki? Ni wlh har na tsorata, zatona babu lfy ne,.Yace. Aa to kin San wadda Yariman zai aura ne? Ta sake zaro idanu tace wa? Yace Bilkisunki ta nan gidan.. Mansura ta mike Bil..... Wa? Yace, Bilkisu. Ta kuma dafa kirji in ji wa? Yace, gashi yanzun na kira magajin Malam ya tabbatar min har an biya sadaki! Sai dai wata tsiyar, shima Yariman bai sani ba, yanzun haka bai ma San za ai masa aure ba, itama nan gashi bata sani ba. Amma Abbanku yace gobe muje kada ki nuna mata kin San komai. Mansura taja tsaki, gaskiya ban so mata Auren Yariman nan mai zafin kai ba, farooq yace, ni ko na mata murna, domin Yarima yana da halin girma irin na gadon gidan su abin da ya faru tsakaninsu wannan shedanne . da zaran sun zauna zama na Auren sunna za su sasanta Kansu, kuma za ya kula da ita. Mansu tace, Allah yasa.


Su ko a nan zariya, Abba ya tabbatar ma da Mamanmu cewa batun aure gaskiya ne haka ne. Ya kara kwantar mata da hankali su da Umman mansura. Sun tafi kan cewa sai gobe in Bilkisu tazo zai zo a fito da kaya a duba.


***************************

Wayarsa ta soma ruri,Chelen ta mike ta dauko masa wayar,yana ganin number Magaji yace,Allah dai yasa lafiya?Ya daga sun gaisa sannan Magaji yace,mai martaba ne yace a tambayeka yaushe zaku samu hutu?Yayi shiru,sannan yace,sai nan da sati kila bakwai,yace ok,zan gaya masa.Yarima yace,lafiya Magaji?I think so.Yarima yace,naso ma nayi hutuna anan.Magaji yace,ok,ka iya yin waya ka gaya masa.Kai fa,bazaka fada ba?Inji Yarima.Magaji yace,No.Ya kashe wayar tare da cewa kada ka fada din,ni zan masa waya.Chelen ta matso kusa tana lasar kirjinsa da yayi laf da suma,tace tana son ya koya mata Hausa tana son yaren,yace bashi da time,kuma shima ba iyata yayi sosai ba,don shima Hausa fulani ne.Idanu ta tsura masa tana gaya masa cewa bazata gaji da gaya masa cewa yana da kyau ba tace shiyasa take kara son sa harma takan kirasa da One in town.Shi ko ce mata yayi yana sonta ne kawai irin na sha鈥榓wa,yace shi fa bai ma gama yarda cewa akwai wata soyayya ta No one but you ba.Shiru tayi don tasan yana nufin abinda ya gaya mata ne,kuma ya jima yana gaya mata haka,tasan bazata taba tursasa zuciyarsa ta so taba,kuma tasha yin fushi dashi,sai ya share ta sai dai ta dawo da kanta don shi bai iya lallashin mace duk da yanda takai da ji da kanta.Shiyasa kawai ta hakura da yin fushi dashi. Sun iso zaria misalin sha biyu,kai tsaye gidansu Mansu suka nufa,sun iske Umma tana shirin fita.Abba kuma ya dan fita shima,tace su zauna tana zuwa,Bily tace bari ta leka gida Umma tace a鈥榓 su dai jira gidansu Maman ta nufa,ta samu Mamman a dakin yace,yauwa Hajiya,shigo kinji fama nake da baiwar Allah nan za鈥榓 kawo kayan nan dakin tayi wa 鈥榶an uwanta waya suzo saboda mutanan nan zasu zo ne su kaita gidan ajiya,an jima kamar yanda nayi muku bayani jiya,duk taki ta bani hadin kai. Umma tace yanzu dai gata nan sun iso suna gidanmu,bari inyiwa Mansu waya ince suzo nan din ko dan tasan halin da ake ciki?Mama tace nima damuwata kenan,gaskiya in maigado bata son abin nan nima bazan so sa ba,dan fari ba mahaukaci bane,koda nake kauda kai kanta ba don bana sonta bane,ina dai kara ne,wulakancin dakayi ta mata cikin gidannan,ko tsinto ta akayi ba鈥榓 mata haka ba,shikenan haka rayuwarta zata zama cikin bakin ciki.Nan bata huta ba kuma tayi auren kudi can ma taje taci gaba da fuskantar wulakanci?Sam bazan lamunta ba,yaja tsaki ai kinji ki da wani zance,ba鈥榓 tuna abinda ya riga ya wuce,batun aji ra鈥榓yinta wannan ba dole bane tunda ko ashari鈥榓 mune masu zaba mata miji.Mamanmu ta kalli Umman Mansu tace,kirasu dai muji zabinta shine nawa nina san wahalar da nasha kan 鈥榶ayana.Bily ta rasa dalilin dayasa suna nufowa gidansu taji gabanta yana ta faduwa,ta dubi Mansu tace,ko dai wani abu ne ya samu Mamanmu?Mansu tace,me kika gani?Ta kama hannu Mansu ta saka akirjinta tace kinji fa kirjina.Faruk yace,ba komai insha Allah.Suna shiga da sauri ta nufi dakinsu,ganin Mama zaune yasa tayi ajiyar zuciya har duk 鈥榶an dakin suka dubeta,ganin Mama hankalinta ya kwanta,sai dai tasan da magana don banza Baba ba zaizo ya rashe haka ba.Ta shiga ta zauna kusa da Maman,tace Mamanmu har naji dadi dana ganki lafiya domin na zata wani abu ne ya sameki.Umma tayi 鈥榶ar dariya tace,鈥榶ar Mama kenan Mama kuwa cewa tayi lafiya lau maigado.Su Mansu suka shigo,Bily ta kara shimfida wata tabarmar,sannan aka shiga gaisawa,ta gaida Baba wanda zuciyarsa ta tafi ga tunanin yanda 鈥榶artasa ta nuna halin ko in kula dashi yau ne kurum abin ya fara masa ciwo,don da baya ma so ta nuna ta damu dashi Bayan gaishe-gaishe,Umman Mansu ta dubi Bily tace,kin san Yarima?Gaban Bily ya fadi,ko dai yasa anci ma iyayanta zarafi ne?Ta tambayi kanta,Umma ta katseta kin sansa nace?Bily ta girgixa kai alamun a鈥榓,tare da cewa ni sam bansansa ba.Yace nayi masa wani abu ne?Umma tace,a鈥榓 sannan ta dubi Malam Mamman tace,malam bani kudin nan.Jiki yana rawa ya ciro ya miko mata,ta amsa sannan ta aje agabanta.Wannan sadakinki ne,Bily ta zaro idanu tare da dafa kirji,Umma taci gaba ga kaya can yanzun za鈥榓 shigo dasu na zance,bikin bazai fi wata biyu da sati daya ba,me kika ce? A rude Bily ta juya ta kalli Mamanmu,sannan ta fada kan Maman tare da fashewa da kuka,tana cewa Mamanmu menene zabinki?Ki fada min zabinki shine nawa.Amma ina so ku sani Yarima zai aure ni ne ba domin yana sona ba,sai domin ya idar da wani nufi nasa na cin zarafina.Malam yace,ke dai kawai kice kinfi son kici gaba da zama agari babu aure,mutane suna zagina,amma ina kika san Yariman da har zaki wani ce yayi ne don yaci zarafinki mutumin da aka ce yana kasashen Turawa?Mama tace,tashi ki share hawayenki,in har ba kya son sa babu matsi,don ba akan kowa kike ba.Malam ya fita fuu yana cewa,ni dai ya rage naku.Uba ke bada aure kuma na bada ta.Sadaki kuma gashi nan a hannunku,in zaku ja da sarakuna ne bismillah.Ya sake lekowa,kada ku manta yau zasu zo su kaita su adana,sai ku shirya abin ce musu in sunzo ni kunga tafiyata,ya shuri takalmansa yayi waje.Umma ta dubi Bily dake kuka Mama nayi,ta waiga gurinsu Mansu inda sukayi shiru tamkar ruwa ya cinyesu,sai Mansu dake kuka,tace ku tashi kuje can gidanmu,ke Mansu har kai Faruk ku bata shawarar data dace,sai mu saurari hukuncin Ubangiji.Mansu ta kama Bily suka fita suna kuka,Faruk yana cewa suyi shiru kada su shiga cikin jama鈥榓 da kuka waton awaje in sun fita.
[4:01AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 42馃彽


Hakika mai martaba yayi murna da zuwan Yarima, fannin Umma kuwa sawa tayi aka shiga shirya ma autan nata gara kala-kala.Dan hutun sai da yayi wanka ya gama kyale-kyalen sannan ya fito gaban Umma yasa aka zube masa komai ya zauna tare da dararrashewa cike da shagwaba yake cin abincin suna shan hira,yace Umma taya naga duk zuwan da nake yi yau ne kuka fi murna da ganina?Ko dannayi zuwan bazata?Yace da haka kuma kazo ne akan gaba,wato kazo sanda ake son zuwan naka ma鈥榓na dama muna bukatar kazo din,ya dubeta saboda me?Tace saboda komai ma babana,kai dai gama zakaji komai gurin mai martaba.Gabansa ya fadi,amma sai ya daure ya jawo wata hirar.Umma kinyi kyau fa,kamar bake kika haifi su anty Salma ba.Umma tace,kai babana ko yaushe kazo zancanka kenan,wane kyau mun tsufa?Ai ba kyau ga tsoho,fatanmu dai mu ga jikokin kowa muga na auta,kasan 鈥榶ayanka sune asalin jikokin gidannan, kuma sune zasuyi gadon sarauta.Yayi murmushi insha Allah nima har nawa jikokin sai kin gani.Umma tace,a鈥榓 babana bana fatan ganin wannan lokacin yace to mu sake labari bana so kina tunanin cewa wata rana zamu rabu,tace ai wannan ya zama dole,yau ina tawa uwar? Yace,shikenan dai Ummata,ina su anty Fulera? Ta dawo daga jiddan kuwa?Tayi murmushi tasan ya kauce wa zancanne.Tace,sun dawo tuni Abban ya samu sauki sosai,haka suka ci gaba da hirarsu cikin nishadi irin na da da uwa. Masu matukar son junansu,sannan Magaji ya shigo inda yayi masa rakiya zuwa sauran sassan don gaida kishiyoyin Maman tasa,daga nan suka isa fada don yiwa sarki gaisuwa.Bayan ya rusuna yayi gaisuwa,sannan ya karasa gefen mahaifin nasa ya dora kai kan kafar mai martaba,wannan abin tun yana yaro haka yakeyi, mai martaba kamar ko yaushe ya shafa kan Yarima tare da furta Allah yayi maka albarka.Sannan Yarima ya zauna yana kallon yanda fada ke tafiya har zuwa lokacin 

Da dare suna cin abinci cikin wani shahararren falon mai martaba,falo ne na gargajiya,yasha kilisa da tim-tim,in yana nishadi yafi son yaci abinci cikin falon.Yanzu ma Umma ce take zuba musu kalolin abincin suna ci,shi ko Yarima fruit yake sha cike da nishadin gashi zaune gaban iyayansa.Mai martaba ya dubi Yarima cikin sigar wasa irin na iyayan da suka shaku da 鈥榶ayansu,yace Allah gafarta Modibbo dama ka samu labarin auren naka ne shiyasa kayi mana zuwan bazata?Nan take cikin Yarima ya kada, kamaninsa suka sauya yace,ranka ya dade dama da gaske ne za鈥榓 min aure?Mai martaba yayi murmushi,sannan ya dubi Umma kinji wani shirme,dama ana wasa da zancan aure ne Modibbo?Umma tace,babana ai ka kusa angwancewa.Shiru Yarima yayi,sai dai duk kayan dake gurin sun fita ransa,duk da son cin dayake yi.Kofin ruwa ya dauka ya tsiyaya ya kai bakinsa yana sha,jin ruwan yake tamkar madaci,amma ya daure yana dan kurba don kada iyayansa su gane,sai dai ya makaro,domin tuni suka fahimci baiji dadin albishir din da suka masa ba sam.Mai marataba ya aje cokalin hannunsa sannan yace,mun maka laifi ko Al鈥榓min?Yarima ya kakaro murmushi yaya zaku min laifi?Ranka ya dade kunyi min gata dai.Ya sunkuyar da kai,na gode Allah ya rama muku.Ya dubi Ummansa banyi rashin kunya ba ko?Suka yi murmushin jin dadi,duk da sun sanya wayance ne.Yarima kam ya shiga rudu,lallai ya gamu da abinda yake tsoro,gashi bashi da mafita, bai saba musu da mahaifinsa ba,ba tarbiyar gidan sarauta bace,sai dai lallai da safe zai samu mahaifiyarsa yana son ya roke ta kan ta lallashi mahaifinnasa duk da yasan ba lallai bane hakan ya yiwu,bacci dai ranar kasawa yayi har nisan dare.Can ya dauki waya ya soma neman Magaji, magaji yana daga waya Yarima yace dan iska za鈥榓 iya hada baki da kai akashe ni tunda har aka kulla min aure baka ce komai ba.Magaji yace,kai haba wace zaka aura?Amma fa nayi murna. Tsaki Yarima yaja sannan ya kashe wayar,ya kwanta badon yana saran bacci ba,sai don kawai yayi tunani,hakace kuwa ta faru domin sai daya dawo masallaci sallar asubahi. Sannan wani nannauyan bacci ya dauke sa.Tara da minti hamsin ya farka, zuciyarsa cike da damuwa haushin koma wacece amaryar yake ji,don ya tsani abinda zai daga masa hankali har ya fita lokacin wani abu ya shiga na wani.Da rigar bacci ajikinsa ya nufi dakin Umma,yana so ne ya dan lallashe ta kila ta goya masa baya duk da yasan babu tabbas.Tana karin kumallo ya sameta cike da fara鈥榓 take dubansa, babana ka tashi?Ya dan turo baki irin na shagwababbun yara ya zauna ba tare da yace kala ba,Umma tayi dariya tare da cewa,auta yau shagwabar ta tashi kenan. Kafin yayi magana, jakadiya tayi sallama, Umma ta bata izinin ta shigo.Tayi gaisuwa gurin Umma,sannan tace,nazo ne in gaida uban dakina, tun jiya bamu hadu ba, naje yana bacci na koma aka ce kuna cin abinci,to yanzun dana je suka ce min ya shigo gurinki shine nace bari dai inzo na kosa inga uban dakina.Umma tace ga uban dakinki nan yana ta fushi.Jakadiya ta dubesa ran uban dakina ya dade,wa ya taba min kai?Yace dubi Umman shi Umma kinji?Tace naji me?Yace don Allah ki gaya ma mai martaba ajanye min zancan auren nan wallahi am too young shekaruna 24,amin aure,ku dubi karatuna mana yana bukatar natsuwa.Umma ta daure fuska,sannan tace kaga kada ka sake min maganar nan,magana an gama ta lokaci ya matso,sannan kazo da shirme?Yasa hannuwansa ya dafe kansa tare da cewa,Oh my God!Please Umma,I hope zaki iya shawo kan mai martaba,ni nafi son inna kai talatin sai inyi tunda kuna son nayi aure,amma yanzun fa 24 nake kafin talatin din ma ace ina da yaran?Bazan iya ba Umma.Ta mike sannan ta kallesa me yasa tun sanda ya sanar da kai baka musa masa ba,sai ni don ka raina ni zaka zo ka tasa ni agaba?To bari kaji bazai yiwu ba.Ta fita,jakadiya na cewa Allah ya huci zuciyarki ranki ya dade. Umma na fita jakadiya ta matso ta zauna kasa agabansa,ranka ya dade ai hakuri kawai zakayi.Ya dubi jakadiya idanunsa jajir yace,jakadiya na san kina taimaka min tun ina yaro,duk abinda nake so kina min kokari musamman agurin mai martaba.

[4:03AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 43 馃彽


 Jakadiya tace,cikin sanyin murya da sigar lallashi ranka ya dade, wannan karon mai martaba bazai yi yanda kake so ba,in kuma mun tursasa shi yayi yanda kake so,to girmansa zai fadi,kimarsa zata ragu,me zai ce da sarkin zazzau wanda shine ma ya biya sadakin tare da kebe amaryar taka,wato ya killace ta?Shi kuma sarkin zazzau me zai ce da iyayan yarinya?Sannan kai kanka bakayi biyayya irinta 鈥榶ayan sarakuna ba,domin tarbiya gurinku ake koyo sai aji karfin iyayanka me jama鈥榓r Bauchi zasu ce?Ko kasan labarin aurenka ya shiga Bauchi da kewaye?Ka dawo tunaninka,ka kwantar da hankalinka tare dana Ummanka,gashi tayi fushi.Yayi ajiyar zuciya,ya sanin yanzun bashi da mafita,sai hakuri, ya dubi jakadiya yace, jakadiya yanzun to yaya zanyi?Tace yauwa uban dakina,ka samu Magaji ku shirya zuwa hira da amaryar taka wannan shine zaisa Ummanka ta sakko mai martaba yaji dadi su kuma yi alfahari da kai cewa zamanka a turai bai sa ka zubar da tarbiyarka ta Hausa fulani da addininka na musulunci ba.Yace shikenan,na hakura amma jakadiya Allah ya sani bana son matanmu na Nigeria,sam kauyawa ne basu ko iya kwalliya ba. Jakadiya tace,kai!Bari uban dakina,ba鈥榓 fi 鈥榶anmatanmu kyau ba da iya daurin dan kwali,asha jan baki da hoda.Yayi dariya,tare da cewa ai kauyancin kenan kullum jiki an rufe shi ruf,jakadiya tace ai wannan kuma haka addini ya tsara,inka aureta nan ne zaka ga kyanta kai kadai,ya taba baki sannan yace,ki sanar da mai martaba ashirya mana zuwa can ina ne ma kika ce?Tace zaria,yace 鈥榶ar masarautar ce?Tace a鈥榓,ba 鈥榶ar sarauta bace, shiyasa aka killaceta don dabi鈥榰n sarauta ya shige ta.Ya fita yana cewa,bari inje in yima Magaji waya.A dakinsa kafin ya kira Magaji,sai daya zurfafa tunanin shi lallai dole ya hakura karya zubar da darajar masarautar mahaifinsa,in yaso ana yin auren sai ya koma makaranta ya barta anan in anyi hutu yaki dawowa yayi zamansa can inta gaji ta nemi su sahale mata, yin wannan tunanin shiyasa Yarima ya saki ransa ya kira Magaji yace ya shirya zuwa Motoci hudu ne cike da dogarawa ata gaban ta bayan 鈥榶an sanda ne ta tsakiya kuwa Yarima ne shida Magaji, sai mai dauke da tsaraba zuwa kayan lashe-lashe wanda ango zai kaiwa amarya.Cikin bacci take jin gabanta ya tsananta da faduwa,ta farka da sauri ta tashi tana salati,ta kalli agogo biyu saura tace, a鈥榰zubillahi mina shaidanir rajim.Har lokaci ya tafi haka?Sai da tayi sallah sannan ta shiga wanka tana zaune cikin bahon wankan tana saba jikinta sabulu tare da kara gode ma Allah yanda ya tsara mata surarta,ga fata mai laushi ita kanta tasan cewa ta keru ne samanta da kasanta,sai dai matsalarta daya ce,rashin dacen miji domin nata ganin me zai ce mata?Allah yasa ma yasan menene auren inma yasani ita kam ai ta masa girma sai dai ya nemi 鈥榶ar sha shida.Haka ta fito daga wankan tana tunane-tunane,ta gama shafa jikinta da mai ta zura doguwar riga mara hannu,tasan yanzu masu kula da kwalliyarta zasu shigo.Sai ko gasu sunyi sallama,ta amsa suka kama aikinsu cikin zuciyarta kuwa haushin wannan kwalliyar takeji,ba don komai ba sai don a iska ake yinta,tunda ba miji gareta da zaizo ya gani ba,ita kuma ba fita zatayi ba bare tace...Atika ta katse ta da cewa ranki ya dade Allah yasa bamu muka bata miki rai ba kike tsaki?Bily tace,ina tsakin wannan kwalliyar ne ta isheni.Suka ce ya kamata ace kin saba da wannan kwalliyar ranki ya dade.Su Yarima kam kai tsaye fadar sarkin zazzau suka zarce,suka kai gaisuwa, sunci sun huta tare da yin sallah sannan suka nufi gidan da amarya take. Yarima da Magaji sai dogarawa guda biyu dake biye dasu cikin wata mota,Magaji ya dubi Yarima cike da tsokana yace,nasan gabanka yana ta faduwa,kana tunanin fara ce? Baka ce?Mai kyau ce bata da kyau?Oho.Yarima ya dubesa kamar bazaiyi magana ba har ma Magaji ya sadakar bazai ce komai ba,sannan Yarima yace,ina ma sonta kenan?Yaja tsaki kada ka raina ma kanka hankali,ka zata sonta nakeyi,ko daya yanzu ma jaje nazo in mata.Da sauri Magaji ya dubesa 鈥渏aje? Yarima ya jingina da kujera tare da share Magaji har sanda suka iso gidan.

[4:04AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKE FARUWA 44馃彽


A falon suka zauna,Magaji ya dubi kuyangin dake zube gabansu suna dibar gaisuwa yace,ina Gimbiyar take?Asabe tace,tana ciki ranka ya dade.Yace shaida mata isowarmu,tunda taji shigowar matoci ta kasa sukuni,ta mike tsaye tana ta kaiwa-da-komowa, sanye take da doguwar riga mai hade da hula. Asabe ta shigo ranki ya dade ki bani goron albishir,da sauri Bily tace,Mansu ce tazo ko Mamanmu?Asabe tace,ranki ya dade Yarima ne yazo.Ta dafa kirji cike da fargaba,tare da cewa,Yarima?Asabe tace,eh ranki ya dade.Bily ta soma zufa,koma kice ina bacci don bazan ganshi ba.Saroro Asabe tayi,amma dole taje ta fada,jiki babu kwari ta sanar dasu gimbiya tana bacci.Yarima kam ko juyowa baiyi ba,Magaji ko yace,to bari mu jirata.Ya dan saci kallon Yarima don ya fada ne kawai don yaji me Yariman zai ce,nan take kuwa Yarima ya dakawa Asabe tsawa da cewa,ki taso ta mana,ita wacece da har za鈥榓ce tana bacci? Duk Bily tana ji,nan take ta tuno da maganganun da Yarima ya gaggaya mata,don haka Asabe tana shigowa kafin tayi magana,Bily ta fita.Yarima yana zaune ne saitin dakin nata,don haka tana fitowa tayi arba dashi,yayi kyau cikin kayan da 鈥榶ayan sarakuna suka fi sawa,sai hula mai gashi da kuma takalman sarakai.Sam Yarima bai ko kalli inda take ba,duk da yasan ta shigo yayi shiru yaji da wacce zata fara?Amma sai yaji shiru,sai Magaji ne yace,ranki ya dade karaso mana.Yarima ya juyo da nufin yaga wai shin wannan wacece ita?Zumbur ya mike yana nuna Bily da dan yatsa tare da fadin dama kece?Ya kalli Magaji ka gane ta?Bai jira amsa ba ya soma tafa hannunsa sai da yayi tafi so uku sannan ya taka a hankali ya isa gurinta.Ya dubeta sai yanzun na fahimci dama kina da wata manufa akaina,kuma kinyi Achieving shiyasa kika ce kin sanni tun randa kika fara ganina?So kinyi kokari,yanzun dama nazo miki da abu biyu ne,na farko in tayaki murna sannan in miki jaje,daga karshe kuma in baki shawara,to amma tunda kece ina nufin ba wata can da nake zato ba,wadda bata sanni ba aka tilasta ma aurena bace,to abu uku zan miki ke maimakon biyu zan fara jinjina miki sannan in miki murna in kuma miki jaje,sannan in baki shawara sai dai shawarar da zan baki tasha banban da wadda nazo da ita,taki ta dabance.Ya juya mata baya tare da harde hannuwansa a kirji, jinjinar da zan miki kuwa?Ita ce na yaba da kokarinki yanda kika shiga kika fita tun daga kakana Modibbo zuwa mahaifina kika kuma hado da sarkin zazzau kinyi kokari har zuwacin nasararki na aurena.Sannan ina miki murnar samun miji kamar ni,hakika kinyi sa鈥榓r samun wanda mata ke so,kuma mai burin zama da mace daya rak karin sa鈥榓rki kuwa?Itace gidan sarauta ba鈥榓 saki mutu ka raba matsawar ba kin zo da wata alfasha bayyyananniya ba Sai shawara da farko nazo in ba wadda za鈥榓 aura min shawara ne akan kada ta yarda ta shigo hurumina, wato ta bijire ma aurena kafin zuwan ranar auren. Amma yanzun ke ya juyo ya nunata,bazan baki shawarar karki aureni ba,domin kece kika nema,kuma nima naso hakan don in banbance miki tsakanin aya da tsakuwa,sannan shawara sai kinyi hakuri da zama da karamin yaro kuma bugu da kari yaron jahili da kakkausar murya ya fada.Magaji ya taso yana cewa a鈥榓 Yarima what are you thinking? Yarima ya daga masa hannu don鈥榯 say anything baka san komai ba akan wannan yarinyar.Bily tace,kaini daina ce min yarinya domin ba sa鈥榓rka bace ni,sannan ka daina babatun na shiga nafita don na sameka wallahi kayi kuskure,yanda kake jin an matsa maka haka ma nima har ma gara kai,nida aka tuge ni kan aikina sannan duk zaman da kake bukata na shirya sai ka sani ni ina da ilmi kuma bana fata nabar tafarkin da musulunci ya shinfida min,don haka zan bika in Allah ya sa kai ne mijin nawa(hawaye ya soma zubo mata)sai dai na cutu don ba irin ka naso in aura ba.Ta juya zata tafi Yarima ya fizgota,kinsan zaman da zamuyi?Ya zuba mata manyan idanunsa cikin nata idanun masu tsananin haske da matsakaicin girma,yace ina tambayarki?Tace sai ka fada.Mace mai shekaru da ilimi mijinta karamin yaro jahili,kuma mai tsattsauran ra鈥榓yi sannan miskili in kin shirya you are welcome ya saketa da karfi ya fita. Magaji ya taso kusa da ita yace kiyi hakuri insha Allah komai zaiyi daidai, murmushin bakin ciki tayi ga hawaye yana zuba ita kam yaya zatayi?Daki ta shiga ta hau gado tana kuka zuciyarta kuwa tana tambayarta sai yaushe zatayi farin ciki?A baki ta furto babu rana,don yanzun zaka shiga sabon babin bakin ciki ne gidan Yarima gashi babu saki MEKE FARUWA  dani ne? Lokaci baya jira sai dai ajira sa inji 鈥榶an magana,wannan haka ne domin yanzun dai saura sati daya bikin Yarima da Bily,gefensu Mamanmu babu zama,duk da ance ba鈥榓 son azo da komai Mamanmu ta dage lallai abada koda daki daya ne don azuba ma maigado kayanta,Mansu kuwa dubu dari ta zube ma Mama tana bada hakuri babu yawa,ban dana Faruk,su Sakina kowa yayi kokari sai dai su Gwaggo Ladiyo su hana kansu sukuni,sunata faman shige-shige 鈥榶an tsibbu suma sunyi nasu shirin.Gefen ango kuwa sam ba wanda ya zaci baya so,nan ya sake aka shiga shirya yanda biki zai kasance dangi kowa ya kosa.鈥榊an kawo lefe gidan Umman Mansu aka saukesu,suna dauke da akwati doxin biyu tare da key din henesy su anty Salma sun raina ma gidan da aka nemo ma Modibbo aure duk da tsarin gidansu Umma Mansu ina to ace gidansu Bilyn ne kila ko zama bazasuyi ba.Sai dai sun dan yaba da tarbar da aka musu,na kayan lashe-lashe da kuma ciye-ciye, sannan tukuicin dubu dari sun ansa a raine don bai wuce kudin shan sweet din yaransu ba,haka suka tafi suna ta surutu.Koda suka je suka gayama Umma,cewa tayi bata son surutu,in ma ba鈥榓 basu tukuicin ba ai ba addini bane.Ana saura kwana uku biki aka dauko Bily,wadda tasha gyara gurin tsohuwar da jakadiya ta tura,ga kuma Mansun ta tazo mata da tata tsarabar,sannan ga mai lalle tare da dilke.Nan fa Bily tayi kyau kamar aljana.Suna sa kai dakin Mamanmu dangin Mama suka kama fadin tubarkalla masha Allah, Allah yanda mutane suke ta cewa kai Bily kece kuwa?Kinyi kyau kaza- kaza,sai kawai ta boye gidansu Mansu,walima kawai suka shirya inda aka sha wa鈥榓zi da kuma nasihohi,bayan daurin aure kenan.

[4:07AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 45馃彽Amarya hijabi har kasa da nikabi tasa ta rufe fuskarta don tunda ta fito daga inda aka killaceta sai ta ringa ganin haske yana haske mata idanu,don ta jima bata ga rana ba.Motocin daukar amarya sun kai ishirin zuwa gidan sarkin zazzau,sauran dangi sun wuce Bauchi a mota amarya ko jirgi zasu biyo su Ladiyo dasu Karime suma sun taho don su danyi 鈥榶an binne-binne nan da bokayensu suka basu. Haka nan yanda Mansu ta tubure sai da Faruk yayi ma Bily kaya haka Bily itama ta tubure sai an raba musu nata.Lallabata akayi Mansu ta diba,don Umma cewa tayi baza鈥榓 raba ba tunda tsadar kayan ma ba daya bane, tunda babu kasa da aura duk cikin kayan Mamanmu ma cewa tayi sai sun raba Mansu taki.Amarya ta isa gidan iyayan mijinta daf da magariba nan zasu fara zama agefensa tunda Malesia zasu wuce,gefen yasha gyara da kayan alatu,sannan ga dakin da aka basu suma su Mama sunyi kokari,sannan ga kuma gara shake da mota,duk fa hidimar nan malam Mamman ba ko taronsa,sai dai fa diyarsa ta auri dan sarkin Bauchi.Dinner daya da daya aka shirya a kayataccen Hotel kusan mutum shida ne akan amarya suna shiryata.Ni kaina muna hada ido nace subhanallahi,to ina ga ango.Yana zaune cikin shiga ta alfarma,wata alkyabba ce karshen tsada cikin motarsa limousine Ya kashingida yana kallon TV kuyangi da sauran dangi suka rakota har gurin motar suka bude mata ta shiga kamshin turarenta ne wanda tun tsawon zamanta agidan da aka killaceta tsohuwar take turareta dashi ya bugesa ga kuma na musamman domin shi Mansu tayi mata wanka dashi,ta shigo ta zauna tayi sallama,ba tare da ya kalleta ba ya amsa,sai dai yana kallonta da wutsiyar manyan idanunsa kyan da tayi tare da kamshin turarukan jikinta sun rikita sa kuma take sha鈥榓warta daya jima yanayi ta motsa masa,sai dai ya dake ya kuma shareta, amma zuciyarsa tana ta fadin she is beautiful.Ita ko Bily kasa kurum take kallo tare da yin wasa da yatsunta, xuciyarta kuwa tana kambama kyan halitta irinta Yarima. Guri yayi guri,dama ango da amarya ake jira shigowarsu cikin hall din zuka tana jama鈥榓 sun tsumu 鈥榶ayan Gwamnonin da 鈥榶ayan sarakuna sun jinjina ma zaban Yarima.Kai wani dan sarki daya kasa daurewa sai daya iska Yarima har mazauninsa ya bashi hannu,bayan sun gaisa sannan yace Prince Al鈥榓min ka dauki ta karshe acikin mata,Yarima yayi dan yake tare da godiya. Mansu ta dafa Bily sannan ta rusuno bayanta tace aminiyata kunyi kyau da yawa kun dace sosai tsaki Bily tayi tare da cewa ni duk kunya ma ta isheni, don abin kunya ne in auri dan wannan yaron.Mansu tace yanzun dai ya zama miji sai adaina ce masa yaro,Bily ta dan dubesa 鈥榶an jarida suna ta hira dashi tace bazan daina kiransa yaro ba,tunda ba girmata yayi ba.Dinner tayi kyau,gurin ya tara duk wani mai ji da kansa,鈥� yanmata da yawa sun kira Bily da mai tsananin sa鈥榓,domin cewarsu samun Yarima sai an tona.Bily takai kunnanta lokacin da wani dan jarida yake tana bayan Yarima wane irin farin ciki yake ciki yau kasancewar yayi aure da abar sonsa kuma mai tsananin kyau budar bakin Yarima sai cewa yayi shi wannan rana itace rana mafi muni cikin ranakun da yayi aduniya saboda me?Inji dan jarida cikin mamaki nan take Magaji ya katse dan jaridan da cewa tsabar murna ce tasasa baya iya saita maganarsa please ka tafi sannan na roke ka daka goge wannan bayanin da yayi.Bily bata ji komai ba don yace haka, dama tana tsammanin zance abinda yafi haka ma.Magaji da Faruk sunyi kokarin ganin Yarima baiyi wata tabargaza gaban jama'a ba gurin yanka cake nan ne suka danyi fama dashi yace bazai tashi zuwa ko ina ba don haka suka dauko cake din zuwa gabansa tare da baiwa jama鈥榓 uzurin cewa kunsan Yarima namu dan gata ne sannan shaukin mulki yana dibansa don haka bazai iya zuwa gaban cake ba sai dai mu kawo masa,haka an sha fama kafin yayanka sannan yasa mata abaki itama bayan Mansu tasha fama gurin lallashinta dan haka hoton ba da cake din nasu duk ransu bace yake,sai dai haka ni bai hanasu yin kyauba,haka dangi sukayi ta rawa suna zuwa suna zuba ma ango da amarya kudi, kasancewa duk sunki rawa Bily kam abin bai birgeta ba,ta tuna 鈥榶an watannin baya kafin ta gamu da Yarima bata da wani buri daya wuce ta samu miji,burinta shine aure farin cikinta taga wanda zai ce wance ina sonki,amma hakan ya gagara,har zuwa wannan lokacin da take aure.Ta dubi Yarima cikin zuciyarta tace,gadai mijin kuma mijin nunawa tsara,ta kalli dinbin mutanen dake gurin wadanda ada sai dai ta gansu cikin TV ko jarida ta dubi kayan jikinta zuwa gwala-gwalan hannunta duk wadannan abubuwan sun kasa sakata cikin farin ciki saboda rasa wannan kalmar ta so.To wai ita MEKE FARUWA da ita ne maza basa sonta?Sai ko ga hawaye shar daidai sanda wani dan jarida yake cewa,wane irin farin ciki kike ciki yau ranar aurenki?Ta bude baki zata ce tana bakin ciki ne ita aranar yau sai muryarta ta hau rawa,nan da nan Mansu tace da 鈥榶an jaridan bazata iya cewa komai ba farin ciki yayi mata yawa gashi har kuka ma takeyi.Bily tanaji bata tanka ba,ita damuwarta tasha mata kai,haka akayi ta shagali dangi suna ta bada kyautukan zannuwa, agoguna,masu dauke da hotunansu,wani iya shege da Magaji yayi shine,duk maroki ko mawaki daya zo gabansu Yarima yayi roko sai Magaji yace, yarima ya baka kujerar makka,ko mota kamar sau hudu ana haka,Yarima yana jinsa da yaga Magaji watan bai san zuri ba,kuma kyautar gidan sarauta babu karya ta bada,don haka sai yace Magaji ya isheka haka, inko ba haka ba duk wanda ka sake yiwa kyauta kaine zaka basa,don ni ban dauki yau ranar farin ciki bare har nayi wata kyauta,dariya kawai Magaji yayi yasan dai ya kunna Yarima. Bayan tashi daga gurin dinner haka akayi jerin gwano zuwa gidan mai martaba inda su Bily suka shige gefensu,sai da tayi wanka sannan tazo tayi alwala ta samu su Sakina duk sun kwanta da sauran jama鈥榓.Bily ce kawai take sallah,nan itama tayi sallarta sannan suka soma hira gurin dinner.Bily dai korafi takeyi akan yanda Mansu ta ringa bada ita gurin 鈥榶an jarida ita ko Mansu zakewa tayi tana ta fadin yanda sukayi yau cewarta bata taba ganin mata da miji da suka dace kamar ita da Yarima ba.

[4:09AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 46 馃彽

 

Sannan ta koma yiwa Bily hirar kayan gyaran jiki,Bily tace don Allah ki kyale ni kina yi kamar baki san wanda na aura ba,wannan yaron ne zan tsaya ina damun kaina saboda shi?Ta dan ja tsaki kinsan Allah koda ina son shine wallahi bazan bata kudina ba gurin wani gyara jiki saboda me ma ya sani game da auren?Ballantana ma ni bai min ba,ba sonsa nake ba shima haka. Mansu tayi dariya har da kwanciya, sannan tace,Bily baki san matasan yanzun ba kenan?Bily ta kwanta tana fadin barni da zancan nan kinji in huta,bacci nakeji. Mansu tace gobe ai ba kya yi shi ba,in mun watse, Bily tace sai ki hanani.Mansu ta kwanta tana cewa,in ban hanaki ba ai Yarima ya hanaki. Cike da tsokana tayi maganar,irinta kawaye. Banza Bily tayi mata taci gaba da addu鈥榦鈥榠nta na bacci,ta rumtse idanunta duk da cewa bata da tabbacin cewa baccin zai dauketa ko a鈥榓.Washegari sabon biki ne ya tashi gidan sarki dama su Umman Mansu suna can gefen Umman Yarima tare da su Gwaggo Ladiyo duk dai iyayen suna can matasan ne kurum anan gun amarya.Misalin sha biyu 鈥榶an yiwa amarya kwalliya suka shigo,sai da sukayi mata turare kusan kala goma daga ita sai vest da skirt,hatta gashin kanta yasha turare iri-iri,sannan ta saka wani leshi marar nauyi aka nade ta da laffaya,zobuna sarkar kafa,鈥榶an kunne,abin hannu. Subhanallah,haka mutane suketa fadi aka fito da ita zuwa falo ana jiran Yarima zasu je gurin sarki yasa musu albarka,sannan azo ayi budar kai.Shi ko gogan yana can ana fama dashi, jakadiya da Magaji sun tasasa da lallashi suka koma masifa.Magaji yayi zuciya ya fita,jakadiya cewa tayi bari taje ta sanar da Umman shi har takai bakin kofa yace jakadiya ta juyo yace yanzun me kike son inyi?Ta dawo cike da fara鈥榓 da kirari,sannan tace ranka ya dade da guda tamkar da dubu wanka zaka soma yi kayi shiga ta alfarma,gimbiya fa na jiranka a falo,na gode ranka ya dade sai ka fito.Ya bita da kallo har ta fita,sannan yaja tsaki ya shige toilet kusan awa biyu ya dauka sannan ya fito yana shigowa falo kuyangi suka mike jakadiya ta tasasu lallai ga zara ga wata, Suka ratsa jama鈥榓 har fada inda sarki yake zaune tare da fadawa da kuma manyan baki 鈥榶an taya sarki murna.Sun zube sunyi gaisuwa suna zaune gaban sarki yayi musu addu鈥榓 sannan yasa musu albarka ya umarci waziri da a miko masa alkyabba ta musamman ce ya tanade ta don yau,nan take yasa ma Bily.Wayaga gimbiya Bily,sarki da kansa yasan dan nasa yayi dace,nan malamai sukayi addu鈥榦鈥榠,sannan marokan sarki suka dora busa da kirari,su Bily suka fito mata suka dau guda ga kuyangi cikin ado suna biye dasu,sai gurin da aka gyara don budar kai,wani katon fili ne nan cikin gidan yasha decoration nan akayi budan kai.Ango da amarya sun samu kudi babu ma kamar ango inda matan sarakai kawan Ummansa da matan Gwamnoni zuwa masu fada aji,banda kyautar kuyangi daya samu daga sakkwato.Ana gamawa dama kamar yana kan kaya ne,suka nufi masallaci da suka dawo wanka yayi sannan ya saci jiki ya fita,wani guest house ya nufa ya kama daki yayi kwanciyarsa da nufin hutu.Su ko can gidan anci gaba da 鈥榶an bukukuwa,yayinda wasu bakin suka soma nade kayansu don tafiya gida.Ciki har da dangin Bily wadda hakan yayi mugun daga hankalita, musamman da taga Mansu ma tana hada kaya,ta zuba ma Mansu idanu tace,Mansu me kike nufi ne? Tace Gombe zanbi mijina,Bily tace ki daina min wannan magana,gaskiya bazaki tafi ba,kuna nufin ni kadai za鈥榓 bari bansan kowa anan ba?Mansu tana dariya tace,ba auren kenan ba?Bily tace amma ke ai na zauna miki. Mansu tace a ina? Tuna dai haka kuka kai ni Gombe kuka baroni,nan take Bily ta soma kuka tun Mansu tana tsokanarta har tazo tana bata magana,itama tana hawaye yanda Bily take kuka duk su Umma Mansu babu wanda baiyi hawaye ba,amma suka ki su kara kwana.Amma Faruk yace kafin su koma Kaduna zasu biyo su Sakina da Maryam suna kuka suka tafi,amma an bar mata auta kafin hutunta na makaranta ya kare,duk daba azo mata da kaya ba tunda ba鈥榓 shirya za鈥榓 barta tun daga gida ba,Umman Mansu ce tace abarta kafin Magariba  duk an gama tafiya sai Bily kwance kan gadonta tana ta kuka,auta ko tana falo tana ta kallonta.

[4:12AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 47馃彽


Can dai taga bata da nayi sai hakuri,don haka ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala tazo ta tada sallah,Asma鈥榰 itama tazo ta tada tana zaune har isha鈥榠 tayi,tana idar da sallah kuyangi suka shigo suna shaida mata batun cin abinci,tace ita kam alhamdulillah,sai dai ga kanwarta nan su bata. Yinin ranar ma ita banda ruwa babu abinda tasha, balle abinci,haka nan suna kwance ita da Asma鈥榰 bacci ma yayi gaba da ita ko kayan jikinta bata cire ba,duk ta gaji take jin jikinta tana cikin baccin taji muryar jakadiya tana cewa,ranki ya dade har kin soma bacci ne?Bily ta tashi zaune,jakadiya tace wanka zakiyi yanzun.Bily kamar tace ki barni inyi baccina,amma sai ta daure tace to ta mike taje tayo wanka sannan tazo zata sa kayan bacci kenan sai ga jakadiya,tare da wasu kuyangin suna dauke da wasu kaya cikin kwalaye,nan take suka shiga yi mata kwalliya, shafa wannan goga wancan fesa wannan gashi kai ma yasha turare yafi kala goma.Jakadiya tana gefe sai data bada izinin su bari sannan ta mika mata wani kwali,kisa wannan ina dawowa.Ba musu ta amsa,jakadiya ta tasa su suka fita,Bily ta bude kwalin nan ko ta dago wata shegiyar rigar bacci bata taba ganin irinsu ba,koda yake yaushe ma ta shigo garin?Cewarta nan take ta saka har da takalmi,jim kadan jakadiya tayi sallama tare da neman izini.Bily tace shigo bayan ta shigo tace ranki ya dade kinyi kyau yanzun sai ki zo muje gurin Yarima.Ita kuma 鈥榶ar uwar taki zanje da ita can gurin Umma mai babban daki.Kamar ta gaddame amma sai ta tuna da maganarsu Umman Mansu,inda suke cewa,ki zama mai biyayya musamman kasancewarki acikin gidan sarauta su ba鈥榓 gaddama don gidan ilmi ne da tarbiya,don haka sai ta mike tabi jakadiya.Suka fita ta cikin falonta suka shiga wata kofa nan ma wani dan madaidaicin falone sannan suka kara shiga kofa,nan ma karamin gurin hutawane ko yin karatu,sai kuma ga kafar bene tayi sama.Bily dai tana biye da jakadiya suka hau sama nan ko wani hamshakin tafkeken falo ne mai tsari.Jakadiya tayi sallama shiru ta nufi wata kofa daga cikin kofofi ukun dake falon ta kwankwasa. jim kadan aka bude,Yarima yana sanye da jallabiya,ya dubi jakadiya kafin yayi magana tace,ran Yarima ya dade,amarya na kawo maka.Ta juyo ta yafito Bily da hannu,Bily tazo ta tsaya kusa da jakadiya. Jakadiya ta nuna mata dakin tare da cewa,mu kwana lafiya.Yarima dake bakin kofar ya hana hanya tare da cewa,haba jakadiya, kuna tirsasani da yawa,shin bata da daki ne?Tana dashi ranka ya dade,amma addini yana tafiya daidai da al鈥榓dar gidan nan,ga al鈥榓dar wannan masarautar gimbiya Bily bata da gurin kwana sai dakinka,kuma saba ma hakan laifine babba.Jakadiya ta dubesa in kaji zafi Allah ya huci zuciyarka,mu kwana lafiya,ta fita.Yarima kam falo ya fito,Bily ta shige ciki.Subhanallahi!!Ta furta afili tare da hangame baki tana kallon dakin,afili tace jama鈥榓 kamar baza鈥榓 mutu ba? Gado ne gashi nan kamar na zinare,in ma ba gold bane to kalar ce asaman gadon.Akwai wasu fitilu kusan guda sha biyu kaloli daban-daban,gadon kawai suke haskawa sannan ga wani net mai ruwan madara ya rufe gadon ruf.Ta tsakiyar net din fitilun suke,ta kai duba kan gadon yana liliye da shimfidu na alfarma ga fuloli da yawa kanana da kuma manya.Kujera daya ce adakin katuwa,sai madubi suk seti suke da gadon,kafet zuwa labule masu kalar madara ne kila ma tare suka zo har da net din.Tana ciki tana wannan juyayin shi ko Yarima yana falo shaidan na tuno masa da sa鈥榠n鈥榮ar su shi da Bily,kalmar jahilci data tofa masa da kuma kiransa yaro sune suka dinga yawo cikin kansa nan take zuciyarsa ta shaida masa cewa ka nuna mata aikin jahilci dana yarinta zunbur ya mike ya nufi fridge din sa ya ciro wani jus na kwalba ire-iren wadanda yafi sha,ya dau kofi ya nufi dakin.Bily tana tsaye ta jingina bayanta da bango,bai ko kalleta ba ya nufi kujera ya zauna, sannan ya jawo dan tebur din gabansa ya jawo wata durowa ya ciro fakitin magani,ire-iren magungunan da suke sha da su Chelen in zasu aikata masha鈥榓rsu,ya balle hancin kwalbar ya tsiyaya jus din cikin kofi ya afa kwayoyin ya bi da sassanyan jus din

[4:14AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 48馃彽


Kan Bily yana kasa zuciyarta ta zurfafa da tunanin makomarta acikin wannan auren sam bata san bikin da Yarima yakeyi ba sai da wayarsa ta soma ringing ta dago idanu ta dubesa gabanta ya fadi kar dai giya ce wannan?Ta tambayi kanta zuciyarta ta yanke cewa lallai giya ce take taji ta kara tsanarsa gami da kyamarsa shi kam cike da isa ya soma hira da Chelen ba tare da shakkar ga amaryar tasa kusa ba,kuma abin takaicin hirar batsa ce tsagwaronta, da turanci suke maganar inda yake nuna mata damuwarsa game da kewarta da yayi acikin hirar tasu yana kara jaddada mata yana bukatarta sai dai inya tuna daren ranar da zaya dawo hutu yana jin saukin kewar a cewarsa tayi masa tanadi inya koma zata gurzu. A karshe ya kira sunan albarkatun kirjinta yace tasa masa wayarta akai shi kuma yayi kissing.Innalillahi wa鈥榠nna ilaihir raji鈥榰n,duk da Bily ba son Yarima takeyi ba hankalinta ya kai matuka atashi,ji tayi tamkar tayi waje da gudu.Da ace ba jakadiya ta kawo ta ba itace ta kawo kanta hakika data zunduma da gudu,sai dai bata san in ta fita ba me hakan yake nufi da sauri ta sulale kasa ta zauna domin sai taji jikinta ya kasa daukarta, kafafunta sunyi sanyi. Hawaye suka soma yi mata zarya kan kumatunta,shi ko Yarima ai suna sallama da Chelen sai ya kira Vicky itama hirar batsar ce dai,kai tir inji Bily cikin zuciya.Bayan Yarima yayi sallama da 鈥榶an matan nasa sai ya mike da kofi ahannunsa ya fita falo jim kadan ya dawo ya aje kofin tare da cewa,in har kina bukata zaki iya sha.Da sauri ta dubesa tare da cewa,Allah ya tsare ni ya dubeta tare da daga kafadunsa gami kuma da taba baki alamun ko ajikina.Bayinsa ma ya shige ya watsa ruwa ya dubeta menene shirinki game da kwananki dakin yaro?Ta mike tare da yi masa wani kallo kafin tayi magana ya kuma cewa,amma ki rike acikin zuciyarki bana sonki kuma baki min ba sa鈥榓rki daya kina da kyau kila in dinga kula ki don kyanki,amma ba don so ba,haka nan kema bana so ki so ni,ya zauna kan kujera yanzun ina son ki cire duk kayan jikinki ki kwanta kasa kan kafet kila inji sha鈥榓warki.Tayi masa wani kallo sannan tace,ai kai abin kyama ne,domin ka kusanta kanka da zina,ka sani baka kai matsayin dani Bily zan cire maka kaya ba,don bana bukatar kayi sha鈥榓wata yanda kuma kake ikrarin baka sona to ka sani nima haka.Yace ashe ilimin da kike ikrarin kina dashi karya ne,don mace mai ilimi iyakacin sanina(koda dai kince ni jahili ne)bata gudun mijinta,matsawar yana matsayin mijinta dolenta ne tayi biyayya ba maganar so agurin,don haka kiyi yanda nace,in kinki zamu gwada kashi duk da kince(yaushe kashina yayi kwari?)domin dole ne na banbance miki tsakanin babba da yaro,ni dake yau dinnan ba sai gobe ba,duk da faduwar da gabanta keyi bata fasa cewa baza鈥榓 cire kayan ba kaji ko,salon kaje ka goga min cuta,fasiki kawai ban cire kayan ba kuma bazan cire ba ban dama rashin kunya har ma ka dubeni kace in cire ka....saukar marin data ji babu zato tana ta masifa shine ya katseta,lokaci daya ya saka kafa ya kwashe ta,ta yunkura zata taso ya sake sa kafa ya maida ta tare da fincike hijabin jikinta.Sun sha kokawa amma ga mamakin Bily Yarima kyaleta yayi take kici-kicinta,don daya tashi lokaci guda ya murdeta sannan ya yaga rigarta haka nan bada soyayya ko lalama yake son maida ta mace ba irin yanda take karantawa cikin littattafai ba,a鈥榓 fyade yake nufi don haka sai ta bar mutsu-mutsu domin ta samawa kanta sauki ta sadakar sai kukan zuci da kiran Allah.Shi ko Yarima duk da ya fahimci budurwace matar tasa sam cikin zuciyarsa babu nufin rangwame,haka nan gyaran da aka mata zuwa kamshinta sun kara taimako gurin fidda shi daga cikin hayyacinsa,har ma ya kasa tuna dawa yake tare illa sunayan 鈥榶anmatansa da yake kira hakan ya kara ma Bily bakin ciki,ta shiga rera kuka.

[4:23AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 49馃彽


Abin mamaki mintina suka shude bayan wucewar sakwanni har aka shiga awa itama ta shude kai har amarya ta kasa fahimtar shin aduniya take ko ko a lahira?Kuma bacci takeyi koko ta mutu ne?Ma鈥榓na ta sume gogan bai san ma me take ciki ba har zuwa uku da rabi inda ya samu sukuni na kyaleta ba tare daya ko kalleta ba ya shige toilet jikinsa ya gyara sannan yazo ya haye gadonsa ya barta nan yashe bacci mai nauyi ne yayi gaba dashi cike da nishadin da yake ji na daban wanda tunda yake harkarsa da matan banza bai taba jin hakan ba.Sanyin asubahi ne ya farkar da ita,dishi-dishi ta soma gani kafin daga bisani idanunta suka washe,daga inda take yashe tana hango Yarima tsaf cikin gadonsa yana sharar bacci fitilun tsakiyar gado sun haske masa fuska,bakin ciki ya cika zuciyarta tayi ta kokarin yunkurawa ta tashi ta kasa dole ta hakura jim kadan ya farka cikin mika da salati tana kallon bakinsa yana karanta addu鈥榓r tashi daga bacci,sannan ya sakko ya tsallaketa ya shige toilet.Ruwa ya watsa tare da alwala sannan ya fito ya saka fara kar din jallabiya ya fita duk abinda yakeyi yana yinsu ne akan idanunta amma ko kallo bata ishe shi ba.Ta tuna da Mansu kawarta daren Mansu na farko da Faruk,Mansu tace kwana yayi yana lallashina, sannan da sassafe jiki yana bari yazo ya daukar mata Bily yana ta faman tarairayarta haka nan cikin littafai inta karanta mazan kan rasa inda zasu sa kansu,amma ita dubi abinda nata mijin yayi mata,sam bata son tunawa da daren farkonta zuwa shida na safe ta danyi karfin hali ta mike zaune ta jawo rigarta wadda duk ya yaga mata gashi duk rigar ta baci da jini haka nan ta zura ta dafa bango da dafa bango ta fito falo yana zaune yana kallon aljazira ya ganta tana kokarin fita,ya mike da sauri.Ke kina hauka ne zaki fita ahaka?Ko kallonsa bata yi ba taci gaba da laluben hanya,da sauri ya kulle kofar sauka kasan,sannan ya zauna ya dauko waya ya soma kiran layin Umma,bayan sun gaisa yace ta turo masa jakadiya Kamar minti goma jakadiya ta soma kwankwasa kofa,ya bude sannan ya nufi kujera ya zauna tana shigowa taci karo da Bily daf da kofa cike da salati jakadiya tace 鈥榶annan lafiya?Ta riketa tace,zomu koma ciki.Bily ta girgiza kai alamar a鈥榓,jakadiya tace yi hakuri ranki ya dade,ai ba kya fita haka ba.Ta rike ta suka juya tana cewa ikon Allah, a garin yaya akayi haka? Yarima dai volume din TV ya kara suka koma ciki. Haka jakadiya ta gargasawa Bily jiki,cikin katon bahon wankan na Yarima,kafin ta nufi sasan Bily don kawo ma Bily kayan da zata sa.Ita kuma Bily tayi wankan tsarki sannan ta daura tawul,jakadiya ta kawo mata kaya ta fita doguwar riga ce baka ta zura sannan ta fito duk jikinta babu karfi,jiri ma take gani.Jakadiya ta nado rigar baccin ta saka cikin leda sannan ta dan rike Bily suka fita kai tsaye dakin Bily suka nufa take cewa ikon Allah,wai gaddama kika masa ne har haka ta faru ni laraba?Bily dai shiru tayi.Jakadiya taci gaba da cewa,banda abinki yanzun wa ke yayin wannan?Yara kanana ma irin na kauye in an kaisu daki shiru kake ji tsakaninsu da miji bakaji ba ka gani balle ke da girmanki da iliinki kuma kinsan su maza ba kunya ce dasu ba,gashi ma shine ya kira azo a dubaki.Bily dai tana jinta,kala bata ce ba.Ta kwanta akan gadonta,sannan jakadiya ta fita,gurin Umma ta nufa tana zaune kan sallaya hannunta rike da carbi tana lazimi,jakadiya ta zauna gefe sannan tace ranki ya dade na dawo daga kiran na Yarima ta cira rigar baccin cikin leda tare da fadin Ubangidana yayi sa鈥榓r mace 鈥榶ar gidan tarbiya,ranki ya dade amarya ta kawo budurcinta gidan miji.Umma tace,kai to menene kuma Yarima bazai bar ma cikinsa sirrinsa ba?Ai yanzu an daina wannan abin ilimi ya ratsa ko鈥榠na.Jakadiya tace ranki ya dade abinne yazo da matsala,dole ya nemi taimako,yarinya ce tayi gardama ne nake ga shi kuma dan yau babu hakuri,wallahi karki ga yanda yarinyar nan tasha wuya jini kyace an yanka karamar kaza,tana can kwance babu yanda take Umma tace to yanzun bari inyi ma Doctor Aisha waya tazo ta dubata Ke kuma kije ki sanar da masu aiki su shirya mata farfesu na kaji dana kan sa ko ta danji dadin bakinta.Haka ko akayi,doctor Aisha ta samu Bily kudundune cikin bargo kuka kawai takeyi,ta duba ta likitar da kanta ta hada ma Bily tea tace tasha don za鈥榓i mata allura ne.Bily ta dan sha sannan ta mata allura tare da bata magunguna duk na gajiya ne,tare kuma da huce radadi,haka nan ma likitar tayi mata mita kan cewa mai yasa bata ci abinci ba kafin mijin nata ya kusanceta?Shiru Bily tayi,doctor Aisha tace rashin cin abincin ya taimaka gurin galabaitar dake sannan kinyi kokarin hanasa kanki,kin matse jikinki har ya kaiga ji miki rauni.Cikin kuka Bily ta kwanta tama tsani yanda suke cewa ta hanasa kanta,basa ma tunanin koda ace ta hanasa kantanne ya dace ya bita asannu,bacci yayi gaba da ita wanda dama bata same shi ba jiya.Biyu da rabi ta farka kamar acikin mafarki taga Mansu da dady da Asma鈥榰,suna ta shan farfesu,da sauri ta tashi zaune jikinta ya daina ciwon sai dai ta jita fayau babu kwarin jiki,ta sakko tana cewa Mansu yanzun kika zo?Mansu tace tun dazun,munzo kina bacci muka je gurin Umman Yarima,Bily tace zo nan dadyna yazo ta dorasa kan cinya tana cewa,ina Abbanka?Ita ko Mansu dariya take ta kunshewa har dai Bily ta gaji tace wai dariyar mecece haka?Mansu ta dubi Asma鈥榰 tace,auta keda dady kuje falo kuyi kallon cartoon suna fita Mansu ta koma gefen gado kusa da Bily tace aminiyata Umma tace baki da lafiya duk rigimar kin bar Mamanmu ne ko?Bily ta soma hawaye ta kama hannun Mansu tace,wallahi ba kukan rabuwa da Mama nakeyi ba,dama yaushe rabona da Maman da aka kaini aka tsare kamar nai sata,tasa yatsunta ta matse idanunta,sannan taci gaba wannan mutumin ne yayi min wani mugun wulakanci,wallahi nayi dana sani sosai na sanin Yarima bama aurensa ba.Mansu tace wane mutumi?Bily tace Yarima nace miki.Mansu tace hala ya zazzageki ne?Bily tace ba gara ya min duka bama da fyaden daya min,wallahi har suma nayi kwana cur yana aikin abu daya, wallahi ni bazan iya wannan bala鈥榠n ba.

[4:26AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 51馃彽


Yarima yayi murmushi dama so yake ya kunna Magaji,kuma yayi nasara.Ya dubi Bily sannan ya wuce tare da cewa,wa ma sunanki? Biyo ni tace,Hum sannan tabisa ranta fal kunci gurin Umma suka soma shiga ta zauna gaban Umma kanta akasa tana gaida Umman,ita ko Umma Allah ya dora mata son Bily,don haka ta jawota jikinta tana cewa matso nan 鈥榶ata,yaya jikin?Cike da kunya Bily tace da sauki.Yarima ko cewa yayi da Allah malama taso in kaiki ni sauri nakeyi,Umma ta daure fuska ta dubesa,bai sake magana ba,Umma tace babu inda ke miki ciwo ko?Tace a鈥榓 to kina bukatar wani abu?Nan ma tace a鈥榓,har ta mike zasu fita Umma tace,amm Bily babana dai baya miki wani abu ko?Da sauri ta dubesa ya ko banko mata harara ta kautar da kai sannan tace ba komai Umma,tace ki gaya min in dai da matsala,ba komai Umma cewar Bily,tace to zanba jakadiya sako ta kawo miki,tace to suka fita duk tausayin Bily ya cika ta don taga hararar da Yarima ya mata da alama tsoransa takeji.Sun zaga ko鈥榠na sannan Yarima yayi hanyar fita ta bishi ta zata nan ma wani sassan ne,ya dako mata tsawa ke!Dabba ina zaki bini?Ta ja ta tsaya,sannan ta juya azuciyarta ko fadi take,ina da aiki.Daki ta koma ta hau gado tana karanta addu鈥榓r yaye kuncin zuciya,nan take taji zuciyarta ta wanke tayi fes,kuma tun daga ranar kullum sai taje ta gaida su Umma,Umma tana nuna mata kauna sosai.Yarima zaune agaban mai martaba yana cewa ranka ya dade,gobe ne ya kamata in koma makaranta, domin tun wancan satin muka soma karatu.Mai martaba ya gyara zama sannan yace to madallah,sai ka sanar da iyalin naka ta shirya ko?Ko ka shaida matan?Yarima ya danne damuwarsa na zaci nan zata zauna?Saboda karatuna yana bukatar nutsuwa.Mai martaba yayi dan murmushi,sannan yace yaro,yaro ne yanzu kai dama baka fahimci don ka nutsun bane nace lallai ina bukatar kayi aure?Ya dafa dan nasa kada ka damu Modibbo, yanzun ne ma zaka samu nutsuwa yanda ya kamata kuma kayi karatunka cikin nasara,tashi kaje Allah yayi muku albarka maza ka sama mata biza kaji ko?Yace to na gode ranka ya dade,ya fita zuciyarsa fal kunci

[4:28AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 52馃彽


Haka ya shigo pallon umman shi rai bace Bily yana ta fadin shi gaskiya an takura mashi tare da nuna billy wai umma da wannan abun zan tafi ai kau umman ta hau shi da fada sosai ita ko billy kanta na kallon kasa  tana ta sharar da hawaye, Yarima ya mike ya fita Bily ta daure ta dubi Umma tace Umma nima nafi son abarni anan.Umma tace a鈥榓 Bily banaso kice komai kinji ko,ke dai kiyi ta hakuri sannan kici gaba da addu鈥榓,share hawayenki kinji ko?Nan take tace to Umma,Yarima ya rasa yanda zaiyi dole shi suka je shi da Magaji suka kammala mata komai,yana ta zafin rai,ai ko suna dawowa har daki ya same ta yayi mata tatas,yace in har kika bini dama kisan kin nemi maganin hawan jini dana ciwon zuciya,don kam kaken dana miki yanzun ne zaki gane dalili,sannan in har kika sake, kika tafi da wata kuyanga bana ji ana wani cewa ai musu biza ba tun cikin jirgin zan turo ki in huta,kinsan zan iya banza wawuya 鈥榶ar matsiyata ya fita,kukan da Bily tasha ranar babu iyaka daga karshe dai ta hakura ta kira Mansu ta gaya mata komai,Mansu ma hakuri dai ta bata,Bily cikin kuka tace,Mansu yaushe zanji dadi ne irin na kowa?Wai ni MEKE FARUWA dani ne?Haka zan dawwama Mansu,wallahi dana so aure saboda kuncin rayuwar gidanmu amma yanzu ga aure ga daula amma gara zamana na gidanmu gara ina gaban Mama su Gwoggo Ladiyo suyi ta min gorin yafi min yanzun.Mansu ma ta soma kuka tana cewa kiyi hakuri wata rana sai labari,haka suka yi sallama zukata abace.Sai da tayi kokari ta natsu sannan ta sake kiran Mansu tace mata ki kula min da Mamanmu.Mansu tace,kinsan wannan dole nane,ko baki ce ba,ni dai fatana ki kwantar da hankalinki duk me ya miki ki daure ki sama ranki cewa kina ibada ne,kinsan kuma bautar Allah sai da hakuri na sani kin sani no condition is permanent. Allah ma ya fada cikin Alkur鈥榓ni kowane tsanani yana tare da sauki,lokaci yana zuwa da zakiyi dariya aminiyata cike da jin dadi Bily tace na gode Mansu,naji dadi insha Allah maganganunki zasu zamar min abin tunanina, duk lokacin dana shiga kunci,sukayi sallama katan guda biyu cike da begen juna. Yanda taga rana haka taga dare, tunani ne ya cika zuciyarta MEKE FARUWA da ita?Me yasa bata da sa鈥榓 ne ita arayuwarta?Duk yanda Mamanta tasha wahala kanta ta kyautata rayuwarta taso kwarai ta samu mijin da zai kula da ita da mahaifiyarta,amma sai gashi wani can wanda bai san kimarta ba marar tausayi mara imani wanda in aka tsare sa koda bindiga ba zai nuna mahaifiyarta ba ya aureta ya kuma sameta abudurwa bai ko kula da hakan ba,wanda ada ita taci buri sosai akan budurcinta,domin tasan abin alfahari ne sai gashi amma shi ya keta ta ba tare da yako juya ba.Shin wane zama zasuyi a Malesia?Tasan sai tayi hakuri tasan zai bi mata,tasan sai dare zai dinga dawowa,tasan yana zuwa club,kila ma wata rana yazo mata a buge, tunani dai barkatai,lallai ta bakin nasa ta nemi maganin ciwon xuciya. Tun shigowarta gidan yau ce rana ta farko da taga ainahin gidan,mutane tankam an fitar musu da kaya,Umma dai tana ta nanata mata cewa,lallai in taji yaya ne ta kirata ta shaida mata,shi kuma taja masa kunne cewa ya kula da ita don ita din amana ce agaresa,kuma ta yabesa da cewa dama kai mai alheri ne,don haka ka lura da ita ka wadatata nan ya tuno da batun Modibbo jiya da yaje masa sallama,yace takwarana don Allah ka lura da matarka sosai,ka sani yanzu ka shiga wata rayuwa ce mai daraja kuma kaima ka zama cikakken mutum,yanzun ka kula da karatunka banda shirme.Yarima yace,insha Allah na kuma gode,an raka su zuwa filin jirgin sama inda Bily ta kara yarda Yarima dan gata ne,saboda 鈥榶an rakiyazuwa jami鈥榓n tsaro ne,suka shiga jirgi zuciyarta cike da addu鈥榓r hawa abin hawa,inda Yarima ya zauna kusa da wani tana ta hangen inda zata zauna kusa da mace 鈥榶ar uwarta tunda shi bai damu su zauna tare ba,don haka sai ta zauna ita daya akujerarta,wani kuwa yana shigowa ya zauna kusa da ita tare da gaishe ta,ta amsa tana satar kallon Yarima,don suna gabansa ne shi kam ko kallo bata isheshi ba,haka nan da jirgi ya tashi mutumin nan ya dameta da surutu har dai ta gaji ta soma baccin karya.

[4:31AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 53馃彽


Kai jama鈥榓!Anya mutane ana cewa babu kudi babu kudi,shin gaske ne?Gidansu take kallo tana fadin haka cikin zuciyarta tana tsaye tsakiyar falon gidan Yarima tana kallon tsarin falon irin dai gidajan da take gani cikin fina-finan turawa ko mujallarsu. Yarima ya nuna mata dakinta yana kusa dana sa ne,ta shiga gado ne madaidaici sai durowoyi wordrop da dai dan sauran abubuwa,ta kintsa daki duk da dai bashi da datti,ta shiga bayin karami ne ta tsaftacesa sannan tayi wanka da alwala wata tsohuwar baturiya ta shigo tana dauke da tire,tarkace ne ita jus din kawai tasha sam bata san wannan tarkacen ba,har wayewar gari bata fito ba,tunda tana da bayi kuma tazo da dambun nama dana kifi wanda Umma tasa akayi musu don haka bata da matsala,dama bata yi zaton Yarima zai nemeta ba,kuma hakance ta faru.Da safe ta lalubi kitchen taje shima ya tsaru,madam Dora tana ta 鈥榶an aikace-aikacenta suka gaisa,Bily ta soma hakilon neman abin karyawa,tea ta hada ta soya kwai babu ko bread taci kayanta ta koshi anan kitchen din take suna hira da madam Dora inda madam din take shaida mata cewa tana da kyau,shin ita 鈥榶ar wace kasa ce?Tace mata 鈥榶ar Nigeria ce,sai tace oh,ta manta dama Prince ya gaya mata cewa ita kanwarsa ce.Bily batayi mamaki ba tace,eh hakane.Madam Dora tace dan uwanki yana da kirki sosai,tun farkon zuwansa nan kasar nake masa aiki ni da sauran ma鈥榓ikatan yasan darajarmu yana mana adalci.Bily ta danyi yake tace ai hakane halinsa yake,tace koya sunanki? Bilkisu inji Bilyn ta shaida mata madam ta kasa sai dai Bikis haka ko taci gaba da kiranta.Da dare tana zaune afalo tana kallon wani fim,zuciyarta ko tana tunanin cewa tunda suka zo bata ko saka Yarima cikin idanunta ba,sai gashi ya shigo kamar ta share shi,sai dai ta daure tace masa sannu da zuwa tamkar baiji ba kuma tasan yaji don haka ta share shi kusan awa daya ya fito cikin 鈥榶ar T-shart fara da 3 kwatan wando ya nufi kitchen mai hade da dinning room.Can dai tana zaune sai taji wani abu yana kara,ashe intercom ne sai taga madam Dora tazo ta bude.Wata mace ce ta shigo tana sanye da siket da iyakar cinya,sai 鈥榶ar bes kana ganinta kaga chanis,suka gaisa da madam sannan ta nufo ciki tana tambayar madam ko prince na nan?Madam tace yana dining room can ta nufa,madam tazo tayi ma Bily sallama da cewa zata gidanta don basu da nisa,Bily tace to mu kwana lafia sai dai tanayi zancen ne kawai amma zuciyarta na gurin su Yarima,shin wacece wannan?Jim kadan suka jero ita da Yarima suna 鈥榶an hirarrakinsu,suka zube nan falon.Tamkar a fim ko cikin mafarki sai ganin Yarima tayi yana wasanni da wannan macen,sam tamkar basu san da mutum agurin ba.Kasa jurewa tayi ta mike ta shige dakinta kan gado ta fada,har yanzun bakin Yarima take gani cikin na wannan matar, tasan bata son Yarima amma dole ne tayi kishin mijinta.Kai ko ba mijinta ba ba zata so taga wani musulmi yana kusanta kansa da zina ba,bare har ya aikata.Tasha kuka daga baya tayo alwala ta soma nafila tana kaima Allah kukanta.Washegari ko da safe misalin goma tayi yo kwalliyarta cikin super riga da zani tayi kyau,tana zaune kan dining tana karyawa ya shigo cikin shirin makaranta.Madam dora ta mika masa dan kofi da plate coffee ne aciki yana sha,suna gaisawa tana masa korafin sister shi tafi son tayi girki da kanta,yace eh ko gida ma haka take.Madam tayi 鈥榶ar dariya sannan tace kuma Bikis tana da kyau,sai ya fita daga kitchen din yana cewa,chelen tana jiransa bari yaje.Can hanyar fita ya nufa,sannan ya aje kofin da plate din ya tafi abin tsoro mata gidan Yarima wasu suna shigowa wasu suna fita,kuma karka ga yanda yake wani shassha musu kamshi,abinda kullum ke bata mamaki har yau da take satinta daya agidan bai taba mata koda magana ba kuma koda ta gaishe shi baya amsawa, haka nan baya damuwa ko agabanta ne yayi yanda yake so da 鈥榶anmatansa hakan nan in sun nemi sanin ko ita wacece agabanta zaice kanwarsa ce.

[4:35AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 54馃彽 


Hankalin Bily bai gama tashi ba,sai daran ranar data cika kwana goma a kasar.Ta fito zata kitchen saboda tana son tashi da azumin alhamis,me zata gani?Yarima ne da mata guda biyu tamkar zasu cinyesa,kowace tana son nuna masa karshen soyayyarta,kuma tana son burgesa har ya juyo gurinta,cikin tsananin tsoro tace, A'uzubillahi minash shaidani rajim.Suka dubeta su biyun banda Yarima wanda ya rungumo su duk da ya ganta juyawa daki tayi ko ganin hanya batayi don tashin hankali cikin sanyin jiki ta zauna tama rasa wane tunanin zatayi ne?Kodai don bata kai kanta garesa ne yake kawo su gida don ya bata mata rai?Inko haka ne ai gara ta kai kanta gurin nasa koda zai riga mata fyaden ne in dai zai daina kawo wadannan matan masu kama da bebyn roba ta sani ba sun fita kyau bane ta sani ba wai tana son Yarima bane sai dai tasan in don rashin zuwa gurin Yarima ne yake zuwa ya kawo mata,to tabbas tana da kamashon zunubi,kila ma nata yafi nasa.Tabbas Yarima baiyi kuskure ba daya ce ta nemi maganin ciwon zuciya dana hawan jin,har gari ya waye tana tufkawa tana warwarewa. 


Yaya batun su Mamanmu? Duk wanda ya auri boka da 鈥榶an tsibbu lallai yana cikin dimuwa ba kuma zai gane ba,har sai ranar da karya ta kare,ga dai su Ladiyo nan anata fama yanzun ma da suke zaune gaba dayansu acikin dakin Karima suna tattaunawa ne akan duk malaman da suka je gurinsu,Salame tace abin kamar hadin baki malaman nan sunce mana inma an daura auren kwata-kwata ta dade tayi sati daya agidan mijin zai koro ta amma gashi yau mun shiga sati na uku.Ladiyo ta gyara zama ga kuma tsohon ciki tace yanzun ko bacci bana iyawa tunda akayi auren nan kullum ina raba idanu ne inga ta shigo gidan nan wutsiya zage,bani da buri sai na ganin bayan Bily.Karima tace kedai bari Ladiyo wallahi baki kaini ba,Ladiyo tace um um daina cewa ban kaiki ba,ni nan da kika ganni ko wannan cikin na jikina bana tunanin ranar haihuwarsa kamar yanda nake tunanin auren nan na Bily gashi kuma shiru. Salame tace mu koma mu sanar dasu aiki baiyi ba.Ni damuwata ma daya yanda mai adashen nan ke ta min sintiri naci na kasa zubi kudin da sune na bada muka kai gun malaman nan yaya tazo tana neman abin dauka, nace indai bani zaki dauka ba,ko yara ga sunan kwancar bani da wani abu dazan iya baki gaki dai ga dakin,in kinga abin dauka to dauki.Duk suka sa dariya,Ladiyo tace nima gado ne kurum yanzu ya rage min,Karima tace wa ma zai sayi wannan gadon naki,ko鈥榠na kudin cizo yayi kashi.Ladiyo tace eh,in zan saida ai dama wanke sa zanyi. Salame tace ai ko yaci klin din dari biyu dukkansu suka sa dariya,tace mu bar dariya mu fuskanci matsalarmu fa?Haka ko sukayi,washegarin ranar suka shiga mota suka nausa.kusan duk bokayan sunce musu kada su damu,aikin zaici ahankali. Shiko asalin bokan nasu cewa yayi yana zaton ma fa anyi sakin kila uwar yarinyar taki yarda su sani ne,sannan takai yarinyar gurin 鈥榶an uwanta.Ya kara musu da cewa haba ku sai kace ba mata ba?Ku kanku ma fa sharri ne mai zaman kansa cikin irin siyasarku ta mata da kissa ai kwaji koda gurin mijinku ne.Kai ita kanta yanayin amsar da zata baku zaku iya ganewa, suka ce hakane.Ladiyo tace malam sai dai fa maigidanmu da kake cewa zamuji gurinsa wallahi yanzun ya juya mana baya tunda yarinyar ta samu dan sarauta shikenan duk ya birkice mana.Malam yace a鈥榓 kuce akwai sabon aiki kenan,to kuna da kudi ko?Suka ce zamu nemo, amma don Allah ai mana aiki mai kyau,yace musu don wannan kada ku damu,an gama kuzo dai da dubu takwas,sannan da kaji biyu.Suka ce to sun gode,sannan suka muke suka dauki hanyar gida.Allah kasa mufi karfin zuciyarmu, amin. Suna shigowa gidan sun samu Mamanmu zaune tana yiwa auta tsifar kai,nan suka kyafta ma juna ido alamar su bigi cikinta,don haka sai suka hada baki gurin yin sallama.Mama ta dubesu ta amsa,sannunku da dawowa suka ce yauwa. Karima tace munje barka ne matar wan Salame,cike da fara鈥榓 Mama tace,Allah sarki to Allah ya raya,ai da kun gaya min da munje. Salame tace umh ni ai gani nayi na gaya musu bikin Bily sunki zuwa, shiyasa nace bazan gaya miki ba tunda abinba tsoro bane,su basa son zuwa

[4:36AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 55馃彽


Amma suna son aje musu.Mama tace,kai sai kace bin bashi?Ai lada ne in naje din,to Allah ya raya suka ce amin.Ladiyo tace,auta anata shan tsifa ne?Mama tace eh wallahi kin ganta nan kitson tunna bikin maigado taki tsefe sa,taje tasa anmata kitso yangu-yangu kuma sai da nace kar tayo kanana,amma da yake tana da kunnan kashi sai da tasa aka mata shi.Ladiyo tace ai duk haka suke,itama uwata gashi nan dama ita ba gashi ba yana nan kan duk yayi dugu-dugu ni dai ai bani da lokacin tsifa.Mama tace nifa tunda taki tsefewa ai tasan tawa tsifar sai na fece kai tas ta mun kuka in nade ta.Salame tace da kina can gidan amarya ai da kin huta.Asma鈥榰 tace ba Mama ce tace adawo dani ba.Karima tace,ina ruwan amare,ana can dai.Duk suka kalli Mama suga yaya fuskartata zata nuna?Mama tace,um suna can,sun ma tafi ni wacce kasa ce inda mijin ke karatun likita.Gaba dayansu suka ce me?Cikin Ladiyo ya shiga juyawa,Mama ta kallesu saboda yanda taji sun hada baki,Karima ta wayance tace,a lallai Allah ya bada zaman lafiya. Asma鈥榰 tace Mamanmu sunan kasar wai Malesia inji anty Mansu.Ai tuni suka sulale kowacce ta shige dakinta zuciyarta tana zogi tare da son tuno MEKE FARUWA ne?Abubuwan suke zo musu ahaka?


 Sumayya taja tsaki sannan ta kashe wayarta,anty Salma ta dubeta ke kuma dawa kike tsaki? Sumayya tace,wannan Magajin Malam din mana ya dame ni wai ni yake so,ni ko gaskiya be min ba.Anty Salma ta harareta,sannan tace to menene aibun Magaji?Momy 鈥榶ar gidan anty Salma itace ta uku tana da kannai da kuma yayye guda biyu maza,tace Mama ita fa Sumayya wai uncle Yarima take so,lokacin bikinsa duk inda mukaje sai tayi kuka.Anty Salma tace ai da kina sonsa kika yi shiru?Sumayya tace, wallahi Ummanmu ce ta hanani magana.anty Salma tace,to ba gara ke ba,da wannan 鈥榶ar matsiyatan. Momy tace,ni ko ina sonta Mama tana da kyau.Anty Salma tace, ja can sakarya tayi ta kyannata mana,sannan ta dubi Sumayya tace,karki damu bari ya gama karatu ya dawo sai mun hadaku. Ai dama itama wannan ba wani sonta yakeyi ba hadinsu mai martaba ne da Modibbo. Murna Sumayya ta hauyi yayinda Momy ta shiga turo baki itama tsarar Sumayya ce Momyn.Tace to baga Magaji yana sonta ba,Sumayya tace to ni bana sonsa Momy ta taba baki sannan ta tashi ta basu guri.Umma ta kira lambobin gidan nasu Yarima na can Malesia ta hanyar land line har sau uku ana ukunne madam dora ce tazo tana buga ma Bily kofa domin Yarima ya fita,Bily taso taki daukar wayar don ita tun fitowar da tayi daren jiya datayi mugun gani koda ta daga wayar jin muryar Umman Yarima yasa tajin wani sanyi,tace sannu Umma ina yini? Suka gaisa tace ina baban nawa?Bily tace ya tafi makaranta,Umma tace ina fata dai kuna nan lafiya babu wata matsala ko?Ba komai Umma cewar Bily,to kiyi ta hakuri dai kinji ko?Tace to Umma. Umma tace yauwa 鈥榶ata ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari,nasan Yarima sarai ki ta hakuri tace to Umma,to na gaisheku in yazo kice masa na kira ina gaidasa, tace to mun gode,zan gaya masa.Ta lura yana shigowa ne karfe hudu, don haka kafin hudu ta shiga kitchen tayi 鈥榶an girke-girkensu na hausawa,sannan tayi wanka,kwalliya tayi sosai irin wadda ake mata, sannan ta saka wani leshi mara nauyi kalar sararin samaniya,riga ne da siket tayi kyau ta saka gwala-gwalai kunne da wuya,da kuma yatsunta,tayi kyau sosai.Yau sai biyar ya shigo shida wani abokinsa dan Africa ne mai suna Saddik,tunda tazo sai yau ta gansa da musulmi,ta fito tace masa sannu da zuwa.Ya kalleta wani takaici ya cikasa aransa yace,har abada wannan ba zata waye ba,yace ai ke yafi dacewa ayi miki sannu, ko don wadannan kayan da kika lafta wa jikinki.Taji zafin maganar, amma sai ta daure tace Umma tana gaisheka, daxun tayi waya hanyar dakinsa yake tafiya amma sai ya dan tsaya ba tare da ya juyo ba yace me tace? Bily tace,ta gaishe mune kawai.Ya shige daki, ta dubi bakon sannu da zuwa ta masa cikin harshen turanci,sai taji ya amsa da hausa duk da hausar tasa batayi gargar ba,suka gaisa ta nufi daki.Bako Saddik ya bita da kallo,sanda tare da shiga daki gaban madubi ta tsaya bata ga aibun kwalliyarta ba,amma har yana wani cewa ta lafta ma jikinta kaya

[4:39AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 56馃彽 


Taja tsaki ai dama ita ba wai tana son sai ta burgesa bane kawai tana son ceto shine daga halakar daya shiga,amma akasan zuciyarta sai tana jin kamar ta canza shiga, amma sai wata zuciyar ta kwabe ta da cewa kinma damu sai kin burgesa kenan,don haka sai ta fasa ta fita zuwa kitchen dai dai lokacin ne taji bakon yana cewa,gaske kanwarka ce?Yarima yace,um hum! Bakon yace don Allah ina sonta she is very beautiful.Yarima ya mika masa littafin hannunsa tare da cewa amsa Saddik,kula min da littafina kasan ba鈥榓 samunsa anan nima sai a England aka samo min duk da cewa muna dasu a library amma ba鈥榓 son a fito dashi.Saddik yace, kada ka damu,yanzu muyi maganar sister dinka,I love her.Ga mamakin Bily, sai taji yace jeka gaya mata mana ni kazo ka dame ni kana sonta. Bily Sai data kusan faduwa don mamaki,shi wanan wato ko kishinta ma bayayi? Koda baya sonta ai ya dace yayi kishinta amatsayinsa na mijinta. Shin me hakan yake nufi? Guri ta samu acikin kitchen din ta zauna ta zabga tagumi,mijinta ne ke turo mata wani daya ce yana sonta,shin ko dai gaske ne Yarima bai san addini ba?Haka ta mike ta nufi daki bata ko ganin hanya sosai,dolenta ne tayi duk yanda zata ceto Yarima,amma duk da haka wata zuciyar tana ce mata Yarima ya wuce da tunaninta,amma sai tana karfafa ma kanta gwiwa da cewa,ai mata yake so kuma su yake nema,haka nan itama mace ce duk abinda wadancan matan suke dashi itama tana dashi,shin me zai hana itama ta bishi yanda sauran ke binsa?Ai itace ma ya dace ta bishi tunda mijinta ne,zata gwada irin nata salon,Allah yasa adace. Ta sani duk inda Yarima zaije baya wuce sha biyu.Wata rana ma baya kaiwa zaka ga ya shigo ko shi kadai ko shida 鈥榶anmatansa,ko sai in yazo sannan su biyo shi,yayi ta ja musu aji.Don haka kafin ya shigo tayi wanka ta gyara jikinta da turaruka,don turare yana motsa sha鈥榓wa musamman irin masu sanyin kamshin nan,rigar bacci tasa kalar pink mai yala-yala,wato mai bin jiki tana da gidan nono kuma shi les ne mai shara-shara, ta gyara gashinta ta daure da ribon pink,ta kalli kanta a madubi tayi kyau ta zauna jiran Yarima Sha biyu saura ya shigo anci sa鈥榓 shi kadai ne ya shigo,sai daya jima da shiga dakinsa sannan ta nufi dakin tana turawa kofar ta bude,ta shiga da sallama baya dakin amma da alamar yana wanka ne, ta kalli ko ina a dakin,lallai Yarima bashi da matsalar komai arayuwarsa,shiyasa yake yin yanda yaso.Zama tayi kan durowar gefen gadon tana cike da fargabar yanda zasu kwashe,kusan mintina goma sannan ya shigo dakin,waton ya fito daga bayin.Ya kalleta fuskarsa da alamar tambaya.Bily dai tana kallonsa bata ce kala ba,shima yaci gaba da harkokinsa.Shafa wannan matso wannan sa a hanci,sa a hammata, mamaki ma yake bata sai kace karuwan namiji,rigar bacci mai wando ya saka,sannan ya nufi wani dan fridge kwalbar jus ya ciro ya dauki kofi asaman fridge ya zauna gefen gado yana tsiyaya,ta gane nufinsa waton kala bazai ce mata ba,tasan zai iya abinda yafi haka ma,don haka sai tace,ina yini?Sai daya kurbi jus din sannan yace menene dalilin shigo min daki ba tare da izinina ba?Ta mike ta nufo shi yanda take tafiyar duk komai na jikinta girgiza yakeyi,kusa dashi ta duka,nazo ne in sauke nauyin da Allah ya dora min a matsayina na matarka.Ya dubi fuskarta idanunsa ya sauke akan lebunanta 鈥榶an yala-yala masu laushi jajaye tamkar ta saka janbaki,sannan ya kauda kai wane irin nauyi?Tayi jim don nauyin kalmar da zata fada.Hakkinka dake kaina.Ya sake kallon saitin kirjinta,sannan ya kauda kai yace, bana bukata,in kina nufin bani kanki ne,wancan lokacin ma nayi ne domin in banbance miki tsakanin yaro da babba,wato aikin da namiji zai iya da kuma wanda mace ba zata iya ba koda 鈥榶ar shekara sittin ce shi kuma dan talatin duk da kince kashina baiyi kwari ba,nasan zaki shaida cewa ni ba raggo bane,don haka yanzun kama kanki bana bukatarki ko da zan ganki tsirara. Kash! Mu hadu a littafi na uku (3) don jin yadda zata kasance,shin yanayin hakurin ko ko,ita tana yin zuciya koko batayi.

[4:42AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽 MEKE FARUWA 57馃彽


Jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta

baci,duk da shakkarsa da takeji gami kuma da

yanda yake cika mata idanu,sai data ce kai ma

kasan baya ga aure mai hada namiji da mace

baka isa in zo ince maka gani ba,ka sani nima

bada son raina bane,don kawai na fita daga

hakkinka ne,kuma Allah ya sani na fita.Ta mike

tayi waje rai bace,da kallo ya bita tun daga sama

har kasa yake kallonta,har ta fita.Ya runtse

idanunsa yana kallon yanda jikinta yake

motsi,wata sha鈥榓warta ce ta mugun tsirga

masa,ta baya ya fada kan gadon hannu ya kai ya

jawo filo ya saka akirjinsa ya matse gam,bakinsa

yana kwadayin lebunanta yana son jin kalar miyanta,nan zuciyarsa ta shiga tuno masa ni鈥榠marta duk da ya kusance ta ne cikin garari ba tare da wasu wasanni ba,amma abin ya tsaya masa a rai .Ya kuma shakar kamshin data tafi ta bar masa a dakin,ya sani bawai yana sonta bane

amma sha鈥榓warta tun ranar daya soma ganinta

ta tsirga masa,ba kamar yau da yaga siffofinta

a fili,yace kai she is a beauty.Yayi tsaki tare da

cewa,ni gaskiya banyi ba,ta kawo kanta amma na tsaya, yayi shiru yana son ya tuno wai ma me ta

masa ne?Yasan dai ta shiga rayuwarsa tunda

tasa an masa aure da wuri,sai ya kasa manta

zagin data masa na cewa jahili.Wata zuciyar tace

kada ka manta kaima ka zageta,yayi birgima

akan gado ya koma rufda ciki,sha鈥榓warta na bin

duk jininsa sai kurum yaji an kwanta a bayansa,ga

zatonsa itace,don haka ya juyo da sauri tare da

rungume ta tsam a kirjinsa,sai yaji muryar chelen tana cewa,oh my prince.Nan ya sassauta mata rikon tare da bude idanu yayi ajiyar zuciya kuma duk sai yaji ransa ya baci,tana kokarin neman

bakinsa ya tsaida ita tare da nuna mata hanyar

waje.tasan wanene prince in ba yayi yana bukatar

a kyalesa,don haka sai kawai ta mike ta fita,haka

ya kwana ranar juyi kawai yakeyi. Bily tana komawa daki kofa ta kulle ta hau gado tana aikin kukan bakin ciki,ta danne xuciyarta ta zubar da ajinta na mace ta kai masa kanta shi kuma ya nuna banza wofi ma ta fita,to daga yau duk abinda zaiyi yaje yayi tayi,ganinta ma bazai kara ba, hakance kuwa ta kasance,domin tun daga ranar Bily ta shiga kulli kurciya tsakaninta da Yarima in yana gidan bata fitowa har sai ya fita,dama tasan shi dan ka鈥榠da ne,lokutan fitarsa dana dawowa ahaka suka kwashe sati uku bai sata a idanunsa ba,tun baya damuwa har ranar ya zauna ya yini,amma bata fito ba,ya tambayi madam dora tace tana fitowa sometimes ita ko duk ta mika lamuranta ga Allah,daga nafilfili sai addu鈥榦鈥榠 sai karatun kur鈥榓ni,sai kuma kuka don tunani wani sa鈥榠n gashi yaushe rabon wayarta da kudi bare ma ta kira wani sai dai Mansu tana kiranta.Malam Mamman ya shigo dauke da buhun doya kofar Mamanmu,ya sauke sannan yace Fatima tana daga ciki tace na鈥榓m.Ta fito tana cewa gani Malam,yace ga doya nan ki kasa.Tayi shiru domin duk tsawon xamanta agidannan malam bai taba kawo mata abu wai ta kasa ba,sai dai su Ladiyo su kasa,kuma bata kwasa sai wanda suka kawo mata,wata rana ma tana kallo za鈥榓 kasa din a hanata.yace kinyi shiru Fatima,tace malam kabasu kawai su kasa kaga sune masu yara,yace nine dai maigidan ko?Tace kai ne malam.Yace to nace ki raba muku, Fatima ni tsakanina da Allah yanzun na gane kuskurena,kadaki zata zanci gaba da muzguna miki ne,nidai afuwarki nake nema.Mama tayi dan murmushi,sannan tace dama ni ban rike kaba malam,na sani duk abinda bawa keyi mara kyau dole lokacin nadama zaizo,ko yayi nadamar mara amfani ko kuma yayi ta lokaci bai kure masa ba.Yace nasan dana ke mai hakuri ce Fatima na gode don haka ki kasa kurum nina fita.Tace to sai ka dawo malam,haka ta kasa doyan su masu yara tasa musu kashi bibbiyu ita ko ta dauki daya,har kofar dakin Ladiyo taje tace Ladiyo kuzo ku kwashi doya gata da malam ya kawo ai fa nan suka fito cike da masifa baki nayi duwawu nayi,su za鈥榓yi ma salo da iyayi?Da itace mai rabawa? Tace malam ne nima yace in raba.Nan sukayi wata shewa,鈥淗e!!! Lallai samun sarari tusar asuba,wannan kinibibin na malam ya isa haka don bamu taba nuna masa bacin ranmu akan sauyin halin daya yi mana ba,Karima tace ai kwadayi ne ba wani abu ba,don 鈥榶arta ta auri dan sarki.Salame ta amshe da cewa,aikin banza da wannan auren ba gara babu ba,daga malam din har ita uwar 鈥榶ar ai ba abasu wata daraja ba,don ko da an basu da yanzun mu gani akasa.Ladiyo tayi shewa,sannan tace fadi ki kara inda za鈥榓 tsare angon da bindiga bazai ce ga surukansa ba.Daidai nan malam ya shigo,yana tsaye suka cigaba da fadin don haka mu yanzu babu wani salon da za鈥榓yi mana,munsan komai. Karima tace,tallarta fa akayi,matar cushe ko bata kwarjini.Malam yace ai tallar hoton ma hanya ce,haka nan in an tallata wani an siya wani ko kyauta aka bada babu mai amsa,in ma kuna masifa kan doya ne,nine nan nace ta kasa,in bakwa ci ku barta yanzu na dawo cikin hankalina,in ma da kun min asiri ne to ya karye,鈥榶an bakin ciki,da hassada,ahaka zaku gama rayuwarku a tsiyace,ita ko kuna mata bakin ciki tana kara gaba.Mama ta dubi malam tace yi hakuri malam,jeka abinka.Nan ko ya juya itama ta nufi daki,su ko sun kasa magana don mamaki. Ladiyo tace yau mun shiga uku da makirci,(ta kwaikwayi muryar Mama)tace har da cewa wai yi hakuri malam,kuji makirci.Salame tace eh tana kuma cewa ya tafi ya ko juya.Ladiyo tace yanda na tsani matar nan da in na kashe ta babu hukunci da tuni na daba ma shegiya wuka,amma duk da haka sai nasa an sabautata.Haka dai suka yi ta surutansu ta inda suke shiga bata nan suke fita ba har suka gaji suka bari. Bily tana zaune tana karyawa akitchen,sai taji anata doko sallama, mamaki taji domin ta manta rabonda taji anyi sallama.Da sauri ta fito don tasan ba Yarima bane,ga mamakinta sai taga Magaji.Murna sosai tayi da ganinsa,sannu da hanya kai kadai ne?Yace wallahi ni kadai ne na kawo ziyarar bazata,ina maigidan?Tace yana makaranta,zauna bari na kawo maka abin kari karfe biyu saura,lallai ku 鈥榶an gayu ne ni dai na karya acikin jirgi sai dai abani na rana mai gishiri.

[4:45AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 58 馃彽


Suka yi dariya taja jakarsa ta kai dakin Yarima sannan tazo ta soma dafa masa taliya,shi kuma ya mike don yin sallah.Suna gun cin abinci ne yake tambayarta shin ko abokina ya canza?Bily bazata iya boyewa Magaji ba,don tasan shi mai gyarawa ne a kowane lokaci,don haka sai tace ya dai canza kila nan gaba,tacigaba Magaji bazan baka aboye ba,ina nadamar zamana da Yarima,munanan halayensa sunyi yawa.Yarima mazinaci ne kuma mashayi.Magaji ya mike tsaye tare da dafa kirjinsa yace,innalillahi wa鈥榠nna ilaihir raji鈥榰n!Me Yarima yake sha?Tace giya.Zufa ta soma tsattsafowa Magaji,yace a ina yake sha? Tace kana duba kowane fridge na gidannan zaka gani.Ya soma dana kitchen,duk jus ya gani sannan ya koma na daki nan ma bai gani ba ya dawo yace,ban gani ba.ta mike ta ciro masa kwalba daya na jus,tace wannan ba ita bace?Magaji yayi ajiyar zuciya sannan yayi murmushi ya mika mata,gashi ki karanta. Zama tayi ta karanta rubutun dake jikin kwalbar tare da ganin nau鈥榠n 鈥榶ayan itatuwan da aka hada jus din dasu,sannan sun rubuta cewa babu giya aciki.Kunya taji kuma ba boye-boye tace,niban san irin wadannan jus din ba,kuma ban karanta ba,amma ai ahaka za鈥榓ce giya ce ko?Magaji yace ga wanda bai sani ba?Ni nasan Yarima baya shan komai na maye,sai dai batun mata yana dan tabawa,kuma zuwa yanzun da kika zo ya dace ace matsayinki na mace kinyi duk yanda zakiyi kin rabasa dasu,tayi murmushi tace Magaji kenan kana yi kamar baka san Yarima ba.Yaushe ya bani darajar yin haka?Ba sai ya maida ni mutum ba sannan zai kula ni,har ma na hana sa abinda yayi niyya?Ni tsoronsa ma nake ji, kai atakaice ma ni nafi karfin wata uku ban gansa da idanuna ba.Yace ba gidan yake kwana ba?Tace anan yake kwana mana, kuma duk 鈥榶anmatansa nan gidan suke zuwa wai da rashin tsoron Allah irin na Yarima har da mata biyu yake kwana?Shine dalilina na kaura ce ma ganin wannan bakin cikin.Ta soma hawaye,Magaji ka taimake ni Yarima ya sakeni,yanzu haka rabona dana gaisa da mahaifiyata na dade banda kati banda kudi kullum tana raina ni ina nan cikin bakin ciki bazan iya ba.Magaji yace kiyi hakuri wata rana sai labari,gidansu Yarima ba鈥榓 saki inba kin aikata wani mummunan laifi bane kamar zina,Allah ya kiyaye shine za鈥榓yi saki,yanzun yana sakinki abinda kowa zai dauka kin aikata kenan.Sai dai kiyi hakuri sauki yana nan zuwa bada jimawa ba,wata rana sai kince ma Yarima ya fita sannan zai fita.Magaji ya fada cike da tsokana tace tabdijam,Yarima ne mace zata juyashi?Lallai kuwa kace wata rana jaki zaiyi kaho.Magaji yayi 鈥榶ar dariya sannan yace,ai gara kema da tawa matsalar. Ta dubesa me ya sameka?Yace ai kin san Sumayya ko?Kanwar su Faruk mijin kawarki? Tace na santa,yace ita nake so tamkar in mutu, ita kuma bata sona wani daban take so,ta gaya min na kasa hakuri.Bily ta tuno hirar dataji Sumayya suna yi lokacin da Mansu ta haihu,sai tayi murmushi tace,nasan Sumayya Yarima take so.Magaji yace yaya akayi kika sani?Tace sun taba hirar a gabana ita da 鈥榶an uwanta.Magaji yace,to yanzu na rasa inda zansa kaina,kwanaki ta zo Bauchi gidan anty Salma ta sauka in naje bata fitowa,sai dai Momy 鈥榶ar gidan Salman ce ke fitowa tana bani hakuri.Bily tace, ni dai nawa ganin kayi ta addu鈥榓,amma ka barta zaifi inko kaci gaba da naci zaka yi ta shan wulakanci,don ko na lura tayi zurfi a son Yarima. Shiru Magaji yayi yana auna yanda za鈥榓yi ya rabu da ita,shin wane hali zai shiga?Yace to zan kwatanta, kuma a nata gefen ma bazata samu abinda take so ba,don Yarima bashi da ra鈥榓yin aje mace biyu.Bily tace ko ma ta nace ta auresa me zata tsinta gidan Yarima in banda bakin ciki?Magaji yace ai kuma baki sani ba,ita tunda tana sonsa zatayi duk yanda zata samo kansa,kinsan namiji shi tamkar yarone wani sa鈥榠n ballantana Yarima mai son matan tsiya, shi yasa nace kema inda zaki rike masa wuta tsaf zaki samo sa.Bily tace ba irinsu Yarima bane,shifa wani irin hali garesa duk da ba dogon zama nayi dashi ba na lura da halayyarsa,sannan ko 鈥榶anmatansa kar kaga yanda yake gara su. Magaji yace Yarima kenan,ni dai hakuri kurum zan baki wata rana komai zai canza,tace to Allah ya kawo mana sauyi na alkairi,yace amin Yarima ya shigo gidan kusan biyar na yamma kamar cikin mafarki yaga Magaji,cikin dariya yace,waton ni har yau ba za鈥榓 daina min zuwan bazata ba ko?Magaji yace sai ranar da ka soma hankali,Yarima yace na gode.Ya shiga dakinsa bayan sunyi sallar isha鈥榠 ne kusan karfe takwas saura Yarima da Magaji suna zaune a wani gurin shakatawa hasken fitilu tamkar rana kowa yana abinda yake so mata kuwa suna ta shawagi ko Yarima zai taya amma yaki ko da kallonsu.Magaji ya dubi Yarima yace,abin na bani mamaki,na me fa?Inji Yarima,yana magana yana danna waya.Yanda mata ko ina ka shiga suke sonka kamar kafi sauran maza.Yarima yayi murmushi to kai me ka gani?Shine ai nake son jin dalili,Yarima yace dalilin kenan, nima ina sonsu. Magaji yace to ai ban gani a goshinka an rubuta Yarima mai son mata ba,sannan in kun hadu bakai ne ke kallonsu ba,sune ke kallonka. Yarima dariya ce sosai ta rike shi yace wannan daga Allah ne,Magaji shima ya dara,sannan yace muyi zancan daya kawo ni garin nan.Yarima ya gyara zama,ina jinka magaji yaci gaba da cewa,Umma ta damu nata ganin ba kwa zaman lafiya da matarka, dalilinta shine duk sanda ta bugo waya ka dauka sai kace kana makaranta in kuma Bily ta kira sai tace ka fita in ko da daddare ne sai kace tayi bacci,shine tace inzo in duba,shi ko mai martaba da bai san abinda ke faruwa ba,yace ne in har tana da matsala to ka kawo ta gida a kula da ita,kadai gane matsalar ko?In baka gane ba yana nufin ciki.Yarima yayi dariya sannan yace,old man kenan,shi yanzun har yana sa ran zan haihu nan kusa?Ya taba baki gami da girgiza kai dubeni fa Magaji am still young,just 24yrs,sannan ace ina da yaro haba mana,Magaji yace to batun Umma fa tana son sanin kalar zaman da kuke yi,yace ka samu matar gidan mana ba kuna shiri ba,nasan zata gaya maka.Magaji yace,tsoronka ya hanata fitowa,sannan abubuwan da kakeyi sun saba ma shari鈥榓 har cikin gida kake shiga da matan banza?Yarima yace ok ta gaya maka kenan? Eh.Inji Magaji, gaskiya ka canza tsari,Yarima yace nidai kace ma Umma muna zaman lafiya shikenan.

[4:46AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 59 馃彽


Magaji yace ai baka isa inyi karya ba,alhalin kai ba akan gaskiya kake ba,ce mata zanyi ka hanata fitowa,mata kake kawowa ka dai san zan iya ko? Dama ita bata san iskancin da kakeyi anan ba,to inna koma zaka sani.Yarima yace to me zan mata?Ita ke kulle kanta zan ta binta ne?Magaji yace,ni dai leken asiri aka kawoni,duk abinda idanuna suka gani kaji na rantse maka shi zan fada,shiru Yarima yayi yasan tsaf Magaji zaya aikata hakan.Don haka suna shigowa gida ya shiga toilet,bayan yayi wanka sannan yayi ma duka 鈥榶anmatansa waya cewa kada wacce tazo gidansa har sai shi da kansa ya nemeta,yana fitowa ya samu Magaji kwance share-share a gadonsa,ya kalli Magaji zamu tuna da kenan, na me?Inji Magajin,na kwana gado daya,sai kace baka da mata?Ko kuma ka kwana a falo ince falo kake kwana,wallahi har ma da sharri inba sai na hada maka ba kace shege nake,in kana son tsira da mutunci to har in tafi in ta ganin zaman lafiya.Yarima yace amma dai kasan ba鈥榓 tursasa ni ko?Magaji yace, nima ai bance dole ba, inna so in maka mugunta ai zance nazo dubaku ne kawai,inga abinda na gani inje in fada.Yarima bai kara magana ba,ya saka kayan bacci ya fita.Ya kai kusan daya saura afalo sannan ya tashi ahankali ya nufi dakin Bily,bai zaci yana tura kofar zata bude ba,amma ga mamakinsa yana turawa ta bude,ya shiga.Kamshi ne ya soma yi masa sallama,ya maida kofar ya kulle,idanunsa masu girman nan ya zuba mata,tana sanye da fara kal din rigar bacci mai yala-yala ta kwanta rigingine.Rigar ta dan zame daga kirjinta,haka nan cinyarta duk tana waje wato rigar taja sama.Ya kafa ma santala-santalan cinyoyinta ido,ya dubi lebunanta ya dan rumtse ido ya bude, numfashinsa yana fita da sauri ya kasa daurewa ya isa gaban gadon ya duka daf da fuskarta,sai wata zuciyar tace masa inta farka fa?Nan take ya mike ya fita kai kawo yakeyi acikin falon 鈥榶an mazan taka ta motsa,ita kurum yake gani ya kasa ya kuma komawa ya kalleta shigarsa ta uku lokacin kusan karfe uku da rabi ya samu ta farka kenan,nan take ta firgita da ganinsa ya dake ya shiga yamutsa fuska sai kace yaga kashi. Yace na lura Magaji an turosa leken asirin irin zaman da mukeyi ne,don haka zan daure inci gaba da kwana nan har ya tafi. Bily tace ba damuwa,ni zan koma falo ko toilet,ya dubeta cikin mamaki amma sai ya boye mamakin nasa yace,ai sai dai ki koma toilet din domin kwananki afalo ba zai yiwu ba,tasan zai iya cewa haka don ba kaunarta yake na,ta mike zata nufi toilet yace ke dawo,ta dawo koma gadonki ni na zauna anan ya nufi can gefe ta dauko bargo da filo ta mika masa yace no barsu ma haka ma is ok,duk su biyun babu wanda yayi bacci ita sai juyi shi kuma yana aikin kallonta,dan baccin daya dauke shine ya samu nasarar yin mafarkin yana saduwa da ita,don haka dole da asubahi sai da yayi wanka sannan yayi sallah.Duk satin Magaji na kula da Yarima,ya zama lazy shi kansa Yarima baisan me yasa sa kasala ba,amma zuciyarsa tana gaya masa matsananciyar sha鈥榓war Bily ce ke damunsa, kullum dakin yake kwana azaune.Magaji yaso tayi amfani da wannan damar ta shawo kan Yarima amma sai ta shiga nesanta kanta dashi,ta hanyar kwana da kayan jikinta yanda baya shiga harkarta ko ya shigo dakin itama bata kulasa,sai dai yakan kira 鈥榶anmatansa awaya cikin dare suyi ta hirar banza.Satin Magaji daya ya soma shirin tafiya,randa ya cika kwana tara ya tafi bayan ya kara yiwa Bily nasiha,tare da jama Yarima kunne.Sun koma 鈥榶ar gidan jiya na wasan boyo,sai dai dan canjin da aka samu, Yarima ya daina shigo da mata gidan sai dai suje Hotel.Sati biyu da tafiyar Magaji,kusan sha daya na safe Bily ta fito tasan kamar yanzun Yarima ya tafi school ta fito tana sanye da rigar bacci light blue,鈥榶ar daidai jikinta ce rigar don haka tabi jikinta ta lafe ta fito tana hamma nan tsakiyar falo tayi mika tsayawa tayi tana kallon wani fim da akeyi cikin talabijin,jefi-jefi kuma tana mika saboda duk jikinta ciwo yake mata.Yarima wanda yayi mantuwar littafinsa ya dawo don ya dauka,tsaf ya tsaya yana ta kallonta yanda take mika shine ya burgesa,ya kwadaitar dashi har ma yasha alwashin yau zai ajiye wannan zafin kan nasa ya sauke ma kansa wannan damuwar ya huta. Bily hankalinta ya tafi ga kallo bata san yazo dafda ita ba,kai bata ma san ya shigo gidanba,tayi dan tsaki aranta ta raya yinwa take ji bari ta dauko abinci tazo ta zauna tayi kallon, wucewar da zatayi kawai sai taji an rike mata hannu cikin tsananin tsoro ta waigo tareda cewa, innalillahi wa鈥榠nna ilaihir raji鈥榰n,Yarima ta gani ya zuba mata manyan idanunsa ta bata rai shi kuma ya daure fuska,taja hannunta alamar kwacewa, ya janyota zuwa jikinsa ta fado kan kirjinsa,matse ta yayi gam har sai data yi 鈥榶ar kara, yace likitoci suna cewa in mace bata da yinwa ko bacci kaga tana mika bata bukatar komai sai namiji,y yaci gaba da cewa,bani da yanda zanyi tunda an daura min ke dole ne duk sanda na ganki cikin wannan feeling in biya miki bukatarki,amma ba wai don sona ba.Bily tace wannan kuma kai ta shafa, nidai nan daka ganni bana bukatar komai daga gareka,yasa hannu ya dago fuskarta yatsunsa yasa ya matse mata baki har taji tamkar ta saki fitsari,yace kina nufin karya na miki?Yasa bakinsa ya tsotsi lebenta na kasa,sannan ya saki mata baki tasa bayan hannu ta share bakinta sannan tace,duk ma likitan daya ce maka in mace na mika namiji take bukata ta gefena bai karanta daidaiba, ka hada bakinka dana kowace banza sannan kazo kasa min?Yace ni duk me zanyi danke zanyi kada kiyi ta shiga damuwa amma kema kinsan baki kai kwatan matan da nake hulda dasu ba,tace wannan fa ni ba damuwata bace,nidai sake ni na wuce.Ya saketa,daki ta nufa maimakon kitchen da niyar dauko zani ta daura,sai dai tana shiga ta nufi gurin daukar zani tana daukowa ta juyo don daurawa sai kawai ganinsa tayi tsaye.Kallonsa kawai ta tsaya tana yi don tama rasa me zatace,ya nuna mata rigarsa da yatsansa,tunda ke zan taimakamawa zoki balle min botiran rigar nan tace cikin fargaba ni dai don Allah ka tafi wallahi bana bukatar komai,ya wani daure fuska zakiyi yanda nace koko sai na miki irin wancan karon,jikinta ne ya dauki bari kayi hakuri don Allah ka barni ya dora yatsansa a leben shi yace shsh!Ya tako zuwa gabanta yayi mata nuni da hannu,ma鈥榓na tayi yanda yace. Ta duba taga ba halin guduwa balle ta gudu

[4:47AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 61馃彽


Duk suna zaune gaban asalin bokansu,Ladiyo ta gyara zama tace,gaskiya boka duk yanda kace muyi haka mukayi amma duk ba wanda yaci,yanzun da haka suna kasashen turawa ita da mijin. Salame tace sannan shima na maigidan munyi kuma yaci amma tamkar ma mun kara masa masifa ne, Karima tace ga 鈥榶ayanmu nan dake gidajan mazajansu suma mun amsar musu duk abinda ya soma tasiri sai kuma ya tsaya.Boka ya dubesu daya bayan-daya sannan yace,ance muku kullum ake kwana agado?Amma dai kun san ba yau muke tare daku ba ko?Sau nawa ina muku aikin yana ci?Duk sukayi shiru,Ladiyo tace to yanzun yaya za鈥榓yi? Yace yanda za鈥榓yi kenan kuje kuyi hakuri danni nan da kuka ganni da zaran mutum yayi min korafin aiki baici ba to aljanu sun daina masa aiki don haka yanzun ku tashi tun kafin su iso keme cikin nan su cire dan su saka miki kwado.ai da gudu suka tattara yanasu-yanasu suka tashi,suna tafe suna jimami har gidan wani malamin,  a takaice ranar yini sukayi garari gidan malamai da bokaye.A hanyarsu ta dawowa suna cikin mota ciwon haihuwa ya kamo Ladiyo suka rasa yanda zasuyi,mai mota yayi parking gefen titi yayi ta masifa yana cewa ku karata can nidai ku saukar min daga motata,in banda bala鈥榠n yawo mace kina da ciki wata tara in banda asibiti ina zaki? Amma ke kin fito shegen gantali ai gara ki haihu a titin kila zai zama darasi ga mata masu shegen yawo irinki,su Karima suna cewa,malam don Allah ka barta taji da damuwarta, shi dai ya sauke su yana cewa ku karata dai. Gyaluluwansu suka cire tare da taimakon wata Bayerabiya suka tare ta har ta haihu,saidai ga maza masu saide-saide a gefen titin ga kuma yara sun taru ta haihu da kyar uwar ta biya,sannan suka rufe jinin da kasa suka nado 鈥榶ar agyalan uwar suka nemi shatar mota duk da babu mai sisi cikinsu sai bayan magariba suka zo gida,lokacin malam mamman yana tsaye kofar gida ransa bace yana son yaga ta ina matannan zasu bullo ne? Karima ce da girki tun safe suka ce zasuje gaisuwar mutuwa har yanzun ga yaran duk yinwa ta ishesu,suna ta kuka,Mamanmu ce ma data gama girki ta zuba ma kananan ta soma sa musu su duka to amma bata yi da yawa ba,don bata san sun fita ba sai da bata ji duriyarsu ba,ta idar da sallar magariba kenan tana tasbihi sai kawai ta jiyo muryar maigidan yana ta zazzaga masifa,yana fadin dukku nemi hanyar gidajanku,badai gidana ba tun safe kuna ina?Yau gari ya waye?Da sauri Mama ta fito ko hijabin bata cire ba,sai taji ashe ma akofar gidane ake diramar,don haka sai tayi waje.Karima da Salame sunyi tsuru-tsuru,malam Mamman nata zabga bala鈥榠,Ladiyo ko tana cikin mota bai ma san ta haihun ba don suna tsayawa yaga sun fito yako hau ruwan bala鈥榠. Mama ta matso tana cewa,lafiya malam duk makota suna jin muryarka? Yace ba dole aji muryata ba,inna yi fada ace na cika masifa,Allah ya hadani da matsiyatan mata,ace macen arziki ta fita gida tun safe tana gantali ita ba ma鈥榓ikaciya ba,ba 鈥榶ar kasuwa ba,yawo kawai shiga nan fita nan?To duk suyi gida dama nina gaji da halinku. Mama tace a鈥榓 malam ka bari kaji uzurinsu mana. Yace basu da wani uzuri, Salame tace malam wallahi muna da uzuri,dai dai nan mai motan ya karaso gurinsu yana cewa,ku bani kudina ina sauri ne,Karima tace malam kaba mai motar nan dari hudu,wallahi Ladiyo ce ta haihu ahanya dalilin dadewarmu kenan,Allah ya tsareni ai ko kudi zasu kasheni bazan baku ba,ai yanzun don wulakanci a titi ta kware gaba ta haihu? Amma Allah ya isa tsakanina daku.Yayi ciki,Mama tace ina Ladiyon?Suka ce gata nan cikin mota,mai mota yace ku bani kudina sannan ku dauke ta na taimaka muku kuna ta bata min lokaci,gashi motata sai karnin jini Allah dana sani da ban taimaka muku ba.Mama tace to ku sallamesa a fito da ita mana.Salame tace,um babu mai ko taro cikinmu, gida Mamanmu ta koma ta dauko dari biyar taba mai motan,sannan aka fito da Ladiyo,suka taimaka mata zuwa cikin gida.Malam yace shifa su fita don yayi musu saki dai-dai,Mama tace haba malam,menene haka? Yace ba ruwanki,ki koma daki kada ki kuma min magana,su fitar min daga gida kawai.Mama ta wuce daki,Salame kuwa ta nufi sashen Gwoggo da kuka.Ta shaida mata cewa malam ya sakesu, gwoggo ta saki butar dake hannunta ta zabga salati saboda me?Inji Gwaggo amarya,saboda munje gaisuwa Ladiyo ta haihu can.Gwaggo tace muje gidan an kada an raya da malam yace dole ne su bar gidan nan yau,haka nan sai yayyansa suka ce to su dai je gidan asan yanda za鈥榓yi,Gwaggo tace ta sani ba haka kawai bane anje ne an kau mata da hankalin da daga kan matansa.Ita ko Mamanmu daya shigo dakinta magana ta shiga yi masa akan cewa ya dawo da matansa don ita bazata iya kula da yara kusan ashirin ba,yace sun cika masa ciki ne amma zai dawo dasu wasa-wasa sunfi sati sannan ya yarda suka dawo,maimakon ya zamar musu darasi,a鈥榓 sai suka shiga tunanin yanda zasu dauki fansa acewarsu Mama ce tayi musu asirin da aka sakesu,don haka itama sai an mata sakin babu ma kamar Ladiyo tace ai gara ku nida na tara uban bashi ina lissafin inna haihu zan dan rage gashi yanzun babu batun suna tunda yace ba wani taron da za鈥榓 masa yasa ma jaririnsa suna dole ne na hakura tunda yanzu an dusashe mana haskenmu daga idanunsa,Salame tace ai ko kun hakura ni sai naga bayan shegiyar matar nan da 鈥榶ayanta.


***************************

 Umma ta dubi anty Salma tace,ke Yariman ne yace miki yana son Sumayya?Anty Salma tace,a鈥榓 Umma Sumayya din ce wai ashe tana sonsa ta kasa fada ashe ma akansa ne taki sauraron samari.Umma tace,to yanzun ai sai ta sauraresu don kinsan Yarima da yaya ma aka samu yayi wannan auren?Don haka tama nemi mijinta inma da yana sonta baya sonta ba, ai daya yi magana, saboda haka kibar ma wannan zancan,ni na mafi son ya nemo matarsa can wani gurin kamar yanda yayi nan itama sai ta nemi mijinta bana son hadin nan su zo su bata mana zumunci,don Yarima bawai yana da dama bane.Anty Salma tace Umma bada wannan da ba asan asalinta ba ni wallahi matar nan ta Yarima bata min ba. Umma tace, karta miki ai badon ke aka aureta ba,don bata miki ba wata tsiyar ce? Bana ma son ta miki.

[4:48AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 60 馃彽 


Ta rumtse idanu sannan ta soma balle masa botiran, shi ko fuskarta ya tsurama idanu,xuciyarsa tana fadin,she is beautiful kwadayin lebunanta ya kamashi ya kasa daurewa,hannu yasa ya kamo fuskarta cikin tsananin zumudi ya manna bakinsa cikin nata.Daga nan komai ya cigaba da wakana,Bily dai tamkar gunki ta zamar masa yayinda shi kuma yake duk yanda yaga dama da ita.Bily wanka takeyi tana kuka,ba wai tasha wuya bane kamar wancan karon,duk da dai taji jiki wannan din ma kukan bakin ciki ne ko na menene ita dai bata sani ba,amma wata zuciyar tana gaya mata cewa kukan rashin mai so ne,ita da dai tana son ta san me yasa maza basa sonta?Ta sani Yarima ba don yana sonta suke zaune ba, yama gaya mata kuma lokaci ya kure mata da jin wannan kalmar ta so daga bakin wani tunda tana da miji yanzun kila ita haka Allah yake son ya ganta ma鈥榓na bai kaddaro ta cikin wadanda zasu samu maza masoya ba.Yarima koda yake kwance cikin bahon wankansa, idanunsa lumshe yana tuno irin halin daya shiga ne lokacin da yake tare da Bily,me yasa yakan fita daga hayyacinsa harma yayi ta surutai,in yana tare da ita?Wanda ko chelen da suke shaye-shaye don nishadinsu shida ita baya samun kansa cikin wannan yanayin,kuma fa wai ma don bada son ran Bilyn bane,in da da son ranta ne zata masa duk abinda su chelen keyi masa yaya zai ji kenan?Tsigar jikinsa ta tashi yarr!A fili yace,kila sai na suma don haka yasa a ransa zaya yi kokari ya gwada yanda zai samu hakan.Ya jima yana tunani kafin daga baya yayi wanka ya fita,yayi mamakin ganin yanda lokaci ya tafi har haka daga yin mantuwa ya dawo dauka shine har kusan awa uku,yayi tsaki kowane lokaci ya bata lokacin sane kan yarinyar nan ce,bai san mutum ya zauna yana tunanin banza ba sai kanta,tun farkon haduwarsu har yau ita kadai ce din dai ke saka sa tunani me yasa?

[4:49AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 64馃彽


Yana gaya mata cewa kada ma ta kama cewar yana da aure karta gayama kowa ma azata gaske ne. Chelen tace to yaya kake da ita? Yace kanwata ce bata son ta ganni da 鈥榶anmata don kinsan addininmu bai yarda ba,tace ai ta yarda ba matarsa bace,tunda ta jima tana zuwa gidan inda matarsa ce tasan da tuntuni zata dauki mataki,yace kin gane ashe.Shi Yarima sam baya so chelen ta kai labarin yana da aure cikin school dinsu,shiyasa yayi haka sam baiyi don ya bata ma Bily rai ba,danne zuciyarsa yayi kawai,ita ko Bily bakin ciki ma ai ba鈥榓 tonawa,ace mijinka ya nuna karuwa ta fika,ko baku son juna ai aure ya wuce wasa,da abin ya isheta da tukuki arai sai ta dauko maganin ciwon zuciya da hawan jini,kai da dukkan wata cuta ma,ta shiga karantawa,wato Alkur鈥榓ni mai girma.Yanzun ta daina zaman dogon tunani,in ranta ya baci Alkur鈥榓ni take dauka sai kaga nan take ta manta da duk wata damuwarta, don Allah kema ki gwada 鈥榶ar uwa,da zaran kin shiga damuwa ki dauko Alkur鈥榓ni ko falaki da nasi kike ta karantawa,sai kinji sanyi aranki in baki manta ba dama shi waraka ne. Yarima ko bayan tafiyar chelen,ya shiga don ya dan watsa ruwa,lokacin sallah ya kusa hankalinsa yana tashe ne,can kasan zuciyarsa tana ta mintsininsa, me yasa zaima beauty haka?Jin damuwa tana son sasa dogon tunani yasashi yin maza ya watsa ruwan, sannan yayi alwala ya fito yana cewa bazai dinga zaman tunani ba,saboda ita amma me yasa kasan zuciyarsa yake mintsininsa? Me yasa zuciyarsa kullum burinta ta ringa kwadaita masa yarinyar? 


Ladiyo ta dubi gefen da Mama take zaune,sannan ta kalli su Karima ta soma magana dubi matar can,sunan 鈥榶arta na gidan sarauta amma kullum fate da rana.Salame tace ke da kike wannan zancan an san da zamansu ne?Har shi malam din da yayi hanyar auren,itama yarinyar tunda akayi auren shiru ko irin tazo din nan.Ladiyo tace ta samu dadi yaushe zata tuna da uwarta? Ai dai ba鈥榓yi dacen haihuwa ba wallahi. Duk Mama tana jin su,yi tayi tamkar bataji ba,aranta tace,oh yaushe rabon ta da faten ma,yau ma malam ne yace ta masa amma da sheri harda cewa kullum fate.

Tana mamakinsu gasu da abin zagi rututu amma sun danne suna zagin wani su da girkin ranar ma sai su debe shekara basuyi ba,ita bata da matsalar abinci,dan ko yaushe ne ma ko sati ba鈥榓yi ba da Mansu tazo ta kawo mata buhun shinkafa,katon din taliya,harda galan man gyada gashi su Sakina da Maryam suna mata aike daidai gwargwado,kuma zancan maigado su daba sa kasar kwana biyu ma basuyi waya ba,ko lafiya?Malam ya katse mata tunani da cewa,hakimi ne ya aiko inzo Fatima,bari inje in dawo.Tace lafiya dai ko?Yace nima ban sani ba,sai dai na dawo. Tace to,ya fita ba tare da musu magana ba,suka soma kwasa dariya suna cewa kila ma 鈥榶ar ce aka sako ta.Ladiyo tace,Allah yasa hakane,da sai na zuba ruwa akasa nasha don dadi.Karima tace,haba dani nan bari dai mu jira dawowarsa. Suka shiga 鈥榶an wake-wake su adole burinsu ya cika.Shiko malam yana isa gurin hakimi ya samu 鈥榶an aike daga Bauchi, mota ce guda shake da kayan abinci zuwa na masarufi,inji mai martaba sirikinsa,鈥榶arsa aka kawo ma mahaifin sirikarsa lokacin da ya iso gida murna dai ta kasa boyuwa,tun daga bakin kofa yake fadin ina Fatima,ga sako daga 鈥榶arki.Nan aka soma shigo da kaya ana kimewa, Mama tace ikon Allah haihuwar 鈥榶a mace mai dadi,yau ga uwar mata tana murna ni Fatima na gode Allah.Ai su Ladiyo sai aka shiga sirarewa ana shiga daki,zuciya fal bakin ciki,hassada ga mai rabo taki ce,haka abin yake. Mama ko cewa malam tayi,wannan kaya shi aka ba,don haka sai ya raba yaba kowace hakkinta, yace a鈥榓 san musu za鈥榓yi,tace ai ba zai yiwu ba,a karshe dole ya amince ya raba musu,sai dai duk da haka sai daya kara mata,sannan ya ware mata wanda zata ba mutane,tayi rabo kam duk sauran sassan ta basu,haka kawayenta Umman Mansu ma takai mata da yawa su Ladiyo ko kunya aka amshe shinkafa har ki ga ana salo gurin dafawa ana ci ana zagin Mama da 鈥榶arta, mutum kenan ba鈥榓 iya masa.Umma tana ta zaton cewa Bily tana da ciki ne,don haka duk sanda sukayi waya da Bilyn sai ta rika ce mata don Allah kada ki biye ma babana da cin zakin nan da shan sanyin nan nasa kinji ko?Bily bata gane ba sai tace,to Umma shima Yarima sai ta riga cewa babana amma gida zata dawo nan gaba ko?Shima bai gane nufinta ba,sai yace dama fa kune kuka matsa sai nazo da ita,duk Umma ta damu har takai ga sanar da mai martaba damuwarta,tace ranka ya dade ina zaton matar Modibbo cikine da ita kuma daga shi har ita babu mai hankali cikinsu kada yaje yayi ta tura mata sanyi azo a haifi dan da sanyi ayi ta fama,mai martaba yace to yanda za鈥榓yi tunda ga azumi yana zuwa,in salla ta kusa sai mu tafi Ummara tare dasu daga can sai mu wuto da ita.Nan Umma taji dadin haka.Abinda yayi mugun bata ran Bily, harma da azumin nan Yarima bai daina kwana da mace ba,al鈥榓marin yayi mugun daga mata hankali, tasan cewa duk wani shaidani yakan aje shedancinsa a cikin wata mai alfarma,wata mai daraja,watan tuba,watan yafiya,watan da Allah yake 鈥榶anta bayinsa,watan lada.Don haka tayi niyar zata yiwa Yarima nasiha koda zai dake tane, shiyasa ma yau tayi nufin zama a falo don yin buda baki.Ya fito dakinsa yana sanye da jallabiya fara tas,yaxo ya nufi dinning bayan ta gama mikewa taji zuciyarta tana karfafa mata gwiwa kan cewa taje ta masa magana,don haka ta isa gurin kallo daya yayi mata ya kauda kai tare da cigaba da buda bakinsa,ta zauna tana fuskantarsa.Nazo ne ina son yin magana da kai,ya dubeta sannan yace 鈥渦mhum. Taci gaba da cewa nazo ne in maka tuni kan wani abu dana san ka sani kila ka manta ne,matsayinka na musulmi bai dace ace cikin watan Ramadan kana aikata alfasha ba,kana zina ka sani duk wani musul.....ke!Ya katse ta da tsawa tare da buga teburin cin abinci har kofin glass ya fado kasa ya fashe,abincin gabansa ya tarwatse,ki shiga taitayinki dani,ni sa鈥榓nki ne? Nace ni abokin wasanki ne?Itama tayi karfin hali ta mike tsaye danna gaya maka gaskiya?Yace bana son ji, ki fita daga idanuna,inba haka ba zan nuna miki waye ne Al鈥榓min.

[4:53AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 65馃彽


Ya daga kyallen tebur din ya watsa mata a jiki ya fita daga gidanma.Tsaye Bily tayi tana tunanin dama Yarima ya iya ihu haka?Allah ya kyauta.Shi kuma tun daga ranar ya bude mata sabon daure fuska,wani bari na zuciyarsa yana zugasa kamar sa Yarima dan sarki wannan zatayi ma wa鈥榓zi? Lallai ta samu sake,duk da cewa kasan zuciyar nan tasa tana masa zogi,tare da hura masa wutar sha鈥榓warta, cikin wannan halin azumi ya kai ashirin mai martaba yace,lallai su zama cikin shiri,Magaji yana nan zuwa su wuce saudi tare,su gobe zasu wuce,don haka su samesu can.Bashi da amsar data wuce to duk da suna karatu,yasan tafiyar bazata shafi karatunsa ba,matsalarsa daya itace mata,zaije ibada ne.Ya tsaya neman mata? Sannan ma zuwan Magaji yau din nan zai sa dole ya hakura da kawo mata,shima gaskiya ba sansa bane kawo matan nan da yakeyi cikin wannan watan,amma da zarar yasha ruwa sai yaji su kurum yake bukata, daren ranar yayi niyyar hakura har sai sun dawo amma bazai iya ba,shida kansa yayi ma chelen waya tazo.Suna tare ne a falo sai ga vicky suna jin haushin juna amma ba sa gwadawa a gaban Yarima,domin sun san sa suna soma 鈥榶an harare-harare zai sallamesu,kila kuma ya zama shine karshen alakarsu,kuma in har kikayi fushi kika tafi,to in zaki shekara nawa sai dai fa ke ki dawo.Shiyasa kullum yake ma kansa kirari baya bin mata sai dai su bi sa.Vicky ta zauna adayan gefen tare da dan tsikarinsa ya dubeta da guntun murmushi,sannan ya duketa a kirji,irin dai wasa na gogaggun matasa.Sun sashi a tsakiya kowace burinta taja ra鈥榓yinsa kanta,suna tayi masa wasanninsu na jan hankali,musamman da yake sun sansa yafi son wasannin fiya da ya kwanta da su don haka sai suka kuke dayi.Sha biyu da rabi Bily ta farka daidai lokacin da take tashi kenan,tunda aka shiga goman karshe tsayiwar dare takeyi har asubahi,in tayi sahur sai ta kwanta bayan tayi sallar asubahi kenan.Don haka inta tashi takan ajiye komanta na sahur ne akusa,kitchen ta fito don nufin dauko ruwan zafi tana fitowa falon sai me zata gani? Yarima ne da matan nan duk basa a hayyacinsu,batasan sanda tace,A鈥榰zu billahi minash shaidanir rajim.Sannan tace haba don Allah haba Yarima,kaji tsoron Allah kana tuna mutuwa kuwa?Kana tuna kabari?Kana tuna ranar da zamu tsaya agaban Ubangijinmu?Watan Ramadan cikin goman karshe kuma karshen goman ma  da duk wani musulmi yake rage bacci,don kwadayin daran nan na (Lailatul kadari)kuka ne yaci karfinta ta juyo da gudu ta koma ta fada kan gado,sai kuka a dhekarun baya ko watannin baya,tayi kuka tayi addu鈥榓 tayi tsayuwar dare duk roko take Allah ya bata mijin aure.Yau ga miji yaro sharaf mai kyau ga ilmi da ake tunkaho dashi a yau ga kudi ga mulki gata cikin daula taci wanda take so tasha kuma wanda take so, amma hakan bai mata rana ba,hakan baisa ta farin ciki ba,zamanta ada gaban iyayanta yafi mata alkairi,zamanta cikin kunci da kiyayyar mahaifinta yafi mata auren Yarima shin dama haka matan da mazansu ke bin mata suke ji?Lallai ta jinjina musu don suna cikin ukuba,jin zuciyarta take tamkar ta fashe don bakin ciki.Shiko Yarima jikinsa ne yayi sanyi,nan take kwadayinsa ya kwanta sannan ya dubi su chelen yace,su tafi cikin daurewar kai suke tambayarsa dalili, tsawa yayi musu tare da cewa su fita mana?Vicky ta mike ta fita abinta, chelen ce ta tsaya son jin me kanwarsa ta gaya masa? Yace ta fita kafin ransa ya baci da ita,haka itama ta figi rigarta ta fita tana gungunai,shiru Yarima yayi azaune tunani ne fal zuciyarsa yasan tuni ta masa amma anasa girman kai yana nufin ita bata isa ta gaya masa ba,nasa ganin ba girmansa bane tayi masa wannan abin ba.Ya mike ya nufi dakinta har lokacin kuka takeyi,kausasa murya yayi yace,ke!Da sauri ta dago tana dubansa,fuskarsa adaure yace,ban hanaki shiga harkata ba?Bance bana son sa ido ba?Ke kin isa ne ki sani nayi abinda banyi niyya ba?To bari kiji karki kuma shiga harkata, nima kaddara ce Allah ya dora min,bata san lokacin da tace daina gaya min kaddara,Allah baya dorama wata rai abinda ba zata iya dauka ba, wannan wani abune daka dorama kanka.

A yau in kaga dama.... saukar marin data ji ne yasa ta dafe kunne,yace ni kike ma ihu?Ni kike gayama magana?Tace bazan gaya maka ba? Kullum ina dana sanin aurenka bazan gushe ba, gara min auren talaka lis wanda sai ya fita yasha wahala ya nemo sannan muci,matsawar ya tsare kansa daga zina nan ya kuma gabza mata wani sabon marin wanda yasa sai da network dinta ya dauke na wucin gadi.Ya nunata in har kina neman zaman lafiyarki to ki cire idanunki daga kaina iyayena ma basu takura min ba balle ke banza wofi kuma yanda kike dana sanin aurena haka nima nake dana sanin ganinki tun farkon ganina dake,kece mutum ta farko data ke min katsalandan arayuwa,bansan tunani ba bansan mugunta ba duk kece sanadi,ban taba marin wani ba ko zagi ke duk kin sani na iya,don haka in kina neman zaman lafiya dani to ki cire idanunki akaina.Kin taba zagina jahili yau kuma kina cemin mazinaci,kece mutum ta farko da kika taba zagina,ko mahaifina lallabani sukeyi,don haka ina gargadinki da babban murya ki fita harakata,in kin manta wanene ni Yarima Al鈥榓min nake,ni daya ne tamkar da dubu agidanmu, dan haka maida hankalinki ya fita.Kai ta kifa taci gaba da kuka wato yanzu duniya babu gaskiya don kawai ta sanar dashi abinda zai amfane sa, shine harda dukanta?Ranar dai kwana tayi tana kuka ko sahur batayi ba.Wayewar ranar ne Magaji yazo shi kansa yayi mamakin ganin yanda fuskar Bily ta kumbura,idanun suma sunyi luhu-luhu ya nemi jin ba鈥榓si tace,ba komai aranar suka gama abubuwansu na tafiya.Ana jibi sallah suka tafi,ko cikin jirgi 鈥榶ar shariya akayi.Magaji da suka zauna guri daya da Yarima yake cewa,kai dama bakaje ba,Yarima yace wai saboda kurewar lokaci? Magaji yace,a鈥榓 bama don haka ba,na gane kana gaba da iyalinka kuma zaka gari mai tsarki.Yarima yace ka barni da yarinyar can 鈥榶ar rainin hankali ce ita,tsaki Magaji yayi tare da cewa Allah dai ya shiryi halinka. Sun hadu dasu Umma da mai martaba gidan da mai martaba ya kama musu nan suka same su.

[4:54AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 66馃彽


Bily ta yarda da zancan Yarima,da yace shi da daya ne tamkar da dubu,domin yanda taga iyayan suka nuna karara son dan nasu suke,haka nan manyan mutane abokan nasa da wasu da suka samu zuwa daga cikin danginsu sai ina ka saka ake dashi.Umma ko sororo tayi lokacin da suka hada idanu da Bily, tasa rai ta ganta tana daga kafa da kyar sai gata tangaran to ko dai karami ne ko kuma yabi jiki?Duk wannan tunanin Umma ne amma tasha alwashin zata tambaye su taji kar dai suna shan kwayoyi ne?Yin wannan tunanin sai da gaban Umma ya fadi tace,inko haka ne sun cucemu.Bayan shan ruwa sunci sun sha ana zaune ana hira kafin lokacin zuwa masallaci,Umma ta dubi Yarima tace,ubana na zaci zanga matar taka da tsohon ciki?Yarima yace,haba dai Umma tun yanzu?Tace kaji shashanci da sai yaushe mu da kullum addu鈥榓rmu muga 鈥榶ayanka,yace dazun ma mai martaba fa cemin yayi wai to kai Modibbo in zamu tafi da matarka zamu wuce inta haihu sai ta dawo,abin ya daure min kai nace ranka ya dade tana da ciki ne?Sai cemin yayi kuji zancan banza, ni zaka tambaya?Suka kwashe da dariya, Umma da Magaji.Yarima murmushi yayi don shi baya kyalkyala dariya.Bily kam sai tayi kasa da kai, Magaji ya mike tare da cewa zo muje masallaci. Yarima yace kwarai muda bamu zo da wuri ba.Suna fita Umma ta dubi Bily wai da gaske ne 鈥榶ar nan baki da komai?Kunya ta rufe Bily,kanta na cikin cinyarta tace,wallahi Umma ba komai,tace ko dai kwaya kike sha ne?Tace Allah bana shan komai,tace ko shine dai ke baki,yace kada ki fada?Don fa karki yarda ki dinga shan kwaya nan gaba ta miki illa,kinga shi namiji ne da zarar yaso 鈥榶aya zai iya karo aure,ke kuma an cuceki. Bily tace,wallahi Umma bama shan komai,to kun taba ganin likita?Cewar Umma,a鈥榓 inji Bily,bamu taba gani ba,tace to wannan ai shirme ne,kafin mubar garinnan sai munje kunga likita. Gurin kwanciya, Bily ta shige gurin Umma dama su Yarima suna can masallaci suma zuwa sha biyu suka nufi masallacin, haka sukayi ta ibada har ranar sallah.

Bily kam ranar data ganta gata ga Ka鈥榓ba,ai addu鈥榓 sai wadda ta manta. Murna kuwa harda hawaye, domin arayuwarta bata taba tunanin yau rana zata zo da zata ganta agaban Ka鈥榓ba ba.A cikin addu鈥榦鈥榠n da Bily tayi ta roki Allah game da aurenta da Yarima,kan cewa in mai shiryiwa ne Allah ya shirya shi sannan ya daidaita tsakaninsu in kuma babu daidaitawa,to Allah ya watsa abin ya kawo mata karshen wahalarta,sannan ta roki Allah ya sassauta ma mahaifiyarta,game da abokan zamanta ya kuma sa mahaifinta ya dawo kan hanya.Ranar sallah mai martaba ya nufo gida,Umma dai ta tsaya sai sunga likita.Daran ranar Yarima ya kasa hakuri da jarabarsa ta motsa,dakin Umma ya shigo Ummar tana toilet sai Bily dake zaune,tana neman layin Mamanmu sun gaisa da kowa amma ta kasa samun Mamanmu ya dubeta ransa ya sake biyawa,amma girman kai ya hanasa yayi mata magana.Har zuwa sanda Umma ta fito,tace yaya ne babana?Ya danyi murmushi sannan ya dubi inda Bily take zaune yace ba komai dama nazo ne nace miki sai da safe. Abinka da manya,nan Umma ta gano nufin dan nata,don haka tace,Bily tashi kije gurin mijinki mana, ni sai naga ma kamar gudunsa kike tunda muka zo banga kina bashi wata kulawa ba.Tana wannan maganar ne bayan fitar Yarima,taci gaba da cewa kin san fa su maza 鈥榶an lallashi ne,suna san kulawa bare irinsu Yarima.Bily tace Umma ba kirana yakeyi ba,Umma tace kaji sokuwa, yanzun yaushe ake jiran kiran miji?Har dai Yarima dan jin kai?To maza tashi ki bishi dama zaman da kukeyi kenan sai yace zo? Tashi-tashi maza-maza kar in sake jin haka.Bily ta mike ranta bace zata tafi,Umma tace,haka zaki je ba ko dan saka turare?Bily kam ta cika ne da mamaki,da bata zata haka Umma take ba,kuma sai tana ganin kamar ko san kai ne Umma take nunawa,don dai Yarima danta ne,duk da ta sani Umma tana sonta.Hoda ta murza sannan tasa turare ta saka kayan bacci sannan tasa hijabi ta fita,yana zaune bakin gado ya rasa me ke masa dadi,kamar ya zama kuda ya dauko Bily yake ji. Ta shigo da sallama fuskarta daure, tamkar an jefa shi cikin gidan aljanna haka yaji,harda yin wata ajiyar zuciya,amma don jan aji irin na Yarima sai ya wani daure fuska tare da cewa, lafiya ?Bata yi magana ba,ta zauna can gefe kan kafet,kin shigo min daki kina ta wani daure-dauren fuska bayan ban kira ki ba.Shiru dai ta masa,yace ok,in baki da magana tashi ki kama gabanki.Ga mamamkinsa sai yaga ta mike zata fita,yasha gabanta, ai bazaki fita ba har sai naji dalilin zuwanki. Bily ta dubesa, Umma tace inzo,oh shine dan kin raina Ummar zaki koma can ko?Tan ki koma din,ya koma gefen gadonsa ya zauna sannan ya dauko laptop dinsa ya soma kunnawa tana dai tsaye.Ta dawo ta zauna inda ta tashi yaci gaba da tura wani assigment ya jima yana turawa har ya gama,lokacin ta soma gyangyadi yace,ke ta farka idanunta fal bacci yace zo ki kwanta ba don halinki ba,tace nan ma ya isa, yace ke komai sai kin min gaddama,harda kice nan ya isa ance miki ina kalanki ne?Kema gulma ta kawo ki ko da Umma tace ki zo nasan kina son zuwan ko don a sosa miki abinda ke miki kaikayi, bani da yanda zanyi tunda an makala min ke.Mikewa kawai tayi taje ta kwanta, sai daya gama mata wulakanci kala-kala sannan ya shiga yin abinda ransa ke so da ita,jikinsa har bari yakeyi duk da dai yau ma kamar kullum,gim ta masa kamar kullum,haka ma da safe gari yayi haske amma ya fake da cewa kada ta kuma dawo masa yau bari ya sallameta gaba daya,bashi ya barta ba sai da Umma ta kwankwasa musu ita dai ta sani arashin 鈥榶anmatansa ne ya kula ta shiyasa bata jin itama zata sakar masa kanta yanda ta kula yafi bukata, ta aje aranta yanda ta rasa wanda zaice Bily ina sonki,haka ta hakura da jin wannan dadin don a duk lokacin da Yarima yake  kusantar ta zuciyarta tana gaya mata cewa makiynki ne ke son hutawa da ni鈥榠marki,don haka sai taji duk mugayan maganganun da yake gaya mata suna dawo mata,kuma sai taji tana kyamarsa saboda matan da yake hulda dasu, sannan burinsa na taji dashi dadi ba zata ji dashi ba har abada,sai dai yanda suka saba.

[6:28AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 67馃彽


Suna zaune gaban likita sun masa dukkan bayanin daya dace,sannan ya shiga dubasu.likitan ya tabbatar da cewa lafiayarsu lau,sannan ya basu wadansu kwayoyi wai su sha bayan sun dawo gida Umma tace,to su zo suje suyi tsaraba don ita gobe jirginsu zai tashi zuwa Nigeria su kuma sai gobe sannan zasu wuce Malesia tace wallahi Umma naso in biku gida nayi missing din Mamana.Umma tace,me zaki je Nigeria kiyi mijinki yana wata duniyar?Ke dai kiyi hakuri ba shekara mai zuwa bace zai gama ko ta sama ce? Kamar yau ne gurin Allah Mamanki ba kuna waya ba?Tace mu kanyi saboda yawanci sai sanda Mansu taje gidan sannan ta kira ni,Umma tace a鈥榓 bata da waya ne?Tana da shi,inji Bily to ni yaushe rabona da wayata taga kati sai zuwanmu nan da Magaji yasa min,Umma ta kalli Yarima, me kenan babana?Yace to Umma yaya zan mata,ita fa tunda taje tafi karfin tace min tana son kaza,ko na ci ko a na sha bare kati, Umma tace to ke kuma ai wannan hauka ne, keda mijinki?Kusan shekara kin kasa sakin jiki dashi to dawa zaki saki jiki?Ki daina haka kinji ko, gaki kamar kanki a waye?Duk abinda kike so ki masa magana tace,to Umma yace kuma da kanta take abinci amma bazata ce tana son abu kaza ba,madam dora ce ma take gaya min cewa, tana cin taliya shine in sun zo shi cefane sai nace ya siyo mata,Umma tace ta daina haka Bily tace to insha Allahu bazata kara ba, azuciyarta sai mamaki takeyi shin Yarima da gaske ne da zata tambayesa abu zai mata?Tasan kila bazai ba don dai yaga mahaifiyarsa ne kurum.Sun shiga siyayya shagunan larabawa,nan taga mamaki Umma cewa tayi duk me take so ta diba na tsaraba nasu Mamanta ma ta dauka sai ta wuce dasu ta bada akai musu,amma ta kasa daukar komai sai Umma ce ke cewa, dau wannan dau wancan daga karshe ta daukar ma Asma鈥榰 auta dankunne da sarka na gold ita da yarinyar Mansu,sannan ta yiwa Dady tasa haka suka yi ta shiga shaguna suna kashe kudi,Yarima dai ya jidi kananan kaya harda 鈥榶anmatansa yayi ma tsaraba,da Umma tace na Bily ne kai tsaye yace a鈥榓 ya sayawa abokan karatunsa ne,kuma ga mamakin Bily Umma ba tace komai ba.

[6:30AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 68馃彽


Komai me lokaci yana da iyaka,su Yarima anyi jarabawa cikin nasara an gamata a sa鈥榓,ya zama cikakken likitan mata gwani,Doctor.Ana gobe za鈥榓 tabbatar musu da zamansu likitoci,su Magaji suka iso tare da mai martaba,da kuma wasu daga cikin yayyansa,tunda Umma ta sanarda Bily zuwan bakin nasu,suka je kasuwa don shirin tarbar bakin,sun kammala komai,sannan bakin suka iso.Su anty Fulera sai 鈥榶an harare-harare akeyi,Bily dai ta kula da take-takensu amma ta share ita farin cikinta daya, kammala karatun Yarima zata gida taga Mamanta da 鈥榶an uwanta,ranar rantsar da likitocin rana ce mai mahimmanci gurin Yarima da mahaifinsa guri yayi guri,manyan mutane daga nahiyoyi sun halarta. Yarima shine dalibi mafi kwazo cikin daliban da suka hattama karatun,don haka hukumar ilmi ta kasar ta bashi lamba ta farko data yabo sannan ta bashi dama ya zabi duk kasar da yake so cikin jerin kasashe goma don yin wani course na daban har na tsawon shekara daya ko biyu,wannan nasara da Yarima ya samu tasa shi farin ciki shida masoyansa,sun shirya 鈥榶ar kwarya-kwaryar party shi da abokansa. Can gida kuma suma suna tasu walimar.Mai martaba dai yana can masaukinsa,tun ranar suka so,a nade kaya farin ciki gurin Bily ba鈥榓 magana, a daren ana gobe zasu dawo gida Yarima an samu nutsuwa,tunanin shi daya inya koma gida babu mata kenan, Allah sarki,Ashly yarinyar da suka hadu babu dadewa tana masifar ji dashi, shiyasa ma yake matukar sonta don shi yana son akula dashi,ko bai sallama da kowa ba dole ne yayi sallama da ita,suna hira ne da 鈥榶an uwansa amma ya mike can gefe ya kirata ya kuma sanar da ita cewa su hadu guri kaza. Ashly irin black american din nan ce,tana da tsawo da kiba,amma kibar ta a mazaunai ne da kuma kirjinta,tana son Yarima musamman data fahimci shi mai sha鈥榓wa ne,tana matsa shi sosai kuma ba tsararsa bace,zata girmesa,kafin yaje gurin ta rigasa,sun lalace son ransu sannan ya tile mata kudi sukayi sallama,kuma ya mata alkawarin indai ya ga da sarari zai mata kwatance tazo Nigeria itama harda kuka,nan Yarima ya kara susucewa danshi yana so yaga mace ta mutu kansa. Sanda ya dawo suna ta hira da Bily,yana shigowa ta kallesa ta kauda kai tasan me yaje yay,haka nan Magaji.Washegari suka hau jirgi sai gida.  Abuja suka sauka,Bily tana shakar iskar kasarta sai taji tamkar an sakata cikin gidan aljanna,nan suka hau wani jirgin zuwa Kaduna,Bily taji tamkar ta sauka zaria lokacin da suka dauki hanyar Bauchi. Lifaya sosai aka shirya musu,sunci sun sha ana ta hira ita dai Umma damuwarta rashin ganin Bily da tsini agaba,haka sauran kishiyoyin Umma sai da sukace amare har yau anata amarcin tukunna?Anty Fatima tace,mu bama son wani amarci,鈥榶aya muke bukata,mun gaji da sai dai aci ayi kashi.Umma tace kadaku matsa mata, haihuwa aita Allah ce,ni damuwata ma ko kiba banga ta kara ba 鈥榶ar tawa. Anty Saliha tace, amma Umma aita murje,dibi yanda fatarta ke sheki,sai kace tarwada?Bily dai tana jinsu,ita dai matsalarta daya tana son ganin Mamanta,zata gwada tambayar Yarima ta gani ko zai barta?Da safe ta shiga gurinsa ta samesa zaune yana kallon(BBC)ta zauna dan kusa dashi tace ina kwana?Ya dubeta dama kin iya gaisuwa?Tace to inna gaishe kane baka amsawa,ya dan taba baki tare da cewa,kina bukatar wani taimako ne?Tace,em dama ina wannan ne ya dubeta kiyi magana bana son kwana-kwana,tace ina son naje naga mahaifiyata ne,yace yaushe?Tace duk sanda kace,yace shikenan kije sai sanda nace din,tace to yaushe? Yace bana son naci ki jirani tukunna,tace shikenan ta mike ta fita.Satin duk bata da sukuni ba ta zuwa sasan shi shima baya nemanta duk da yana bukatarta,jin shiru ne yasa ta sake nemansa taje da dare baya nan da safe zata shiga kenan tazo falonsa na kasa sai gashi ya sauko tayi sauri tace,ina kwana?Ya amsa da lafiya, zai wuce tace gurinka fa nazo,ya tsaya sannan ya juyo yana kallon lebunanta da matsala ne?Maganar zuwa gida kaga tunda nazo ban taba zuwa ba ka dubi tsawon lokacin?Ya soma tafiya da cewa duk sanda kikaga ya dace sai ki sanar dani,tasha gabansa da sauri yau ko gobe,yace fine ya fita ta tsaya shiru ko dai gatse yake mata?Kai takan rasa gane hali irinna Yrm,shi kullum ana tarasa nan yana botsewa data shiga gurin Umma suka gaisa ta sanar da Umma cewa tana son zataje gida don taga mahaifiyarta,kuma ta sanarda Yrm yace ko yau ko gobe,Umma tace sai dai goben don sai an sanarda mai martaba,tace to data shiga dakinta murna harda tsalle,sai kace karamar yarinya.Ta kira Mansu ta shaida mata cewa gobe tana zuwa,ta kira su Maryam da Sakina duk ta sanar dasu,ta kira Mama tace gobe tana hanya,Mama tafi kowa murnar zuwan Bily,saboda gorin da kishiyoyinta suke mata cewa sukeyi tir da wannan 鈥榶ar ta samu daula ta mant da uwarta,gori harda surukarsu Gwoggo amarya,tace inda kwadayi to da wulakanci,an tura yarinya gidan miji gidan sarauta don kwadayi gashi nan kila ma tana can tana wahala,inba haka ba shekara nawa bata zo ba,kamar an saida ita.haka nan 鈥榶an unguwar akayi ta surutu,wasu ma sai sun hadu a sha鈥榓ni sai kaji sun ce ina amare?Ana can dai,Mama kance um tana can da an dameni batayi aure ba batayi aure ba,yanzun kuma tayi an koma kan bata zuwa indai tana zaune lafiya acikin dakinta ai alhamdulillah, sai kaji mutane ana cewa hakane fa,Mama tana sa tare da cewa insha Allah maigado tazo garin nan sai nace ta shiga duk makotan nan ta gaidasu. Malam ya shigo tace, Malam gobe fa maigado tace tana hanyar zuwa,murmushi ne ya subuce masa cike da fara鈥榓 yace ikon Allah,nidai dama kullum yarinyarnan tana raina,lallai muna da babbar bakuwa,Allah yasa ta iso lafiya,Mama tace amin.Bily daren ranar batayi baccin kirki ba, saboda tsabar murna,tunda duku-duku ta shiga gurin Umma, umman lazimi takeyi don haka gefe ta samu ta zauna bayanta gama suka gaisa,Umma tana murmushi tace,Bily kin kosa kije gida ko? Tayi dariya tare kuma da sunkuyar da kai,Umma tace to kinyi tsaraba ko?Bily tace,sai dai wadda muka yo daga malesia, tace a鈥榓 wannan tayi kadan tunda kila wasu kika gayyade kika sai musu wannan ko ganin gida zaki je,gashi baki taba zuwa ba,sannan gashi kina gidan sarauta,ina Yariman?Tace am yana daki,ta dai fadane don ita yanzun dai bazata ce ga inda yake ba,Umma tace ya dace ma ace tare kuka je dashi,donsu gansa,tunda bai taba zuwa ba

[6:31AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 69馃彽


Bily tace to sai dai inya shigo ki masa magana kiji,Jakadiya ta shigo da sallama,sannan ta zauna ta gaida Umma suka gaisa da Bily,Umma tace Jakadiya a duba cikin store din nan afito min da bandiran zannuwa da kuma shaddodi,tace to ranki ya dade,zamu sha sababbin dinkuna kenan?Umma tace a鈥榓 ba naku bane,Bily ce zata ziyarci mahaifanta. Jakadiya tace, a lallai gimbiya yau sai murna,Umma tace da Yariman ya shigo ai da kunje kuyi ma mai martaba sallama,kafin ta rufe baki sai ga dan halak din nan shikenan ma kuje ta yiwa mai martaba sallama kaima kuma ya dace ace kaje ka gaida surukan naka. Yarima  ya dan ya mutsa fuska sannan yace gaskiya sai wani lokaci Umma,don yanzu ina Busy na shirye shiryen Zan je wani course wanda muke matsalarsa anan Nigeria ma鈥榓na in samu wani horo game da wata cuta wadda babu likitocinta sosai anan gida,Umma tace um Allah ya taimaka,amma ka sallame ta da tsara ba ko?Yace to ai batace min zatayi tsaraba ba,Umma tace to ni nace maka, yanzun ku shiga gurin mai martaba ta masa sallama. Mai martaba yaji dadin wannan ziyarar da zataje, sannan yace ki sanarda mahaifanki duk su biyun zasuje aikin hajji bana,ta shiga godiya,Yarima yana tayata mai martaba yace, babu komai wannan kyautar ya kamata ace tuntuni akayita, kasancewar basa kasar sai abin ya kwanta masa da murnarta take sanarda Umma tana godiya tayi tare da ce ma Yarima babana kadai ji kunya kaine ya dace ace kayi wa surukanka wannan kyautar,Yarima ya mike tare da cewa Umma bari nayi wani aiki cikin computer.Ya fita Umma tace kace dai bari ka gudu baka son fadan gaskiya. Bily tayi shiri sosai ga tsaraba Yarima ko kudi ya zube mata sababbi dal 鈥榶an dari bibbiyu,鈥榶an naira dari,鈥榶an dari biyar zuwa dubu daya,kasa magana tayi ta tsaya kallonsa,yace nace ne ki dauki yanda zai isheki tace ni nafi son ka bani da kanka,yace ni kuma nafi son ki dauka don kina sa Umma tana daukana marowaci,baki tambayeni abu ba yaya zanyi in san kina da bukata?Tace to naga karatu kakeyi shiyasa banason matsa maka, yace wannan ba hujja bace,tunda baki taba ganin don ina dan makaranta yau nace wayyo yaya zanyi bani da kudi ba. Don haka dauka in kika dauka duka ma ba matsala,ya juya zai fita tace,to bari na dauka sai ka wuce dashi cikin kowane dauri ta dauki daya,sannan tayi godiya yace a鈥榓 ki gode ma Allah ya dauki jakarsa ya fita. misalin karfe sha daya su Bily sun dauko hanya ga tsaraba mota guda,farin ciki gurin Bily karki tona yau za鈥榓 ga Mamanmu.Ita ko Mamanmu ba zato sai ga Maryam daga kaduna zuwa jimawa kuma ba sai ga Sakina ba,suna cikin gaggaisawa ne sai ga malam da kaji guda shidda yankakku,yace Fatima gashi ku tashi kuyi azama ku gyarama bakin nan me da me za鈥榓 siyo na cefane?Su Sakina suka fito suna gaidasa tare da cewa,ai ko bari muzo mu kama aikin,cikin fara鈥榓 yake cewa duk yanzu kuke tafe?Yaci gaba sannunku da zuwa,Allah ya shi muku albarka,cikin mamaki suka ce amin,yace kun samu labarin zuwan 鈥榶ar uwar taku ne ko? Suka ce ta kiramu ne ta shaida mana yace to to madalla tunda gaku sai kuyi azama ku shirya musu abinci ko?Ya miko dubu biyu gashi sai kuyi cefane,ya zamana dai an shirya musu girkin mai kyau kan lokaci,suka ce to baba.Mamanmu dai ranta kar,yana tafiya sukace oh abin mamaki yanzu baba kara sonmu yakeyi dibi yanda yake ta rawar jiki,Mamanmu tace to ku addu鈥榓 banza ce 鈥榶ayan nan?Kuna fa gani babu dare babu rana ko yaushe cikin du鈥榓鈥榠 nake.Sakina tace,kuma muma munayi bamu zauna ba,nan suka hau aiki,auta ma ta dawo daga aike itama nan ta hau aikin.Su Ladiyo ko sun ga shigowar malam da kaji don haka suka kafa dandali suka soma tsegumin nasu,karima tace tunda nake gidan nan ban taba ganin malam yazo da ko kaza guda yace a soya ba,sai yau. kodan su Sakina ne ya siyo?Ladiyo tace kince kaza ko kwai ya taba kawowa?Don haka kan kajin nan sai anyi tsiya,inma dansu Sakina ya sawo mu fa da 鈥榶ayanmu suke zuwa me ya taba kawowa suka dafa?Salame tace,bana zaton donsu Sakina ya kawo nafi tunanin wani sabon wulakancin za鈥榓 fara mana don ko ni ashirye nake dan ko daidai za鈥榓 raba kajin nan,nan dai suka kasa suka tsare kowacce tana cika tana batsewa.

[6:32AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 70馃彽


Su ko su Sakina suna ta aikinsu girka wancan dafa wannan soya wannan har suka gama suka share gidan suka gyare dakin auta wato dakin Bily na da suka cire gadon suka shimfida babbar tabarma,suka jera abincin ciki.misalin karfe uku sai gasu Bily sun shigo birnin zazzau,jinta take tamkar anyo mata wahayi cewa an mata gafara.Sai da suka bita masarautar zazzau sannan suka wuto,ita daya ce sai kuyangi biyu Atika da Asabe,dayar motar kuwa dogarawa ne sai tsaraba,tunda suka shigo cikin unguwarsu take ta kalle-kalle,unguwar tana nan yanda ta santa,wasu gidajen sun kara lalacewa, wasu gidajan kuma sun samu gyara,daidai kofar gidansu motoci ne suka tsaya gidansu shima ya kara lalacewa sai dai duk da haka an share kofar gidan tas, yayinda mahaifinta da kannansa da kuma shi kansa mahaifinnata duk suna kofar gida suna ta alwala,nan suka tari su Bily da dogarawa aka bude ma Bily mota ta fito,subhanallahi,ganinta sukayi tamkar ba mutum ba don kyau,ta kara fari fatarta shar,duk da bata kara kiba ba daka ganta kaga hutu,durkusawa tayi tana gaida iyayanta suma kuyanginta haka sukayi, Asabe tana rike da jakarta suka shiga cikin gida, matan gidan suna nan gurin da suke suna sakawa suna kwancewa game da girkin da suka ga anyi an turasa cikin dakin auta,yanzun sun karkata tunaninsu kan cewa kila mazansu ne zasu zo shine akayi wannan girki,Karima na cewa wallahi bari zamuyi sai mazajan sunzo suna cikin cin abincin muje gurin Fatimar mu tada masifa muce sai an bamu hakkinmu, kunga mun kunyata ta gaban surukai.Ladiyo tace don surukai ba sufi surukai ba,namu surukan ko fiya wata ya taba sai musu?Sallamar Bily da kuyanginta ne ta tsaidasu daga hirar da sukeyi,cike da doki ta shigo tana cewa,sannunku Gwaggo,mamaki hade da firgici suka hanasu magana,bata kula ba ita dai burinta tayi arba da Mamanmu,tun kafin ta isa dakin ta soma kiran Mamanmu!Mamanmu!!Su Sakina ne su uku suka fito da gudu suka rungumeta suna oyoyo anty Bilki.Nan take hawayen farin ciki suka soma zubo mata. Mama tana zaune abakin gado cike da fara鈥榓,Bily taje ta zube jikinta Mamanmu tace menene haka?Nan suka zauna aka shiga gaggaisawa,su Asabe ma suka gaishe su daga nan sai dakin auta,nan suka zube suna cin abinci.Dogarawa kuwa sun wuce sallah ne tare da su malam ,suna dawowa yasa suka shiga dakin Sani,nan kofar gida ya shiga ciki ya amso musu nasu girkin.Nan kuma jikinsu Ladiyo yayi sanyi,sunma rasa me zasu tattauna ne akan wadannan mutanan. Mama ta kira auta tazo tace amso kwanukansu Ladiyo azuba musu mana,su Sakina ne da gaddama tun dazun ina cewa su zuba musu suna cewa baza鈥榓 basu ba,auta ta samesu jugun-jugun tace,Mamanmu tace ku bada kwanuka asa muku abinci.Salame ce kurum tayi karfin halin nuna mata kwandon kwanukan ta dauka taje ta kawo musu ta aje su dai suna nan yadda suke.Bily ko bayan sunci sun sha sunyi sallah, sannan tace Mamanmu bari naje gidan Umman Mansu.tace to ki shiga sauran sasan gidannan ku gaisa,duk da nasan sunji kinzo,amma Gwaggon sasa ce kawai ta shigo wajan nan, sannan duk makotan nan ki shiga ku gaisa,tace kash!Gashi kuma ban tambaya ba,amma zan masa waya ko gobe ne sai na shisshiga tare da su Sakina da kuma kuyanginta suka nufi sasan,Asabe na rike da jakarta yayinda Atika take rike da wayoyinta kafinsu wuce sai data shiga dakunan su Gwaggo ladiyo suka gaisa, dukkansu jiki babu laka yaransu kuwa sai kallonta sukeyi nan tace,Asabe ban jakar nan ta ciri bandir din 鈥榶an dari bibbiyu ta mika ma auta,gashi ki raba ma yarannan sunsha alawa.Nan ko suka yance ta suna Asma鈥榰 ni baki bani ba,iyayan suna lekowa suka gani nan kowa ta soma raya abinda zatayi da na 鈥榶ayanta in sun kawo.Ta babban sasa suka fara inda gayyar gidan take,suna ko tsakar gida suna ta labarin zuwanna Bily yaran gidan suna ta bada labarin zuwanta suna cewa taci gayu ga wasu hadaddun motoci masu burgewa,kai kunga masu tsaronta sun rike wasu manyan bulalai, sallamarsu ce ta katse Mairo lokacin da take cewa,uwarsu yau sai ji da kai.Bily ta shigo tare da gayyarta,daki-daki tabi kowa suka gaisa yayinda Asma鈥榰 ta shiga rabawa yaran dari bibbiyun.

Mansu ta kira wayarta, Atika ta miko mata wayar tare da cewa,ranki ya dade an kiraki.Ta amsa ta duba sunan Mansu data gani ne duk ta rude tana cewa mutuniyata kin iso ne?Tace mun kusa na jira dady ne ya taso daga islamiya, tace a鈥榓 aminiyata kina son tafiyar dare,sai kin iso tawan,ki wuce gidan Umma don can zan nufa,tace to sai na karaso,amma fa gidana zaki kwana,ban tambayo ba.Cikin dariya Mansu tace yayi kyau,inna iso aida kawai waya akira itama cikin dariya tace,sai kin iso din,ta kashe ta mikawa Atika,sannan suka cigaba da gaisawa,sai kallonta sukeyi ganinsu salo take musu da iyayi gami kuma da yanga,don haka tana fita suka hau kwatanta yanda take magana.Gurin Gwaggo sasa suka shiga,sun gaisa cikin barkwanci take cewa ina angon namu,shi ba zaizo ba?Bily tace,zaizo yanzun aiki ne yayi masa yawa,daga nan sai gurin kakarsu,wadda tayi wani kici-kici da rai suka shiga suka gaisa,sannan ta soma cewa ke kuma sai yanzu kika ga damar zuwa garin,ance miki aure hauka ne,don kinyi aure shikenan sai ki manta da batun iyaye?Ba鈥榓 tamu kakanni,to da mijin naki kuka zo ko?Tace a鈥榓 mu kadai muka zo shi yana aiki ne,Gwaggo ta turo baki tare da cewa,um ba wani aiki shi dai yace bazai iya zuwa gidan talakawa ba,kila ma ke kanki ba鈥榓 bakin komai kike agurinsa ba,banda haka ace aure shekara nawa amma iyaye ace in mijinki ya gansu bazai sheda su ba?Bily ta mike zata fita,to kin fita mana tunda na dauko batun gaskiya,Bily tace ba haka bane,kwata-kwata yaushe ne ma muka dawo kasar, ai zaizo ne.Gwaggo tace kada ma Allah yasa yazo,wannan ruwansa ne.Sakina ta mike zo muje kinji anty,tunda dai kina zamanki lafia da mijinki kada ma yazo din,Gwaggo tace to shugaban marasa kunya, naci ubanki yanzun ni sa鈥榓rki ce da zaki gaya min magana?Nan dai suka fice suka barta. Bayan sun shiga ko鈥榠na sai kuma suka koma gida inda malam ya samesu dakin Mama sai sannan suka gaisa yace yaya me gidan naki?Yaya iyayan nasa duk dai kuna lafia ko?Tace lafia lau,to yaya gurin Umma fa?Wato kakarta Umman Mamanmu, tace suna nan lafia

[6:34AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 71馃彽


Bayan mun dawo dana yiwa kawu Aminu waya sai gasu sunzo,inna koma zanje, yace to madalla, tsohon nan fa?Tace Modibbo?Yace,eh ,tace shine dai bai jin dadi ban ma samu zuwa ba,sai dai in mun koma yace,to yace Allah yayi muku albarka, tace amin,ta dubi su Asabe tace kuje su bude a fito da kayan nan a shigo dasu,suka ce to ranki ya dade suka fita nan aka soma shigo da kaya ana jibgewa akofar dakin Mamanmu,cikin dakin kuma Bily ta sanarda iyayannta batun zuwansu hajji a bana,in Allah ya yarda,nan suka shiga murna inda su Sakina suka dauki sowa,har mutan gidan suka kara yin tsirmar-tsirmar dama ganin kayan da ake shigowa dasu ya tsinka musu gwiwa,sai kuma sukaji shewa.ikon Allah kenan,Allah mun gode maka cike da farin ciki malam ya fito yana fadin haka.Ladiyo ta tare sa lafiya malam?Yace,hajji zamuje bana nida Fatima, kunji abin Allah ko?Ada ban taba zaton zanje koda filin jirgi ba sai dalilin Bilki, Allah dai ya shiwa yarinyar nan albarka.Ladiyo tace, mu kuma namu sai ka tsine musu ai,yace ke ni yau rana ce ta farin ciki agurina banida lokacinku, sarakaran bakin ciki, komai naku sai kunyi hassada shine dalilin da yasa bakwa yin gaba banzaye kawai.Ya fita yana shaidawa 鈥榶an uwansa,daga nan kuma ya nufi gurin mahaifiyarsa Gwaggo amarya.ita ko Bily cewa su Sakina tayi su zo sukama hanyar dakunansu nan suka ce wallahi anty cewa fa mukayi zamu kwana,daga nan suka nufi gidan Umman Mansu,suna fitowa direba ya taso tace,a鈥榓 koma abinka da kafa zamuje,haka suka ratsa ta tsakiyar layinsu, jefi-jefi tana ganin wadanda ta sani suna gaisawa,har gidansu Umma. Rungumeta Umma tayi tana cewa Hajia Bily maigadon zinari,saukar yaushe?Bily tace yanzun nan,Umma tace kinsha hanya nan suka zauna aka hau hira, basu fi minti sha biyar ba sai ga sallamar Mansu tayi kiba,Bily tace lallai aminiyata,dibi yanda kikayi kiba haka?Ina yarona ta dauki dady tana cewa,yarona ya girma,ta ajiyesa ta kama hannun Sa鈥榓datu tana cewa, Mansu dubi yanda mai sunan Umman Yarima ta zama,Mansu dai kallon Bily takeyi tana cewa na zaci zan ganki da ciki? Bily tace kedai zo muje ciki,ai da hira ta kaure basu san ma lokacin da su Sakina suka tafi ba su kam dai suka yi sallar isha鈥榠,sannan suka nufi gurin Mamanmu sannan ne ta gaisa da Mansu daga nan Mansu ta matsa mata su tafi gidanta ita kanta tana son zuwa gidan Mansu,sai dai fa bata tambayo ba, Mansu tace dauki waya ki kirasa mana.Bily tace,ina ma da numbersa kuwa,ai ni ban taba kiransa awaya ba.Mansu taja tsaki, sannan ta mike taso muje don Allah na kula kema kina bukatar duka,Bily ta mike tana cewa dukan lafiya?Mansu dai tayi gaba tana cewa sai da safe Mamanmu,nan dai Bily ta bita su Asabe kuwa tare da su Sakina suka kwana nan dakin auta.Sai da suka lallaba su dady sukayi bacci sannan suka zube nan kan kafet suka soma labari.Mansu tace wai kawata wane irin zama kukeyi ne ke da Yarima shekara nawa ko bari ko dai kuna shan kwayoyi ne?Bily tace,ko daya yana can gurin matan banza shi yaushe zaizo gare ni bare inyi ciki?In kin gansa gurina to yayi ma 鈥榶anmatan nasa wulakancin daya iya kuma yana jin girman kan ya basu hakuri to nan fa zaki gansa yazo ni kuma in share shi yayi kidansa yayi rawarsa ya kara gaba. Mansu tace ai duk laifinki ne saboda iskanci mata har cikin gida?Bily tace wallahi harda mata biyu yana kwana,kuma da zaki ce laifina yaya kike son nai masa?Mansu tace, Allah in kin nuna baki son ya shigo miki da mace cikin gida dole ne zai bari,Bily tace Mansu da kinsan halin Yarima ba zaki ce haka ba,shi fa mutum ne dan ra鈥榓yin kansa,in yasa kansa abu babu wanda ya isa ya hanasa, ga kuruciya shiyasa bana ma shiga shirginsa,Mansu tace aiko dolenki ki shiga shirginsa, shiyasa nace laifinki ne,aganina da ace kinja shi ajikinki kin nuna masa so kin tattalasa,Allah ko zaibi mata sai dai aboye,ta cigaba da cewa ki tuna kefa mace ce kinada kyau,shi kuma mata yafi so,wallahi zaki iya shan kansa,Bily tace nifa wulakanci ne bana so shi da zaki ga yana wani shasshan kamshi.Mansu tace dubeki sai kace wadda batayi karatu ba,dazun fa cewa kikayi ko number dinsa baki da,Bily tace Allah kedai ina da numb dinsa amma ban taba kiransa ba

[6:35AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 72馃彽


Dubi fa ki gani tafiya nayo ya dace ace ya kirani yaji shin yaya muka sauka?Mansu tace bari kiji.Duk abinda Yarima ya miki ke kika so,sufa maza ayau suke daukar kai saboda suna kallon matan dake yawo a titi kowane haki garesa inba shirka yakeyi ba to kiyi kokarin rike abinki in kin ki na waje su sa rike miki,shawarata gareki lokaci yayi da zaki aje batun so ko rashin so,ki jawo mijinki gareki ki hada da addu鈥榓 sai kiga Allah ya shirya miki shi,batun kice karamin yaro ne bai taso ba,Bily ta katseta da cewa nifa don wadannan matsalolin naso in auri babba mai shekaru wanda sai dai in hakurinne shi zaiyi dani,ya ririta ni amma yanzun duba fa nice zan ririta shi,Mansu tace ke ba gara wani yaron ba yanzu akan wani babban?Manyan nan masu budurwar zuciya kinsan Allah ki kama mijinki,musamman yanzun da babu 鈥榶anmatan a gabansa gashi mai nacin son mace,sannan yanzun duk 鈥榶anmatan nasa basa kusa sai kace ba mace ba?Haka Mansu ta zauna tana tsara ma Bily yanda zatayi tasamu Yarima akarshe tace bani wayarki a kirasa, sai ki nuna masa kin damu dashi.Bily tace,kinsan Allah in kin kirasa kila ma wulakancin zai min.Mansu ta dubo numba din sai taga wai Bily ta rubuta(Y)a numba din tace to kalla fa don Allah,numba din mijinki ne kika rubuta(Y)to me yake nufi?Bily tace(Y)Yarima  kenan,farkon sunansa na doka masa.Mansu ta goge tasa sweetheart,Bily tace su sweetheart anji jiki nan dai Mansu ta kira layin yayi ringing har ya katse ba鈥榓 daga ba,Bily tace kin gani ba? Mansu tace an masa uzuri,ta sake kira nan take ya daga tare da cewa hello wanene?Mansu ta mika mata,nan duk Bily ta daburce lokacin da yake sake cewa wanene?Tace nice,baka ma san me numbar ba ko?Yace,kece wa?Haushi ya kamata tace lallai Yarima to nice Bily matarka,shine saboda tsananin rashin so ko numba na ma baka da ita.Ya gyara zama to ke in banda abinki me numba dinki zatayi min bayan ban taba ganin kin kira ni ba,ko kina nufin sai na ajiye ta cikin phone dina alhali bata da wani amfani gare ni?Yaci gaba da bana yin haka duk numba din dake phone dina masu amfani ne. Nan Bily ta gane laifinta don haka sai tace shikenan zan rika kira sai kayi savin dinta ko? Yace lafia kika kirani?Tace lafia lau na dai kira ne naga kai baka kirani kace yaya muka sauka ba? Yace,to kun sauka lafiya?Ban zaci zaki so kiran nawa ba ai I hope kowa lafia?Tace,lafia lau,yanzun ma ina gidan Mansu ne,nace bari na shaida maka bance zanzo ba kada nayi laifi,yace No,ba wani laifi kina da 鈥榶ancin zuwa duk inda zakije,ni mutum ne wanda yasan 鈥榶ancin dan Adam, tace na gode sai da safe. Ya rigata kashewa ta kalli Mansu wadda itama taji duk abinda suke cewa saboda sun sata a handsfree.tace kin soma gano laifin ki ko?Yaron yasan abinda yakeyi don haka ki gyara takunki da safe ma sake kiransa ki gaishe shi.Bily tace,ni duk komai ina ganinsa banbarakwai ne,anya zan iya?Mansu tace,zaki iya sannan sai ma kinsha gyara zaki bar nan,da kin koma kada kiji kunya ki saki jiki ki jawosa ki mantar dashi matan banza ya zama kafin ma ya koma kin dasa kanki garesa,Bily tace,to Allah yasa zan iya,ni kunya ma nake ji inna tuna shekararmu daya dashi, nan gaba yazo yace yarinya yake so.Mansu tace ai sai kiyi,shin haramunne aurenku?To in baki sani ba bari in sanar dake,Manzon Allah (S.A.W)matarsa ta farko ta girmesa,kuma bazawara ce,shin in haramunne haka zata kasance?Bily tace,a鈥榓 Mansu tace don haka saki jiki ki rike mijinki,Allah ne yasan dalilin zaba miki shi, kuma gata Ubangiji yayi miki sai nan gaba zaki gane,ga lada in kikayi sanadiyar shiriyarsa.Bily ta soma yarda da shawarar Mansu,don haka cikin kwanaki ukun da zatayi sun shirya duk yanda zatayi inta koma ga gyara tasha,ta shirya sosai kuma ta dauri aniyar ba sakaci daga yanzun cikin kwanakin sunyi rabon tsaraba,su Sakina ma sun koma gidajansu cike da tsarabobi masu yawa,su da 鈥榶ayansu har ma da abokan zama,Bily ko ranar da zasu tafi ta kara shiri sosai sauran batu zasuyi shi awaya, itama Mansu haka ta juya Kaduna cike da tsarabar da Bily dinta ta cikata dashi. Tun acikin mota tana kwance zuciyarta ta shiga kai kawon yanda zata jawo Yarima gareta. nan take ta ciro wayarta ta soma neman Yarima,sai ta samu kanta da karya muryarta,lokaci daya dauki wayar yana fadin,hello tace mijina ganinan ina dawowa yayi dan jim,don muryar ta dokeshi,sannan yace,to sai kun iso.Tace kana murna kuwa?Yace to murnar me zanyi,me kike min in kina gidan?Tace la,dama kana son inma wani abu shine baka sani?Yace,au,da sai na saki?Ina ce tun kafin kizo gurina an karanta miki zaman aure?Tai 鈥榶ar dariyar kissa,oh yes,na manta ne yace shikenan yanzun tunda kinje ai sai a tuna miki ko,yacigaba da cewa sai kin iso yanzun ina driving ne,ya kashe wayar.Sun iso daf da magariba ta shiga gurin su Umma suka gaggaisa ta kuma sanarda Umma iyayanta suna godiya kafin suzo an shigo da tsarabar zaria,su kuka ne,kubewa da dai sauransu,tunda kowa da sandar hannunsa yake kai duka.Data koma sasansu kuwa,lokacin an gama share mata ko鈥榠na an goge.tayi wanka ta shirya cikin wani material bulu da ja,tayi kyau bata daura dankwali ba,sai ta daure gashinta da dankwalin.ta nufi sasan Yrm gabanta na faduwa,ta samesa kuwa yana waya da Ashly ta danne zuciyarta har suka gama,ya dubeta fuskarsa kamar kullum, wato gim,ta zauna kusa dashi ta rike hannunsa tana murmushi tace,mun dawo.Ya dubi idanunta kun dawo lafia? Da idanu ta amsa masa tare da daga gira,wani iri yaji ajikinsa, har sai da yayi tsam.ta fito da harshe ta dan lashi lebenta kowa yana gaishe ka.muryarsa ta dan sarke ina amsawa. Ta mike kamar zata fita ya bita da kallo tamkar yace dawo,amma girman kai y hana,sai ta juyo nan take ya wani dauke kai ta dawo, kaci abinci?Kin damu inci ne? Tasa yatsanta daga goshinsa ta biyo dashi takan karan hancinsa har zuwa lebunansa,tana cewa sosai ma,me kake so?Shi kam tuni ya soma sakin layin da yake,don duk jikinsa ya motsu gani yake Bilyn daya sani ce 鈥榶ar kauyen nan mai boye kanta?Ya dai dake yace,na koshi.ta nufi fridge ta dauko jus din dayafi so tazo ta tsiyaya cikin kofi ta mika masa,to sha wannan.

[6:37AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 73馃彽


Ya amsa babu gardama, ganin yanda Yarima bai gwaleta ba shine ya bata karfin gwiwar shige masa,shi kuma ya kasa gwaleta ne don yana cikin bukata sosai,kwanakin duk a matse yake.tace ni ina jin yinwa bari naje naci abinci, kamar yace zaki dawo ne?Amma sai ya share ta fita,koda ta gama cin abincin sai data sha kankana da rake tasha hadaddiyar zumarta, sannan tabi duk gabobinta tasa turare,bata sa komai ba sai rigar bacci shi ko lokacin yayi wanka ya saka rigar bacci ya kasa nutsuwa jinsa yake tamkar ya dauki waya ya kirata.nan take ya samu kansa da addu鈥榓r Allah ya kawota,yana ta kai kawo tsakanin bedroom zuwa falo,kamar daga sama sai ya soma jiyo kamshinta,sai daya shaka sannan ya dan juyo. itan ce cikin rigar bacci ja,yana iya kallon duk abubuwan kallon dake jikinta,wanda nan take ya shiga rudu,har ya kasa dauke idanunsa daga kanta,ganin haka yasa ta gane tarkonta ya hadu,don haka da taje kusa dashi sai ta sassauta murya tace,dama nazo ne in maka sai da safe.yayi ajiyar zuciya,sannan yace to sai da safe.Ta juya zata tafi ya wani dauke numfashinsa, zuciyarsa ta kasa daurewa,nan da nan yayi taku daya na biyu ya riko hannunta ya jawota zuwa kirjinsa,yasa hannu ya dago fuskarta nan take ta bude masa bakinta tare da miko masa harshenta. Cikin doki ya amsa,nan ta tuna Mansu da tace duk abinda yayi miki ki masa, ki nuna kin iya dama can baki son yi masa ne,nan take ta zage gurin son ta burgesa,sai ga Yarima ya kasa tsayiwa sunma kai ga zubewa,da zai yiwu in baku labarin wannan dare da kunsha mamaki,domin Yarima ya samu kansa ne cikin wata duniya mai nisa, ita kanta Bily sai ranar tasan da tayi wauta, duk da suna ikirarin basu son juna.koda suka samu nutsuwa sai Bily ta nemi ta koma dakinta,sai ya dubeta zuciyarsa tana masa fari yana wana sunsunar ta yace,ki kwana anan kinji Beautyna?Yana magana ne yana kallon fuskarta,gira kurum ta daga masa a ran ta tana mamaki lallai Yarima hada sabon suna na samu yau ke nan,don haka sai ya janyota zuwa jikinsa. Safiyar ranar sai gurin goma ta fito daga sasannasa, tana kuma mamakin yanda Yarima ke nan nan da ita,lallai gaskiyar Mansu ne,harda laifinta.Tana sasan su Umma ya shigo yana ta wani shan kamshi,kuyangi na gaisheshi,ita kuwa sai tayi murmushi ya dan saci kallonta,sannan ya zauna ya gaida Umma itama ta gaisheshi ya amsa yana wani daddakewa.Umma tace kunje kun gaida Modibbo kuwa?Yace,a鈥榓 sai da dare,Bily tace inaso ma inje in gaishe da kakata, itama ta danyi fama da ciwon kafa, Umma tace shikenan ai saiku wuce gaba daya,ya mike ya fita.Yinin ranar jinsa yake tamkar wani sabon ango,ya dade yana son ganin ranar da Bily zata amsa gayyatarsa wato ya kusance ta tana so batayi masa tamkar gunki ba,sannan wani abu daya tsaya masa cikin rai shine,yana jin ta fiye da duk matan daya bi duk da kasancewarsu farar fata bai ma san yanda zai kwatanta ta ba.matsalar daya ba wai yana sonta bane,amma banda haka ko ta ina tayi fiye da zatonsa, yana jin zai iya zama da ita tunda shi so ba matsalarsa bane,nasa ganin ma inka dauke son Allah da Manzonsa da son abu tamkar kaga kaya kowani abincin haka kace ina son kaza ka siya to bai yarda da wai soyayya ba.nasa ganin mace da namiji ba wai suna son junansu don komai bane sai don sha鈥榓war su biya ma kansu bukata,amma game da wancan son bai sansa ba,daren ranar ta shirya cikin atamfa super ta dora after dress ta nufi dakinsa yana sanye da shadda mairuwan siminti,tana ta sheki yayi kyau,tace kafi kyau cikin dogayen kaya,yace ni kuma damuna sukeyi ya dubi shigarta,nifa duk irin kayan nan basa birgeni, nafi son wadanda zaki fito a beauty dinki,amma zamu shiga kasuwa in saya miki,tayi murmushi ta dubi kanta kana nufin banyi kyau ba?Yace,a鈥榓 ke kullum kina da kyau ai dan ke mai kyau ce muje ko? Cikin mota suna tafiya yana tuki jefi-jefi kuma idanunsa suna sha鈥榓war kallonta,tace wash!Ya dubeta yaya ne?Tayi kasa da murya ina jin bacci ne,yace kwanta mana,ga mamakinsa sai kurum yajita acinyarsa,nan take kan motar yaso ya kufce masa domin ba kwanciyar kawai tayi ba,sai data kai hannunta wata jihar cikin salo,da sauri ya tsaya gefen titi ya dubeta,kina son mu fadi ko? Tayi dariya,sannan suka dau hanya tace,haka zamuje babu tsaraba?Don haka suka shiga wani super market suka yi shopping Gurin Umma suka soma zuwa,haka kawai yaji tsohuwar ta masa, musamman yanda tayi ta yi ma Bily nasiha kan cewa tayi masa biyayya, shiko ga son girma sai kace gyambo,ya tsani Bily ta nuna ita sa鈥榓rsa ce, daga karshe tayi ta shi musu albarka suka fita suka nufi gurin Modibbo ya samu sauki sai dai jikin girma,nan yaji dadin ganinsu. Ya musu nasiha sosai ya kuma jaddada ma Bily tayi hakuri da mijinta sannan tayi biyayya,don haka suna mota yake cewa,kin dai ji ko鈥榠na ana cewa kimin biyayya,amma ke sai ki dinga nuna kin ma girmeni, tace to da gaske dai ai kasan na girme ka fa yasa bayan hannu babu xato ya buge mata baki ta rike bakinta da hannunta shi kuma ya daure fuska har suka je gida bai kuma ce mata kala ba.Bayan sun isa gida ta dubesa yana sauri ya fita daga motar ta rike masa hannu,sorry nasan kai ne babba don Allah kada kayi fushi kaji mijina?Fita kawai yayi sannan itama ta fito,ta kofar da kai tsaye zata kaisu sasansu suka shiga gida,da kyar ta shawo kansa sannan ta nufi gurinsu Umma ta shaida musu sun dawo, tare da sanar dasu cewa duk suna gaishesu.Cikin satin banda soyewa basa komai,yanzu Yarima bashi da matsala game da mace, domin duk sanda yazo da bukata bata nuna ta gaji,duk kuwa da cewa tana karfin hali ne dan kuwa Yarima namiji ne ba kadan ba Koda sukayi waya da Mansu ta yiwa Mansu complain na cewa Yarima ya like mata tana daurewa ne kawai,Mansu tace ki cigaba har ki saba,sannan idan zamu zo bikinsu Magaji zan zo miki da wani magani in kina amfani dashi kema zaki daina saurin gajiya, yanzun amma baya waya da 鈥榶anmatan nasa ko?Bily tace,tabdi!Yanayi,sai dai ina yin dabara ina kashe wayoyin nasa tun daga ranar da muna tare amma ya amsa wayar wata shegiyar muna kwance fa,wai danayi magana sai ya nuna yafi ni fushi da kyar ma na shawo kansa,tun daga nan dana kula hankalinsa ya soma nisa sai in kashesu.Mansu tace ki dai dage kuma ki daure zanzo miki da wasu sinadaran,Bily tace,to sai kinzo.

[6:37AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 74馃彽


Yarima ya gama komai game da course din nasa,wanda zaiyi Beverly Hills ta kasar America zaiyi course din ne akan gyaran fata,wato(plastic surgery)don yaga cewa bamu da wadannan likitocin anan gida,sai dai ya saita tafiyar tasane bayan bikin amininsa wato Magaji. Zaman Yarima da Bily su kansu yana musu dadi,duk da hakuri kawai takeyi da halinsa na saurin fushi da isa da kuma jin kai,sai dai tana kokari taga ta kauce ma duk wani abu da zaisa suyi sabani,tun daga ranar da suka soma kwana guri daya har yau babu wanda ya kuma tunanin kwana shi kadai,domin hakan yana sasu farin ciki.Daren yau saura kwana shida bikinsu Magaji,Yarima babu zama yi nan yi can,yau ita kuma Bily duk bata jin dadi sai dai tana sharewa ne domin ta fahimci tana da shigar ciki,wanda shi kuma Yarima ba ra鈥榓yinsa kenan ba, in har ya sani zasu yi rigima ne.ta shigo falon Yarima yana zaune yana duba sauran katunan wadanda ba鈥榓 kaisu ga masu su ba,tace sannu da hutawa abokin ango,ya dubeta sai ya ajiye katin, zo kiji,ta isa gurinsa kin kara kyau yau sai dai yaya naji dumin jikinki yafi na kullum?Tace,ko, ya kuma mannata ajikinsa ko kina zazzabi ne? Tace a鈥榓 kalau nake,ya dubi fuskarta muje in sai miki kaya irin na gayu ko?Tace muje to.Wani katon Boutique suka shiga,sam Bily bata ga abinda ya burgeta ba cikin boutique din,shi ko Yarima sai jidar kayan yakeyi yana ayyana yanda zai gansu ajikinta,suka  koma gefen takalma nan ma ya diba haka aka biyo su da kayan ledoji cikin mota,takaici ya cikata babu halin ta nuna yanzun nan ya hau fushi sai dai tana ganin an kusa jin kansu indai ita yake nufi tasa kayan nan.bayan sun iso gida da zumudinsa yace ta gwada kayan,duk wanda ta dago sai ta gansa bingil daga siket din har wandunan rigunan kuwa daga mai hannu daya sai mai hannun singileti,sai wadda sam bata ma da hannu Ta dubesa wai kana nufin ni sZan saka wadannan kayan?Ya murtuke fuska bansani ba,tunda ina da wata matar ne bayan ke?Don rainin wayo zakice ina nufin ke zaki sa?Tace tsaya kaji abin bana fada bane, bazan iya sa kayan nan ba,saboda ka duba gidannan gidane na jama鈥榓 haushi ya turnuke sa yace me ya hana ki sanar dani tun a can,sai da nayi asarar kudina, dakin sani tunda mukaje sai kice kai nifa bazan sa ba, sai kika barni na siya sannan don kin raina min wayo yanzu kice bazaki sa ba,ta tausa murya baka fahimceni bane mijina,nifa saboda mutane ne? Yace to gurinmu da akwai mutane ne?Gaya min wanda yake shigowa nan gefen?Tace masu aiki zuwa su jakadiya,kaga bai dace ba,ransa ya sake baci afusace ya dubeta, shin wai ke harma kin isa mu tsaya ja-in-ja dake?To bari in sanar dake,nine wanda 鈥榶anmata suke son in nuna ina son kaya su sa kudinsu su siya don in gani a jikinsu inji dadi.ya mike tsaye yaci gaba da cewa,amma ke ko baki da burin daya wuce kiga raina na baci,ban san bacin rai ba sai dana hadu dake,please kwashe kayan nan kibar min dakin tun kafin ranki ya kai ga baci,in ma zaki kona ne jeki kona,ke kin gama rainani kin maidani tsaranki,tunda mu sa鈥榓nnin junane koba haka kike cewa ba?Zata sake yin magana yace,fita nace banason jin muryarki. haka ta kwashe kayan ta fita jikinta a sanyaye,shi kuma ransa bace ganinsa ta maidashi mara tunani karamin yaro tunda bai aunaba ya sayi kayan.lokacin kwanciya yanayi tayi shiri ta nufi dakinsa tana zuwa cikin dar-dar baya falo ta shiga bedroom tana shiga yana fitowa daga wanka,wani kallo ya watso mata tareda daga murya gurin cewa me kuma ya kawoki dakina? Sai data zabura sannan tace,yi hakuri ta daure ta nufosa kawona goge maka jikink..fita nace,bana bukatarki babu wata mace data isa in saurareta matsawar bazata min yanda nake so ba,matan waje ma suna min biyayya ballatana matar aurena,wallahi nina sani mata da yawa da zasu samu in auresu ko tsirara nace ina son su min yawo cikin gidana sunsan yanda zasuyi,don haka fita kawai kin bata min rai sannan ynzu kin wani debo jiki dan gani jarababbe ko?

[6:39AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 75馃彽


To ki sani kwanciyar hankali ce take sawa ayi komai,haka Bily ta koma daki ta fada kan gado lallai ta tsokano,shima Yarima koda ya kwanta sai yaji daban,cikin 鈥榶an satukan sun shaku da juna musamman gurin kwanciya.Bily ta mirgina ta janyo filo ta dora akan kirjinta,kewar mijinta ce fal aranta,shima daidai wannan lokacin duk da ransa ya baci amma jikinsa yana maraicinta, hakan zuciyarsa zogi takeyi harma ya soma tunanin ko dai ya dauki waya ya kirata ne?Ya tashi ya zauna tsakiyar gado,ba wai sha鈥榓war tace ta hana masa bacci ba,a鈥榓 zuciyarsa ce daga can kasa take tsananin son ta ganta.ya janyo waya zai kirata sai wata zuciyar ta soma cewa,shin ka yarda ka zubar da ajinka ka kirata?Tayi ma laifi fa?Kuma kaine ka koreta in harka kirata gobe zata iya maka abinda yafi haka tunda tasan ba zaka jure ba zaka sake kiranta.tsaki yayi sannan ya jefar da wayar kan gado,itama duk ta damu sai tana ganin cewa in har biyayyar zatayi me zai hana tayin yanda Yarima ke so, wannan duk laifinta ne yau gata zata kwana ita daya,tana kewar kamshin Yarima ,ranar ko an tafka ruwan sama haka suka kwana jin sanyi duk da bargo da kowannansu ya shiga sannan babu wani bacci sai juye-juye.Oh!    Allah shin me yasa suka damu da juna haka?Da safe bayan Bily tayi wanka,nan ta soma daddaga kayan taga wanne ne ya dan fi dama-dama,tasa dan taje bandaki,shi ko Yarima kosawa yayi lokacin zuwa gaida Umma yayi don yaje gaisheta ko zai ga Bilyn,don zuciyarsa ta daina zugi.Bily koda kyar ta samu wani siket gashi dai har kasa dogo sai dai tsagu tun daga kasa har cinya,sannan rigar bata rufe cibiya ba,kuma daga sama duk kirjinta waje,sannan kuma baya ma kusan rabi awaje ta sama,haka dai ta daure ta saka tare da sa takalmi daya daga ciki mara tudu sosai,hijabi ta dora sannan ta fito,amma kafin ta saka hijabin sai data kalli kanta a madubi tace oh,dubeni sai kace 鈥榶ar iska,ko irin 鈥榶an good evening din nan Tana shigowa falonsa na kasa shi kuma yana sakkowa, zogin da zuciyarsa keyi sai ya tsaya cak,wani sanyi yaji yayinda ya ganta tamkar ya ruga ya rungumeta sai wata zuciyar tace masa yana sai ka nuna mata ka damu?Nan take ya dake sannan yayi nufin fita,da sauri tasha gabansa sannan ta cire hijabin,wani dadi ya rufesa amma sai yasha mur,tace me zaisa ka daure,kalli fa banyi kyau ba ne?Ya kalli kwayar idanunta masu hanasa yayi mata gaddama,yace Beauty kina son ki bani wahala me yasa ko yaushe burinki raina ya baci?In zaki min adalci nima fa dole aka min kamar yanda kema aka miki,amma bana son in matsa miki ke ko kinfi son ki ta bata min.ta dubi fuskarsa na daina duk abinda kake so shi zanyi,yayi ajiyar zuciya sannan yajata zuwa kirjinsa, sai yaji tamkar sun shekara basuga juna bane,harma baisan lokacin da yace I miss you ba,sai dai yaji tace me too Nan suka manne juna,ji suke tamkar su shige cikin juna,ko saboda menene?Oho!Bayaji su kansu sun san dalili.Nan suka nufi falonsa suna manne da juna,sai gashi ranar tare suka karya, har ma Yarima yana tunani aransa cewa dama cin abinci da mace haka yake da birgewa?Duk sanda zaisa abinci a baki sai ya kalli idanun nan nata masu narkar masa da zuciya,tana murmushinta dake kara mishi sanyi cikin zuciya,koda aka jima sai ma ya barcin abincin bai san ya zuba tagumi yana kallonta ba.a zuciyarsa son yake ya gano shinme yasa ita wannan ta fita daban cikin duk matan da yayi harka dasu?Sauran 鈥榶anmatansa baya damuwa in sun samu matsala ko su zo ko kada su dawo ko ajikinsa, sannan duk lokacin daya gama biyan bukatarsa dasu,sukan fitar masa arai,sai dai ya daure amma wannan tunda ya hadu da ita ta sauya masa wasu abubuwan da dama shi ada baisan damuwa ba,baisan tunani ba, kullum yana samun kansa sayau ne,amma sanadinta duk yasan wannan,ga tunaninta gashi baya son tayi nesa dashi,haka nan duk lokacin daya kusanceta, inya samu nutsuwa wani sabon sha鈥榓warta ne ke shigarsa, kullum yana son yaji ta manne cikin kirjinsa,yana bala鈥榠n son dumin jikinta.

[6:39AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 76馃彽


Yanzun ma da suke karyawa jinsa yake tamkar wata rahamace ke sakko masa cikin jiki,ta hura masa iska da bakinta a fuska,sai ya lumshe manyan idanunsa sannan ya budesu kar akan fuskarta tace ka koshi ne?Gira ya daga mata alamar eh.ta mika tafin hannunta ta sakalo nashi ta hada yatsunta da nasa ta matse gam,dim yayi yana jin wani abu yana ratsasa,shin me yasa kullum jikinsa ya hadu da nata sai yaji tamkar ranar suka fara taba juna?Ya mikar da ita tsaye ya zagayo da ita inda yake kan cinyarsa ya dorata, sannan yace jikina ya shaku da naki,tace nima haka har na soma tunanin inka tafi course dinka yaya zanyi?Ta tsura ma fuskarsa idanu,yayi murmushi zanso muje tare,me yasa bamu saba ba alokacin zamanmu a Malesia?Tace kaine kaja sai kayi ta kawo mata bayan gani, yace in kawo su ko su kawo kansu?Kema da kina kawo kanki da mun saba,tace nazo ka min wulakanci ai to mubar wannan zancan,anjima zamu je ki gyara gashinki ko?Nima ina son yin aski duk nayi muni,ta dubesa ni ko bana ganin muninka,ya kwanto da ita kan kafadarsa saboda me?Tace saboda kana da kyau,yayi murmushi. Sallamar Magaji ce kusa dasu tasa suka daga kai yace,tun a bakin kofa nake zuga sallama anyi min shiru,Bily ta soma kokarin silalewa daga jikinsa,ya riketa yana cewa,wane kauyanci kenan?Magaji bakonki ne?Magaji yace yi zamanki,in Allah yaso muma mun kusa shiga wannan ajin. Sunne kai tayi ga kunyar kayan jikinta,gata ganinta da yayi jikin Yarima. magana sukayi akan dinner din ya tafi yana cewa to gimbiya nina wuce tunda yau kam ko gaisuwa babu. Yarima ya mike zo muje daki ki dan danna min bayana,tace da mun gaida Umma mun dawo ko?Ki bari koda yaushe ne ma gaisa,ya zura hannunsa cikin rigarta yana matsar na shanunta tace toh muje. Bikin Magaji ya kacame ranar daurin aure aka kawo amarya,su Mansu kirjin biki,dakin Bily ta yada zango har dasu auta Asma鈥榰 ta biyo Mansu. ranar kuwa aka yi dinner Mansu tayi musu dinkin kayan da zasu saka ita da Bily,da suka shirya gaskiya sun hadu,Mansu ta kalli Bily tace,sai kace kece amarya?Kin tsaru fa. Yarima yana falonsa sun gama shirinsu ya soma kiran layin Beauty kamar yanda ya rubuta cikin wayarsa,amma sai yaji wayar tana ringing nan kusa dashi,ya dauko wayar ya duba sai yaga tasa Sweetheart.ya tsura ma sunan idanu,da gaske ne shi sweetheart dinta ne?Sai kuma ya samu kansa da jin dadin hakan,ya dubi Magaji kaga ita wannan ma anan tabar wayar tata,ina son ince suyi sauri donni bana cikin tsarin nan na African time. Magaji yace hakane, sai gata ma ta shigo, shagala Yarima yayi da kallonta,tayi kyau cikin riga da siket din na wani yadi golden mai walkiya dinkin ya fito da surarta tsan-tsan ga kuma net da aka nada shi dan daidai,takalmi mai tsini ne Magaji yace,gaskiya Bily kada fa kufi amaryata kyau,tunda Yarima yake sai yau yaji ya taba jin kishin mace a ransa, domin ji yayi baya son kallon da Magaji yake yiwa Bily,don haka sai yace,me yakai idanunka kan adon matata?Fita ka jirani ina zuwa, Magaji ya fita yana dariya tare da jin dadin yanda 鈥榶an kwanakin nan abokin nasa ya soma hawa kan layi. Yarima ya dubeta ina ta kiran waya ashe ma nan kika barta,tace eh wallahi mun gama shirin.ya sake kallonta sama da kasa,tayi murmushi nayi?Kai ya daga kawai, sannan yace muje tace bari in dauko jakata in sanar da Mansu taje ta fito da amarya. Mota daya suka shiga da amarya su Yarima kuma da ango,sun riga zuwa sannan amaren suka iso,shi Yarima sai ya samu kansa da zare idanu yaga ta inda Beauty zata bullo domin kwalliyar datayi yana ganin kallonta kawai mazan gurin zasuyi,ita ko tunda suka rako amarya sai suka koma gefe ita da Mansu suna labarin kayan harka tana ce mata sai in mun natsu zan baki ai naga acan keda Yarima naki,tace wallahi wani sa鈥榠n in kin gammu zaki zata tun dama can mu masoya ne,Mansu tace,zama kuso juna ne,Bily tace ina ai nayi rashin wannan kalmar har abada,bazan taba samun mai sona ba wanda zai dubeni yace,Bily ina sonki.wannan tunanin ma tuni na ciresa cikin raina,tunda na riga nayi aure,mijin kuma bawai yana sona bane bare ya dinga gaya min.Mansu tace ke wata rana zai so ki ne.

[8:33AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 77馃彽


Bily tace ban yarda ba,nida shi zaya yi wuya mu so juna,don Hausawa suna cewa in mutum yaki ka da safe sannan da yamma yazo yace yana sonka wallahi karya ne, kuma Yarima bashi da rufi yana gaya min cewa yanda ba so nake ba akayi aurenmu shima haka ne bawai yana sona bane, nidai zaman lafiyan da mukeyi ne yanzun yayi min.suna ta zuba basu sanshi can Yarima ya shiga rudanin rashin ganinta ba,don haka ya ciro wayarsa ya shiga neman layinta zuciyarsa kuma tana raya masa cewa kilama wani namijin ne ya kirata.abinda bai taba yiwa wata mace ba shine ya kirata fiye da daya don inya kirata mace sau daya bata amsa kiran ba ko da bata gani bane to yabar kara kiranta amma yau kira harna biyar,wayar tana cikin jaka batama sani ba sai ana biyar din ne ta an kare da vibration din da takeji,tana ciro wayar call din na yankewa,5 missed calls ta gani,ta dubi Mansu, Yarima na nemana bari naje.Mansu tace nasan tare zaku zauna ni bari mu zauna dasu auta,Bily tace Faruk ya gudu ana gama daurin aure tace shima dole ne kinsan yanayin aikinsu,Bily ta nufi gurin Yarima wanda zuwa lokacin ya cika yayi dam,koda tazo ta zauna bai ko kalleta ba,ta dubesa sai ta samu kanta da shakkarsa,tace gani ya mata banza tace,ina fa tare da Mansu ce,sai ma ya kalli gurin Magaji yana cewa gasu Shettima can da Yakubu Sunusi dama sunzo ne?Yace eh sunzo bamu hadu dasu bane mun daiyi magana ta waya,jin suna hirar abokansu sai taja bakinta tayi gum nan dai guri ya kacame,masu ciye-ciye nayi masu shaye-shaye nayi shiko Yarima sarkin kalkali ana ta faman shan kamshi sai dai zuciyarsa taki nutsuwa,gani yakeyi kusan duk mazan gurin beauty suke kallo,don haka duk sai yaji zaman gurin ya ishe shi. lokacin da amarya da ango suka fita domin yiwa masu waka liki nan Yarima ya tashi yana yiwa amininsa ruwan 鈥榶an dubu- dubu, Sumayya kuwa sai ta soma zuba ma Yarima Magaji da Bily sun san dalilinta na yiwa Yarima liki amma shi bai san ko me take nufi ba. Ita Bily ta shigo tana ma ango da amarya liki sai Yarima ya juyo yace fita tace liki fa nake amarya da ango yace ibada ne ko kuwa tazo fita kawai wani ya biyota yana mata liki har wurin zaman ta ai kau ta tsorata ta juyo tace kai malam lafiya ni fa matar aure ce yayi murmushi yace nima ai mijin aure ne sai tayi banza dashi Yarima kau ashe ya ga abun da ya faru rai bace idanunsa har da canja kala kawai ya fita daga hall din billy.tayi sauri ta bishi amma ina tana zuwa har yayi reverse ya ja motar da wani matsiyacin gudu ta dawo wurin Mansu tace na shiga uku Mansu Yarima yayi fushi nasan kan na shawo kan sa sai naji jiki Mansu tace ki kwantar da hankalinki mu koma gida haka dai har aka tashi hankalin ta baya kwance suna isa gida Mansu tace taje wurinshi ta lallame shi tace nifa tsoro nake ji ko in bari dai sai ya huce

[8:36AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 78馃彽


Mansu tace ai baki sani ba,in kika ki zuwa sai yafi jin haushinki fiye da in kinje,kije kawai ki kwantar da kai inma yayi fada ne kadaki nuna kin damu,ki bashi hakuri. a haka ta fito jiki a sanyaye.Dakinsa ta nufa yana kwance kan doguwar kujera,kafafunsa suna kan hannun kujerar yana karkada su,fuskarsa tana kallon silin.wani zugi zuciyarsa keyi daya rufe idanu gayen yake gani sanye da farin yadi yana yiwa beauty liki.Ta shigo da sauri ta tsugunna gaban kujerar shine zaka taho ka barni?Ya dubeta ga mamakinta sai taga yau kwayar idanunsa tayi jajir,tsawa ya daka mata fita-fita nace, tace bazan fita ba sai ka gaya min me na maka?Ya mike zaune a fusace,kina nufin baki ma san me kikayi min ba?Tace yi hakuri kwantar da hankalinka, sai ka gaya min,yayi tsaki nace dai ki fita ko? Bana son kina damuna, in kuma zaki koma ne gurin wanda ya tsare kin har kamar ni in kiraki sau biyar a waya ki ki dagawa don kina tare da wani sannan ko kunya bakuji ya fito fili yana miki liki? Da sauri ta dafa kirji tare da cewa, a'uzu billahi! Kasan me kake fada kuwa?Wallahi-wallahi bansan shi ba,hawayen takaici ne ya soma zubowa daga idanunta, kasan daga Allah babu wani,ni da Mansu muka tsaya wannan mutumin bansansa ba,lokacin kawai na gansa yana min liki kuma na fita agurin amma in kana tunanin na sansa ka barni da Allah. Kuka ya kufce mata ta mike tana cewa ko ina hauka zan saurari wani ne, alhalin na sani sarai ina da aure?Nan kuma zuciyarsa ta shiga jin zafin kukan da takeyi,ta mike zata fita,ya kasa daurewa ya janyota jikinsa da sauri, tsam ya rungumeta ba tare da yace kala ba,sai shasshekan kukan ta dake tashi.sun jima ahaka sannan ya dago fuskarta ya saka yatsansa yana share mata hawaye. Idanunta yake kallo cikin idon har sai daya manne bakinsa cikin nata,daga nan sauran abubuwan suka cigaba da wakana, zancan bai kuma tashi ba. Washegari data shigo gefenta Mansu ta soma yi mata tsiya da cewa,daga zuwa ba miji baki shikenan sai muji shiru?Tace um ai sai da nayi kukan bakin ciki wai fa tsayawar da mukayi da kece yake zaton wanda nace miki yazo yana min likin nanne ya tsaidani, Mansu tace kishi kenan!Wallahi ina zaton Yarima yana sonki ne tunda in baka son mutum baka kishinsa,Bily tace ba wani so,haka akeyin so?Shi dai kawai rigimarsace ta motsa,sukasa dariya. Mansu tace,rigima sai kace yaron goye?To ba garama dan goyen ba da abinda Yarima yakeyi,inji Bily.haka akaci bikin Magaji aka cinye, washegari su Mansu suka nufi Gombe,daga can suka nufi KD duk kwanakin Bily karfin hali kawai takeyi kuma bata son Yarima ya gane,don ta tuna wata rana suna kwance take ce masa har tausayi Umma take bani saboda son taga danka, inda zaka yarda kurum ka sake aure ko matar zata haihu,ya tashi zaune ya dubeta bakida lissafi,ni yanzu kina ganin ko cikin kika samu zan barshi ne?Ai bamu isa haihuwa ba tukunna,ni dake har yanzun babu wanda yakai so kibar wannan batun ballatana har in wani kara aure,God for bid. Ta masa shiru yace ke na gane kina son ki haihu ko?Tace,no bawai ina son in haihu bane, kananan yara suna birgeni ne,ya kalleta da wutsiyar idanu sannan ya taba baki gami da cewa in kina so yayyena suna da yara sai ki amso,amma ki ajesu gurin Umma,shiru kawai tayi masa,tuna hakan da sukayi ne bata son ya san cewa tana da ciki burinta dai ya tattara yayi gaba ana gobe zai tafi suna kwance yanata wasa da yatsun hannunta lallan da aka matane yayi matukar birgesa,ya kamo dayan hannun wanda ba鈥榓yi mata lalle ba yana dubawa sai kurum tagaya mike zaune yana sake kallon gurin kunbunanta, da sauri yace ke tashi ta tashi zaune cire rigarki ingani,tace menene?Tsawa ya daka mata nace ki cire ko,cikin rawar jiki ta cire ya tsurama nonuwanta idanu,ya kama kan yana dubawa yace tun yaushe rabonki da al鈥榓da? Gabanta yayi mugun faduwa,tace ai ai lokacin ma baiyi ba,yace kada ki raina min hankali yau ba 20 ba date?Yaci gaba kina zaton tunda na soma kwanciya dake sosai bana lissafe da lokacin al鈥榓darkine

[8:36AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 79馃彽


Tayi zaraf tace,to ai on 27 nake yi,yace on 17 ne ina sane,tace Allah on 27 ne,kadai manta ne,nan take sai kuma ya rude, kwakwalwarsa ta shiga caji ya kasa tunawa,ita kuma ganin haka sai ta shiga kawo masa hujjoji ita wai nan a dole zata tuna masa a karshe cikin dar-dar tace in kuma baka yarda ba ne ka iya yimin test kila kafi yarda dani,jin haka sai yace is ok na manta ne.a hankali tayi ajiyar zuciya shi kuma ya rungumo ta yana cewa har hankalina ya tashi da cikin daren nan zaya shige toilet.Washegari ya shirya komai amma kuma sai me?Zuciyarsa ta shiga cikin damuwa,wai bata son rabuwa da beauty,yaja tsaki yana jin haushin zuciyar tasa,me zaisa ta matsa masa inma don tana son ta nishadu ne ga mata can 鈥榶an garari masu ji da iya soyayya, lokacin dayaji shigowarta sasan sa sai ya daga idanu yana kallonta,so yake ya gane me tafi sauran mata da zuciyarsa ta damu da ita haka?Ta rusuno daidai fuskarsa ta hura ma idanunsa iska tace,kallon fa?Kamshinta ya shaka ya lumshe idanu,sai bakinsa ya furta cewa,ina tunanin yanda zan rabu dake ne.ta ware idanu cikin mamaki tace, kana dai tsokanata ne kawai kaida zaka tafi zaka manta dani,cikin sigar shagwaba tayi maganar, yanda ta lura muryarta bai san sanda ya mannata jikinsa ba.yaya zan manta da hutuna ina nufin gurin hutawa,bayan kinsan ni dan hutu ne?Ta daga idanunta tana kallon nasa cikin idon,tace da kaje nasan abokan hutun su zaka fara samu kai din sai ya samu kansa da gudun damuwarta don haka sai taji yana cewa,a鈥榓 na daina ki sani cikin addu鈥榓 bazan sake ba.dadi taji ta kara rungumesa to yaya zakayi ne gashi baka da hakuri ko dai zakaje dani ne?Ya sanyaya murya bansan yanayin gurin ba amma ki bari innaje naga gurin yana da tsarin da matar aure zata iya zama sai nazo na tafi dake ko kuma zai yiwu in zauna ba yaya zakayi?Yace ki bani shawara tace ka riga yin azumi ga lada sannan zai dauke hankalinka daga shagala,tsam ya sake matseta yana cewa na gode beauty. Haka ya hada kayansa ya tafi Magaji ya kai shi airport tare da billy sai sumayya da ta biyo mijin ta ko a airport sai da ya kara rungume billy sumayya dai ta kauda kanta suka yi bankwana ya shige jirgi sai.da suka ga dagawar su sannan suka juya billy cike da kewar mijinta

[8:38AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 80 馃彽


Hakika Yarima yana son mata shi likitansu ne,sannan yanzun cikin course din nan ya gano zasu iya maida tsohuwa yarinya,domin ana iya canza fata suna dasa nono daga zubabbe ya koma tsayayye har yake tunanin na billy inda ba tsayayyu bane da sai yayi mata aiki ya gyara su toh amma yayi sa'a nata masu kyau ne sosai tsaye suke kyam irin wanda ko tsufa baya sawa suyi sharab dinnan sai dai su dan russuna .yana zaune cikin dakin daya zama mallakinsa,wani abu yake son sani cikin laptop game da course dinsa, yarinyar bata fi sati daya itama da zuwa ba,ita 鈥榶ar mutanen Maroco ce,tana da kyau sosai itama tazo yin course ne irin na Yarima tun ranar daya soma ganinta ya shiga rudu,sannan jinkai da sarauta suka motsa.yana dago kai ya ganta tsaye cikin dakin,ya tambayeta shin tana bukatar taimako ne?Bada bata lokaci ba tace,tana son yin magana dashi ne,yace mata babu matsala,amma fa sai dai ba yanzun ba domin yana da abin yi,tace to ta iya jiransa?Yace,inbata da abinyi ta iya yin hakan mana.tace shikenan,ya nuna mata gurin zama yaci gaba da aikinsa.tana kallon Yarima komai nasa yayi mata,tana sonsa tun sanda idanunta suka soma ganinsa yana da kyau sosai,tsawon awa daya da mintina sannan ya gama komai,ya dubi agogo sannan ya dubeta tare da cewa,lokacin sallarsa ya kusa shigowa,amma zata iya yin maganar cikin minti sha biyar?Tace bazai kai ba ma,ita kawai tana son su zama abokai ne kawai,yace me yasa tayi tunanin su zama abokai?Tace haka nan kawai ne taji ya kwanta mata cikin rai,sannan ta lura yana son yayi abinda ya kawosa ne, tana son mutum mai kwazo da ilmi.yayi godiya tare da mika mata hannu,sunnan shi ya sanarda ita wato Prince Al鈥榓min,cike da jindadi tace,ita kuma sunanta Tina Abraham. Tun daga ranar suka zama aminai duk da cewa basu taba aikata wata masha鈥榓 ba,suna dai sha鈥榓war juna amma duk sun danne.sai wata ranar lahadi yana waya da Bily ta shigo,zama tayi tana kallonsa tare da sauraron yaren Hausar da yake magana da ita,sai daya gama sannan tace masa tana son ta iya wannan yaren,yace to gaskiya bai alkawarin koya mata ba,amma inya samu lokaci zai dan kwatanta,ta matso kusa dashi tana shafa gefen wuyanta tare da lasar lebunanta tace masa ita in tana kusa dashi sai ta samu kanta cikin wani yanayi,shin zai yarda su dandani juna? Baice kala ba kuma bai mata tsawa ba sai data zo kusa dashi ta rungumesa, wasu abubuwan data soma masa sune suka sa shi kasa daurewa,harma ya fito mata da kwarewarsa awannan harka.Tina ta raina kanta da kwarewarta agurin yarima, ta kuma kara samun kwarewa tare da sonsa mai tsanani, tun daga ranar ta tare a dakinsa suka cigaba da lalacewa,Allah ya kyauta musu.Bily tana zaune cikin kujera bayan ta gama kwara amanta,sanyi ne takeji tana zato na zazzabi ne.Jakadiya ta shigo tace da jakadiya taje ta kawo mata bargo. jakadiya taje gurin Umma tana cewa,ranki ya dade gimbiya Bily fa duk kwanakin nan batajin dadi,ba ko za鈥榓 kira likitar nan ta dubata ba ko mun samu karuwa ne?Ai jin haka da sauri Umma tace,bani wayar can, jakadiya ta miko,Doctor Aisha ta kira tace mata tazo yanzun,kamar minti hamsin ta iso.bayan gwaje-gwaje da 鈥榶an tambayoyi ta gano cikin wata biyu da 鈥榶an satittika, nan take ta sanar da Umma, murna gurinsu ba鈥榓 magana,nan dai aka daura mata karin ruwa. mai martaba harda goron albishir ya hadama doctor Aisha dashi.ita dai Bily damuwarta daya,in Yarima ya samu labari yaya za鈥榓 kwashe?A dare ko ya kirata sai tayi tunanin ta sanardashi kuma ta nuna masa ita bata so don in wani ya sanardashi to zasu kwashe ta babu dadi,yanzun ko ta siyasa zata bi.yace beauty yaya ne?Tace,um kai dai bari,muna cikin matsala fa,ya gyara zama tame kenan?Tace banga al鈥榓da ba gashi har na soma rashin lafia,Umma ta turomin doctor Aisha ta dubani bansan me tace ba naga dai gidan ya cika da murna,nidai gaskiya banason in haihu ka fada min me zanyi? Yarima ya kasa magana ma don takaici can yace gaskiya matsalar ma babbace, ko dai inzo ne acire shi? Gabanta ya fadi,amma sai ta daure tace kada kazo in akwai wata kwaya mai karfi ka min text dinta in aika asiyo min insha,yace yauwa kin kawo shawara, to amma wazaki aika?Tace Atika don batayi karatu ba kuma in gargadeta nasan zataje, yace shikenan zan turo inbai fita ba ki gaya min,tace to amma fa insu Umma sun kiraka sun maka murna kadaka nuna baka so don inmun cire kadasu gane ko su zarge mu. yace, haka ne beauty kada ki damu kin ji? Tace to sai na gani.

  Hankalin Yarima ba karamin tashi yayi ba,shin wace kwaya zai ba wa beauty? Nan take ya shiga cikin asibiti gefen magunguna ya bincuko, nan take yazo ya turo mata su in ta samu kuma ga ka'i'dojin su, sannan ya kira ta yace ta gani? Tace, ta gani ta share ta ci gaba  da sabgarta, shi ko kullum nacin tambaya ya ya fita? Tace Aa yace to zata iya ganinshi a kowane lokaci. Zai zo ya cire mata shi tace to gara haka din ma, ya ce ai su Umma sun kira ni har da mai martaba na dai nuna musu murnata tace to sai na ganka, ai suna gama waya ta kira magajin Malam a waya tace tana Neman shi yanzun nan, cike da far gaba ya zo don bata taba kiran shi ba.

Bilkisu ta sanar dashi Komai tace in yazo kasan dole ne ya cire cikin nan, ni yanzun ban san ya ya zan yi ba, kuma bana son in fada ma Umma, magajin Malam yace to lallai Yarima, amma kada ki damu ki barni dashi ni nasan yanda zan mishi in hana shi zuwa, nan take ya kira shi. Yarima ya soma mishi tsiya ango kasha kamshi, sai yau aka ga damar kiranmu? Magaji yace kai me ya hana ka kira ni? Yarima yace Aa bana son in takura maka ka samu gurin Hutu gashi kuma abun ya hada maka biyu, wato ga sabon shiga ga ka tuzuru yace ba komai, dama na kira ne in ce maka ina murna da samun baby, yaci gaba sai dai wani abu da bai min dadi ba, shi ne na shiga gaida bilkisu na same ta a galabaice, sai da aka dauko Doctor Aisha nan ta gano tasha wata kwaya ne don zubar da cikin, a tsorace Yarima yace yanzun ya ya ake ciki, su Umma sun sani? Magajin Malam ya kuma dagewa tamkar gaske yace yanzun dai da mun gama waya zan sanar dasu don na hana Doctor Aisha ta sanar dasu, musamman da na fahimci da saninka zata zubar da cikin, magana daya dai yanzun ko Ku janye ra'ayinku kai da matar ka ko kuma wlh zan sanar da su, musamman in har kazo don na sanka sosai zaka iya cewa zaka zo kayi aikin da kanka. 

Jikin Yarima ya mutu, sannan yace amma dai magaji kasan haihuwa ba ra'ayina ba ne ko? Tsaki magaji yaja sannan yace, wannan sai ka gaya ma ubangijin da ya baka cikin, ya kashe wayar shi.ya dubi bilkisu bar shi kawai, ba zai zo ba, suka yi ta dariya ita da magaji tayi mashi godiya sannan ya tafi.

[8:38AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 81馃彽


Ya kira bilkisu yana cewa, ya ya aka yi ta bari magaji ya sani? Tace ya shigo gaishe ni ne ya same ni cikin wani hali shi ne ya kira likita.... Ta soma kuka cikin kissa ni gaskiya ba zan iya ba, gashi yace zai gaya ma su Umma kuma kasan yanda su Umma suke murna za su dauki mummunnan mataki ne a kanmu, yanzu ya ya zan yi? Yace ya ya zaki yi kuwa in ban da hakuri? Kina nufin zan zabi bacin ran iyayena saboda ranki yayi fari? Ba ki kai wannan matsayin ba, ta soma sabon kuka wato danni baka kaunata in zan mutu ne in mutu ko shi kenan, ta kashe wayar sannan ta soma dariya tana cewa in kasan wata ai baka San wata ba, don ma kada ya dauka fushin wasa take yi sai ma ta kashe wayarta bayan ta kira Mansura ta mata bayanin komai, sannan ta ce zata kashe wayarta don kada ta nema ta ji shiru, Mansura ta kara ma ta wasu dabarun sannan suka yi sallama, hankalin ta kwance ta gode ma Allah tasan bata da matsala ta gefen Yarima, Allah yaga niyyarta Yarima da farko bayan ta kashe wayar cewa ya yi ke dai ki ka sani ko a jikina da bacin ran iyayena ai gara naki.


Amma kuma me? 


Kunnuwanshi sun kasa daina jiyo mishi kukan da ta kashe waya tana yi yayin da zuciyar shi ta shiga cewa kamata ya yi ace ka lallashe ta ne, zugin zuciyar ya matsa mishi nuna mishi take yi bai yi mata adalci ba, haka dai ya daure yayi jarumta har zuwa washe gari inda abin ya ishe shi har ya nemi layinta cikin wayarshi amma a kashe, yayi ta kira shiru ya bata awa daya ya sake kira nan ma shiru, jikinshi ya yi sanyi, zuciyar shi ta dame shi yinin ranar babu kuzari duk wadanda suke tare dashi duk sun fahimci yana da damuwa, musamman Tina. Shi kanshi ya rasa dalilin damuwar tashi, akan matar da ya tabbatar ba sonta yake yi ba, wasa- wasa yau kwana hudu yana neman layinta babu dare babu rana, duk da ya kira magaji ya tambaye shi shin bilkisu tana nan? Magaji yace, ban sani ba sai dai ka kira wayarta, Yarima yace yau kwana hudu wayarta tana rufe, magaji yace to ka kira ta cikin gida mana? Yace bari ya yi hakan.


Umma ya kira bayan sun gaisa yace, Umma wai ya ya jikin bilkisu ne? Yaci gaba ina ta neman layinta amma shiru? Umma tace, jikinta da sauki babana, dazun nan ta shigo nan amma zan kirata in ji, yace to suka yi sallama.


Koda Umma tasa aka yi mata kiran bilkisu, ta tambaye ta ko lfy wayarta take ana ta nema ba a samu? Sai bilkisu tayi karya da cewa, batirin wayar tata ne ke da matsala, amma ta aika yanzu za siyo mata wani, Umma tace to dama maigidan ki ne yake ta nemanki, tace zan kira shi in nasa batir din.


Bayan taje daki sai ta kunna wayar ta cikin sa'a yana neman ta sai gashi ya samu wata irin ajiyar zuciya ya yi tun kafin ta dauka sai ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi,  sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Da sauri yace, beauty, beauty, kina jina? Ta soma shassshekar kuka,sai kurum ya samu kanshi da cewa innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai beauty me ke faruwa ne? Cikin kuka ta ce dole mana ka ce meke faruwa? Ka min ciki sannan ga wulakancin ka har da cewa baka damu da bacin raina ba to ni ba zan iya zama ba gidanmu zan tafi. Yana son yace ki tafi din mana, amma sai zuciyar shi ta ki furta haka,sai kurum ya ji bakinshi yana cewa, haba saurare ni ki ji.in ji wa ya ce ban damu da ke ba? Da kin tausaya min. Don Allah kiyi hakuri. Sai kuma yayi shiru yana mai jin haushin kanshi, yaushe ne yake baiwa mace hakuri amma zuciyarshi murna take yi musamman da taji bilkisu tana cewa shi kenan ba zan kara kashe maka waya ba, to kana son cikin? Yana tayi maganar cikin sigar shagawaba sai da tsigar jikinshi ta tashi, sannan nashi ra'ayin shi ne ya ce mata A'a amma ya kasa fadin hakan, sai ya samu kanshi da gudun bacin ranta, don haka sai yace ya ya zan yi ni dole in so shi tunda ni na diga shi, sannan shakuwarmu dake tasa ba zan guji duk abin da ke jikinki ba, tace kana nufin yanzun ka damu dani? Yace, ke baki damu dani ba? Tace na damu mana, sosai ma. Har fa tunanin ka nake fa zama in yi da baka nan.

[8:39AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 82馃彽 


Ta marairaice murya,kai fa kana tunanina? Yace inna ce miki banayi ai zaki musa ko ban tunoki don komai ba ai na tunoki ko don hutu beauty,ina bukatarki kusa dani,tace kilama ka samu wata,da sauri yace haba dai ni yanzun naki ne ke kadai taji dadi sosai sannan tace nima haka,yayi dan murmushi na sani beauty tun ranar farko dana soma kwanciya dake nasan cewa nayi dacen mata,Allah yayi min baiwa,bai duba halina ba,bai hadani da 鈥榶ar uwata ba wato mazinaciya, sai ya bani mai kofa a rufe nina budeta, tace ni ko kaga bana son in tuna wannan rana,yace don me?Dan wulakancin dakayi min, yayi 鈥榶ar dariya niko abubuwa da yawa sun tsaya min a rai ranar,zan gaya miki in nazo,tace shikenan sai anjima?Yace kin kosa muyi sallama ne?Tace a鈥榓 nace kona tsare maka aiki ne,yace shikenan zamuyi waya da dare,tace sai naji ka kenan itace ta fara kashe wayar shi ko tsayawa yayi tamkar wawa,yana son tuno tabargazar da yayi shin me ma yace mata?Kasa tunowa yayi sai ma wata annashuwa da zuciyarsa keyi,hira tayi dadi tamkar acigaba sam ya manta me yakeyi ne,ya nutse cikin tunaninta.Tina ce ta dafa kafadunsa da sauri ya dubeta tare da fatan Allah yasa beauty ce ganin Tina sai yayi tsaki, jikinta babu kwari ta sakesa ta zauna tuni itama ta soma sabawa da halinsa,sai dai Allah ya jarabceta da sonsa,shiko duk sanda yake kan begen beauty yakan manta da komai da kowa baya son a matsa masa,wanda nasa ganin shakuwa ce duk ta kawo haka.Bily kuwa yanzun hankalinta kwance ga tattalin da surukanta suke mata, labarin cikinta ya yadu ko鈥榠na,don ko su Mamanmu da Mansu ta sanardasu sunyi murna, sannan gashi Yrm duk ya birkice kanta,don da taba Mansu labari Mansu cewa tayi Allah sonki yakeyi Bily tace a鈥榓 duk hirar da mukeyi bai taba cewa yana sona ba,yadai nuna kulawarsa gareni,so kam ai na riga nayi rashinsa bazan taba samun wannan kalmar ba,Mansu tace shikenan za kuma ki gane nan gaba.  


Yarima da Tina an sake dinkewa,a zuciyarsa yana kara shige matane da tsawonta da tsawon gashinta suna tuno masa da beauty, ita ma ta fahimci yana da wata a cikin zuciyarsa domin in suna kwance sunan beauty kawai yake kira.sannan inya shiga wanka takan dauki wayarsa ta masa bincike tana son sanin wacece beauty din nan?Yaya take ne don ta samu matsayi mai girma gurin wannan tsadaddan yaron.Kimanin wata hudu kenan da tafiar Yrm,cikinta kuwa yana wata biyar kenan tana zaune tana cin kwakwa da tasa aka siyo mata, Sumayya ce ta shigo tana sanye da leshi ja da kuma ratsin baki yaune zuwanta na uku gidan,ta zauna tare da cewa Maman biyu,Bily tayi 鈥榶ar dariya tace,Allah amin ya biya bakinki Sumayya tace amin.nan suka soma hira duk data hakura da Yarima amma duk sanda ta gansa ko taga hotonsa sai taji ma kanta haushin rashin samunsa, yanzun ma da take zaune kallon hotonsa takeyi tare da yaba kyansa, cikin zuciyarta. Bily tace,Sumayya kina kallon wuta ne fa,yakamata ace yanzun kin cire Yarima acikin rayuwarki,sannan ki godema Allah daya baki Magaji matsayin miji,tace ai tuni na hakura anty Bily, matsalata daya yanda zan cire shi daga zuciyata,ki dinga addu鈥榓 inji Bily,ki rike mijinki Sumayya so da yawa abinda ka kwallafa rai kansa baka samesa ba to sai kiga alkairi ne rashin samun,ni kaina ban taba tunanin zan auri kamar Yarima sa鈥榓na ba,babu irin takaicin dabanyi ba game da auren amma yanzun sai ina ganin alkairai da dama acikin aurenmu.don haka ki kama mijinki ki samu ladan aure,Sumayya tace to nina rasa sam sai inga sam Yarima yafi Magaji komai, Bily ta hade fuska Sumayya lallai zaki daina zuwa gidana,domin babu wanda yafi wani gurin Allah face wanda yafi tsoronsa,in dai kina so mu shirya to ki kama mijinki. Sumayya tayi 鈥榶ar dariya ganin ran Bily ya baci,tace na daina anty Bily,shima Magaji cewa yake duk ranar dana zo nan gidan wai bana bata masa rai,shiyasa yake son inzo gurinki,ina aiki da shawararki,nan dai suka cigaba da hirarsu.Wani dare Bily tana bacci sai kawai tayi mafarki wai ga Yarma an kawosa ya rasu,nan take ta farka duk tayi sharkaf da zufa,ta kalli agogo sha biyu da 鈥榶an mintuna duk da lokaci ba daya ba ne ji tayi bazata iya komawa bacci ba har sai taji muryarsa nan take ta kira layinsa daidai lokacin ya shiga wanka,Tina ce kwance rigingine a tsakiyar gadonsa,don haka wayar tana yin ringing ta dauka ta duba(beauty)taga an rubuta,da sauri ta daga wayar tare da cewa, wacece ke?Cikin harshen turanci. Bily ta tsorata, gabanta na faduwa tace,kiba mai wayar,Tina tace sai ta fada ko ita wacece,ran Bily ya baci dama Yarima yana nan yana harkarsa da matan banza,shine yace mata ya daina?Wani tukuki taji azuciyarta nan take ta kashe wayar cikin tane ya shiga murdawa,ji take tamkar zata haihu Yarima yana fitowa daga toilet din yaga phone dinsa ahannunta,nan take tayi saurin cewa an kiraka amsar wayar yayi ba tare da yace mata kalaba,koda ya duba yaga beauty ce ta kira kuma har ta daga nan da nan sai yaji hankalinsa ya tashi,da sauri ya soma kiran layinta,tamkar kada ta daga amma sai ta kasa tana dagawa sai ta saki kuka ya rasa me zaice,sai yace kiyi hakuri beauty na kasa controlling din kaina ne yau amma insha Allah bazan sake ba,na amsa laifina kiyi min addu鈥榓 kinji?Cikin shesshekar kuka tace, Yarima baka min adalci ba,yaya na tsare kaina a gida kaika dinga bin wasu,ina tsoron kada Ayar Allah ta sauka akaina,domin Allah yace in har kabi matar wani sai anbi taka,in 鈥榶ar wani kabi kaima za鈥榓 bi tak,haka kuma mazinaci baya aure face sai da mazinaciya 鈥榶ar uwarsa,ban kasance mazinaciya ba. Yarima ma jikinsa yayi sanyi yasan gaskiya ta fada ina ma gata gashi ne ya rungumeta tare da lallashinta, duk da haka sai yace na sani beauty ban kyauta miki ba,amma kada kiyi fushi dani zan shiga damuwa kinji?Tayi ajiyar zuciya,sannan tace bazaka daina ba Yarima ,yace ki daina fadin haka,insha Allah zan daina nidai kimin afuwa, tace Allah zaka roka donshi kayiwa laifi,da sauri yace zan rokesa,don Allah beauty kadaki kashe min waya kinji yanayin yanda yayi maganar sai taji dadi,tace bazan kashe ba

[8:40AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 83馃彽


Zuciyarta tayi sanyi domin lokutan baya Yrm yana neman matansa a gabanta, zai iya kwanciya da mace a gabanta,amma yau gashi wayarta kawai mace ta daga duk ya birkice, ta san ko har yanzun Yrm yana neman mata to ta samu wani matsayi agurinsa tunda yake boye mata baya son ta sani,bugu da kari Yarima ne harda bata hakuri,tayi mamaki domin tasan sa sarai baya daga cikin mazan da suke bawa mace hakuri,baya lallashin mace amma ita sannu a hankali ya soma yi mata abubuwan da yake ikirarin bazai iya yiwa mace ba, zata dage da rokon Allah har Allah ya shirya mata shi. Shi kuwa Tina ya tsirama idanu cike da bacin rai irin wanda bata taba gani ba,don haka ta tsorata har ta shiga bashi hakuri,cewa yayi ta fita kawai.tana fita ya fada kan gado yana rubuta ma beauty dinsa text na ban hakuri, sai daya gama sannan yayi shiru yana mamakin kansa,shine Yrm kuwa?Shine mai ja ma mata aji? Shine wanda mata suke bi bashi ne ke binsu ba? To menene yasa shi rikicewa kan beauty?Yanda ya dade dasu Vicky bai dade da Bily haka ba me yasa zuciyarsa bata shaku dasu kamar yanda ya shaku da ita ba?Me yasa ita baya jin ta gunduresa?Me yasa baya son bata mata rai ne? Domin inya bata mata rai zuciyarsa sai ta ringa yi tamkar zata fashe,bai saba da damuwa ba,don haka baya son zama cikin damuwa,inya bata mata rai sam cikin damuwa zai zauna shiyasa yake kiyayewa.


 A kwana atashi babu wuya agurin Allah, yau gashi Bily an shiga watan haihuwa.duk wani abu daya kamata mai jego da jariri 鈥榶an gata su bukata, tuni Umma ta tanadeshi, can ma Zaria su Mama suna ta shirye-shiryensu na talakawa. Yrm ko hankalinsa ya kasa kwanciya ina ma a hannunsa beauty zata haihu baya son ya rasata,wayewar garin Alhamis ta tashi da ciwon haihuwa,tuni Umma tasa akayi asibiti da ita,inda take awo wato asibitin Doctor Aisha.har zuwa yamma shiru Modibbo ne yayi mata wasu addu鈥榦鈥榠 ya tofa su cikin ruwa aka kai mata daidai lokacin Yrm ya kira wayarta har ya gaji,ya kirata cikin gida,Asabe ce ta dauka ya tambayeta Bily,nan take shaida masa tana asibiti zata haihu,yace tun yaushe? Tace tun jiya,nan take ya kira Magaji,Magaji yace duk suna asibitin ance nan da awa daya zata haihu,tsaki kawai yayi nesa bata maganin kusa,amma in yaga za鈥榓 bata masa lokaci xai bar komai duk da suna tsaka da karatu,kasancewar sun kusa gama course din ya kira wannan ya kira wancan har awa dayan ta shige ya kara minti talatin duk yaji babu bayani,nan take sai ya soma shirin zuwa gida. nasa ganin likitar bata san aikinta ba,domin in shi zai amshi haihuwa ne yana ganin cikin awa daya mace zata haihu. sai washegari sannan ya samu tasowa, bai sanar da kowa cewa yana hanya ba kuma yana cigaba da kiran waya suna sanar dashi ta kusa harma ya soma tunanin ko ta mutu ne suke boye masa? Yana dira dama daga shi sai kayan jikinsa,yayi wa Magaji waya,wane asibitin?Suka masa kwatance ya nufa, doguwar nakuda Bily tayi likitar tace su kwantar da hankalinsu zata iya haihuwa da kanta. ana cikin haka sai ga Yrm,duk suka cika da mamaki, office din likitar ya nema ya shige ya nemi son ganin matarsa kasancewar tasan aikinsa ne bata musa ba,suna tafe tana masa bayani shiko saurarenta baiyi ba shi dai burinsa shine ya isa gurin matarsa.yana shiga ya ganta tana ta fama ga Nurse kanta a tsaye ya isa gurin da sauri ya kamota lokacin abun ya kan kama sosai,nan ya shiga aikinsa cikin minti tara dan ya sawo kai,nan Yrm ya jawosa ya mika ma Nurse bayan ya yanke cibi.bai ko tsaya kallon yaron ba shita matarsa yake,duk abinda ya dace shine yayi mata,sannan yayi mata allurar hutu. Koda ya fito ana ta kallon jariri wannan yaba wannan, wannan yaba wancan duk sai yaji sun bashi haushi,su ta yaro sukeyi ma ga matarsa can a galabaice.shi kam me zaija masa kara haihuwa?Gida kawai ya nufa,ya watso ruwa,yana dawowa tana farkawa. Ta dubesa da dan murmushi,me muka haifa?Ya dan daure fuska bakiyi murna da ganina ba sai abinda kika haifa ko?Ta yunkura ta tashi,yayi saurin riketa kada ki tashi tace naji karfi fa ya zauna kusa da ita,tace naji dadin zuwanka sosai mana.

[8:40AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 84馃彽


Kallon fuskarta yakeyi,ji yake tamkar ya bude kirjinsa ya sakata ciki,yace beauty kinji jiki,hankalina ya tashi sai zuciyata take sanar dani kamar zaki mutu ne tunda naga Allah ya kawo mana da sauki kila gobe na juya dama ina tsakiyar ayyuka,nan da wata uku zan gama in dawo mu zauna tare.tace yanzun ba zaka tsaya ayi suna ba?Sallamar su anty Salma ce ta katsesu,suka shigo suna faman taba baki,anty Fulera tana dauke da yaro,anty Fatima ce ta soma cewa,maijego kin tashi?Ai nazata bazaki iya tashi yanzun ba, saboda tsabar ragwanta. anty Salma tace gaskiya raguwa ce. Yrm yace kinfa san tun shekaran jiya take aikin abu daya,gaskiya tayi kokari,ni likitar cema naga alamar kamar bata san aikinta ba.suka ce ba wani nan ragwanta ne,Bily ta nuna ita dai tana jinsu yace to shikenan ku barta ta huta,suka mika masa yaron ya amsa yana kallon fuskarsa,sai yaji yaron ya burgesa,tunda ya amshi yaron shi take kallo ta gani shin yaya fuskarsa zata nuna,ga mamakinta sai taga yayi murmushi tare da cewa,yana da kyau bebyn,ta kalli su anty Fulera ta sunkuyar da kai,har suna hada baki gurin cewa munafunci in zakiyi magana yi mu kinga fitarmu,abinda haihuwarma kinyi kikayi kin tsaya sai yazo suka fita.Yrm yace,sun cika hayaniya,ya mika mata yaron yayi gashi ki ganshi ta girgiza kai,yayi dan murmushi yace,baki sonsa ne?Ta kallesa tana dan murmushi,sannan ta kalli yaron tace kai kana sonsa?Ya dago yaron zuwa bakinsa ya sumbacesa agoshi ina sonsa yanzun yana da kyau,tace kama da kai yayi?Yasa matashi a cinya kallesa ki gani,ta zata axuciya tace hasbunallahu wani'imal wakil,ya dubeta tace tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya bamu wannan yaron,鈥榶ar dariya yayi kin rude ko?Likitar ce ta shigo ta dubata sannan tabasu sallama tana tsokanar Yrm.yaso tafiya washegari, amma beauty da yaronta suna daukar hankalinsa har ya kara kwana,dazai tafi hadasu yayi ya rungume wayarsa ya fito da ita abin mamaki yana ta daukar hoton Bily da bebyn ta Lallai abin mamaki ne domin in kaga Yrm yana daukar hoto cikin waya to wani abu ne mai mahimmanci daya danganci aikinsa bazaka samu hotunan banza cikin wayarsa ba,domin bashi da lokacin zaman kallon hoto,tsiraici a hoto baya burgesa,yafi son ya gansa muraran.bayan ya gama yana bakin gadonsa itama ta zauna,idanunsa suna kan jaririn yace beauty ji nake tamkar kada na tafi, ya juyo da dubansa gareta yana kallon tsakiyar idanunta,nazo da sha鈥榓warki zan koma da abuna.ta matso ta kama tafukan hannunsa ta matsa,abin ya ratsasa har ya lumshe idanu tare da jn numfashi,tace daba don ina cikin biki ba,ko ban warke ba zan baka kaina har sai ka gaji,amma kada ka damu zan dinga zuwa maka cikin mafarki.ya tallabo fuskarta ya soma kissing dinta baki cikin baki,kukan yaron ne ya dawo dasu,shine ya rigata dauko yaron ya mika mata tasa shi a kafada yace no bashi nono in gani zama kiyi kyau da shayarwa?Tayi dan murmushi,ta soma kici- kicin ciro nono yana taimaka mata,yaron ya kama yana sha,Yrm ya tsura ma nonon idanu,sun cika sun kara girma, sannan basu kwanta ba,ya lura da kasan nonon yana da fadi,lallai ya taka sa鈥榓 wannan baya faduwa komai tsufa,domin da irin masu faduwan ne ma gareta da sai yayi mata gyaransu sun mike.ya matso ya rataya hannunsa akafadarta ya saita wayarsa ya daukesu hoto su biyu ne suka fito don yaron yana cinyarta yana shan nono. Kwankwasa kofar ce ta dawo dasu daga shirman hotunan da sukeyi,Yrm ya bude kofar anty Saliha ce tace ina maijegon tun dazun nazo da baki 鈥榶an barka suna can a zaune tazo nan ta nane inba zata samu zuwa su gaisa ba to ta bani yaron.cikin fushi take maganar,yace haba anty tana zuwa muna sallama ne, ta juya fuu, yace taso kina da baki ni dai saura minti kalilan jirgin Lagos ya tashi,suka kalli juna tace sai munyi waya,yace to,sannan ya shafa kan yaron tare da sumbatar lebunanta sannan ta fita.yana rike da kofarsa yana kallonsu har ta sauka daga falon,yayi ajiyar zuciya ya koma yana hada shirginsa.Koda ta isa dakinta haka anty Saliha tayi ta mata masifa agaban dangin mijinta,wai ita 鈥榶ar dadi miji,tabi ta like masa menene-menene, dhiru kawai tayi mata hardai suka fita haka akaci gaba da shagalin har zuwa ranar suna,inda yaro yaci sunan mai martaba,tun ana gobe suna 鈥榶an Zaria suka iso,Mansu kuwa tun kwana hudu da haihuwa ta iso.anyi suna irin na 鈥榶an gata,kyautuka dai maijego ta samu,kaya kuwa tasa har ta gaji,har washegarin suna jama鈥榓 ce.sai da gari ya kara wayewa sannan Mansu ta tafi,bayan sun kammala komai ta bata kudade tasa mata cikin account dinta,don ita bazata samu fita zuwa banki ba.mai martaba doki yava takwaransa,Yrm yana kwance yana kallon hotunansu baya gajiya da kallon hotunan,wasu abokan course dinsa sunsha mamakin ganinsa yana kallon hoto harma suka tayasa kallo,sai gashi Yrm mai boye cewa yana da mata shine mai fadin matarsa ce da dansa,sun rude wanda har yaji haushin kansa me yasa ya nuna matarsa?Murna suka tayasa kan cewa yayi matukar dacen family koda yaushe Yrm yana nane da wayarsa,jira yake ya samu dan sarari zai kira beautynsa,waya ga ba sabon ba,su Yrm an shiga tarkon so sai dai shifa har yanzu bai san wai son matarsa yake ba kuma bai samu wanda zai sanar dashi ba.nata bangaren kuwa ba don har yau Yrm baice mata I love you ba data ce sonta yakeyi,koda bata san yaya so yake ba ai tana kallon fina-finai tana kuma karance-karance yanda Yrm ke nuna mata yasa ta bashi wata daraja cikin ranta.ita da Yrm yanzun kullum suna cikin lissafin kwanakin da suka rage masa,sannan anan gefen tana shirya masa kanta tana son ta tare shine yanda zai san tana da banbanci,sannan yasan har yanzu itace din dai,shiko nasa gefen tsaraba ce yake ta jibgo mata ita da danta,duk abinda ya gani sai zuciyarsa tace beauty zata so wannan,sai kawai ya loda in ma na yara ne sai yace kai bari in sai ma son,haka yake kiran yaron (son)wata rana kuma yace(my friend)wai yaron abokinsa ne tunda wai kwata-kwata da shekara nawa ya girmesa?Sai Bily tayi dariya.

[8:41AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 85馃彽


Tunda Yarima yace ma Bily beauty cikin satin nan zan diro,amma ba zance miki ga rana ba,ta kasa zaune ta kasa tsaye, harma su Umma sukai ta mata dariya.yau ta shirya wannan tayi wancan da kanta take shiga kitchen amma shiru sai kiga har dare babu labari,yau kam tasha alwashin ba zatayi komai ba,tana falon Umma bayan sallar la鈥榓sar, Umma tana zaune kan kujera yayinda ta dora kafafuwanta kan tuf-tuf.yallabai wato jaririnsu Bily yana kan cinyarta,Bily tana zaune kasa kusa da kafafun Umma tana shafa mata maganin ciwon kafa,tare da dan mammatsa mata kafar Umma tace,鈥榶ata yau baza鈥榓yi wa ubannawa girkin ba?Cike da tsokana tayi maganar,Bily tace,na gaji Umma,babankin nan ja min rai kurum yakeyi bawani zuwan da zaiyi.Umma tace,muma kinga ai munci girki kwana biyu, dama haka kika iya girki?Kafin Bily tace wani abu sai sukaji sallamar Yarima da wannan muryar tasa ta kasaita. Zaraf Bily ta mike tsaye tare da cewa, dama kana hanya? Shiko kallonsu yakeyi ransa yayi fari kar yanda ya samesu yaji dadi,Bily ji tayi tamkar ta rungumesa,shiko ita ya nufo sai tayi maza ta zauna ya kalli Umma yana dariya,sannan yasa hannu ya dauki dansa yana cewa, Umma son yayi girma fa,kuma ya kara kyau, gaskiya beauty ta iya haihuwa.Umma tayi dariya sannan tace, shirmen kan nan yana nan dai babana?To kaki sanar damu ranar dawowarka, kullum sai Bily tayi maka shiri na musamman in baka dawo ba mu da 鈥榶an gida kakarmu ta yanke saka sai mu kwashi gara, yace Allah sarki beauty yau dai gani ta dan harare sa cikin wasa tace,yau kam sai dai aci na gida nan ya gaida Umma sannan ya nufi sasansu Bily ta zauna zata cigaba da shafa ma Umma kafa tace a鈥榓-a鈥榓 na yafe jeki gurin mijinki,haka ta bishi. Ai suna shiga falon farko ya ajiye(son)kan kujera ya jawota zuwa kirjinsa,wata irin ajiyar zuciya ya saki, jinsa yake tamkar an masa gafara,yace I miss you beauty,sannan ya lalubi bakinta.sun jima sannan suka dauki dansu zuwa sasansu. Nan ma da suka shiga ya kara jawo ta  jikinshi ya tura hannuwan shi cikin rigar ta yana wani sansanar kamshin ta ta dan ture shi abban son kaki bari nayi maka sannu da zuwa ma ya dan tsotsi bakin ta toh ai beauty wannan ita ce sannu da zuwan ko? Ko akwai wanda yafi wannan ya kara shige mata dole ta hakura saida ya ja ta suka lula duniyar da suka kwana biyu basu je ba sannan suka yi wanka ta kawo mashi abinci yana ci yana kallonta yana jin nishadi da farin cikin dawowarsa wurin kyawawan iyalansa. 


Da dare sun gama shirin kwanciya tana jikin Yarima son na gefen su sai kawai wayar Yarima ta fara ringing kuma tafi kusa da ita sai ta dauko Wayan kan screen din taga an rubuta T.girl ta mika masa sai ya kasa dauka tun a nan ta gane bashi da gaskiya sai ga call din ya kara shigowa sai ya dake dan kar ta zaci wani abu ya dauka duk da haka tana kwance jikinshi kuma tana jiyo muryar ta kadan kadan tana lura da a darare Yarima ke amsa mata har ya kashe tace kai da wa kake waya ya dake yace abokiyar karatun sa ce tace iya matsayin ta ke nan? Yarima yace ban gane ba tace kasan abunda nake nufi ai ko ita ce wadda ka maye gurbi na da ita da ka tafi sai ya hau fada shi baya son zargi kaza kaza ba dama yayi wata hulda da mace sai kice ina neman ta sai kawai ta tsura mashi ido kawai har ya gama tace masa Yarima da duk abun da kake ba wani damuna yake ba amma yanzu kasan wannan ta canza kuma da baka boye gaskiyarka amma yanzu ka koyi karya ta tashi ta dauki dan ta ta bar masa dakin ya bita da kallo tamkar ya bita sai kuma ya fasa,ransa ya sosu, yace tayi ta tafiyarta mana don taga na damu da ita shiyasa take yi min abinda take so,ya koma yayi kwanciyarsa,duk da bawai yaji dadin kwanciyar tasa bane, kuma yana zargin kansa da cewa shine bai mata adalci ba,ita kuma data kwanta sai ta soma tunanin cewa fushinta ba mafita bane,shin dama fushin tane ya dawo mata dashi kanta?Lallai fa ba fushinta bane,hakurinta ne da kuma addu鈥榓 dole ne taci gaba da hakuri tare da addu鈥榓,amma bari ta barsa sai da safe ta koma gurinsa. Da safe tayi wankanta tana sanye da riga da siket na blue jeans kanta babu dan kwali ta tufke gashinta da ribbon blue,tana zaune tsakiyar gado tana yiwa son shafa, tafi son ta shirya yaronta da kanta. Yarima ya rasa sukuni dole ya nufo dakin beauty ya iske ta tana kici-kicin saka masa pampers. tsayawa yayi ya harde hannu daga bakin kofa yana kallonsu, cikin tsananin sha鈥榓wa, ajikinta taji da akwai mutum a bakin kofa,da sauri ta juyo tana kallonsa,murmushi ta sake tare da cewa, abban son muna sauri muzo mu kwashi gaisuwa shine ka rigamu zuwa?Ya shigo cikin jin dadin yadda ta tarbe shi,shima gadon ya hau ya zauna kallonta yakeyi sannan yace,ni da kuke fushi dani?Ta dora masa son akan cinya, kafafunsa kuma suna kan gado tana kokarin sa masa wando,tace haba nawa, wazai fushi da aljannarsa?Yasa hannu ya shafi kumatunta,dama matan duniya suyi koyi da kyawawan halayanki na hakuri da saurin yafiya,ga mazajansu,saboda ladabin da kike min yanzun ina jin kunya ki kamani da wani laifi tace ni dama ina jin kishinka bana son ka dinga rabar mata abin yana soya raina,ta zuba masa idanu gami da tagumi ya jawota zuwa jikinsa,insha Allah ba zan kuma ba,kinji?Tace to ka yafe min jiya na barka kai daya amma kasan banyi wani bacci ba,yace na yafe miki beautyna, inda kana gurin kai ko baka san so ba zaka fahimci wadannan suna cikin mayen so amma su basu gane ba.


Ranar da Yarima zai fara halartar asibiti don fara aiki a matsayin babban likitan mata,duk hankalin Bily ya dagu,gani takeyi matan zasu kwace mata miji,ya gama shirinsa tsaf cikin suit,takwas saura kwata ya kalli beauty yace duk wannan damuwar ta mecece?Tace to doctor ba ka fa karya ba zaka fita,ya tura mata kofi zuba min lipton kinsan bazan iya karyawa 8:00 ba,tace to in ten din tayi in kawo maka office?Ya girgiza kai,bance ki fita ba,tace to ni don Allah kada fa ka kalli mata,cikin sigar shagwaba tayi maganar, yace cikin dariya kema kinsan dole na kallesu tunda sana鈥榓ta ce kallon nasu,ina nufin aiki nane duba lafiyarsu, in ta kama ma har taba jikinsu zanyi,t tace daina gaya min abin haushi,ya dubi agogo beauty barni in tafi,kinsan cikin tsarina babu African time 8 nayi alkawarin halattar office kinga saura mintuna,ta dauki jakar muje in raka ka Umma tayi maka addu鈥榓.yace ta min tun asubahi zan dai musu sallama a tsaitsaye, suka fita tare.goma daidai ta kirasa cikin hanzari ya daga wayar tace yaya aiki nawa?Ya lumshe idanu ya bude,aiki kam gashi nan inayi,kamar ni aikin ke jira,dama kinsan Allah beauty?Yacigaba tunda na zauna kan wannan kujerar marasa lafia suke shigowa ga kuma katunan wasu nan jibge,so ki tayani da addu鈥榓,tace zanyi amma break fa?Yace babu time tace haba don Allah shikenan nima bazanci komai ba,yace no,no kada kiyi min haka, me son zai sha yau?Tace duk mu hakura har dashi yace,a鈥榓 zanci to nan da sha biyu kinji beautyna. tace zan kira sha biyun dai,ta kashe wayar.


**************************

Haka suke rayuwa mai ban sha鈥榓wa,sai dai a boye Yarima yana amfani da wani cream lokacin saduwarsu wanda a lokacin tarayyarsa da Tina yasan wannan in ya shafa shi yana tsinka spam ba zaiyi da ba sam bata sani ba ta dai gaya daina mata zancan tsarin iyali.

[8:41AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 86馃彽


Duk wannan satin Bily rigima takeyi ita tana son taje Zaria,ta jima tana naci yana cewa son bai saba da iska ba,baya so a debo masa sanyi,ta hakura amma yau ta tada daru. kallonta kawai yakeyi duk taki cin abinci yanzun ma da zasu kwanta sai ta saka kanta gurin kafafunsa komai tayi sai yaji birgesa takeyi,ya tashi zaune yanzu beauty ba zaki ci abinci ba?Ta tashi zaune tana shasshekar kuka,don Allah yaya zanyi in iya cin abinci?Ni dai in kana son inci ne sai dai inka yarda inje inga mahaifana. sun jima suna son ganina kuma su suna min kara ne irin na 鈥榶ar fari bazasu iya zuwa gidana ba,sai yaji tausayinta yace to naji zakije,amma shine kika juya min baya,alhalin kin san na tsani hakan ko?Ta fada jikinsa to yi hakuri yaushe zan je?Yace jibi amma kwana nawa zakiyi?Tace sati ya zaro idanu,to wallahi a fasa tafiyar,ta kankamesa sorry,to kwana nawa zanyi?Yace zan daure kiyi daya,tace haba dai yaushe muka gaisa?Ta turbune fuska ta ja baya,indai daya ne na hakura,yace to naji biyu,tace ina laifin uku don Allah,shima a maneji, yace to naji amma gida nawa zaki bana sonki yawaita fita ana kallonki, tace to ina zanje ma daga fa gidanmu sai gidansu Umman Mansu,sai ko makota sai gidan Mansu din,ya zaro idanu Kaduna?Tace eh,ya girgiza kai ina hauka nike in barki kije Kaduna mutanan da aka ce suna kwace matan aure?Yanayin yanda yayi maganar sai data yi dariya, tace duk ba gaske bane fa ni dai iyakata gidan Mansu,sai kasuw... ya katseta da cewa kasuwa? Tabdijam, ki fasa zuwan ke nan salon kije maza suyi ta kallonki bazan iya ba,tace to shikenan na fasa zuwa kasuwan kaji?Amma fa gobe zanje gidan Umma muyi sallama da kuma Modibbo,yace goben sai da daddare na kaiki.ta shirgi tsaraba ga kudi da Yarima ya jibge mata, sirikanta ma sun hada mata tasu. su Mama sunyi murna da zuwanta, wannan karon ranar data zo tasa babansu ya kira masu aikin gini sukayi mata lissafin kudin da gidan nasu zai ci,fulastan bangon tsakar gida da kuma yin barandar waje tare da siminte bangon waje,Nan ta cire kudin ta bada ga abinci lodi-lodi sannan tabawa Umman Mansu kudi in an gama gyaran ta siyawa Mama kayan daki.itama ta bata nata.su Ladiyo duk sun zama ababen tausayi, suma ta basu kudi dama kowace bashi yayi mata kanta,nan sukayi ta godiya,da dare tana kwance Umma tana shafa鈥榠 da wuturi,Yarima ya kirata yace waton yau an sami Mama an manta dani ko?Ta dan dubi gefen Mama,sannan ahankali tace,haba nawa komai na keyi kana raina,ban manta da kai ba,shine kaima kaki ka kirani yace ina sane na zata zaki kirani ne,tace to ya aiki? Yace lafia ina son dina?Tace gashi nan kusa dani yana bacci yace Mama fa?Tace gata can tana sallah,yace a鈥榓 kice ba hira to bari muyi text to tace ina jira.sai ga Yarima yana kwance ya dage yana rubuto ma beauty maganganu masu dadi da nuna kulawa akan mutum, itama tana bashi amsa.Mama ta idar sai Bily ta ari bakin Yarima tace Mama ya kira ku gaisa kina sallah,yace yana gaisheki,tace ina amsawa haka sukayi ta text har nisan dare.kafin suka hakura.dangi da makota sun san Bily tazo,dan kuwa sun sha tsaraba,washegari kuma Kaduna ta diba zuwan bazata ta yiwa Mansu,sai da suka zo kofar gidan ta kira wayar Mansu tace Mansu kina gida?Tace ina zani Bily,menene?To ki fito kisa abude mana gate. Mansu tace bana son wasa fa,na taba maki wannan wasan?Inji Bily,ta fito da gudu tana kiran baba maigadi,har ya tsorata tace leka ka gani muna da baki Yana bude kofa sai ga zungureriyar Jeep din Yrm wadda ya bada aka kawosu ciki suna shigowa ana tsayawa ta fito da murna suka rungume juna.Asabe ta fito dauke da son yayinda Atika ta fito da jaka da kuma wayoyi,Bily kenan an zama manyan mata,daga kin ganta kinsan matar manya ce, tayi 鈥榶ar kiba tajin dadi,ga wata gogewa da fatarta tayi, ita kanta tasan tayi. Nan suka shige ciki,hira ta balle labarin daddadan zaman da su Bily sukeyi ne take labarta wa aminiyarta,nan Mansu ta shiga tsokanarta da cewa,da ko kin raina masa wayo ke ya miki yaro,Bily ta rufe mata baki da cewa,yi shiru an daina wannan zancan tuntuni tunda na gane halittarmu ba daya bace. Namiji komai kankantarsa indai ya balaga to namiji yake, suka sa dariya,tace bare nawa gara kowa dashi baya gajiya nan suka koma hirar kayan gyara jiki dana kwalliya.kwana dayan da Bily tayo gidan Mansu tayo guzurin tsarabarta mai yawa tare da shawarwari,itama kuma dama ta cika Mansu da tsaraba da kuma kudi har Mansu taso taji haushi.Bily tace,nasan ba don baki dashi bane na baki don kawai kullum burina in kyautata miki,suka dawo Zaria washegari suka dauki hanyar Bauchi. bayan ta cika iyayanta da kudi. shiko Yarima duk bayan mintuna sai ya kira waya ya kosa yaji tace sun iso gida,tazo da tsarabar su doya ne, dankalin turawa da dai sauransu,tasa aka gyare musu gida ta turare shi da turaren kamshi tayi gayu cikin riga da wando shigar da bata taba yi ba duk da Yarima na son haka, Mansu ce tasa ta lallai ta ringa yi tunda yana so,kuma yanzun babu kalolin matan da ba zai gani ba masu kuma kalolin dressing dama ta gyara kanta ta shiga kitchen ta shirya girki masu dadi koda Yarima ya shigo sasan nasu sai kalolin kamshi suka masa sallama,kan kujera ya ajiye jakarsa ya nufi dakin beauty kwana ukun nan a daddafe yayi su baya son ya dawo idanunsa basu ganta ba,amma me?Yana shiga bata ciki,sai gashi yana ta nemanta,kitchen ne toilet ne ya nufi sasan sa basa can,ya sauko falonsa na kasa ransa ya sosu ya ciro waya yana neman layinta,sai kawai ji yayi an rungume shi ta baya,tace oyoyo nawa!Yayi ajiyar zuciya sannan ya birkitota gabansa tsayawa yayi yana kallonta sannan ya jawota da karfi ya matseta a kirjinsa,kinyi beautyna I love....da sauri ta dago tana kallon bakinsa,shi kansa bai san lokacin daya soma furta kalmar ba,tace da gaske kakeyi? Ya lumshe idanu tare da jan numfashi yace ban sani ba beauty ta kwantar da kanta laf cikin kirjinsa sannan tace don Allah ka soni kaji? Shine kawai abinda na rasa a rayuwata. ya dago fuskarta yana kallo tace,tana kallon kwayar idanunsa zuciyata zata so ka,don ta aminta dakai tana girmamaka tana darajaka,kila ma tana tsananin sonka.Ya manneta har sai da ta kasa numfashi,sannan ya nemi bakinta,kukan son ne ya dawo dasu cikin hayyacinsu,ya fadi daga kan kujera inda yake zaune,babansa ne yayi zafin naman cafko sa ya daga shi sama 


Haka suke gudanar da rayuwarsu kowa yana kaf-kaf da dan uwansa tare da gudun bata ma dan uwansa  Yarima yana zaune cikin office dinsa marasa lafia suna ta shiga da fita kowace mace tafi son ganin doctor Yrm,a cewarsu yasan aikinsa,da yawa sunce in sun gansa kuma ya rubuta musu magani ko yace aiki ne in anyi suna samun salama, wasu 鈥榶anmatan kuwa son ganinsa ke sa suyi ta ziyarar asibitin,nurses har ma da wasu daga cikin likitocin mata su kan so ko da hira ne ya dinga yi dasu,amma shi sam baya sakin fuska,ko tiyata ce ya shiga yana gamawa yake kame kansa,shiyasa suke shakkar shi tare da ganin girmansa.wata nurse ta shigo da kati ahannunta tace,likita ga Emergency an kawoma doctor Salihu yace akawo maka,ya dago ya dubeta idanunsa cikin farin glass shi me ya hanasa dubata?Tace yace ka fishi sanin wannan matsalar,ya dan taba baki gami da daga kafadu shigo da ita na gani,bai san lokacin daya mike tsaye tare da cewa,oh my God!Ganin yanda fuskar yarinyar yayi caba-caba duk ta lalace da ruwan batir,ya dubi nurse din ita da matar dake tare da mara lafiyar yace,kuje gurin doctor Salihu kuce nace yayi mata abinda ya dace ya bata gado zan dubata inna tashi,kuje dai zan kira phone dinsa.鈥榶ar wani hamshakin dan siyasa ne aka batawa fuska kuma 鈥榶arsa daya ce shi baya nan ma yana saudi anyi masa waya dai kuma yace zuwa gobe yana kan hanya.kafin Yarima ya shige gida sai daya dubata,tana bukatar aiki ne sai dai akwai karancin kayan aikin a nan kasar,shi yana dasu amma ko fara amfani dasu baiyi ba,domin asibitinsa ya shigo dasu.hankalin mahaifin yarinyar yayi mugun tashi da yaga 鈥榶ar tashi.doctor Salihu ya samu a office yana cewa don Allah ataimaka masa ko nawa ne zai bada ya sani anyi haka ne don kawai abata masa rai a daga masa hankali,Dr. Salihu ya dauke su zuwa office din Dr. Yarima .

[8:42AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 87 馃彽


Nan Yarima ya yiwa mahaifin bayanin cewa matsalar ta kayan aiki ne,cewa yayi shi zai bada kudin kayan aikin ko nawa ne. Yarima cikin satin yayi aike kayan suka iso, ya bukaci hoton yarinyar lokacin da take lafia,Allah cikin ikonsa sai gashi aiki ya kammalu zuwa wasu kwanaki ya bude aikin,an sha mamaki ganin fuskar yarinyar ta samu,shi kansa sam bai zaci aikin zaiyi kyau haka ba,sai dai kamanninta sun dan canza kadan,sai tafi da kyau ma,wannan aikin ya jawo daukakar sunan Yarima a fadin kasar nan inda asibitoci masu zaman kansu dana gwamnati suka yi ta gayyatar Yarima ire-iren wadannan aikin har ya kasance baya samun isasshen lokacin zama a gida,wani lokacin kuma cikin dare ne zaki ga anyo masa waya ana nemansa Emergency. Tiyata da makamantansu,abin yana cin ran Bily,domin aikinsa yanzu yasa bata samun kulawa sosai zata tsaya tayi gayun da kananan kaya ne da shaddodin ne zuwa lesuka,atamfofi amma wani lokacin ma har ta cire tasa kayan bacci bai dawo ba,yana dawowa kuma duk a gajiye da yayi wanka shikenan zai kwanta sai bacci.yau ma kusan kwana tara kenan haka na faruwa,domin wannan karon har asibitin Ibadan yaje yayi kwana biyu.yau tana sa ran sati ne da Lahadi dole yana gida,tunda yayi sallar asubahi ya koma ya kwanta,tara daidai ta tashi ta shi ta koma dakinsa ta zauna kusa da fuskarsa tace,abban son bazakayi wanka ba?Yayi mika barni inyi bacci beauty jiya nayi aiki sosai,mutum shidda na fede,tace shikenan mu kuma yanzu aiki yafi mu, ya tashi zaune yana kallonta,kamar yaya?Ta dubesa to yanzun fa bakada lokacinmu,yau kana aiki nan gobe kana aiki can.ya matso kusa da ita ya jawota jikinsa wannan aikin fa in kinyi tunani beauty dalilinsa ne na bata shekaru ina karatu,kuma an samu Allah ya taimakeni inda zaki lura aikin taimako ne,kin sani na fiki son hutu tunda kika ga sai mu kwanta mu tashi ban lalubeki ba kin san wani aikin yasha gaban wani Amma kiyi hakuri ko wane dan adam yanacin zamaninsa ne,yanzun lkcina ne akan aikina wata rana sai kiga an sami wanda ya doke ni,to ba kya ganin gara nayi amfani da damata da lokacina in samu aljannata, nasan dama ke ba makawa in dai miji ke daga kafa a shiga tawa dama a dage take shikenan sai ki jagoranci sauran matana na gidan aljanna,tayi driya to kwanta ka huta,yace a鈥榓 na fasa yanzun 鈥榶ar hira zamuyi irin wadda muka kwana biyu bamuyi ba, tace yau ai kana gida harda irin wadda bamu taba yi ba duk zamuyi. Yanzun dai kwnta kurum kayi baccinka,kuma matseta yayi sai sukaji kiran waya,ya kalleta fuskarta daure ya dauki wayar yana yi mata dariya,bataji kome aka ce masa ba ta daiji yace zanzo to nan da 10.ya fada tare da kallon agogo,ta mike zata fita yace zo nan gimbiya bana fushi bane maigadon zinari,marasa lafia na zan duba ance biyu daga cikin wadanda nayiwa fida basu farfado ba,amma ina ganin ba wata matsala bace,kafin goma zasu farka,tace um ai kai nasan in kaje sai kuma na ganka,yace shirya muje tare ta dubesa da gaske? Yace na taba cewa ki shirya muje?Tace a鈥榓 ta fita ta zuwa dakinta cikin doguwar rigar shadda ta fito aslin soly ja,takalmi da jaka da gyale farare,hatta abin hannunta fari ne, shi ko farin yadi ne mai shara-shara wnda kana gani kaga yadin manya,salon daurin dankwalin Bily ya burgesa yace kai beauty dafa naso inyiwa kaina asara tayi fari tareda cewa ko?Yace ina son? Dashi zamu dakkosa in kina cigaba da min wannan farin tafiyar tamu zata iya fasuwa,tace yana hannun Asabe,yace amsosa mukadai zamu baki so muyi 鈥榶ar hira irinta sirri?Tace to muje in amshesa sai muyi ma Umma sallama.Son yayi kyau cikin wandon jeans,pink da fara kar din shirt, takalminsa pink da 鈥榶ar safa fara,shine ya dauki son din suka yiwa Umma sallama da cewa sunje asibiti,hakan yayi matukar birge Umma,suka nufi katuwar jeep dinsa tace tunda nazo gidannan yau ne rana ta farko da na shiga unguwar nan da rana kamar yanzun,ya dubeta yanzun ma shahada nayi don fa ni bana son ana kallemin ke,tace um wata rana inna kallemu sai inga tamkar masoya? Ya dubeta yaya ake gane mutum ya kamu da so?Tace kaine fa doctor nawa, zaka fini sani yayi murmushi ni ba likitan zuciya bane,kuma ban karanci so ba,kuma bai taba kamani ba,don haka ban san shi ba,tayi shiru yace kin taba so?Ko kuma sanin yanda yake?Tace ban taba so ba,sai dai ina sha鈥榓war aso ni,ina so in sanshi inyishi,da sauri ya dubeta kiyi ma wa? Tace kai mana nawan. Ta cigaba na taba karantawa wani littafi, marubuciyar cewa tayi shi so wani halitta ne wanda da zaran mutum yaga abinda yake so zai shige shi nan take,da zaran ka kamu da son wata baka da sauran nutsuwa,zaka kasance cikin tunanin abin sonka tare da kasancewa da abin son naka duk rintsi duk wuya,Yarima yayi dariya tare da cewa,malamar so kice kinsan so kenan?Tace a鈥榓 naji dai labarinsa amma banyi saba ban kuma sansa ba.suna isowa asibitin shine ya dauki son suka jero duk da cewa Asabar ne asibitin yana cike da mutane,sai kallonsu akeyi ballantana nurse din da suke nan sai kallon Bily sukeyi,a cikin zukatansu suna cewa lallai dole ne Dr. Yrm ya dinga yiwa mata kallon baku yi ba,daf da zasu shiga office dinsa wata Dr. Jamila ta iso tana cewa a鈥榓 Dr. kai da madam ne?Ta amshi son suka shiga office din ta bisu,tamkar ba asibiti ba office din domin ya tsaru(AC)ma kusan guda uku ne tace dama shi dan sanyi ne,gadon dake gefe ne irin wanda marasa lafia kan kwanta kawai zai nuna maka cewa nan office din likita ne.kujerar da aka tanada domin likitan itace ya nuna Bily tare da cewa beauty please sit down,ta zauna tana kallonsa tare da cewa,yau nima nazama doctor. Dr. Jamila ta dubi Bily yaya gajiya madam ya kike? Lafia,inji Bily fuskarta ba walwala tace Dr. Familyn ka masu kyau,yace na gode me kika zoyi asibiti yau Sunday?Tace ina da mara lafia,maman kawata ce ba lafia,yanzun sukayi min waya wai jikinta din ya tashi shine nazo in duba,Allah ya sauwake.

Yace zaki zauna anan ne in dawo?Ta mike muje nima na samu ladan gaishe da marasa lafia.yasa hannu ya dauki jakarta mu gani kina da kudin da zaki basu sadaka ko,tace duba ka gani ni na jima rabon da nasa jakar nan kila kuma asamu koba yawa,ya dago daga kallon cikin jakar da dan murmushi,yace Haj. Bily ai jakar taki tam take,ai na sani ke din babba ce,indai kudi ne,tace oh zagina zakayi,me nake saidawa?Yace au bakya sai da komai fa shine kike da kudi haka? Cikin tsokana yake mata maganar,ta warce jakarta nidai muje,Jamila itama dariya takeyi a xuciyarta tana mamkin dama ashe Dr. Yarima yana wasa haka?Ya mika hannu zai amshi son tace muje in rakaku. Bily ko yanda Jamila keta iyayi da salo shine yake bata haushi,kodai mijinta yana kula ta?Suna shiga dakin da marasa lafiar suke sai da ya fara shiga inda nurse din dake kula dasu suke zaune daga ganinsa duk suka tashi, Bily ma suka shigo suka gaida Bily tare da cewa madam din Dr. ce,Bily tayi murmushi suka amshi son suna cewa fine boy dayar tace Dr. dukansu sun farfado yace Alhamdulillah, bari mu duba su suka tafi dukansu,daga kansu Bily ta soma rabon kudin sannan tabi sauran marasa lafian,suna godia,nan taga da sauran kudin tasa sister guda daya ta rakata sauran dakuna don basu taimakon dubu daddayan,sannan taxo taba wadannan nurses din guda biyu ta samu ya gama rubuta ma mara lafian maganin daza a siyo,sannan suka fito har gurin mota sukayi musu rakiya harda Dr. Jamila ya amshi son yana cewa,to mun gode,sai Monday suka ce Allah ya kaimu,ta zauna agurin zamanta shi kuma ya shiga gurin tuki,ta kai hannu tare da cewa,zo nan son baba yayi driving ko?Ya rike baban gam, Yarima yace bazai zo ba,da kin iya da kin ja mu,tace to ka koya min yace sai kin gama fushin,tace fushin me?Yayi dan murmushi sannan yace haba beauty ni yanzun ko ido kika kifta nasan me hakan yake nufi bare fushinki,tace to wai fushin me zanyi ne? Yace kin fini sani kila ganin Jamila ne, tace umh wannan sarkin shisshigin nifa batayi min ba sai wani kaudi takeyi maka, yace to banda ke beauty kema mace bata miki ba bare ni?

[8:42AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 88馃彽


Ni dake da kamarki sanin kanki ne kaf kasar nan ke daya ce kike burgeni,tace um ai so bashi a muni, haka sha鈥榓wa yace wai wanene so din nan ne?Ban fa sanshi ba, sha鈥榓wata kuwa bata zuwa irin nan guraren,don haka kibar damun kanki ni naki ne ke daya,tace to yaya batun koyan motar mu fara yau mana?Yace, ok bari muje ko dana minti talatin ne.an kammala gina katafaren asibitin na Yarima,asibitin katon gaske ne mai dauke da fannoni na kalolin cututtuka,ga na鈥榰rori na aiki irin wanda ake cewa sai an fita kasashen turawa ake samu,ga gefe na musamman saboda tada komada wato gyara fata da sauran abinda yayi course akansu an tsaida ranar bude asibitin,nan Yrm ya shiga yo gayyar jama鈥榓 musamman abokan karatunsa wadanda ke kasashe daban- daban.da kuma abokan course dinsa ciki harda Tina.yaso da zai yiwu daya dauki Tina aiki a asibitinsa,saboda ya samu abokiyar aiki fannin fata domin itama ta kware,amma zaya gwada ya gani indai ta amsa gayyatarsa tun ana jibi bikin bude asibitin baki suke sauka,鈥榶an Zaria ma sunzo gida da masaukin baki tam da jama鈥榓 banda otal-otal da aka kama cikin katon filin asibitin akayi taron inda manyan likitoci,kwamishinonin lafia,zuwa ministocin lafia,ga kuma 鈥榶an uwa da abokan arziki. Su Tina an duro domin tana ganin sakon sai taji tamkar yayewar matsalarta ce,don haka bata yi kasa a gwiwa ba,ta amsa gayyatar, domin tana azabar son Yarima.taro yayi taro,bayan yin duk abinda yakamata aka bude asibiti inda mai martaba ya wakilta sarkin musulmi ya bude asibitin mai suna(Dr. Yarima Hospital)an dunguma cikin asibitin don ganin cikinsa,hatta bakin kasashen wajen sun jinjina dukiyar dake cikin asibitin,wato kayan aiki zuwa kayan kawata asibitin kafin sati daya tuni asibitin ya kama aiki gadan-gadan.gashi dama ya tanadi likitoci da kuma nurses kwararru.Tina ma ta yarda da gayyatar da Yrm yayi mata,amma sai taje ta dawo. Al鈥榓mura sunci gaba da tafia yanda yakamata,beauty kam yanzun ta gama yarda Yarima nata ne,yanzun ne ta gane cewa halayan Yrm masu kyau ne in ta cire neman matansa wanda ayanzun take tunanin ya daina yana da kyauta ga sadaka yana da kulawa gami da ibada.girman kan da ada take ganin yana dashi yanzu ta gane shi mutum ne mai matukar saukin kai da kuma tsokana duk da bai cika dariya ba,zaya tsokaneka yayi fuska tamkar bashi yayi maganar ba,tuni ya soma ginin gidansa babu nisa sosai da asibitinsa,  son ma tuni ya soma takawa shiko Yarima kudi sun kara zaunawa dama dogo ne ga kuma 鈥榶ar kiba irin ta hutu, azumi yana gabatowa tuni Bily ta cire son daga nono,yana gurin Umma tana son zuwa zaria kafin azumi,amma Yarima yace a鈥榓. Auta Asma鈥榰 tunda ta gama karatu tana gidan gurin Bily duk dangin Bily daga Asma鈥榰 sai su Sakina, Yarima ya sani sai dai yana musu aike ko yanzu da take hankoron zuwa zaria kafin azumi,tana son ne takai musu kayan azumi,bata san tuni Yarima ya tura musu dashi ba,sai gashi babansu yayo waya yana cewa tayi musu godiya gurin Yarima ,azumi yana ishirin suka nufi saudi, wayewar garin sallah suka dawo.rayuwar Bily abin sha鈥榓wa,yanzun ta manta da komai da duk matsalolinta na baya kuma ta yarda da batun Mansu cewa suna son juna koda Yarima baya sonta ita dai tayi imanin tana matukar sonsa, shiyasa kishinsa yanzun yayi yawa azuciyarta, harma bata iya boyewa, duk da bata da masaniya game da Tina sai dai tana zargin kamar yana neman wata,in tayi magana ya kalallame ta da baki kan cewa shifa nata ne ita daya Ranar wata litinin tana kwance a falonta, asma鈥榰 ta miko mata waya cewa ana kira,tana dubawa sunan Umma ta gani tana dagawa ta shaida mata ta fito suje gidan Modibbo zasu dubashi yanzun nan akayi mata waya kan cewa jikinsa yayi tsanani,ta mike da sauri ta nemo mayafi ta soma kiran layin Yarima ,yanayin muryarsa yasa ta wani zargi tace lafia naji muryarka wata iri?Yace na gaji ne kawai tace to zamuje duba jikin Modibbo inji Umma,sai taji yace umh humh sai kuma taji an kashe wayar.yanayin sautin muryar yafi kama da wanda yake tare da mace, don kada Umma suyi ta jiranta sai ta nufi gurinsu Umman,suna mota ta kuma kiran wayar a kashe, sauran layikan kuma suna ta ringing ba鈥榓 daga ba. zuciyarta tamkar ta fashe don bakin ciki,amma dole tayi hakuri ta shanye.suna isa gidan suka shiga gurin nasa Umma ta tallaboshi lokacin ya dubeta duk sukayi masa sannu yana tayi musu godiya,sauran kishiyoyin Umma sun dawo sun barsu acan ita da Bily,ya dan samu bacci suka shiga cikin gidan, kamar minti goma Kawu ya shigo hankali tashe yana ce musu Modibbo dama ashe baccin nan tafiar kenan?Hawaye ne suka soma zirya akan kumatun Bily,ta sani in zata tuna da tarihin rayuwarta to zata tuna da Modibbo,Allah ya jikansa ba zata gushe ba gurin yi masa addu鈥榓 duk sallah.ta soma neman layin Yarima taci sa鈥榓 an kunna a zuciyarta tace an gama kenan,wani irin takaici ne yasa taji sabon hawaye ya zubo mata ya daga wayar da cewa,hello beauty.wani tukuki taji, itace banza ya raina mata hankali cikin shasshekar kuka tace inka gama ne sai kazo nan gidan Modibbo Allah yayi masa cikawa,ta kashe wayar ta shiga neman 鈥榶an zaria. Yarima yaji rasuwar sosai,dole yayi wanka kafin ya nufi gidan,don haka sai da yaje gida saboda a cikin gidan Tina dake nan asibitin ya tara da ita kuma bazai iya yin wanka a gidan ba. bayan dawowa daga makabarta su Yarima suka shigo cikin gidan,Bily kam ko son ganin Yarima batayi,tana zaune da carbi kanta na kasa,Yarima ya zauna kusa da Umma yana mata gaisuwa,ya dubi Bily,beauty yaya muka ji da hakuri?Banda Umma dake gurin da sauran mutane da bazata amsa ba Amma duk da haka bata dubesa tace mun gode Allah,Umma tace Bily ta kasa daina kuka shi Modibbo yanzun ai sai addu鈥榓, a ranta kuwa cewa tayi yaya ma zata iya daina kuka alhalin mai tayata addu鈥榓 akan Yarima yanzun babu,sai yanzun ne data kamu da son Yarima shine zai koma bin matansa,ita kam ta gaji da hakuri bazata iya ba.har ranar da akayi uku Yrm ya kasa gane kan Bily,sam ta fita harkarsa galarin gabanta kawai takeyi ko tana dariya ne data gansa sai kawai ta daure fuska. washegari bazasu je gidan rasuwar ba domin an riga ya anyi sadakar uku,har ya fita sai kuma gashi ya dawo kusan misalin karfe sha daya tana kwance cikin dakinta ya shigo,Asma鈥榰 ya fara gani a falo yace mata ina antynki?Tace tana ciki.ya shiga tayi rigingine fuskarta tana kallon sama tunani takeyi koda iyayanta suka zo gaisuwa Yarima bai ma zo sun gaisa ba har suka tafi,duk da yayi ta kiran waya yana cewa gashi nan zuwa wai yana duba wanine sai bayan sun tafi sannan yazo.ya zauna gefen gadon beauty tashi muyi magana,ta tashi zaune ba tare data kallesa ba,tace ina jinka yace a haka zamuyi maganar kina kallon wani guri ta juyo ta kallesa sai dai ranta a daure yace wai ni shin menene ya faru ne kika saka ni cikin damuwa?Me yasa kika saba min da kanki da hirarki da dumin jikinki kinsan ba zaki dore ba?Shin ko rasuwar nan ce duk tasa kika koma haka?In ma rasuwar ce niya kamata infi jinta, domin duk yanda zaki damu ni zaki yiwa kara.ta dubesa rai bace, in kana zaton kara nayi ma donna damu da rasuwar Modibbo kayi kuskure, domin duk wanda yayi kukan mutuwa kansa ya yiwa,kuma da zaka ce na saba dayi maka kaza da kaza ina ce yanzun ka samu madadina ce?Ya dubeta ban gane ba?Tace ai bazaka gane ba,bari kaji nifa yanda na juri huldarka da mata da yanzun bazan iya ba,Allah sai in kama gabana. A haka kowa ya ganni zai zata ina jin dadi ana min kallon sha鈥榓wa da hutu amma zuciyata ba hutu?Ya daga mata hannu saurara min,me kike nufi da zuciyarki ba hutu,me na miki? In kana so dole sai na sanarda kai zan iya domin kayi ne dama don inji kana kwance da mace na kira,ai sai kaki daga wayar amma don ka cuzguna min sai ka daga, kana ce min wai ka gaji,saboda ka raina min hankali,ya mike don yin abin nan da hausawa suke cewa tabarmar kunya da hauka ake nade ta.ke ki shiga taitayinki,kin tabbata ina tare da wata ne?Kin yarda Allah ya tsaida ke ranar shaida?Tayi shiru ya cigaba da cewa,shikenan tunda da ina neman mata yanzun bani da damar nayi wani dan kuskure sai ace ina tare da mace,to duk yanda zakiyi kiyi,tace haka kace?Shikenan ya dubeta ko da sanda nake yima baki daga min hanakali irin haka ba sai yanzun? Tace gara da lokacin baka gabana kuma kaima baka damu dani ba,ballantana kasan kona damu ko ban damu ba,sannan ko banza lokacin baka boye gaskiyarka, amma yanzun fa?Shikenan kawai tunda kace duk yanda zanyi inyi ni kuma zan nema ma kaina mafita,ta mike ta shige toilet.ya rike kansa tare da yin ajiyar zuciya sannan ya fita.wasa-wasa rigima taki karewa ranar ya ritsata da cewa wallahi shi bazai iya ba,yaya yana matsayin mijinta zata barshi yana walagigi shi in ta ci gaba da wannan halin zai hadata da Umma, tace zanfi son haka domin sai tasan me kakeyi,kila in tayi maka fada kaji nata,ta cigaba da shafa manta,yace to yanzun naji na amshi laifina shikenan me kike so inyi miki ki huce?Ta dubesa alkawari zaka dauka tsakaninka da Allah cewar bazaka sake bin mata ba,yace naji zanyi amma kinsan mutum yace zai dauki alkawari tsakaninsa da Ubangiji ba karamin abu bane,nasan muhimmancin alkawari nidai ina bukatar addu鈥榓rki kuma zanyi kokarin kiyayewa, kenan ka yarda kanayi?Yace a鈥榓 bawai na yarda bane,don dai ranki yayi fari ki daina fushi shiyasa nace miki na yarda,don Allah kinji? Ta tsura masa idanu,yazo ya rungumeta,don Allah beauty in na sake ki mini duk hukuncin da kikeso, tace shikenan ya wuce, duk da haka tana masa komai amma ta kasa sakewa dashi kamar da, yanda take wasa ajikinsa suyi ta wasa ta bashi abinci abaki amma yanzun batayi.

[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 89馃彽


Ya kuma samunta da complain shifa bawai tamai abinci yaci ya kwanta da ita ne farin cikinsa ba,yanzun farin cikinsa bai wuce ta saki jikinta ta koma normal ba,data zauna tayi tunani  da tayi banzan nan dashi in yayi gaba can zai tare inda kadangarun bariki suke sai yaga dama bacci zai kawosa amma shi yana ta faman binta sai ta kara rikosa tare da jansa jikinta saboda ta samu ta rabashi da kowace,cikin kwanakin suka koma daidai da sharadin cewa inya kara duk hukuncin data ga dama ta masa shi yaja. yaita kokarin ganin bai kuma barin wata baraka da zatasa beauty ta gane yana tare da wata ba.Hankalinta kwance yanzu,damuwarta bata wuce son samun ciki ba,wanda in tayi magana sai yace ta daina damun kanta,kwata-kwata shekarun son nawa da za鈥榓ce sai anyi masa kani?Sannu a hankali ta soma zargin cream din da yake shafawa in zasu kwanta, domin ta kula inya kare komai matsuwar da yayi da ita yakan hakura,don haka sai ta dauko salon cewa ita dai tana jin zafi maimakon ce matan da yayi cream din zai sa su jin dadi,ta tubure tace ita sam bata so ga zatonta zai bari sai taga yayi matukar daukan zafi da ita harma ya fita harkarta, gami da kaurace mata, ita ma ta yarda da hakan suka share juna na kimanin sati uku,su duka sunji jiki domin shima duk da yana da Tina ya gane bawai biyan bukata ne kawai amfanin beauty ba tana da wani matsayi wanda mata da yawa basu takashi ba a cikin zuciyarsa.ita kuma babu abinda yafi kona mata rai yanda ya daina cin abinci agida wani sa鈥榠n ma sai tayi kwana biyu bata sashi a idanunta ba,kuma zuciyarta ta dinga raya mata cewa yana can tare da matan banza.Ganin bazata iya cigaba da wannan zaman ba yasa ta samesa, sai ce mata yayi indai bazata yarda suci gaba da amfani da wannan cream din ba sai dai su zauna a haka Ga Allah ta koma ta cigaba da gaya masa kafin wani tsawon lokaci sai gashi ya soma sakkowa,tana zaune yazo ya sameta yace tayi masa tuwon semo,bata tsaya jan aji ba ta shirya masa tuwo miyar danyan kubewa,sannan tayi kwalliya irin wacce bata taba yi ba,lokacin da yazo cin tuwon sai ta bayyana donta zuba masa tun yana satar kallonta harma daga karshe ya zage da kallon nata ita kuma tayi amfani da wannan damar ta saki jikinta tamkar wani abu bai taba faruwa ba.ganin haka shima yabar cin abincin suka koma wani fanni,sai da suka tausaya ma junansu,aranar lallai sun fahimci sunyi missing din juna daga nan suka ci gaba da harkokinsu. amma kuma sai me?Data samu ciki wata daya biyu sai ya zube kuma ya dubata acewarsa ba wata matsala anyi haka har kashi hudu,inda abin ya soma damun Umma,su anty Saliha kuwa cewa sukayi ita ke cirewa shi kuma tsabar son mace ya hanasa ya gane hakan, tsana suka kuma saka mata tare da zuga Umma akan Yarima ya kara aure, umma cewa tayi babu ruwansu amma anty Salma sai data kirasa tace, lallai ne ya sake aure,sannan sukayi kungiya suka samu Bily suka ce inma tana cire ciki ne don tayi sisi to su karuwa suke so kuma Umma tace dole ne ma ya sake aure.hankalin Bily yayi matukar tashi,jin cewa harda Umma cikin lamarin.da sauri ta kira Mansu ta shaida mata halin da take ciki,Mansu tace mijinki ya canza miki?Tace,a鈥榓 shi yana boye min maganar nema bai san sunzo har gida sun gaya min ba,tace to ko da wasa kada ki canza masa kinji ko?Tace to sannan kadaki yarda ki sanar dashi duk abinda 鈥榶an uwansa suke miki tace shikenan Mansu tace shawara daya itace ki dage da addu鈥榦鈥榠,nafilfilu kiyita gayama Allah,tace to cikin kwanakin shi kansa Yarima ya fahimci tana da damuwa,haka nan inya farka sai ya ganta tana nafilfili,wannan karon data samu ciki bata bari ya sani ba,don tana tunanin da sa hannunsa yawan barin ta tunda bai taba nuna damuwarsa kan cikin ba don ya fita,sai dai ya damu da lafiarta,ita kanta tana son ta sake haihuwa ballantana ga bala鈥榠n danginsa duk da nuku-nukun data ke har cikin yakai wata uku. Nan fa ya farga ya tambayeta kan cewa ciki ne da ita ko?Tace me ka gani?Yace, alamu da dama,tace shine don Allah ka tayani addu鈥榓 wannan karon Allah ya bar min,yace to yanda yake amsa zancan tasan bai kai zuci ba,sai dai zatayi taka tsantsa da duk wani magani da zai bata.har aka kwana biyu bai bata komai ba kuma bai canza mata ba,yana ma taji da ita ne,ashe yana amfani da wani mai ne in yayo wanka sai ya shafashi cikin toilet din a gabansa da zaran ya kwanta da ita sai cikin ya fita wannan karon ma haka yayi bayan ya fita,zuwa asibiti misalin sha biyu sai taje fitsari nan taga jini,da sauri ta fito taje ta shirya ta nufi gurin Dr. Aisha,bayan gama bincikenta ta gano cewa Yrm yana amfani da wani sinadari ne dan fitar mata da ciki,sannan tace wannan cikin ma fita zaiyi.Bily bakin ciki ya isheta,Dr. Aisha tayi mata allura tace taje gida.har zata gida sai kuma taga ba zata iya daurewa ba sai taje asibitin ta tabbatar masa ta gano komai kuma zata shaida ma Umma komai,tana zuwa baya office nan nurse din dake kula da marasa lafian dake shiga gurinsa ma鈥榓na mai kai masa katuna tace yanzun nan ya fita gama marasa lafia suna jiransa zai dubasu da yake sun san ita matarsa ce,tace ina to yaje nurse tace,kila suna wani aiki ne a cikin gidan Tina,har zata shiga office din ta zauna sai kuma tace am nurse ina ne gidan?Tace gashi can bari in nuna miki suka fita ta kaita har bakin gate din gidan kai tsaye ta shiga ta ratsa dan tsakar gidan mai kyau da furanni ta isa kofar da take zaton ta falo ce,ta tura sai taci sa鈥榓 abude ne ta tura ta shiga ta shiga falon mai kyau ta waiga ko鈥榠na babu alamun mutum sai dai taga kofofi guda uku.ta juyo da nufin ta fito sai taji maganar TV cikin wani daki ta nufi gurin har zata kwankwasa sai dai ta fasa ta kama murfin kofar ta murda sai taga kofar ta bude,duk da gargadin da zuciyarta ta rika mata kan cewa ta fa yi gangancin shigo ma mutane gida,hakan bai hanata leka dakin ba,TV ta hango sai ta cusa kai,take numfashinta ya soma zarya da kyar ta iya furta Inna lillahi wa鈥榠nna ilaihi raji鈥榰n da karfi. Wanda hakan yayi sanadiyar jawo hankalin Yarima da wanda kamu ta masa irin wanda ake cewa turmi da tabarya, da kyar ta lalubi hanya ta fita,tana mai data sanin wannan zuwan da tayi. data jirasa ya koma gida ta zauna acikin mota ji tayi jinin yatsunko mata gaba daya da sauri ta ciro wayarta ta kira direbansu tace dan Allah ya hau mashin ya sameta asibitin Yarima tazo ne bazata iya dawowa ba,babu jimawa sai gashi ya jata zuwa gida,dakyar takaicin gidan yasa ta isa dakinta ganin halin da take ciki ne direban ya shiga gurinsu Umma ya shaida musu.lokacin da jakadiya ta iso ciwon baya da mara sun tirnike ta,nan take jakadiya taje tana ya mutsa baki tana cewa Umma wannan mata ta Yarima bata da dabi鈥榓 to gata can ta kuma yo allurar zubar da cikin tana ta murkususu jini yana zuba,Umma ma haushi ne ya kama ta, amma duk da haka sai tace jeki kula da ita jakadiya,ba laifinta bane laifin mijin ta ne da tun farko ya nuna mata bacin ransa daga na daya ai bazata kuma ba,bari in kirasa yazo ya dubata su dai suka sani,ni menene nawa Allah na tuba jika wane iri ne ban gani ba.lokacin da Umma tayi masa waya ya zaci ko tazo ta fada ne a tsorace ya daga wayar,tace masa sai kazo ga matarka nan kila barin zata kuma yi ta kashe wayarta,lokacin daya iso tama sume bata san wanda ke kanta ba a firgice ya dauke ta zuwa mota Asabe ce kurum ta bisu suna isa asibitin a gigice ya sureta zuwa Emergency su uku ne kanta shi ya kasa yi mata komai ma,cikin ya fita sukayi mata wankin mara sannan suka kaita daki na musamman ta farka ne ta ganta a dakin asibiti. kwananta biyu duk babu wanda yazo dubata kaf dangin Yarima ance sai Umma lokacin tana bacci su Salma cewa sukayi bazasu zo duba taba tunda tana sani.Yrm ne ko yaushe yana dakin sai dai ya kasa ce mata komai kamar yanda ko ganinsa bata son yi shi dai bashi da tacewa ne, sannan ga carin da 鈥榶an gidansu suka rutsa sa suna masa yayyinsa ne suka tsara shi a gaban Umma sunce matarsa tana zuwa tana cire ciki yakasa yin komai akai saboda ta mallakesa, don haka zasu nema masa aure, Nan take anty Saliha tace 鈥榶ar mijinta Nafisa ta jima tana son Yarim kuma Nafisa tana da hankali sosai,shidai jinsu kawai yakeyi shi damuwarsa daya mummunan kamun da matar tasa tayi masa, yanzun bai san yaya zasu kwashe ba in ta warke, gashi shi ne silan wannan wahalar da tasha duk da yana zaton bata san shi ne sila ba inda ma yake jin da dan sauki kenan.da yamma su Magaji suka zo dubata tace haba Magaji maimakon kabar Sumayya ga tsohon cikin nan?Yace to nace ta zauna tace ita dai zata zo Bily tace shikenan na gode, duk surutun da akeyi cikin gida Magaji yaji sai dai bai yarda wani Bily ce ke cire cikin ba sai dai ko Yrm so yake ta fito daga asibitin yaji komai kuma yasha alwashin sai su Umma sunji. washegari ta fito daga asibiti,Yarima yazo yace an sallameta tazo ya kaita gida,bata musa ba dama kala bata ce masa ba ta shiga mota suka nufo gida. nan shima ya dan zauna shiru sannan ya fita jim kadan su anty Salma suka zo sukayi mata ta tas,har da cewa dama dan talaka bai iya samun guri ba,anty Fulera tace zaki ga tsiya aike baki ma iya abun ba inma cin dukiyar kike so dakin haifa kin tara dakin samu,yanzun kuma zamu kawo wadda zamu karu da ita 鈥榶ar masu dashi, suna fita ta tashi zaune ta ma rasa meke mata dadi duniya,nan ta dauko jakarta ta dibi 鈥榶an kayanda basu fi biyar ba sai dai kudi ta dauka ta zari makullin mota ta fita.sai data hau titi tama rasa ina zata?Kai tsaye ta dauki hanyar Kaduna, gidansu Mansu taje ita kanta tasha mamakin tukin da tayi domin bata taba fita cikin Bauchi da mota ba,Mansu bata Kaduna suna zaria kuma daga nan zasu wuce Gombe saboda hutun karshen shekara da Faruk ya samu,maigadin ne yace mata basa nan tace ta sani itama wani aiki zata yi a Kaduna ta shiga ta aje kayanta cikin dakin Mansu,sannan ta zauna ta rubuta ma Yrm text kamar haka.

[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 90馃彽


Na baka guri ka shakata sannan kasani bazan iya zama dakai ba, ka kasa tsaya wa akan halalin ka alhalin ban rage ka duk wani jin dadi ba. Baka sona baka son karuwa dani, burinka in mutu gurin cire min ciki ta hanyar da kai ka sani ni bansani ba, amma naje gurin likita ta min bayanin komai dama ance duk mutumin da baya kaunarka zai iya yi maka komai ciki harda neman rayuwarka. Da fatan daka samu sakona zaka rubuto min sakina koda ta waya ne sai 鈥榶an uwanka su aura maka wadda suke so 鈥榶ar masu kudi kuma wadda zata tara musu 鈥榶aya kamar yarda suka ce,tana turawa ta kashe wayar gaba daya.shiko Yarima yana ganin sako ya shigo ya duba ai a rikice ya nufi gida, ta tabbata nan kuma babu motarta yaje yace ma Umma ina Bily? Umma tace ni ban sani ba bata nan ne?Yace a'a na zaci tazo ne ya fita,gidan Umma ya nufa yana tafe yana neman layinta amma a kashe,bayan sun gaisa sai yace shin ko Bily ta iso?Umma tace ta nufo nan ne?Yace dana ce tazo ne ina zuwa kila tana gida ya fita duk inda yasan Bily tasansu sai da yaje har magariba ta shigo ya dawo gida ta gurinsu Umma ya shigo tana sallah son ma yana ta binta sallar.ya fita ya nufi sasansu,ya daure ya watsa ruwa sannan yayi sallah ya ci gaba da neman layinta shiru sannan ya kira Magaji bai boye ma Magaji komai ba,Magaji yace shikenan gaskiyarta ne tunda ta tafi ba sai ka huta ba? Haushi ya kama sa yace haba Magaji na kiraka ne fa don ka taimaka min yanda zan bulloma al鈥榓marin ka kuma dauko wata caftar, Magaji yace to in ba haka ba me zance?Yarima yayi shiru can yace da zan iya dana ce tayi tafiyarta amma na kasa ba zan iya ba, cewa fa tayi wai in sake ta? Magaji yace ka saketan mana to yaja tsaki,sannan ya nuna ma Magaji kofar fita,fita baka da amfani,Magaji ya mike ya fita Yarima yabi shi da kallo. Bacci ranar sai dai barawo amma kasa bacci Yarima yayi,baya son su Umma susani amma dole ne suji,sai dai zai ce musu taje gaida iyayenta ne,to kuma zasu ce babu ko sallama?Haka yayi tayi ya saka ya kwance,har gari ya waye.Magaji daya koma gida sai ya kira layinta yaji sa akashe, washegari ya fito ya shiga gidan sasan Yarima ya shiga lokacin Yarima shima ya gama tunanin cewa dole ya koma gurin Magaji,domin shine yasan zaria, kai shi abin kunyar nasa ma yana da yawa shekara nawa shida matarsa bai san kowa nata ba sai wanda ya kawo kansa yanzu gashi zai je dalilin yana bukatar ta dawo?Magaji ne ya katse sa da cewa abokina yaya ne? Yarima ya dubesa mun tashi lafia?Lafia lau inji Magaji sukayi shiru can Yrm yace ko can gidan iyayanta zamuje? Magaji yace to sai muje,kaga kaima tunda yanzun tayi dalili sun san kai Yarima yace to sarkin sheri naji yanzun yaushe zamu tafi?Magaji yace ko yaushe,Yarima ya mike yace jeka shirya mu tafi.sun iso zaria misalin karfe biyun rana,unguwar suka shiga kai tsaye, kallon unguwar yakeyi yana mamakin dama beauty a irin wannan unguwar take?Duk da an ce iyayanta talakawa ne da za鈥榓barsa inya iso(G.R.A)zai nufa nemanta,bai kara tsinkewa ba sai da suka tsaya akofar gidan,yace Magaji don Allah nan ne gidan iyayan beauty?Magaji yace tabbas Yarima yace,amma baka kyauta min ba da ka kasa sanar dani kamar ni ace surukaina suna cikin wannan gidan, ai samuna yazama na banza.Magaji yace lokacin gyaran ne baiyi ba shiyasa Allah bai horeni da sanar dakai ba amma yanzu ai kaga lokacin yayi tunda ance gani ya kori ji.suna fitowa daga mota Asma鈥榰 tana fitowa daga gida,tace a鈥榓 yaya Yrm sannunku da zuwa,Yrm cikin zumudi yace Asma鈥榰 beauty tana ciki ko?Asma鈥榰 tace wace antynmu?Yace eh,tace bata zo ba.Magaji yace babanku yana nan?Tace yana ciki,yace to shaida masa ga baki. Da sauri ta koma tace Mama ga yaya Yrm mijin anty,ta mike da sauri tace,to ina malam kirasa dakin Salame ta sanar dashi da sauri ya fito sai daya canza 鈥榶ar riga mai haske sannan ya fita wajen yayinda Umma ta shiga gyara gurin. malam ya shigo dasu Asma鈥榰 ta fita siyo musu lemu mai sanyi.Yrm cikin tausayi yake kallon gidan hakama dakin,bayan sun gaisa Asma鈥榰 ta kawo musu swan water mai sanyi da lemu,Yrm dai ruwan kawai yasha.Magaji ne ya gabatar da Yrm, sannan yace sun zo ne su duba ko Bily tazo gida,s saboda wata 鈥榶ar matsala da suka samu.Mama ta kalli malam shima ya kalleta sannan yace ikon Allah,amma ko daya ban zaci haka daga gurin Bily ba,domin yarinya ce mai hakuri,amma kunga bata zo nan ba,tun yaushe ne?Magaji yace jiya ne. Yarima ya cire hula saboda wata zufa data feso masa,a hankali ya furzar da wani huci mai zafi.sannan yace,ni babbar damuwata bata da isasshiyar lafia,to amma baba ba kuji anan din akwai inda zata?Malam yace kun duba cikin gidan Umman Bauchin kakarta?Magaji yace duk bata can,Mama ta nisa tace kun tuntubi Mansura?Duk da dai Mansu ma tana nan zaria,kila gidan Mansu taje.tunda kunce jiya ne ni kuma shekaranjiya Mansu tazo nan,nan aka hada su da Asma鈥榰 zuwa gidan Mansu,sun samesu har Faruk dinma yasha mamakin ganin Yarima a gidansa.Mansu ta musu kyakkyawar tarba sai dai Yrm ya kasa cin komai domin baiga beautynsa a gidan ba,sannan bai tsaya kwauron baki ba ya shaida ma Faruk dalilin zuwansu.cikin mamaki Mansu tace,Bily tabar gidanka?Yace wallahi tun jiya babu inda banje ba,Mansu tace shiyasa na dinga neman layinta shiru?To ina Bily zata?Wai ma meya faru haka da zafi ne har ta saka kafa ta fita?Yrm yace gaskia laifina ne,na sani kedai kawai abar zancan sai in Allah yasa anganta.wasa-wasa har kwana uku,su Yarima sun koma gida,Magaji shine ya sanarda Umma komai, amma ya boye kama shi da wata da Bily tayi, ya dai ce Yarima ne ke cire mata ciki shine ta gaji ta gudu gashi kuma su anty Salma suna ganin laifinta. Hankalin Umma ya tashi ta shiga cewa dama nayi tunanin yarinyar nan bazata aikata wannan aikin ba.

[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 91馃彽


Hankula sun tashi ana ta nemanta,ita ko tana can tana zamanta gidan Mansu na Kaduna,ta kashe wayarta,bata bukatar ji daga kowa kuma ba wanda hankalin sa yaje gurin.mai martaba daya samu labari ranar Yarima yaga bacin rai irin wanda bai taba gani ba,sannan mai martaba ya bashi kwana uku rak mazamaza ya nemo inda Bily ta shiga inko ba haka ba zaisa a tsare sa har sai an ganta.al鈥榓marin ya wuce duk yanda Yrm ya zata,domin wai don ma basu ji dayan ba.Waziri da Magaji sune suka roki mai martaba kan batun tsare Yarima,amma fa yayi fushi dashi sosai daidai da magana ta daina hadasu, ko Yrm ya gaisheshi baya amsawa.ranar data cika kwana goma cikin dare ta kunna wayarta,sakwanni tayi ta gani suna shigowa na Yrm ne,tayi ta delete bata karanta ba,amma nasu Mansu,Magaji,su Sakina da Maryam harda auta,kowa dai rokonta yakeyi ta dawo,hankula sun tashi Magaji har abinda mai martaba da Umma suke ma Yrm sai daya shaida mata sai taji dan sanyi cikin ranta damuwarta iyayanta,don haka sai ta tura ma Mansu text cewa tace suma su kwantar da hankalinsu tana nan lafia,sai dai bata Kaduna in lokaci yayi wato in Yrm ya saketa zata dawo ta tura sannan ta tura ma Yrm cewa,tana fa jiran sakon sakinta,tana tura masa ta kashe wayar. Lokacin da sakon ya shigo yana zaune kan sallaya ya idar da nafilfilun da suka zamar masa a madadin bacci yanzu,yana ta addu鈥榦鈥榠 gani yake tunda iyayansa suna fushi dashi bama zai ganta ba,shi dama zasu barshi da zafi gami da radadin rashin ganinta domin yanzun da baya ganinta dinnan yafi kowa tashin hankali,ya yarda sonta ne ya kamashi tuntuni bai gane ba sai yanzun.ganin sako ya shigo da sauri ya dauki wayar yana dubawa,jiki na bari ya soma kiran layin a kashe.haka yayi ta kira har ya gaji,yanzun yama daina zuwa asibiti,kuma sai yanzun yayi kukan rashin Modibbo,yasan da yana nan da iyayansa ba zasuyi fushi dashi ba,yaji da batan masoyiyar tasa. Mansu sun wuce Gombe bayan Bily ta shaida mata cewa tana nan lafia lau,sai dai bazata sanarda ita inda take ba,wasa-wasa shiru har sai da aka kai dasa rokon Allah ko ta wane gefen,gurinsu Umma ne gurinsu Mamanmu ne Allah ya bayyanata,su Umma yanzun sun sassauta ma Yrm saboda ganin halin da yake ciki,duk ya sukurkuce jin cewa su Mansu sunzo Gombe ya nufi Gombe ko zai samu wani labari.Yrm da kansa ya zauna gaban Mansu yana shaida mata cewa alhakin Bily ne yake binsa,Allah ya jarabce sa da sonta,yace kalleni kiga yanda na dawo shin baki sami wani labari daga beauty ba? Tausayinsa ya cika Mansu,tace tayi min text cewa tana nan lafia,yace to ni dazan san inda take wallahi ko ina ne zanje kome zata min indai zata huce zan yarda,tana da hakuri,Mansu tace,ai tasha a nonon hakuri ne haka mahaifiyarta take ya gyara zama don Allah bani labarin beauty mana? Nan ko Mansu ta zauna ta zayyane masa komai,sai kawai taga hawaye yana bin kumatunsa,dama cikin mafarki Bily ta soma saninsa?Lallai aurensu hadin Allah ne,dama tasha wuya agidansu?Yanzunne ya gane taki zuwa gida ne saboda kada kishiyoyin Mamanta suyi mata dariya.lallai bai dace ya wulakanta Bily ba tun farko lallai ya mata laifi dayawa.Mansu tasha mamakin ganin Yrm yana kuka,mai saka mata kuka yau gashi yanayin kuka don mace lallai gara da Bily ta tafi gashi sanadin haka ansamu cigaba, domin su anty Salma ma mai martaba ya saba musu yace dasa hannunsu Bily ta bace,kuma yana fushi dasu bazai gushe ba sai sun roketa gafara.Faruk yazo kuma sun lallashi Yrm, daya dawo hankalinsa yace yana so ya taimaki iyayan Bily amma kada suce sai da 鈥榶arsu ta bata,Mansu tace bazasu ce ba,shida Faruk da Magaji suka je zaria inda suka samu shahararren mai gini ya tsara musu yanda za鈥榓 maida kafdin gidan kirar zamani ba tare da an shiga hakkin kowa ba,nan ya yarda da aikin yace kuma yana bukata cikin gaggawa Abu indai da kudi yanzun ne sai gashi cikin sati biyu an tsara guri,matan gida kuma duk sai kowa ta koma neman shiga gurin Mama,gefen su Mama yafi kyau ga kayan alatu daya zuba musu,ya saiwa malam wanda yanzun ya koma Alhaji Mamman tun shekarar da suka je makkah,katon shago yasa akayi daga waje ya cika masa da kayan masarufi na saidawa,sito kuma cike da abinci,lokacin Yrm gani yake koda zai karar da dukiyarsa bazaiji komai ba.su Ladiyo anga babu sarki sai Allah an hakura, domin dai nagaba yayi gaba wadda suka tsana yanzun arzikinta suke ci.hassadar da sukeyi baya suke ci ba gaba ba.Yau watansu Mansu guda da kwana goma tuni sun soma shirin komawa gida,don ma sun tsaya ne sunsha sunan Sumayya,ta haifi 鈥榶arta mace,inda Yrm ya rada mata Bilkisu.sai da suka bita zaria sannan suka wuce,abinda Mansu ta rinka tunawa tana dariya a mota,lokacin da suka je yiwa Mama sallama,sai ta samu su Goggo amarya(kakarsu Bily)zaune a falon Mamanmu suna kallon TV.Ladiyo kuma an leko cikin falon tana cewa yaya gashi na fere miki doyar ai Goggo kuna kallo ne?Nima bari inzo in kallata. shima Faruk sai daya dara da Mansu ke bashi labari.abin al鈥榓jabi suna shiga farfajiyar gidansu sai taga motar Bily ta fito da sauri tana cewa abban dady ko dai nan gidan Bily tazo?San da suka shiga tana bacci kan kujera, gabanta kwalbar maltina ce da plate din farfesun kaji.duka Mansu ta dada mata tare da cewa,鈥榶ar iskar nan dama kina nan?Bily ta tashi tana dariya tace,kash!Da nasan yau zaku dawo dana cigaba kafin kuzo,Mansu tace wannan 鈥榶ar duniya ce dama nan kike?Kin shammace mu kina nan kici goma ki tsoma biyar,lallai 鈥榶ar duniya kin wahalar da Yarima kuma sai Allah ya saka masa.ta daure fuska wane abu ne kuma Yarima ?Don Allah kadaki sani nayi amai, Faruk kuwa mamaki ne ya hanasa magana,sai dai kallon Bily yakeyi,Mansu tace dole ka rasa bakin magana.Mansu tana shiga daki ta kira Yrm tace yazo ga Bily agidansu, sannan ta sanar dasu Mama.yarima jin abin yayi tamkar mafarki,a gurguje ya nufi toilet yayo wanka yana fitowa ya kira Magaji awaya cewa ya shirya suje Kaduna anga Bily,suna mota ne Magaji ke cewa da munje kayi aski gami da gyaran fuska,yace muje zanyi acan.cikin dare suka iso,Mansu lokacin ta soma bacci,Bily kuma tuni tayi baccinta,suna shiga Mansu ta nufi kiran Bily,tace wallahi bazata fito ba dole aka kyaleta Faruk yakaisu masauki.b bacci ranar Yarima baiyi ba gani yake inya kwanta zai farka yaga cewa cikin mafarki ne.babu yanda Mansu batayi ba ta fito su hada abin karyawa takai musu,tace Allah ya tsareta. Koda Mansu ta gabatar musu da kari,sai Yarima ya debe tsammanin ganin Bily,harma yace Mansu ban taba zaton zaki tsokane niba,zolayata kikeyi ashe.tace kai dai kugama tana zuwa,sam ko sha鈥榓war karyawar baiyi ba,ya koma ya zauna can kuma harda kuka Bily wai ita bata ko son ganin Yrm.Faruk shida kansa ya shigo yace dan Allah tazo,tana kuka tace kayi hakuri baban dady bazan iya kaffara ba kan cewa bazanje ba.ya mike ya fita kai tsaye gefen bakin ya nufa yace suzo ta hada kai da gwiwa suka shigo da tasan zasu shigo data shige toilet,Yrm yana yin arba da ita da sauri ya nufi gurinta kusa da ita ya zauna tare da cewa, beauty!Da sauri ta dago idanu jajir ta zabga masa harara.yayi murmushi tare da yin ajiyar zuciya, sannan ya mike ya kalli gabas ya tsugunna yayi sujjada,yana daga zaune agabanta yana kallonta shi duk tausayinta yake ji tunda yaji tarihinta agurin Mansu.yace beauty ki min duk abinda kike so nidai bukatata ki yafeni bazan kara ba,na dauki alkawari tsakanina da Allah.ta dubesa kabani takardata cikin mutunci kafin mukaiga kotu,yace kin manta ne beauty aure gidanmu ba鈥榓 saki,har sai mace tazo da alfasha, keko saliha ce.ya dubi Magaji sa baki abokina, Magaji yayi gyaran murya sannan yace kiyi hakuri Bily kiyafe masa komai ya wuce,tace Magaji ina ganin mutuncinka kayi shiru kawai cikin wannan maganar,yace to nayi shiru Allah ya huci zuciyarki.

[8:43AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 92馃彽


Ya tashi ya fita Yrm ko sai gashi y zube gwiwa biyu gaban mace,macen ma 鈥榶ar Nigeria 鈥榶ar Arewa wadanda ada yake kira kauyawa.yana cewa ta yafe masa ki yarda dani wallahi ina sonki da sauri ta dubesa gami da bude idanuwanta sosai,ina tsananin sonki beauty ban farga da tsananin sonki daya kamani ba sai da baki tare dani,na azabtu na wahalu,kalli yanda sonki ya maidani.hawaye ya soma gangaro mata tace yaya ka gane cewa kana sona?Ban yarda ba zaka yaudareni ne zaka cuceni ne,ya matso ya rungumeta duk da ta game jikinta guri guda, yana cewa I love you my beauty,I love u so much,I miss u a lot.turesa tayi tare da cewa ni bana sonka don Allah kabarni a takaice duk yanda suka zaci shawo kan Bily cikin sauki sai abin ya faskara, har Umman Mansu ta shigo ciki amma Bily ta kekashe nan ta tasa ta suka nufi zaria tace da Yarima yaje yayi hakuri zasu kawo ta ya dubi Umma yace don Allah kada ku mata fada laifina ne.bari in sanar dake laifukan dana mata.Bily ta dubesa da sauri an tambayeka ne?Yace a鈥榓 zan dai fada musu ne don kada suyi miki fada suga laifinki bada hakkinki ba,tace suma kasheni ina ruwanka ba鈥榓ce dai kafada ba,harma abin yaba Umma dariya tace to kai tunda bata son aji laifin naka ba sai ka barsa ba?Ku koma zamu maida ta insha Allah. A zaria idanu Bily ta zare tana kallon yanda aka fitar da titi cikin layinsu ga kwalbati layin yayi kyau bata gama tsinkewa ba sai data ga gidansu taga gefen mahaifyarta nan tayi sororo,Umma tace duk aikin Yrm ne,kuma yace shi don Allah yayi bawai saboda yana aurenki ba,ni kaina mota ya sai min wai in dinga zuwa aiki,baki kurum Bily ta taba ita abin bai burgeta ba.washegari sai gasu anty Saliha dasu Salma mai martaba yace suje su bada hakuri harda son suka zo yayi lakur jikin mamansa suka ce ta yafesu,tace insha Allah ya wuce.amma ita sai jibi zata dawo,Yrm yana samun labari sai yahau gyaran gidan aka sake fenti ya kwashe komai ya zuba sababbi don da tuni ya kammala nasu to hankalinsa ba kwance ba. Kafin ta dawo sai da Mansu tazo sukaje aka yimata gyaran gashi da lalle sai kace sabuwar amarya,ga kuma ainahin gyaran duk anyi suka nufi Bauchi.hutawa kawai Umma da Goggon sasa suka yi mata nasiha suka tafi.tana kwance kan sabon gadonta tana kallon kudin da Yarima ya kashe acikin dakin kawai sai kace baza鈥榓 mutu ba,son yana bacci a gefenta,Yrm ya shigo cikin kayan bacci,zo muje mu kwanta beauty ko nan zamu kwana?Tayi masa shiru,ya matsa jikin gadon daidai fuskarta ya tsugunna cikin kunnenta yace baki huce bane?Tace,subhanallah don girman Allah ka barni nace ya mike na barki sai da safe.komawa Bily tayi tamkar bakuwa agidan, kowa na gidan tana dari-dari dashi har Umma sai datayi mata magana tace wai shin 鈥榶ar nan kin kasa sakewa kodai baki yafe bane? Tace,a鈥榓 Umma aini dama ban riki kowa cikin zuciyata ba,ko Yrm da yayi sanadin komai tun kafin ya ganni ma na yafe masa,Umma tace Allah sarki,ai haka ake son bawa na kwarai,me saurin yafiya.Ubangiji yana yafe ma mai yafe laifin dan uwansa,Allah ka yafe mana zunubanmu wanda muka sani da kuma wanda bamu sani ba.Bily sai da ta dan kara gyara Yrm na sati daya sannan ta dauri aniyar karbarsa ranar juma鈥榓 ta shiga cikin kitchen ta tsara girki sai ranar ta shiga gefensa tunda ta dawo,yanda ya tsara gurin ya burgeta sosai ta jere masa abinci,sannan taje tayo gayunta cikin riga da wando na yan ubansun gurin Umma ta tura son ita kanta data dubi madubi tasan tayi ne.Yrm suka shigo da Dr. Salihu duk da yana dar-dar din kada ta bada shi ga mamakin Yarima sai ya ganta cikin gayun da yaji dama bai shigo da Dr. Salihu ba,domin zai kalle masa ado.tace abinci yana samansa,ai fa Yrm sai doki nan suka hau ta zuba musu,Dr. Salihu yace yana son abincin gargajiya ita matarsa tafi son na nasara,zai kawota su saba ta koya don ta rika masa,Bily tace sai sunzo.Yrm ya rakasa ya dawo. Ya zauna yana dubanta gaskia kinyi kyau,ta dubesa da fara鈥榓 ko?Yace sosai ma,har fa sai naji haushin shigowa da Salihu,tayi 鈥榶ar dariya ka kara abincin naga kamar baka koshi ba,yace ai kallonki ya kosar dani beauty,dan dawo kusa dani in dan ji kamshinki,da dan dumin jikinki.ba musu ta dawo,wayyo yau Yarima jinsa yake tamkar yau ne ya cire beauty dinsa daga leda,surkulle dai kala- kala ta jisa har sai daya bata tausayi kalaman so kuwa har sai da tayi hawaye don dadi ashe za鈥榓 gaya mata wannan kalmar a rayuwarta? Fahimtar da Yarima yayi beauty tana son a so ta sai ya shiga nuna mata so a baki a aikace,fili a boye a waya,nan fa ya tsumata itama ta shiga fiddo masa da nata son filla-filla.tuni Yarima ya sallami Tina duk da sai da yayi mata jan ido ta tafi.zama suke na tsantsan so babu algus a cikinsa suna kaf-kaf da juna,in yana gida suna like da juna in ko yana office suna nane da waya,wai wayaga sabon shiga?Abin zallar sha鈥榓wa ko aiki yake cikin laptop zaki samesa ya tada kai ne da cinyarta ita kuma tayi wasa da sumar kansa,wanka tare cin abinci tare,in yana gida zatayi musu abinci shima sai ya shige kitchen din.tafia suke cikin mota zasuje ganin sabon gidansu shida ita suna gaba abayan kuma son ne da Bilkisu 鈥榶ar gidan Magaji,ta kwanto kanta akan kafadarsa yayi dan murmushi tare da sa hannunsa ya shafi cikinta.yarona yana damunki ko?Tace yaya zanyi cikin shagwaba,yayi fakin gefen titi bari na gani sauran kwana nawa yazo ne ma?Cike da shagwaba tace,in Dr. acikin mota?ya kwantar da kujerar sannan ya kwantar da ita ya daga rigar yana aunawa,son yana dariya yace lah!Dady kana duba bebyn ne?Yace eh yayi kusa yazo son yace dady kullum sai kace ya kusa yazo ni nafi so in gansa.Bily tace don Allah nidai daga min kujera in tashi kun cika zumudi kaida yaronka,nina fiku kosawa in haihu in huta. Makeken gidane tsarin ginin abin sha鈥榓wa,an gama komai anata fenti.Bily tace nawan wannan gida sai kace mai mata hudu?Gaskia yayi mana girma,yace to shikenan zan sake aure,sai mu zau.....ta banko masa harara yace,ai subutar baki ne,tace yanda kayi subutar baki kace kai nawa ne ni kadai haka zaka hakura,ya kalli inda yaransu suna ta guje-guje cikin dakuna,ya jawota jikinsa ya tsotsi lebenta na kasa,yace ke dayace matata nan duniyar baki da kishiya,ta kalli idanunsa cikin ido tace inna mutu fa?Ya rumtse idanu ya kara matseta jikinsa,insha Allah bazaki rigani mutuwa ba,domin inkin mutu beauty nizan lalace ne na sani zan koma useless rayuwata zata daina amfani ko yaushe ina addu鈥榓 ki rayu ki rike min yarana ni kuma in mutuwar tazo ta daukeni,Bily tace baka min adalci ba nawa inka mutu nima binka zanyi,yace to yaran fa?Tace ga su Umma,yace su Umma sun tsufa,tace bazamu mutu bama yanzun duka-duka shekarunmu nawa ne?Yace beauty bata nan ake daukar jariri ma? Tace to ya isa muje gida.Yrm yanzun ne yake tashensa,shekarunsa talatin da hudu in bakin sani ba baki cewa yana da aure,duk inda ya shiga mata suna kallonsa,sai dai duk wata mace gani yake ta biyo bayan beauty.arziki yanata bunkasa yanzun ya gina asibitin(surgery)daban sunan Yrm ya zagaya ko鈥榠na cikin kasa,ko鈥榠na kaji ana kwararren likitan mata Dr. Yrm,jaridu,gidan talabishan,da kuma radio,sunsha hira dashi maza da mata Yrm birgesu yakeyi,ga kyau ga kudi ga kuma aji.Bily ta fara nakuda misalin karfe daya na rana lokacin Yrm yana asibiti amma bini-bini zakiga ya bugo waya,dama yana sa ran haihuwar tata gobe ne,ko kuma cikin dare ita kuma taki sanar dashi cewa tana nakuda,yana cikin duba marasa lafia sai kuma ya sake kiranta,matar dake zaune gabansa ya dubata yace yi hakuri madam,ya daga wayar da kyar yace beauty are you ok?Muryarta na rawa tace eh,yace ke ban yarda ba,meke damunki?Sai kawai yaji tace Innalillahi wa鈥榠nna ilaihir raji鈥榰n da sauri ya mike ya dubi matar don Allah ki jirani ya fita da matsiyacin gudu ya figi mota

[8:44AM, 12/28/2016] 鈥�+234 814 912 1821鈥�: 馃彽MEKE FARUWA 93馃彽


Yana isa cikin gida ya fita zuwa sasansu yana shiga dakinta beby yana fadowa,da sauri ya riketa beauty me yasa kika min haka?Nan ya kira Umma ta waya sannan ya dauko zaninta ya nade bebyn ciki.duk yanda zan baku labarin suna ya wuce nan,domin anyi sunan ne acikin sabon gidansu wanda suka tare ana jibi suna,washegarin sunan ne,Yrm ya shigo ya wuce Faisal babban dan anty Fatima suna hira da Asma鈥榰 auta,ya samu Bily tana bawa Al鈥榓min nono wato Yarima karami kenan,Bily ce ta zaba masa sunan,ya kalleta tana murmushi tace sannu da zuwa,ya zauna kusa da ita yasa hannu ya rungumota ya kai hannun ya matsa nonon,ta dubesa zakasa ya kware fa?Yace wai me ke tsakanin auta da Faisal ne?Bily tayi dariya tare da cewa, oho.adai cikin 鈥榶an kwanakin nan kullum suna tare,ina zaton har free call sukayi shekaranjiya dana cemata meke tsakaninku sai tace min wai yana koya mata karatu ne,nace shine karatun har cikin dare?Sai kuma tayi shiru.Yrm yace,Faisal yana da hankali kuma ya gama karatunsa yana aiki wannan ba matsala bane,da zaran sun sasanta sai ayi magana. Bily tace,Allah yasa mu dace.yayi dan murmushi,鈥榶an suna sun watse azo a san yanda za鈥榓yi dani fa,tace Allah basu tafi ba su Sakina suna can baya suna soya nama.Mansu ma tana nan,yace don Allah kaima Mansu beby kizo ki duba wani bebyn,tace kasan kuwa kai ne asalin bebyn nawa kayi kokari kwana takwas bari nazo inma irin hikimomina kaji nawa?Bily tasan kalar mijinta wurin bukata,dole ne ta kula dashi ta samu da rokon Allah da rigima ya daina neman mata bata fatan ya koma ruwa.kai radadin da tasha na neman matan da mijinta yayi bata fata ko makiyiyarta mijinta ya nemi mata,shiyasa bata barin sa cikin sha鈥榓wa ko wane lokaci yazo mata takan jure ko tana so ko bata so,in lokacin tana al鈥榓da ne zatayi amfani da hikimominta har sai ya gamsu ba tare da sun keta haddin musulunci ba,ciki ko laulayi basa hanata sauke nauyin daya rataya a wuyanta. Yarima kansa yana tausaya mata domin ya sani tana kokari, don haka sai ya koma tamkar bawanta, duk abinda take so cikin sauri zai mata,gashi yana dawainiya da duk wani mai hulda da ita bama danginta ba,amintakarsu da Mansura kuwa babu wanda ya kaisu murna da farin ciki,haka lokacin da suka ji cewa Faisal na son auta murna suka yi domin sun san duk halinsu daya da Bilkisu.haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin sha鈥榓wa,鈥榶a鈥榶a maza Bilkisu tayi ta tarawa abinda mai martaba yaso yanzun gashi Allah ya bashi 鈥榶a鈥榶a biyar maza,t tuni suka amshe uku.Son da Al鈥榓min,da kuma Abba (wato mai sunan malam mamman)suka barsu da Saddik da Usman,ga kuma ciki mace? Namiji? Sai dai an haifa. 


Tammat Bihamdullah!

0 Response to "MEKE FARUWA Hausa Novel"

Post a Comment